Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazarin Wasan Kwaikwayon Soyayya Ta Fi Kudi a Mahangar Ra’in Mararanci

Table of Contents

Citation: Yusuf, J. (2024). Nazarin Wasan Kwaikwayon Soyayya Ta Fi Kuɗi a Mahangar Ra’in Mararanci. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, 3(1), 282-291. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.032.

Nazarin Wasan Kwaikwayon Soyayya T a Fi Ku ɗ i a Mahangar Ra’in Mararanci

Jibril Yusuf

Department of Nigerian Languages and Linguistics
Kaduna State Uni v ersity, Kaduna
Phone no: +2347030399995
Email: jibreelzango@gmail.com

Tsakure

N azarin ayyukan adabin Hausa a bisa wasu ayyanannun ra’o’i abu ne da bai da ɗ e da bayyana a duniyar nazari ba . Da yawa daga cikin marubuta adabin Hausa sukan yi rubuce-rubucensu ba tare da sanin cewa aikinsu ya yi daidai da wani ra’i ba. Wasu masana sun a ganin cewa, wasu nau ’ukan ra’in k amar ba su da muhalli a nazarin ayyukan adabin Hausa . Wannan ne ya sa aka yi ƙ o ƙ arin ɗ ora ra in Mararanci (Romanticism theory) da manufofinsa a rubutaccen wasan kwaikwayon Hausa domin ganin ko ana iya nazarin ayyukan adabin Hausa ta hanyar amfani da wani ayyanannen ra’i . A wannan aiki an duba manufofin ra’in ne da yadda suke wanzuwa a cikin ayyukan adabi, musamman wasan kwaikwayon Hausa. An bi hanyoyi da yawa wajen tattara bayanan da aka yi amfani da su wajen wannan aiki, wa ɗ anda suka ha ɗ a da karance-karance a littafai domin samun ƙ arin haske kan ra in da aka ɗ ora aikin, da kuma za ɓ o wasan kwaikwayon Soyayya Ta Fi Ku ɗ i wanda a kansa ne nazarin ya ta’alla ƙ a. Binciken ya tabbatar da yiwuwar nazarin wasannin kwaikwayon Hausa ta hanyar amfani da ra’in Mararanci . A ƙ arshe binciken ya gano cewa , irin wa ɗ annan wasannin kwaikwayon Hausa suna da matu ƙ ar tasiri a kan abubuwan da suka shafi zamantakewar al umma .

Fitilun Kalmomi: Ra’i , Mararanci, Nazari , Wasan Kwaikwayo

1.0 Gabatarwa

Nazarin rubutaccen adabin Hausa ba sabon abu ba ne , amma amfani da ra’i wurin nazarin rubutaccen adabin Hausa wani ba ƙ on al amari ne da za a iya cewa bai da ɗ e da ɓ ulla cikin duniyar nazarin adabin Hausa ba. Masana da manazarta sun da ɗ e suna amfani da hanyoyin gargajiya wajen nazarin ayyukan adabi musamman na Hausa, ta yadda sukan nazarci wani aiki tare da ƙ imanta shi ko ba shi wata daraja ta musamman, ko kuma a bi dukkan sassan aikin a yi masa sharhi ko kuma a yi tarkensa. Daga bisani an gano cewa akwai wa ɗ ansu ra’o’i da za a iya ɗ auka a nazarci ayyukan adabi ta hanyar ɗ ora su bisa kan wani ra’i tare da la’akari da manufofin da suka gina ra’in.

A wannan nazarin an yi ƙ o ƙ arin ɗ ora rubutaccen wasan kwaikwayo ne bisa ra’in mararanci domin a ga yadda ya dace da manufofin ra’in. Wannan nazarin zai fito da ra’in a fili domin a fahimci yadda yake fitowa cikin ayyukan adabin Hausa.

2.0 Ma’anar Fitilun Kalmomi

A nan za a kawo bayanin fitilun kalmomin wannan bincike, wannan zai sau ƙ a ƙ a fahimtar abin da takardar za ta tattauna a kansa.

2.1 Ra’i

Kalmar ra’i tana nufin ganin dama ko ra’ayi (CNHN,2006), sai dai a fagen nazari kalmar tana nufin tsararriyar hanyar nazari bisa fahimtar magabata, wadda take ƙ unshe da wasu ƙ a’idoji da manufofi da ake amfani da su domin ɗ ora bincike a kai don samun kyakkawan sakamako.

2.2 Mararanci

Kalmar Mararanci (Mustapha, 2013) kalma ce ta nazari wadda aka samo ta daga kalmar ‘marari’. Kalmar marari suna ne jinsin namiji, wanda ke nufin jin da ɗ i ko ɗ oki (CNHN,2006) a fagen nazari ana amfani da kalmar ne domin bayyana soyayya da ke tsakanin mace da namiji. Kalmar mararanci (romanticism) tana nufin hanyar nazari ce da aka samar domin yin nazarin ayyukan adabi da suke da ala ƙ a da soyayya ko shau ƙ i ko kuma ɗ okin abokin soyayya da kuma irin yanayin da soyayyar kan jefa ma’abotanta.

2.3 Nazari

Kalmar nazari suna ne jinsin namiji, jam’insa shi ne nazarce-nazarce. Kalmar tana nufin duba abu, ko tsokaci ko karatu a zuci ko kuma yin bincike game da wani abu (CNHN, 2006). Idan aka ce ana nazari a kan wani abu to ana nufin ana bincike ke nan a kansa domin gano wani abu a cikinsa.

