Ticker

6/recent/ticker-posts

Sassaka Sana’ar Sakke: Nazarin Wasu Kayan Aikin Sassaka a Kasar Hausa

Citation: Rambo, A.R. & Aminu, N. (2024). Sassaƙa Sana’ar Sakke: Nazarin Wasu Kayan Aikin Sassaƙa a Ƙasar Hausa. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, 3(1), 266-275. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.030.

Sassa ƙ a Sana’ar Sakke: Nazarin Wasu Kayan Aikin Sassa ƙ a a Ƙ asar Hausa

 

Daga

Dr. Rabiu Aliyu Rambo

Sashen Nazarin Harsuna Nigeriya ,

Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato

Email: dirindaji12aa@mail.com

Phone No: 08125507991 or 08140736435

 

Da

Dr. Nasiru Aminu

Sashen Nazarin Harsuna Nigeriya

Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwat o

Email: nsrklg@gmail.com

Phone: 070677706006

Tsakure

Babban dalilin gudanar da wannan bincike shi ne ganin cewa masassa ƙ a a ƙ asar Hausa na da muhimmaci wajen samar da muhimman abubuwan da suke taimakawa wajen inganta tattalin arzikin Hausawa musamman abin da ya shafi sana’o’insu na gargajya. Masassa ƙ a na aiwatar da sana’arsu ne ta yin amfani da wasu kayayyaki da ke taimaka masu yayin da suke gudanar da sana’ar. Bisa ga wannan ake ganin ya dace a fayyace wa ɗ annan kayayyaki domin al’umma ta san su, ta fahinci yadda ake amfani da su a wajen aiwatar da sana’ar. Wannan bu ƙ atar ta taso ne ganin cewar da yawa daga cikin al’ummar ba su san su ba , balle su san yadda ake amfani da su. Manufar wannan bicike ita ce ƙ o ƙ arin fito da nau’ukan kayan aikin sassa ƙ a da masassa ƙ a ke amfani da su a ƙ asar Hausa. An aza wannan binciken bisa Ra’in Ayyukan Al’adu (Functional Theory of Culture) wanda aka ƙ ir ƙ iro tun a shekarun 1939 a ƙ asar Czech. Masu rajin wannan ra’in suna ganin ana iya nazarin al’adun ne duba daga irin gudummawarsu wajen gina al’umma. Sun bayyana cewa, ɗ ai ɗ aikun al’adu a cikin al’umma su ne musabbabin ginuwar a’umma. Dabarun binciken da aka yi amfani da su wajen tattaro bayanai domin gudanar da wannan bincike sun kasu gida biyu, manya da ƙ anana. Manyan hanyoyin sun ha ɗ a da ziyarar gani da ido da tattaunawa da masana. Sauran ƙ ananan hanyoyin kuwa sun ha ɗ a da binciken wasu ayyuka da aka buga da wa ɗ anda ba a buga ba masu dangantaka da wannan bincike. A ƙ arshe binciken ya gano nau’ukan kayayyaki daban - daban da yadda masassa ƙ a ke amfani da su wajen aiwatar da sana’ar sassa ƙ a a ƙ asar Hausa.

Fitilun Kalmomi: Sakke, Sassa ƙa, Sana’a

1.0 Gabatarwa

Masana da dama sun bayyana cewa, a zamanin baya da Ɗ an‘adam ya samu kansa a doron ƙ asa, babbar hanyarsa ta samun abinci a wancan lokacin ita ce ta farautar ƙ anana da manyan dabbobin daji ta hanyar amfani da itace a matsayin makami. Daga baya ya gane amfani da duwatsu domin sarrafa su a matsayin makami. Bayan tafiya ta yi tafiya, sai ya gane dabarar tsayawa wuri guda ya yi noma. Idan kuwa haka ne, sassa ƙ a ita ce hanya ta farko da Ɗ an‘adam ya fara amfani da ita domin sarrafa wani abin amfani a cikin albarkatun ƙ asa da ya samu kansa a cikin muhallin da yake zaune domin biyan wasu bu ƙ atocin rayuwa na yau da kullum a duniya baki ɗ aya. http://www.htm.cguYenN9.wood.com . Don haka, sha’anin sassa ƙ a abu ne mai dogon tarihi da asali a duniya.

Hausawa na cewa, “Sanin asali shi ya sa kare cin alli.” Wannan zancen ko shakka babu haka yake, musamman idan aka ɗ ora shi a bisa faifan wannan bincike. Ganin cewa, sana’o’in gargajiya na Hausawa sun taka muhimmiyar rawa wajen bun ƙ asa tattalin arziki a ƙ asar Hausa, ba a jiya ba har ma a yau. A wannan haujin kuwa, masana da ɗ aliban ilimi da dama sun tofa albarkacin bakinsu dangane da ma’anar sana’a ita kanta. Daga cikinsu akwai: Bargery (1934:896) da Newman (1977:177) da Sharifai (1990:17) da Garba (1991:1) da Yahaya (2001:48) da CNHN (2006:387) da Ɗ an’iya (2006:vii) da Kabakawa (2007:20) da Wushishi (2011:23-36) da dai sauransu da dama.

Ita dai kalmar sana’a kalma ce ta Larabci. A Larabce kuwa kalmar na nufin aiki. Daga baya Bahaushe ya ari kalmar tare da ma’anarta daga Larabci. Bayan tafiya ta yi tafiya sai ma’anar kalmar a wurin Bahaushe ta ƙ ara fa d a ɗ a har ta ƙ unshi duk wani aiki da za a yi don gudanar da wani abu da za a musanya a tsakanin ɗ ai ɗ aikun al’umma ko rukunin jama’a. Maigandi (2014:242) ya ƙ ara da cewa:

Kalmar sana’a dai kalma ce wadda ake hasashen asalinta daga harshen Larabci ne. Kalmar a harshen Larabci / swana’atu/ ce, sai Bahaushe ya yi mata kwaskwarima don ta dace da yadda yake fa ɗ a. Babban dalili shi ne, a Hausa babu harafin /swa/ sai ya mayar da ita /sinun/. Haka kuma aka shafe harafin /tu/ sai aka Hausance kalmar ta zama sana’a.