3.0 Ma’anar Wasa da Wasan Kwaikwayo a Ta ƙ aice

Masana sun bayyana ma’anar wasa da kuma wasan kwaikwayo daidai fahimtarsu, ta yadda kusan a iya cewa ma’anonin da suka kawo sun yi tarayya ne kan abu guda. Dangane da ma’anar wasa, a cikin Malumfashi (1990) da CNHN (2006) an bayyana cewa, ita dai wasa na nufin duk abin da ba gaskiya ba, yana kuma ɗ auke da raha da ban dariya da nisha ɗ i . Wato dai duk wani abin da ke ƙ unshe da nisha ɗ i da raha a lokacin aiwatar da shi, kuma ana yin sa ne ba da gaske ba to za a iya kiran sa wasa. Dangane da wasan kwaikwayo kuwa masana da manazarta da dama sun bayyana fahimtarsu dangane da ma’anar ta.

Kofowor ol a, (1978) da Crow (1983) da Ɗ angambo (1984) da Ahmed (1985) da Malumfashi (1990) da ‘Yar’aduwa (2007) da Sambo (2012) da Aliyu (2021) duk sun yarda cewa wasan kwaikwayo fasaha ce da ta shafi koyi na wata rayuwa ta hanyar sake kama domin samar da nisha ɗ i da raha da annashuwa da kuma isar da sa ƙ o ga al umma.

A dun ƙ ule za a iya cewa wasan kwaikwayo aiwatar da kamancen halaye ne a wasance cikin raha da nisha ɗ i don kwatanta yadda wani lamari ya ta ɓ a faruwa ko kuma yadda wani ya ta ɓ a yin sa a zahiri.

4.0 Samuwar Rubutaccen Wasan Kwaikwayo n a Hausa a Ta ƙ aice.

Tarihi ya nuna cewa rubutaccen wasan kwaikwayo ya samu ne bayan zuwan Turawa a ƙ asar Hausa. Hausawa sun iya karatu da rubutu, wannan ya ba su damar samar da wasannin kwaikwayon ta yadda ake bu ƙ atar rubutawa kafin a gabatar da shi, ko kuma domin masu karatu. Shi ya sa ma ake kiran sa rubutaccen wasan kwaikwayo.

Masana suna ganin littafin wasan kwaikwayon da Dr. R.M East ya tsara kuma aka sa wa suna Six Hausa Plays shi ne rubutaccen wasan kwaikwayo na farko a al’ummar Hausawa, wanda kuma ya samu ne bayan zuwan Turawa a ƙ asar Hausa. Sai dai wasu masana irin su Ahmed (1987) da Malumfashi (1985 da 2014) suna ganin wasannin Turbar Turabulus (1902) da Turbar Ƙ udus (1898) da ‘Yan Matan Gaya (1900) da Tarihin Rabeh (1902) da Wasan Gizo Da Ƙ o ƙ i da Wasan Boka Da Majinyaci ( 1910) wa ɗ anda Rudolf Prietze da shi da Malam Muhammadu Ajingi (Ahmadu Kano), suka samar, su ne rubutattun wasannnin kwaikwayo na farko na Hausa.

Wani abu da ya kamata a fahimta a nan shi ne, a lokacin da Turawa suka kafa Hukumar Fassara a shekarar 1929 ayyukanta sun ha ɗ a da samar da littattafai don karantawa. Bisa wannan tsari ne shugaban Hukumar Dr. R. M. East da Malam Abubakar Imam da masinjan Hukumar Malam Basankare suka tsara wasan kwaikwayo na farko da Hausa a shekarar 1936, wanda suka sa wa suna Six Hausa Plays , (Malumfashi, 1990).

Marubucin wato R.M East ya bayyana a cikin gabatarwar littafin na Six Hausa Plays , daga cikin dalilan da ya sa aka soma wannan al'ada bai wuce neman nuna wa jama'a yadda ake tsara wasannin kwaikwayo a rubuce ba, musamman ta hanyar canza tatsuniyoyi da tarihi da tarihihin ƙ asar Hausa zuwa wasannin kwaikwayo. Ganin wannan littafi ya samu kar ɓ uwa, yara kuma suna karantawa ga kuma lokuta da aka ajiye a azuzuwa domin yin wasannin da kuma shirya wasannin kwaikwayo, sai wannan al'ada ta shige rayuwar jama'a, daga wannan lokaci yara da malamai suka shiga rubutawa tare da aiwatar da wasannin kwaikwayo a makarantu da lokutan karatu da bukukuwa, (Malumfashi, 1990).

Daga wannan lokacin aka shiga cin kasuwar rubutun wasan kwaikwayo, aka kuma ci gaba da samar da su daga ma ɗ aba'u daban-daban har zuwa yau da ake da wasannin kwaikwayon Hausa a rubuce masu tarin yawa, (Malumfashi, 1990).

5.0 Ɓ ullar Ra i a Duniyar Nazarin Adabi

Dangane da samuwar hanyar nazarin adabi kuwa, masana sun yi musayar ra’ayi kan yadda ya samu musamman daga Larabawa da Turawa har zuwa Hausawa.

Ɗ angambo (2008) ya bayyana cewa mazahabobi na tarke sun fara kunno kai tun wajen ƙ arni na 16 zuwa 17 a ƙ asashen Turai, wanda hakan ya yi tasiri ƙ warai wajen ginuwar ayyukan adabi masu inganci. Su kuwa Larabawa sun fara bincike kan ayyukan adabi da rayuwar ɗ an’adam tun zaman farko na Jahiliyya. Sun mayar da hankali kan nazarin ayyukan gargajiya da suka danganci maganganun azanci da wa ƙ o ƙ in baka da labaru da al’adu da sauransu.