Bisa ga wannan fahimtar, masana da dama sun bayyana ra’ayoyinsu dangane da ma’anar sana’a.

A cikin The New Age Encyclopedia, (1980:423) an bayyana sana’a da cewa: Sana’a ta ƙ unshi duk wani aiki da mutum ke aiwatarwa wanda ya ƙ unshi saye da sayarwa domin samun abin bu ƙ ata. Haka a Ƙ amusun Hausa na CNHN (2006:186) an bayyana sana’a ko sana’o’i da cewa:

Aikin da mutum yake yi don samun abinci, misali manomi sana’arsa noma, wanzami kuwa sana’arsa aski ne. A Ƙ amusun Bargery (1934:896) ya ba da ma’anar sana’a kamar haka: Hanya ce ta kyautata gudanar da rayuwa. Shi kuwa Newman (1977: 177) cewa ya yi, Sana’a ita ce abin da mutum yake yi don sabawa kamar gini. (Fassarar Maibincike). Bugu da ƙ ari , Wushishi (2011:26) yana da ra’ayin cewa:

Sana’a hanya ce ta samun aiki na dogaro da kai don tanadar abubuwan biyan bu ƙ atu da neman rufin asiri kan harkokin rayuwa da kuma sarrafa albarkatu ta hanyar kimiya da fasaha da karkatar da su wajen saye da sayarwa da musayar kaya don mallakar abin da ba a iya samar wa kai.

Ga misali, Yahaya da wasu (1987:48) sun bayyana sana’a da cewa: Hanya ce ta amfani da azanci da hikima a sarrafa albarkatu da ni’imomin da Ɗ an adam ya mallaka don bu ƙ atun yau da kullum.

Don haka, kenan sana’a wata aba ce wadda mutum ya ji ɓ anci yi da nufin samun abin masarufi don gudanar da harakokin rayuwa. A ra’ayin Garba (1991:11) cewa ya yi , Sana’a ita ce ginshi ƙ in rayuwa da tattalin arzikin yau da kullum na Hausawa. Sannan kuma tana ɗ aya daga cikin muhimman hanyoyin da ake gane martabar mutum da ƙ asaitarsa da matsayinsa a cikin al’umma”. Wannan yana nuna sana’a tamkar wani madubi ne da za a kalla a iya gane matsayin mutum a cikin al’ummar Hausawa.

 Bisa ga la’akari da wa ɗ annan misalai na ma’anonin sana’a da ke sama, idan aka yi nazarin wa ɗ annan ra’ayoyi na masana za a fahimci cewa, kusan duk bori guda suke yi wa tsafi, domin kuwa kusan duk manufar su ɗ aya dangane da ma’anar sana’a. Bisa ga wannan, a ta ƙ aice a kuma tawa fahimtar, ana iya cewa, sana’a wata aba ce da mutum ke aiwatarwa da nufin samun abin masarufi domin gudanar da harkokinsa na yau da kullum da kariyar mutunci a cikin al’umma. Idan kuwa haka ne, ba shakka sana’a ta taka muhimmiyar rawa wajen bun ƙ asa tattalin arzikin al’umma baki ɗ aya.

Kamar sauran ƙ asashen duniya da ake aiwatar da sana’o’i daban - daban, ƙ asar Hausa ma ba a bar ta a baya ba wajen aiwatar da sana’o’i masu yawa domin inganta rayuwar al’umma, daga cikinsu kuwa har da sana’ar sassa ƙ a. Kasancewar ƙ asar Hausa shimfi ɗ e a farfajiyar Sabana da yankin Sudan mai tattare da nau’ukan itatuwa daban-daban a cikin muhallinta, wannan ya ba al’ummarta damar na ƙ altar fasahar sarrafa wa ɗ annan itatuwa zuwa abubuwa daban-daban na bu ƙ atocin rayuwarsu. Masu aiwatar da wannan sana’ar a ƙ asar Hausa su ne masassa ƙ a.

Sana’ar sassa ƙ a wata tsuhuwar sana’a ce da ke samar da kayayyakin amfanin yau da kullum a cikin al’ummar Hausawa. Don haka, tana taka mihimmiyar rawa wajen inganta tattalin arzikinsu ta fuskoki da dama. Daga cikin kayayyakin da sana’ar kan samar a cikin al’ummar Hausawa sun ha ɗ a da na ayyukan gida da noma da suf u ri da ya ƙ i ko farauta da kayan ki ɗ a da dai sauransu da dama.

Wannnan ma ƙ alar ta yi duba ne ga irin kayayyakin da masu aiwatar da wannan sana’a ta sassa ƙ a ke amfani da su wajen samar da kayayyakin amfanin a l ’umma.

2.0 Waiwayen Tarihin Sassa ƙ a a Ƙ asar Hausa

A ƙ asashenmu na Afirka, musamman a ƙ asar Hausa , sha’anin sassa ƙ a wata tsuhuwar fasaha ce da ta da ɗ e da wanzuwa a tsakanin sassa daban–daban na nahiyar Afirka. A nan binciken ya yi ƙ o ƙ arin waiwayen wasu ayyukan da suka danganci sassa ƙ a musamman na mutanen Nok culture da wani kwale-kwalen da aka gano a Yobe domin samun ƙ arin haske.

Samuwar tarihin sassa ƙ a a wannan nahiya kuwa ba zai kammalu ba, ba tare da an yi waiwaye a kan ayyukan sassa ƙ a na mutanen ‘Nok Culture’ (al’adun mutanen Nok) ba. Wannan kuwa yana da muhimmanci domin a nan ne aka fara samun kayan sassa ƙ a na farko a wannan yanki da suka yi shekaru aru-aru a duniya. A shafin yanar gizo na http:// www.htm.historyof AfricanArt.com an bayyana cewa:

The characteristic sculpture of Africa, which forms the largest part of what is usually considered primitive art, can be seen as early as 500 BC in the Nok culture- named from the village in Nigeria where pottery figures of this kind were first found.

Siffofin kayakin sassa ƙ a da ake samarwa a ƙ asashen Afirka, da yawa daga cikinsu an ɗ auka na mutanen karkara ne. Wa ɗ annan ayyuka kuwa an samar da su tun shekaru ɗ ari biyar kafin haihuwar annanbi Isah (500BC) daga al’adun mutanen Nok (Nok culture). An ba wa ɗ annan kaya yya ki wannan sunan ne daga sunan wani ƙ auye a Nijeriya inda aka fara samun wa ɗ annan kayan sassa ƙ e-sassa ƙ e .

  (Fassarar Maibincike)

Wannan kuwa ko shakka babu, ya ƙ ara nuna m a na irin da ɗ ewar da sha’anin sassa ƙ a y a yi a wannan nahiya ta Afirka.

Baya ga mutanen Nok, haka ko a baya-bayan nan wani bincike ya gano wani tsohon kwale-kwale (jirgin ruwa) da masana ke ganin shi ne mafi tsufa a nahiyar Afirka kuma na uku ga tsufa a duniya baki- ɗ aya. A shafin yanar gizo na Infor@naijatrekg.com an bayyana cewa, Malam Ya’u ya gano tsohon kwale-kwale a Afirka a kogin Koma-Dugu-Gana a jahar Yobe Nijeriya a wani ƙ auye mai suna Dufana. An gano wannan kwale-kwale a ranar 28-May, 1987. Wannan shi ne kwale-kwale mafi tsufa a Afirka kuma na uku ga tsufa a duniya. An yi ƙ iyasin ya kai shekaru dubu takwas (8000) kafin bayyanar Annabi Isah (AS) (6000BC). Tsawon shi ya kai mita takwas da ɗ igo hu ɗ u (8.4m) fa ɗ insa ya kai mita ɗ igo biyar (0.5m), kaurinsa kuwa ya kai santimita biyar (5cm). Bayan kiran ƙ wararru n masana daga jami’ar Maiduguri da Jamani, an samu nasarar fid da wannan kwale-kwale a 1989. A yanzu haka wannan jirgin yana nan aje a ɗ akin adana kayan tarihi na Damaturu , J ahar Yobe.

Wannan ya nuna mutanen Afirka sun da ɗ e da fasahar sarrafa itace zuwa wasu abubuwan bu ƙ atunsu na yau da kullum, amma abin tambaya a nan shi ne yaya suke aiwatar da wannan aiki, domin shekarun wannan kwale-kwalen sun nuna an samar da shi ne tun lokacin iron age (lokacin amfani da ƙ arfe) .

Samar da gamsasshen bayani dangane da masassa ƙ in farko a ƙ asar Hausa da abin da aka fara sassa ƙ awa da inda aka fara sassa ƙ a r , wannan wani abu ne mai wuya r tantancewa. Don haka, kamar yadda ba za a iya sanin Bahaushen farko a ƙ asar Hausa ba, haka ba za a iya sanin masassa ƙ in farko a ƙ asar Hausa ba. Samuwa da wanzuwar sana’o’in Hausawa sun dogara ne daga irin bu ƙ atocinsu na yau da kullum, haka ita ma sana’ar sassa ƙ a ta samu ɓ ullowa ne tsakanin Hausawa na wancan lokacin tun zamani mai nisa , Rambo, (2018 : 30) .

Akwai hasashen cewa, sana’ar sassa ƙ a a ƙ asar Hausa ta samo asali ne tun lokacin da Hausawa suka fahimci aiwatar da sana’ar noma da farauta a muhallinsu. Masu wannan hasashen sun kafa hujja da cewa, a lokacin da suka je farauto namun daji, sukan gamu da dabbobin daji masu ƙ arfin gaske wa ɗ anda kan iya kashe mutum domin tsananin ƙ arfin da Allah Ya ba su. Ganin al’ummar Hausawa na samun kansu cikin wannan halin, sai suka fara tunanin samun wani abu (makami) da za su yi amfani da shi wajen farautar wa ɗ annan namun daji a matsayin abinci da kariyar kai. A wannan lokacin abu mafi sau ƙ in samu a muhallin da suke ciki shi ne itace. Don haka, sai suka fara sarrafa itace zuwa sanduna masu tsini da kauri da mari ƙ i domin farauto dabbobin a ƙ o ƙ arinsu na samar wa kansu abinci , Rambo, (2018:31). Daga wannan lokacin ne masu wannan hasashen ke ganin aka samo asalin sassa ƙ a a ƙ asar Hausa. Wannan kuwa ya ci gaba da wanzuwa daga lokaci zuwa lokaci, sha’anin sassa ƙ a na ƙ ara ci gaba har jama’a a wancan lokacin suka samu wayewar kai ta fasahar sassa ƙ a, ya zama masassa ƙ a suna iya sassa ƙ a muhimman abubuwa masu yawa da za su taimaka wajen gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum, musamman abin da ya shafi kayan sassa ƙ a da suka shafi noma kamar ɓ ota da sungumi da akushi da turmi da ta ɓ arya da dangarafai da ƙ yaure da muciya da kwale-kwale da sirdin dawakai da ra ƙ umma da sauransu da dama da ake amfani da itace wajen sarrafa su jiya da yau a ƙ asar Hausa. A lura cewa, duk da irin tsufan fasahar sana’ar sassa ƙ a a ƙ asar Hausa, Hausawa ba su da al’adar sassa ƙ a r mutum-mutumi, balle su yi amfani da shi wajen bautarsu , Rambo, (2018:31). A mafi yawan lokutta, Hausawa ba su sassa ƙ an sururin wasu abubuwa musamman masu rai, sha’anin sassa ƙ ansu ya ke ɓ anta ne a kan sarrafa itace ta hanyar samar da kayan amfanin al’umma na yau da kullum.