Turawan da suka fara share fagen nazarin ayyukan adabi, sun yi rubuce-rubuce da dama inda aka samu ayyukan Plato (427-347 BC) da Aristotle (384-323 BC). Daga nan aka ci gaba da bayyana ra’ayoyi dangane da tarken adabi, masana irin su Horece (65-8 BC) da Sidney (1554-86) da Barcon (1561-1626) da Wordsworth (1770-1850) da Coleridge (1772-1834) da Sauransu da dama, duk sun bayyana hanyoyin nazarin adabi dangane da tunane-tunanensu don nazarin matani. ( Barry , 2002 )

Daga ƙ arshen ƙ arni na 19 aka samu gwagwarmayar siyasa da tattalin arziki, abin da ya haifar da samuwar marubuta adabi irin su Karl Marx da I. A. Richard da sauransu. A shekarar 1920 nazarin ya shiga jami’o’i da cibiyoyin ilimi. A wannan lokaci I. A . Richard ya rubuta littafi mai suna , Principle of Literary Critcism (1924) . Daga wannan ƙ o ƙ ari ne aka samu ƙ ungiyar “New criticism” (1945-1950) wato sabbin matarka, da suka fara amfani da nazarin ƙ wa ƙƙ wafi (Close reading) wannan ya sa ake wa wannan ƙ ungiyar kallon ta farko wajen tarken adabin , (Aliyu, 2021).

Gusau, (2008) y a bayyana malaman da suka fara nazarin adabin Hausa zuwa rukunoni daban-daban, wato rukunin Turawa irin su : D.W . Arnolt da Neil Skinner da M arvyn Hiskett da Paul Newman da Grah a m Furniss da sauransu . Y a kuma rarraba ‘yan ƙ asa zuwa rukunoni biyar dangane da lokutansu, sannan ya rarraba masana ta fuskar ɓ angarorin nazarin Hausa wato adabi da al’ada da kuma harshe. A ƙ arshe ya ambaci makarantun nazari na farko da lokutan da aka bu ɗ e su da malamansu na farko da marubuta masu sha’awar nazarin Hausa.

Ɗ angambo (2008) ya bayyana cewa tun kafin Turawa su mi ƙ a mulki, nazarin Hausa ya kankama cikin Turanci, kuma tsofaffin ‘yan mulkin mallaka su ne malaman farko da ke koyar da dabarun nazarin Hausa, wa ɗ annan manazarta su ne suka je suka yi sansani a wata makaranta da ke ƙ ar ƙ ashin Jami’ar Land a n (SOAS), wasu suka tafi Oxford wasu kuma Amurka da Jamus da sauransu. To daga can ne fa suka yi ta horar da malaman da ke dawowa Nijeriya su koyar da harsunan ƙ asar, ciki har da Hausa.

Don haka, aka samar da manazarta adabin Hausa da tsarin nazarin ra’o’in tarke na duniya. Sun tasirantu da adabin Turawa wajen nazarin, wannan ya sa adabin Hausa ya cu ɗ anya da abubuwa da dama. Da farko akwai adabin gargajiya kafin Hausawa su cu ɗ anya da ba ƙ i, sannan akwai adabin Hausa wanda ya tasirantu da zuwan Larabawa, wanda yake ɗ auke da ruhin addinin Musulunci, ga kuma tasirin adabin Turawa .

6.0 Ra’in Mararanci da Samuwarsa

Akwai hasashen cewa wannan mazahabar ta Mararanci an ƙ ir ƙ iro ta ne a ƙ arshen ƙ arni na 18, wato bayan shekarar 1750 (Roberts, 2009). Wasu na tsammanin cewa, sai a shekarar 1798 ne aka sam u wasu aikace-aikacen da suka tabbatar da kafuwarta a ƙ asashen Turai. Domin ta yi zamaninta ne a tsakanin shekarar 1750 zuwa wajen 1870 da abin da ya biyo baya har zuwa yau. Ta kuma fara ɓ ulla a Faransa da Jamus da Ingila (musamman a Faransa lokacin da suke cikin guguwar sauyi a 1879) , (Mustapha, 2013).

An fara tunanin gabatar da hanyar rubutun adabi na mazahabar Mararanci tun farko daga wasu manyan fasihai guda biyu. Na ɗ aya shi ne wani mafalsafi ɗ an ƙ asar Faransa mai suna, Jean Jacques Rousseau; da na biyu kuma wani adibi na ƙ asar Jamus, mai suna, Johann Walfgang Goeth. Shi Jacques shi ya fara fito da wani take a cikin rubuce-rubucensa mai cewa, “I felt before I thought” (Na ji a jikina kafin in tunana). Wa ɗ anda suka ƙ arfafa ta wasu ‘yan ƙ asar Ingila ne da suka rubuta wani littafi kan tarken Mararanci, wato William Wordsworth da Samuel Taylor Coleridge da suka rubuta, The Lyrical Ballads (1798) (Mustapha, 2013).

Wannan mazahabar ta ya ɗ u ne kamar wutar daji zuwa wasu ƙ asashen Turai da ma na ƙ etare. A ta ƙ aice, wannan mazahaba ta ya ɗ u zuwa ƙ asashen Turai kaf ɗ insu da kuma ma ƙ wabtansu da sauran ƙ asashen da marubuta da makaranta adabin Mararanci ya isa cikin duniya. Ta isa Amurka a wajen shekarar 1758; a Faransa da Ingila a wajen 1775; a Jamus a shekarar 1793; a Italiya a 1834 da sauransu.

Bayan haka, akwai wasu matarka da adibai da suka yi wasu rubuce-rubuce masu nuna lokacin da mazahabar Mararanci ta isa can ƙ asashensu. Daga cikinsu akwai:

a.   Ba’ a murke William Blake da ya rubuta, America, A Prophecy (1794)

b.   Ba’ i ngile Sir Walter Scott da ya rubuta, The Day of the Minstrel (1805).

c.    Ba’ i ngile William Wordsworth da Samuel Taylor Colerigde da suka rubuta, The Lyrical Ballads (1798) .

d.    Ba’ i ngile James Thompson da ya rubuta, The Seasons (1726).   

e.   Bajamushe Johann Gottfried Von Herder da ya rubuta, Von Deutcher Art Und Knst (Of German Style and Art) (1773).

f.      Bajamushe Schlegels da ya rubuta Athenacum (1798).

g.   Ba’ i taliye Alessandro Manzoni, da ya rubuta The Betrothed (1834).

Wa ɗ annan da wasu da dama sun yi rubuce-rubuce kan mazahabar Mararanci a da da kuma yanzu. A ta ƙ aice, wannan mazahaba ta sami marubuta masu yawan gaske a fannonin adabi daban-daban (musamman a fannin rubutacciyar wa ƙ a ta ƙ arni na 18 da na 19) a ƙ asashe daban-daban. Kuma ta sami bun ƙ asa a tsakanin shekarun 1800 zuwa 1830. Ta kuma sami ya ɗ uwa a ƙ asashen Larabawa da sauran ƙ asashen duniya ta hanyar tasirin ha ɗ uwar Turawa da wasu al’ummomi wajen mulkin mallaka da siyasar dimokura ɗ iyya da sauransu , (Mustapha, 2013) .

6.1 Manufofin Ra’in Mararanci

Mazahabar Mararanci tana da irin manufofinta kamar yadda kowace mazahaba take da su. Manufar na nuna irin al ƙ iblar da aka kalla da kuma irin salo da ma ƙ asudin aikace-aikacen adabinta. Saboda haka, wasu daga cikin manufofin mazahabar Mararanci da suka shafi ma ƙ asudin aiwatarwa sun ha ɗ a da:

a.      Ƙ o ƙ arin bayyana abubuwan da ke damun adibai game da halaye da dangantakar ɗ an’adam kamar soyayya da juyayin abin da ya wuce da hangen gaba da sauransu. Kamar dai yadda Jean Jacques Rousseau ya ce a cikin jawabinsa, “I felt before I thought” (Na ji a jikina kafin in yi tunani) .

b.      Amfani da tunanin adibi, tunaninsa na kansa, game da abin da ke kewaye da shi, a muhallinsa.

c.       Samun ‘yancin bayyana tunani da fa ɗ in ra’ayi da abin da ke hangen ɗ an’adam ta auna dangantakar yanayi da muhallin da yake ciki, kamar ba ƙ in ciki da fata, da mamaki da juyayi da takaici da kewa da sauransu, don a fahimce shi sosai da sosai.

d.     Neman tabbatar da abin da ke damun mutum da hoton zuciyarsa da kuma hangensa a kan irin harkoki da halayen rayuwa a cikin al’umma.

e.      Bu ƙ atar kasancewa masu ‘yanci wajen neman kiyaye ha ƙƙ i da mutumtakar ɗ an ’a dam, ta la’akari da irin rayuwarsu, musamman rayuwar mazauna karkara .

f.        Kawo batun harkokin shugabanci da tarihi da na zamantakewar al’umma a cikin wa ƙ o ƙ i da zube a rubuce-rubucensu.

g.      Sanya ra’ayin kare ha ƙƙ in ɗ an ’a dam da tausaya wa dabbobi a cikin aikace-aikacensu na adabi. ( Mustapha, 2013).

7.0 Ta ƙ aitaccen Tarihin Malam Hadi Bawa Alkanci.

A n haif i Hadi Abdullahi Alkanci a ranar 1 ga watan J anairu , 1957 a unguwar Alkanci da ke B irnin S a k kwa to. Ya yi karatu a Ƙ ofar Marke Nizzamiyya School wadda yanzu a ke ce wa makarantar Alhaji Alhaji Model Primary School, Sokoto. A shekarar 1973 ya tafi Sultan Abubakar College , Sokoto, in da ya samu shaidar malanta ta Grade II a 1977. Ya yi aiki a Sashen I lmi na Ƙ aramar Hukumar Sokoto, daga bisani kuma ya koyar a makarantar ‘ya’yan sojoji wato ‘ Army Children School ’ da ke Sokoto daga 1977 zuwa 19 78.

Daga nan kuma sai ya tafi Cibiyar Horar da Ma’aikata wato ‘ Staff Training Centre ’ wadda yanzu ta zama Kwalejin Koyar da Sha’anin Mulki wato ‘ College of Administration ’ da ke Sokoto, inda ya samu takardar shaida kan f assara , daga 1978-79. Ya yi aiki a gidan radiyon Rima da ke Sokoto , inda daga nan ne ya yi ritaya ya fara kasuwanci .

Ya yi aiki na wucin gadi a N.T.A Lagos, inda yake gabatar da wani shiri mai suna "WAZOBIA" da kuma karanta labarun duniya a shekarar 1981 zuwa 1982. Ya zama ɗ aya daga cikin manyan daraktocin kamfanin ‘Alkanci Enterprise’. A wannan lokaci ya samu damar ziyartar ƙ asashen duniya da dama.

A shekarar 1986 ne ya bar harkar kasuwanci ya dawo ya du ƙ ufa a kan harkar rubutu da aikin jarida. Malam Hadi Alkanci ya gabatar da ma ƙ alu a tarurruka na marubuta da jami ’o’i daban - daban , sannan kuma fitaccen marubucin wasan kwaikwayo ne na Hausa. A shekarar 1982 ne aka buga littafinsa na farko mai suna Soyayya Ta Fi Ku ɗ i wanda Sashen Al’adu na Ma’aikatar Al’adu ta Tarayya ya buga. Ya kuma rubuta littattafai da dama , wasu daga cikinsu sun ha ɗ a da:

Soyayya Ta Fi Ku ɗ i

Harsashin Kasa

Karatun a Cikkin Hot u na 1

Shin So Gaskiya Ne?