3.0 Kayayyakin Ayyukan Sassa ƙ a a Ƙ asar Hausawa

A al’adance Hausawa suna aiwatar da sana’o’insu daban-daban domin inganta rayuwarsu ta yau da kullum musamman abin da ya shafi bun ƙ asa tattalin arzikinsu da yanayin zamantakewarsu da addininsu da shugabancinsu. Daga cikin wa ɗ annan sana’o’i har da sana’ar sassa ƙ a. Sana’ar sassa ƙ a sana’a ce da Hausawa suka gada tun daga kaka da kakanni kuma sun ɗ auke ta da matu ƙ ar muhimmanci. A ƙ asar Hausa kowace sana’a akwai yadda al’ada ta tanadi yadda ake aiwatar da ita, musamman abin da ya shafi kayan aikinta. A fagen sana’ar sassa ƙ a akwai wasu muhimman abubuwa ko kayayyaki da mai sana’ar sassa ƙ a ya kamata ya tanada domin gudanar da sana’arsa . Muhimmai daga cikinsu su ne , itace da gatari da gizago da mahuri da makwashi da guru da masurhi da igiya da basharta da magagari da kuma tukar sassa ƙ a da sauransu.

3 . 1 Itace

Itace (itaciya) shi ne ƙ ashin bayan sana’ar sassa ƙ a, domin itace wani muhimmin abu ne da dole sai mai sana’ar sassa ƙ a ya tanada kafin sassa ƙ a duk wani abu da yake so ya samar na sassa ƙ a. A fagen sassa ƙ a, akwai itace daban-daban da ake amfani da su gwargwadon yadda suka samu a muhallin da masassa ƙ i ya samu kansa da kuma irin sassa ƙ a r da yake so ya aiwatar. A misali, itatuwan da ake amfani da su a wajen sassa ƙ a r kwale-kwale (jirgin ruwan itace) ba lalle ne a yi amfani da su a wajen sassa ƙ a r ɓ otocin fartanya ko kujerun zaman mata ko kayan ya ƙ i ko na ki ɗ a ba. Bugu da ƙ ari, akwai itatuwa masu sau ƙ in sassa ƙ a wasu kuwa suna da wuya r sassa ƙ awa. Haka wasu itatuwan suna da ƙ arfi da juriyar zafin rana da ruwan sama da gun ɗ a (cin gara) wasu kuwa ba su da wannan juriyar. Ko dai yaya abin ya kasance, akwai bu ƙ atar mai sassa ƙ a ya tanadi itace mai nagarta da aminci wajen sassa ƙ a r duk wani abin da yake bu ƙ atar sassa ƙ awa domin kauce wa na ƙ asu a cikin sana’arsa. Da ɗ in da ɗ awa, akwai bu ƙ atar kauce wa amfani da itatuwa masu ido, domin yin haka na kawo na ƙ asu ga kayan sassa ƙ a.

Akwai muhimman hanyoyi biyu da suke amfani da su wajen samo itatuwan da suke amfani da su wajen aiwatar da sana’arsu. Hanya ta farko ita ce ta zuwa daji su saro itatuwan da suke bu ƙ ata. Hanya ta biyu kuwa ita ce ta bayar da ku ɗ i a saro musu itatuwan.

A gargajiyance hanya mafi sau ƙ i da masassa ƙ i ke samun itatuwan aiwatar da sana’arsa ita ce ta ɗ auka r gatarinsa ya shiga daji ya saro irin itacen da yake bu ƙ ata. Duk da yake, a yanzu akwai dokokin gandun daji da suka haramta saran wasu nau’ukan itatuwa musamman masu ‘ya’ya, don haka suna taka-tsan-tsan da irin wa ɗ annan itatuwa domin kauce wa hushin hukuma. Haka a wasu lokuta, ba kowane itace ake iya sara ba, domin akwai wasu itatuwa da ke da iskoki ( ƙ wan ƙ wamai) ta yadda kafin a sare su sai an yi shiri na musamman wanda ya ha ɗ a da dabaru da asiri na nuna waibuwa daga masassa ƙ i; wasu kuwa sukan ha ƙ ura su koma wa wani icen na daban.

Hanya ta biyu kuwa ita ce ta amfani da ku ɗ i. A nan ana samun wasu masassa ƙ a da ba su zuwa daji saran itacen da za su aiwatar da sassa ƙ ar su, a maimakon haka sai dai su bayar da ku ɗ i su fa ɗ i irin itacen da suke bu ƙ ata a saro masu domin aiwatar da sana’arsu. Galibi wannan yana faruwa ne saboda a yanzu daji ya yi ƙ aranci, don haka samun ingantaccen itacen sassa ƙ a na bu ƙ atar tafiya mai nisa, kuma wasunsu ko abin hawa ba su da shi. Wani lokaci kuwa, wannan na faruwa ne saboda ba kowane masassa ƙ i ke da irin surkullen da ake yi w a itatuwa masu waibuwa ba, domin wasu masassa ƙ an ba ‘yan gado ba ne mahaya ne. Wani dalili na wanzuwar wannan hanya ta samar da itace ga masassa ƙ a ita ce, domin kauce wa wahalar zuwa dajin da neman sau ƙ i wajen gudanar da sana’ar. A yau wanzuwar wannan hanya kuwa a bayyane take idan aka yi la’akari da yadda ake sayar da itacen sassa ƙ a gunduwa-gunduwa a wasu sassan ƙ asar Hausa. Misali a garin Yauri, a tattaunawar da na yi da shugaban masassa ƙ a jirgin ruwa na Yauri, Abdullahi Isah Takware ranar 26-6-2016 ya shaida min cewa, masu sana’ar yin kwale-kwale (jirgin ruwa na itace) a yanzu mafi yawansu sun dogara ne ga filanki-filanki da ake kawo musu su saya domin aiwatar da sana’arsu.