Zaben Allah

Jagora g a Mai Aikin Hajji .

Baya ga wa ɗ annan , akwai wasu da dama da ya rubuta wa ɗ anda ba a buga ba. Malam Hadi m amba ne a ƙ ungiyar marubuta reshen jihar Sokoto , wanda ya ba da g u dunm a wa sosai wurin ha ɓ aka adabin Hausa , musamman a Sokoto . A lokacin rayuwarsa shi ne ya ri ƙ a buga mujallar Sahihiya a Sokoto.

Malam Hadi Bawa Alkanci ya rasu a shekarar 2009, ya bar matan aure da ‘ya’ya. ( http://marubutanhausa.blogspot.com/2008/09/hadi-abdullahi-alkanci.html )

7.1 Samuwar Littafin Wasan Kwaikwayo na Soyayya Ta Fi Ku ɗ i

Littafin wasan kwaikwayo na Soyayya Ta Fi Ku ɗ i wanda Hadi Abdullahi Alkanci ya rubuta, ya samu ne a dalilin gasar da Ma’aikatar Al’adun Gargajiya ta Tarayya ta shirya a shekarar 1980, wanda kuma aka buga a shekarar 1982. Littafin ɗ aya ne daga cikin guda bakwai wa ɗ anda suka ciri tuta aka kuma za ɓ e su aka buga domin karantawa, kuma shi ne ka ɗ ai wasan kwaikwaiyo a cikinsu. Sauran ƙ agaggun labarai ne da kuma wa ƙ o ƙ i. Ga su kamar haka:

Turmin Danya na Sulaiman Ibrahim Katsina

Tsumagiyar Kan Hanya na Musa Muhammad Bello

Ƙ arshen Alewa Ƙ asa na Bature Gagare

Za ɓ i Naka na Munir Mohammed Katsina

Dausayin Soyayya na Bello Sa’id

Wasa Ƙ wa ƙ walwa na Yahuza Bello.

Wa ɗ annan su ne littafan da aka rubuta cikin harshen Hausa da suka yi nasara a gasar, wadda tun farko manufar shirya ta ita ce, don ƙ arfafa wa mawallafa yan ƙ asa guiwa tare da matasa masu rubutun ƙ agawa a cikin harsunan Nijeriya.

7.2 Bayanin Wasan a Ta ƙ aice

Wasan kwaikwayon So yayya Ta Fi Ku ɗ i wasa ne da ya ƙ unshi wasu matasa guda biyu; Ɗ aha da Jummai wa ɗ anda aka nuna su a gari ɗ aya. Ana nan sai soyayyar juna ta shiga tsakaninsu ba tare da sun sanar wa juna ba. Ɗ aha ɗ an makaranta ne da ke karatu a jami’a. Wata rana sai ita Jummai ta fa ɗ a wa ƙ anwarta Jamila irin ƙ aunar da take wa Ɗ aha wanda Jamila ta ba ta shawarar su je unguwar su Ɗ aha idan Allah ya sa sun ha ɗ u ita za ta fa ɗ a masa abin da ke zuciyar yayar tata. Ko da suka isa unguwar, tun daga nesa sai Ɗ aha da abokinsa Himma suka hango su. A haka dai suka ha ɗ u har suka bayyana wa juna abin da ke ransu, ashe da ma fa ɗ uwa ce ta zo daidai da zama.

Soyayya ta ƙ ullu har ta kai gaban iyaye, sai ƙ watsam wani attajiri mai suna Alhaji San ƙ arau ya fito neman auren Jummai, amma mahaifinta ya ce sam ba zai amince ba, domin kuwa ya riga ya yi m ata miji kuma suna son juna. Don haka ƙ u ɗ i ko wani abin duniya ba zai tsole masa ido ba. Aka yi ta ɗ auki-ba-da ɗ i da Alhaji San ƙ arau tare da taimakon uwar yarinya. Daga bisani dai Ɗ aha ya auri Jummai, kuma ya kammala makaranta ya samu aikin gwamnati. Shi kuwa Alhaji San ƙ arau daga ƙ arshe an ɗ aure shi saboda samun sa da laifin ba da cin hanci ta hannun Sakataren ma’aikatar da Ɗ aha yake aiki, sannan aka rage wa sakataren girma, aka kuma tabbatar da Ɗ aha a matsayin babban sakataren ma’aikatar.

8.0 Littafin Soyayya Ta Fi Ku ɗ i Bisa Ra’in Mararanci.

Kamar yadda aka kawo bayanin ra’in da za a yi nazarin wasan a kansa da kuma irin manufofin da ra’in ya ƙ unsa, sannan kuma a dubi ta ƙ aitaccen bayanin da aka kawo kan wasan za a fahimci cewa akwai wasu manufofin da wannan wasa zai zauna daram a kansu, wa ɗ anda kuma za a iya kafa hujja da su a yarda cewa an gina wasan Soyayya Ta Fi Ku ɗ i ne kan ra’in mararanci. Bari mu ɗ auki manufofin mu ga yadda suke da kuma yadda suka yi daidai da wasan.

8.1 Ƙ o ƙ arin Bayyana Abubuwan d a Ke Damun Adibai Game d a Halaye d a Dangantakar Ɗ an’ a dam Kamar Soyayya d a Juyayin Abin d a Ya Wuce d a Hangen Gaba d a Sauransu.