Allah Ya albarkaci ƙ asar Hausa da nau’ukan itatuwa daban-daban da ake amfani da su a muhalli daban-daban na inganta rayuwar Ɗ an‘adam baki- ɗ aya. Ita kuwa sana’ar sassa ƙ a ta dogara ne kacokan ga sarrafa wa ɗ annan nau’ukan itatuwa zuwa b u ƙ atoci da dama da suka shafi rayuwar al’umma. A wannan bagiren, binciken ya yi ƙ o ƙ arin za ƙ ulo wasu muhimman itatuwa da masassa ƙ a ke amfani da su wajen aiwatar da sana’arsu ta sassa ƙ a a ƙ asar Hausa. Duk da yake, amfani da itutuwan a wajen aiwatar da sassa ƙ a ya danganta ne daga nau’in abin da ake son a sassa ƙ a. A hirar da na yi da shugaban masassa ƙ an Yauri a jihar Kebbi, Abdullahi Isah Takware da Sarkin masassa ƙ an Holai Umaru a jihar Sakkwato da Umaru Basakke Ɗ aki takwas jihar Zamfara da Sa’adu Maza Minjibir Jihar Kano da Labaran (2016:49) sun bayyana cewa, daga cikin jerin itatuwan da aka fi amfani da su wajen aiwatar da aikin sana’ar sassa ƙ a a ƙ asar Hausa sun ha ɗ a da:

1. Dogon yaro ( bedi, dalbejiya) 2. Ka ɗ e 3. Kaiwa (Kanya) 4. Gawo 5. Gamji 6. Danya ( Ɗ unya) 7. Loda 8. Kalgo 9. Geza 10. Faru 11. Marke 12. Dashe 13 Aduwa 14. Ce ɗ iya 15. Moro 16. Ma ɗ aci 17. Wuyan Damo 18. Ƙ o ƙ iya 19. Malga 20. Turare 21. Kurya 22. Katsari 23. Ƙ irya 24. Maje 25. Taura 26. Ɗ oruwa 27. Alilliba 28. Doka 29.Tsamiya 30. Kandare da sauransu, Rambo, (2018).

Wa ɗ annan jerin sunayen itatuwa suna daga cikin itatuwan da aka fi amfani da su wajen aiwatar da sana’ar sassa ƙ a a ƙ asar Hausa. Duk da yake cewa, amfani da itatuwan ya danganta ne da yawaitarsu a sassa daban-daban na ƙ asar Hausa. Alal misali, itutuwan da ake amfani da su gabashin ƙ asar Hausa suna iya bambanta da na arewaci ko yammaci, wani lokaci kuwa suna iya tarayya ya zan kowane yanki ana iya samun nau’ uka n ita tuwan kuma a yi amfani da su gwargwadon nau’in abin da ake son a sassa ƙ a . Misali, itacen aduwa ana amfani da shi wajen yin ɓ otoci da alluna, ka ɗ e da ƙ irya da ma ɗ acci wajen yin turame, kurya da gawo wajen yin kujerun zama na mata da wasu nau’ukan kayan ki ɗ a na Hausa kamar kalangu da ganguna da sauransu.

3.2 G atari

CNHN (2006:61) sun bayyana gatari a matsayin, Wani masari mai ƙ aramin ruwa da ɓ ota da ake saran itace da shi. Gatari yana daga cikin muhimman kayan aikin da mai sana’ar sassa ƙ a ke bu ƙ ata domin aiwatar da sana’arsa. A cewar Sakken Holai Malam Ummaru, cewa ya yi gatari ya kasu gida biyu, akwai babba akwai ƙ arami. Babban gatari da shi ake amfani wajen sare itacen da ake so a yi sassa ƙ a da shi. Ƙ aramin gatari kuwa da shi ne ake amfani wajen sare itacen da aka kayar zuwa gunduwa-gunduwa gwargwadon bu ƙ atar abin da masassa ƙ i ke bu ƙ atar sarrafawa. Haka da gatarin ne ake fara fid da siffar abin da ake so a sassa ƙ a watau kwakkwafa.3.3 Gizago

Hausawa na yi masa kirari da “Gizago manta sabo.” Sanyinnawal (2015:52) ya bayyana shi da cewa, Gizago wa ni kayan aiki ne da masassa ƙ a ke amfani da shi wajen fit da cikakkiyar surar abin da suke son samarwa. Haka CNHN (2006:168) sun bayyana gizago da “abin sassa ƙ an turmi.” Gizago wani ƙ arfe ne mai kama da fartanya mai zurfi da kaifin gaske tare da ɓ ota, sai dai bai kai fartanya girma ba. A lokacin aiwatar da aikin sassa ƙ a, ana ƙ ara masa kaifi ta hanyar washi ta amfani da magagari ko dutsin washi domin a samu damar sassa ƙ a cikin sau ƙ i da sauri.