Idan aka dubi wannan manufar za a ga cewa kusan wasan ya ginu ne a kanta, domin kuwa an nuna soyayya ce da mar m arin juna kamar yadda yakan faru a zahiri ko a gaske. Misali; tun a farkon wasan an nuna yadda Jummai take tsananin son Ɗ aha wanda har hakan ya sanya ta shiga damuwar da ta bayyana a fuskarta, ha r ta kai ga ƙ anwarta Jamila ta fahimci akwai abin da ke damun ta. Ga misali;

Jummai: Babu wanda ya yi mani fa ɗ a, ina tunanin Ɗ aha ne kawai. Tun lokacin da na gan shi shekaranjiya raina ya shiga tunaninsa. In gaya maki gaskiya yau duniyar nan babu wanda nake so kamarsa, don kuwa shi ka ɗ ai ne zuciyata ke bege kodayaushe kuma ina fatar ya zama mijina.(Shafi na 1).

Idan aka duba za a ga cewa marubucin yana ƙ o ƙ arin bayyana dangantakar da ke tsakanin ‘yan’adam ne wadda ta shafi soyayya. Domin in aka dubi kalaman Jummai za a ga cewa cike suke da shau ƙ in soyayya da mararin ganin abin ƙ aunarta wato Ɗ aha.

Ba ma wannan ba, shi kansa Ɗ aha a nasa ɓ angaren yana can yana tunanin ta ba tare da ta san cewa ma yana son ta ba, duk da cewa shi ma bai san tana yi ba. Dubi abin da yake ce wa abokinsa Himma;

Ɗ aha: Himma ka san ban ɓ oye maka komai, to wallahi gaskiya a yanzu a nan garin da makaranta baki ɗ aya ba wacce nake so kamar yar gidan Malam Gafaka, wato Jummai. Da zai yiwu da na aure ta. (Shafi na 2).

A nan ma idan aka duba za a ga cewa shi ma yana ƙ o ƙ arin nuna irin tsintsar son da yake yi wa Jummai ne duk kuwa da cewa bai sanar da ita ba. Ke nan za a iya cewa wannan ita ce irin dangantakar da wannan ra’in yake magana a kai na tsakanin ‘yan’adam.

 

A wani wurin kuma wannan manufar ta sake fitowa fili musamman inda Jummai ke nuna tsananin son da take wa Ɗ aha har take hangen cewa shi ma Allah zai iya yi masa arzi ƙ i nan gaba duk da ba shi da shi yanzu. Dubi abin da take cewa;

Jummai : Bisa ƙ ashin gaskiya wanda nike so shi ne Ɗ aha, shi zuciyata ke tunani tun daga hudowar rana har ta koma ga Ubangijinta, har ta sake fitowa. Arzi ƙ i da rashi duk suna ga hannun Allah, wata ƙ ila shi ma Allah shi yi masa nasa fiye ma da Alhajin. (Shafi na 11).

Idan aka dubi bayanan Jummai a nan za a ga cewa bayan tsananin soyayya akwai kuma kyakkayawar fata ga abin ƙ aunarta wanda ya ha ɗ a har da hangen gaba wato rayuwar da take fata nan gaba, ba wai kawai yanzu take kallo ba. Wannan ne ma ya sa ta ƙ i amincewa da mai ku ɗ i wato Alhaji San ƙ arau bisa hangen cewa akwai rayuwa mai haske ga Ɗ aha nan gaba.

A wani misalin na daban kuma za a iya ganin inda mahaifin Jummai Malam Gafaka yake nuna cewa ba wani dalili ne ya sa ya tsaya kai da fata cewa sai ya aura wa Ɗ aha yarsa Jummai ba illa mutuncinsa da kuma so da ke tsakaninsu. Dubi abin da ya ce:

M.Gafaka : To saboda kalmar nan ta mutunci da kuma so shi ya sa na ga ya fi mani alheri ni da Ya ƙ utatu da kuma su yaran tun da mun gane suna son juna hai ƙ an kuma ba son shegantaka ba, na ga daidai ne mu ha ɗ a su aure. (Shafi na 61).

A nan Malam Gafaka ya nuna irin soyayyar da ke tsakanin ‘yarsa Jummai da Ɗ aha inda ya nuna cewa ai soyayyar da ke tsakanin yaran nan ba ka ɗ an ba ce, har ya nuna hai ƙ an ce.

A wani wurin kuma Malam Gafaka ya bayyana wa Allah-ba-mu wato wadda ta kawo kayan auren Ɗ aha cewa;

M.Gafaka : ...... Ɗ aha dai ya san ba sayar masa da yata na yi ba, so da ƙ aunar da suke yi wa juna shi ya sa na ba shi Jummai. (Shafi na 64).

Shi ma dai a nan soyayyar ce take ƙ ara fitowa fili inda ake ƙ ara tabbatar da irin soyayyar da ke tsakanin Jummai da Ɗ aha, wadda ita ce ta zama tsanin kaiwa ga aurensu.

8.2 Samun ‘Yancin Bayyana Tunani da Fa ɗ in Ra’ayi da Abin da Ke Hangen Ɗ an adam ta Auna Dangantakar Yanayi da Muhallin da Yake Ciki, Kamar Ba ƙ in Ciki da Fata, da Mamaki da Juyayi da Takaici da Kewa da Sauransu, Don a Fahimce Shi Sosai da Sosai.