Hoton Kayan Sassaka

3.4 Mahurin Ɓ ota

Wannan shi ma yana daga cikin muhimman kayan aikin sassa ƙ a. Galibi akan yi aiki da mahuri ne bayan an gama aiki da gizago. Labaran (2016:39) ya bayyana cewa, ana amfani da shi ne domin a ƙ arasa gyaran abin da ake so a sassa ƙ a musamman a nau’ukan sassa ƙ a r da ke da zurfi kamar turmi da kwale-kwale (jirgin ruwa na itace). Haka Sanyinnawal (2015:52) ya bayyana cewa, ana amfani da mahuri musamman ga kayan sassa ƙ a r da gizago ba ya iya shiga a yi aiki da shi. A siffance mahuri kamar gizago yake, sai dai bakinsa ya bambanta da na gizago, domin gizago bakinsa bu ɗ e yake a shimfi ɗ e, shi kuwa mahuri bakinsa a nanna ɗ e yake.

Hoton Kayan Sassaka

3.5 Mahurin Turmi

Wannan masassa ƙ a na amfani da shi ne wurin kwashe duga-dugan sassa ƙ a domin sassa ƙ ar ta fito gwanin ban sha’awa. Haka ana amfani da shi domin gugar abin da aka sassa ƙ a ta yadda jikinsa zai yi sul ɓ i ba tare da ko da mutum ya shafa ba ya yi masa sartse (rauni) ba .


3.6 Matari

Kamar yadda Umar Sakken Holai ya shaida min a hirar da na yi da shi cewa,

Matari yana daga cikin muhimman kayan aikin sassa ƙ a da masassa ƙ a ke amfani da shi wurin aiwatar da sana’arsu.

Matari wani guntun itace ne da masassa ƙ a kan shimfi ɗ a a ƙ asa inda za su ri ƙ a ɗ aura abin da suke sassa ƙ a a kai. Ana yin wannnan ne domin kauce wa sassa ƙ a r ƙ asa ko dutsi lokacin da ake sassa ƙ ar. Wani lokaci kuwa domin ɗ ago abin sassa ƙ a r dai-dai yadda za su ji d a ɗ in sassa ƙ arsa. Ga masu sassa ƙ a r jirgin ruwa kuwa, suna amfani da matari a matsayin waigi ga jirgin da ake sassa ƙ awa domin kada ya motsa daga inda aka girke shi a lokacin da ake aiwatar da sassa ƙ ar.

3.7 Atanda

Atanda kamar matari yake, sai dai shi galibi masu amfani da shi su ne masu sassa ƙ a r jirgin ruwa. Labaran (2016:64) ya bayyana cewa,

Atanda wasu katakai ne da ake sanyawa a gefe-gefen jirgin da ake sassa ƙ awa domin kada jirgin da ake sassa ƙ a ya rin ƙ a motsawa a lokacin da ake aiwatar da sassa ƙ ar.

Wannan kuwa shi kan ba masassa ƙ a damar yin sassa ƙ ar su ba tare da motsawar jirgin da suke sassa ƙ a ba.

3.8 Bakin Aku

Bakin Aku shi ma wani nau’in kayan aiki ne na masassa ƙ a jirgin ruwa. Bakin Aku galibi wani itace ne na musamman da masassa ƙ a kan samo su gyara shi ta yadda siffarsa za ta zamo kamar ta bakin Aku. Kamar Matari da Atanda, amfaninsa shi ne domin ya kange itacen da ake sassa ƙ a wanda za a aiwatar da jir g in ruwa da shi ya bar motsawa. Ana amfani da shi ne ta hanyar kama itacen da ake sassa ƙ a da wannan itacen da aka sassa ƙ a mai lan ƙ wasa kamar bakin aku , Labaran (2016:65) .

3.9 Igiya

A al’adance , masassa ƙ an gargajiya suna amfani da igiya ne wajen auna tsawo ko gajartar abin da suke so su sassa ƙ a. Sanyinnawal (2015:53) ya bayyana cewa, wannan igiyar tana a matsayin ‘tape-line’ wajen auna mita ko ƙ afa nawa ake bu ƙ atar abin sassa ƙ a r ya kasance. A wata fuska, masassa ƙ a na amfani da igiyar wajen ɗ auro kayan sassa ƙ a r da suka sassa ƙ a a daji kamar turame da ta ɓ are da muciya, su ɗ auro wa abin hawansu ko su ɗ aura su aza a kai zuwa inda za su aiwatar da sana’arsu. Duk da yake, a cewar Umar Basakke Ɗ aki takwas , wani lokaci masassa ƙ an kan yi amfani da hannu ko ƙ afafunsu wajen auna tsawon abin da za su sassa ƙ a.

3.10 Dutsin Washi

Sambo (2016:38) ya bayyana cewa: Dutsin washi wani ƙ an ƙ ara ne (dutsi) wanda masassa ƙ a ke amfani da shi wajen ƙ ara wa kayan aikinsu kaifi musamman idan sun dallashe a lokacin da suke aiwatar da aikace-aikacensu na sassa ƙ a.

Ganin cewar kusan dukkananin kayayyakin da suke amfani da su masu kaifi ne, wannan shi ya sa suka samu fasahar amfani da dutsi domin wasa wa ɗ annan kayayyakin aikin nasu. Ana amfani da dutsin ne ta hanyar goga shi ga abin da ake so a wasa har sai abin aikin ya yi kaifi gwargwadon bu ƙ ata.

3.11 Magagari

Bro B (1996) sun bayyana shi da : “Duste ko gwangwani ko ƙ aramar wu ƙ a lan ƙ wasassashiya a goge ƙ warya ta yi tsantsai.” Ta fuskar magagarin masassa ƙ a kuwa, a nan magagari wani ɗ an ƙ arfe ne da ake amfani da shi wajen ƙ ara wa kayan aikin sassa ƙ a kaifi domin samun sau ƙ in amfani da shi a lokacin da ake aiwatar da sassa ƙ ar. Ana amfani da shi ne lokacin da masassa ƙ i ya fahimci kayan aikinsa sun dallashe ba su da kaifi, a nan ne yake amfani da magagari yana gogawa har sai abin aikin ya yi kaifi kamar yadda yake bu ƙ ata.