  Idan aka duba a cikin littafin Soyayya Ta Fi Ku ɗ i za ga cewa Jummai ta tsaya kai da fata cewa Ɗ aha take so. Wannan ne ya sa ta tsaya take fa ɗ a wa mahaifiyarta Ya ƙ utatu abin da ke ranta, wanda a cikin wasan an ba ta yancin bayyana wa iyayenta wanda take so, kuma ba ta bari mahaifiyarta ta yi nasarar cusa mata ra’ayin w ani don son abin duniya ba. Dubi abin da Jummai take cewa:

Jummai: Abin da ya sa daga ƙ arshe kika ga raina ya ɓ aci shi ne, don irin halin da kike son ki tura ni, ga shi Allah ya ba mu uba mai son mu, mai son mu ji da ɗ in aure, ina tsammanin auren tilas ya wuce, kowa na da nasa ha ƙƙ i, ko da kike son ki cusa mini ra ayin auren A. San ƙ arau. Bisa gaskiya ba na son sa, kuma ba ruwan a d a limancinsu da ku ɗ insa. (Shafi na 9).

 

A nan an nuna yadda Jummai ta samu ‘yancin bayyana abin da ke cikin zuciyarta ba tare da shakka ko tsoro ba, inda take nuna cewa tana da ha ƙƙ in bayyana ra ayinta kan abin da take so, kuma tana da yancin yi wa kanta za ɓ in abokin rayuwar da take so wanda take ganin ya dace da ita. Har ta ƙ ara da cewa yanzu zamani ya zo da kai ya waye aka daina auren dole. Don haka tana da ha ƙƙ i kuma tana da za ɓ i.

Bugu da ƙ ari, a cikin wasan an ga yadda Jamila da Jummai suke takaicin yadda lamarin aurenta da Ɗ aha ya haifar da matsalolin da suka kawo rabuwar mahaifinsu da mahaifiyarsu. Dubi yadda suke tattaunanwa:

Jamila: Wallahi babu maganar zolaya a nan, ni dai kawai ina tunanin farkon wannan lamari ne da irin abubuwan da suka jawo wa gidan nan.

Jummai: Wane abu ne aurena ya jawo wa wannan gida?

Jamila: Yanzu yaya ki duba a wannan aure ne ita uwarmu ta sa kanta cikin jidalin da ya sa ta yi hasarar gidan nan ƙ ila har abada. (Shafi na 59)

 

A nan suna tattaunawa ne kan abin da suka hango a matsayin silar rabuwar auren iyayensu, wanda ko daga jin yadda suke tattaunawa suna alhini ne tare da ba ƙ in ciki da juyayin rashin kasancewar mahaifiyar tasu a gidan. Wanda kuma a dalilin wannan auren Ɗ aha ne aka samu wannan matsalar.

8.3 Neman Tabbatar d a Abin d a Ke Damun Mutum d a Hoton Zuciyarsa d a Kuma Hangensa a Kan Irin Harkoki d a Halayen Rayuwa a Cikin Al’umma.

A wannan yanayin akan samu adibi ya zayyana wani a cikin aikin adabinsa wanda ke bayyana yadda hoton wannan abin yake a cikin zuciyar mai karatu. Misali; An nuna yadda Jummai take da damuwa, amma ba ta bayyana wa kowa ba. daga nan sai aka nuna yadda ƙ anwarta Jamila ta zo ta same ta take tambayar ta ko akwai abin da yake damun ta.

Jamila: A’a na gan ki kin yi tagumi ne, kin zugum ko fa ɗ a aka yi maki?

Jummai: Babu wanda ya yi mani fa ɗ a, ina tunanin Ɗ aha ne kawai........yau duniyar nan babu wanda nake so kamar sa, don kuwa shi ka ɗ ai ne zuciyata ke bege kodayaushe kuma ina fatar ya zama mijina. (Shafi na 1)  

A nan idan aka duba za a ga cewa wurin neman tabbatar da abin da ke damun Jummai ne Jamila take tambayarta abin da ya sanya ta cikin damuwa, har ta ce ta yi zugum. Kalmar zugum zai sa mai karatu hango hoton Jummai da irin damuwar da take ciki. Sannan kuma wannan ya sa Jummai bayyana irin halin da take ciki da abin da yake damun ta.

8.4 Bu ƙ atar Kasancewa Masu Yanci Wajen Neman Kiyaye Ha ƙƙ i da Mutuntakar Ɗ an adam, ta La akari da Irin Rayuwarsu, Musamman Rayuwar Mazauna Karkara.

A cikin littafin Soyayya Ta Fi Ku ɗ i an nuna yadda mahaifin Jummai ya ba ta ‘yancin za ɓ in mijin aure ba tare da an takura mata ba. Wanda hakan bai yi daidai da son zuciyar mahaifiyarta ba, har ya sa take zargin cewa mahaifinsu ya ba su ‘yanci fiye da kima. Dubi abin da mahaifiyar Jummai ta ce:

Ya ƙ utatu: Ga ‘yar neman lalatatta marar albarka, yaushe kike irin wa ɗ annan maganganu gaba gare ni ko kunya ba ki ji a zo a iske kina fa ɗ in wa ɗ annan kalmomi gaba ga ɗ i a gabana. So? Yaushe kika san wani abu so? Amma ba ki da laifi, Malam ya ba ku yanci har kuke son ku fi ƙ arfin mutane, ai ya san mu ba haka aka yi mana aure ba. Tashi ki ba ni wuri! (Shafi na 11).

A nan mahaifiyar su Jummai ce ke fa ɗ a tana ganin bai dace a ba ta yanci ta za ɓ i miji ba sai dai ta bi umarninta ta auri wanda take so ko da kuwa ita ba ta son shi. A nan an nuna yadda mahaifinsu ya ba su ‘yancin y in za ɓ i da kansu domin guje wa matsalar da za ta iya biyo baya sa ɓ anin hakan.

A wani wuri an nuna inda Malam Gafaka yake da-na-sanin hana yayarsu za ɓ ar wa kanta wanda take so, inda ya za ɓ a mata ba tare da ya ba ta yancin jin ra ayinta ba, daga baya aka samu matsala, kamar yadda ya ce:

M.Gafaka: Ai wannan magana ma ta sa na tuna da yarinyar nan da kai wa Kwasau wai ni na ga mai hankali ne amma ina! Ban yi tunanin ko tana son sa ko ba ta son sa ba. Ka ga dai ƙ arshe ga shi ya sako ta da ciki da goyo... (Shafi na 17) .  