3.12 Basharta

A hirar da na yi da Sa’idu Maza a Minjibir ta jihar Kano ya shaida min cewa, basharta wata ‘yar aska ce ko wu ƙ a ta musamman da masassa ƙ a ke amfani da ita wajen yin wasu ‘yan zane-zane na kwalliya ga abubuwan da masassa ƙ a suka sassa ƙ a domin ɗ aukaka darajarsu. Wa ɗ annan zane-zane akan yi su ne ga kayayyakin sassa ƙ a da aka kammala sassa ƙ arsu. Daga cikinsu akwai irin su kujerun zama na mata da turame da akushi da dankai da dai sauransu. Irin wannan basharta ce mafe ƙ a (gyartai) ke amfani da ita wajen fi ƙ an ƙ orai a ƙ asar Hausa.

Hoton Kayan Sassaka

3.13 Wambali

Wambali wani nau’in kayan sassa ƙ a ne da masassa ƙ a kan yi amfani da shi musamman a wajen sassa ƙ ar abubuwa masu zurfi kamar turmi ko jirgin ruwa da sauransu. Umar Sakken Holai ya ƙ ara bayyana cewa: “Galibi ana amfani da shi ne bayan an fara amfani da gizago ta yadda za a samu damar ginan abin da ake sassa ƙ awa.”

3.14 Tukar Sassa ƙ a

Tukar sassa ƙ a ita ce sa ƙ e-sa ƙ in itacen da ake sassa ƙ awa a lokacin da ake aiwatar da sassa ƙ ar. Har wa yau, Umar Sakken Holai ya ƙ ara bayyana mini cewa:

Amfanin tukar sassa ƙ a ita ce gugan abin da aka sassa ƙ a domin jikinsa ya yi sul ɓ i, amma a yanzu masassa ƙ a na amfani da fasahar goge kayan sassa ƙ a r da sam-fefa a madadin tukar sassa ƙ a.

Fasahar yin wannan ita ce, zai ba da damar masu amfani da kayan sassa ƙ a r su ri ƙ a amfani da kayan ba tare da shakkun yi masu rauni (sartse) ba.

3.15 Magirbi

Kamar yadda Malam Ummaru Sakken Holai ya tabbatar mini cewa, magirbi yana daga cikin kayan aikin da suke amfani da shi a ƙ o ƙ arinsu na samar da wasu kayan sassa ƙ a. Labaran (2016:38) ya ƙ ara bayyana cewa, a nan masassa ƙ a suna amfani da magirbi ne wurin ginan sayyun itacen da suke so su kayar, domin wani lokaci ana bu ƙ atar a sare itace tun daga sayyunsa, wannan kuwa ba zai samu ba sai da amfani da magirbi. Haka a cikin BroB (1996:141) sun bayyana shi da wani , ma’aikaci ko magirbin saran ƙ asa.”

Hoton Kayan Sassaka

3.16 Makwakkwafa

Makwakkwafa (Makwakkwaha): Wannan wani kayan aiki n aiwatar da sana’ar sassa ƙ a ne da ake amfani da shi a ƙ asar Hausa. Sambo (2016:38) ya bayyana cewa shi wannan ma’aikaci ya yi kama da gizago, amma abin da ya bambanta su shi ne, shi gizago bakinsa a bu ɗ e yake, amma ita makwakkwafa bakin nata a na ɗ e yake ta yadda idan ana amfani da ita za ta rin ƙ a shiga kusurwar da gizago ba ya iya shiga. Misali , masu sassa ƙ a r ɓ otoci suna amfani da ita wajen fid da kan ɓ ota ta ciki. Sambo (2016:38) ya kawo wannan a cikin jerin kayan aikin sassa ƙ a inda yake cewa:

To kamar kowace sana’a, ita ma sana’ar sassa ƙ a ba a bar ta a baya ba, domin ita ma akwai kayan aikinta kamar irin su gizago da gatari da makwakkwafa ... ..

3.17 Mazurfi

Wannan wani kayan aiki ne da masu sana’ar sassa ƙ a ke amfani da shi wajen aiwatar da sassa ƙ a r abu mai zurfi kamar turmi ko kwale-kwale (jirgin ruwan itace). Wasu na kiran wannan da ‘taitaima’, shi wannnan ma’aikaci ya yi kama da fartanya amma ya fi ta tsawon ɓ ota da ruwan ƙ arfen da ake sanya ma shi.

Hoton Kayan Sassaka

3.18 Kwalle

A hirar da na yi da Maidawa Ummaru Gidan Sakke ranar 17-2-2017 ya bayyana kwalle a matsayin wani ma’aikaci da masassa ƙ a ke amfani da shi wajen sassa ƙ a. Kwalle shi ne wanda ake amfani da shi wurin fasa itace ko da gatari ya kasa fasa shi. Ummaru ya nuna a lokacin amfani da shi, za a ɗ an yi w a itacen da ake so a fasa wata ‘yar alama a bakin itacen da ake so a fasa, daga nan sai a buga wannan kwallen da wani itace mai nauyi da hannu. Ya nuna cewar nan take za a ga itacen ya fashe. Wajen samar da wannan kayan aiki, akan za ɓ i itace mai ƙ wari a yi amfani da shi.

3.19 Guru

Wannan wani kayan aiki ne da masassa ƙ a ke amfani da shi wajen aiwatar aikin sassa ƙ e-sassa ƙ en kayan sassa ƙ a masu zurfi kamar turmi ko kwale-kwale ko akushi ko dankai da sauransu. Galibi ana amfani da shi ne bayan an yi amfani da mazurfi wajen ƙ ara ginan abin da ake sassa ƙ a, musamman ganin shi guru ƙ aramin ma’aikaci ne da kan iya shiga inda mazurfi ba ya iya shiga. Akwai babba da ƙ aramin guru.

Hoton Kayan Sassaka

Duba da irin wa ɗ annan kayan aiki da masassa ƙ a kan yi amfani da su, za mu ga cewar sana ar ta amshi sunanta na sana ar gargajiya, domin duk wa ɗ annan kayayyaki na gargajiya ne da fasahar Bahushe ta samar da su. Wannan kuwa nuni yake da cewar, duk da ƙ o ƙ arin ci gaban fasahar zamani, har yanzu masassa ƙ a a ƙ asar Hausa suna amfani da kayayyakin da suka gada tun kaka da kakanni wajen aiwatar da sana arsu.

4.0 Kammalawa

Bisa ga abubuwan da wannan bincike ya yi nazari a kai, za a fahinci cewar, ko shakka babu sha’anin sana’ar sassa ƙ a a ƙ asar Hausa, sana a ce da ke ɗ amfare da hanyoyin samar da abubuwan bu ƙ atun al umma na yau da kullum. Su kuwa wa ɗ annan ababe da masassa ƙ a kan samar sun dogara ne ga amfani da wa ɗ ansu kayan aiki da suke amfani da su domin aiwatr da sana’arsu. A wannan bincike an yi ƙ o ƙ arin gano ire-iren wa ɗ annan kayan aiki da yadda masassa ƙ a ke amfani da su wajen aiwatar da sana’arsu ta sassa ƙ a a ƙ asar Hausa.

Manazarta

 Abdu, G.K. (1989). “Itatuwan Ƙ asar Hausa: Ire-irensu da Fa’idojinsu ga Rayuwar Hausawa.” Kano: Kundin Digiri Na Farko, Sashen Koyar da Harsunan Nigeriya Jami’ar Bayero.

Ambursa, S. S. (2015). “Sana’a Sa’a: Nazari a Kan Sana’ar Sassa ƙ a a Garin Birnin Kebbi.” Sakkwato: Kundin Digiri na Farko, Sashen Koyar da Harsunan Nigeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

Bargery, G.P. (1934). A Hausa-English and English-Hausa Vocabulary. London: Oxford University Press.

BroB, M and Baba, A.T. (1996) . Dictionary of Hausa Crafts a Dialectal Documentation . Rudiger : Koppe Verlag Koln.

CNHN, (2006). Ƙ amusun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press.

Dan‘iya, M.A. (2006).Tasirin Kimiya da Ƙ ere- ƙ eren Zamani a Kan Sana’o’in Hausawa na Gargajiya. Kano: Kabs Print Services Nigeria.

Garba, C.Y. (1991). Sana’o’in Gargajiya a Ƙ asar Hausa. Ibadan: Spectrum Books Limeted.

Kabakawa, B.U. (2007). “Sana’o’in Hausa na Matan Hausawa.” Kano: Kundin Digiri na Farko. S a hen Koyar da Harsunan Nijeriya Jami’ar Bayero.

Labaran. S. (2016). “Gudummawar Sana’ar Sassa ƙ a r Jirgin Ruwa a Garin Yauri.” Sakkwato: Kundin Digiri na Farko. Sashen Harsunan Nijeriya Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

Maigandi, A. (2014). “Hanya Mai Ha ɗ in Zumuntar Dole: Cu ɗ e ɗ eniyar Al’adun Hausawa d a n a Fulani a Gundumar Sakkwato.” Sakkwato: Kundin Digiri na Uku, Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

Newman, P. (1977). A Hausa-English Dictionary. London: Yale University Press.

Rambo, R. A. (2018). “Nazarin Ayyukan Sana’ar Sassa ƙ a da Fasalolinsu a Rayuwar Hausawa”. Katsina: Kundin Digiri na Uku. Sashen Koyar da Harsunan Nigeriya. J a mi’ar Umaru Musa Yar adua.

Sambo, J. (2016). “Tasirin Zamani A Kan Sana’ar Sassa ƙ a A Garin Sakkwato.” Sakkwato: Kundin Digiri na Farko. Sashen Koyar da Harsunan Nigeriya, Jami’ar Usmanu Danfoiyo.

Sanyinnawal, S. I. (2015). “Cu ɗ e ɗ eniyar Sana’o’in Gargajiya a Adabin Bakan Bahaushe.” Sakkwato: Kundin Digiri na Biyu. Sashen Koyar da Harsunan Nigeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo

Sharifai, B. (1990). “Take da Kirarin Sana’o’in Gargajiya: Nazarin Ma’anarsu da Muhimmancinsu ga Rayuwar Hausawa”. Kano: Kundin Digiri na Biyu. Sashen Koyar da Harsunan Najeriya. Jami’ar Bayero.

The New Age Encyclopedia, (1980). Volume 3, Lexico Publication.

Wushishi, S.S. (2011). “Dangantakar Magani d a Wasu Sana’o’in Gargajiya Na Hausawa.” Sakkwato: Kundin Digiri na Biyu, Sashen Koyar da Harsunan Nigeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

  Yahaya, I.Y. da da wasu (2001).Darussan Hausa Don Manyan Makarantun Sakondare 2. Ibadan: University Press Plc.

Yahaya, I.Y. da wasu (1987). Sabuwar Hanyar Nazarin Hausa Don Manyan Makarantun Sakondare Littafi na Biyu. Ibadan: University Press.

Post a Comment

0 Comments