A nan ya nuna dacewar bai wa ‘ya’ya mata ‘yancin za ɓ en mazajen aurensu da kansu, ba tare da an tilasta masu su auri wanda ba shi suke so ba, wanda hakan na iya haifar da matsala kamar yadda ta faru da wata daga cikin ‘ya’yansa da ya aurar.

8.5 Sanya Ra’ayin Kare Ha ƙƙ in Ɗ an ’a dam d a Tausaya w a Dabbobi a Cikin Aikace-Aikacensu n a Adabi.

A nan za a ga cewa adibi yana ƙ o ƙ arin sanya wani ra ayi da yake ƙ o ƙ arin nuna muhimmancin kare ha ƙƙ in ɗ an’adam, yadda zai nuna dacewa a bai wa kowa ha ƙƙ insa ba tare da tauye masa ba. Irin wannan ya fito a cikin wasan Soyayya Ta Fi Ku ɗ i, musamman inda Jummai ke cewa:

Jummai: Abin da ya sa daga ƙ arshe kika ga raina ya ɓ aci shi ne, don irin halin da kike son ki tura ni, ga shi Allah ya ba mu uba mai son mu, mai son mu ji da ɗ in aure, ina tsammanin auren tilas ya wuce, kowa na da nasa ha ƙƙ i, ko da kike son ki cusa mini ra ayin auren A. San ƙ arau. Bisa gaskiya ba na son sa, kuma ba ruwan a d a limancinsu da ku ɗ insa. (Shafi na 9).

A nan ana nuna cewa, yadda mahaifin Jummai ya ba ta ‘yancin za ɓ en mijin aure haka ya kamata kowane uba ya bai wa ‘ya’yansa, domin su ma mutane ne, sun san abin da ya dace da su da wanda bai dace da su ba. Don haka a ba su ha ƙƙ insu kada a tauye su.

Idan aka dubi bayanan da aka kawo a baya za a fahimci cewa littafin Soyayya Ta Fi Ku ɗ i yana ƙ unshe da wasu abubuwa da suka yi daidai da manufofin ra’in Mararanci (Romanticism theory), domin kuma an ri ƙ a ɗ aukar manufofin ɗ aya bayan ɗ aya ana kwatanta shi da wasan ta hanyar kafa hujja daga abin da ‘yan wasan suka fa ɗ i.

9.0 Sakamakon Bincike

Kamar yadda aka bayyana tun farko, nazarin ayyukan adabi ta amfani da ra’i wani sabon fage ne da bai da ɗ e da shigowa duniyar nazarin adabin Hausa ba. Kodayake wasu suna ganin cewa ra’o’in ba su dace da nazarin adabin Hausa ba, amma kuma ko daga wannan nazarin za a iya fahimtar cewa ana iya ɗ aukar ra’i a yi nazarin aikin adabi kuma a samu sakamakon da ake bu ƙ ata.

Daga cikin abin da wannan nazari ya gano shi ne, za a iya ɗ aukar ra’i a yi nazarin aikin adabi da shi kamar dai yadda aka yi amfani da shi a wannan nazarin.

Haka kuma nazarin ya gano cewa akwai ayyukan adabi da dama ba a wasan kwaikwayo ka ɗ ai ba wa ɗ anda za a iya ɗ ora su bisa ra’in Mararanci kuma su zauna daram a yi nazarin su.

10.0 Kammalawa

Wannan takarda ta shafi rubutaccen wasan kwaikwayo ne, inda aka za ɓ i littafin Soyayya Ta Fi Ku ɗ i aka yi nazarin sa bisa ra’in Mararanci. Tun da farko an fara kawo ma’anar wasan kwaikwayo da samuwar rubutaccen wasan kwaikwayo a ta ƙ aice. Sannan aka kawo bayani kan ra’i da samuwarsa a duniya, daga bisani kuma aka kawo bayani kan samuwar ra’in Mararanci da bayanin manufofinsa. An kuma yi nazarin wasan ne ta hanyar bin manufofin ra’in ɗ aya bayan ɗ aya ana danganta su da sassan wasan tun daga farko har z uwa ƙ arshe.

Manazarta                               

Ahmad, U.B. (1985). Nau’o’in Wasannin Kwaikwayon Hausawa . Zaria: Ahmadu Bello Press

Aliyu, A. (2021) . Ra’in Zahiranci: Nazari Daga Wasan Kalankuwa da Littafin Da ƙ i ƙ a Talatin. Aikin da aka gabatar a ajin masu neman digiri na Uku. A kwas ɗ in NLH 9308- Hausa Advanced Dramatic Composition. Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua, Katsina.

 

Aliyu, A. (2021). Akwai Shigar Giza-gizai Masu Duhun Gaske Dangane da Rabe-Raben Wasan Kwaikwayo a Duniya: Bi Diddi ƙ in Wannan Zance Dangane da Rabe-Raben Wasan Kwaikwayo a Hausa. Aikin da aka gabatar a ajin masu neman digiri na Uku. A kwas ɗ in NLH 9308- Hausa Advanced Dramatic Composition. Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Umaru Musa ‘Yar’adua, Katsina.

Alkanci, H. A . (1982) Soyayya Ta Fi Ku ɗ i . Zaria: NNPC

Barry, P. (2002) . Beginning Theory : An Introduction to Literary and Cultural Theory. U.K: Manchester University Press.

CNHN (2006) Ƙ amusun Hausa na Jami ar Bayero . Zaria: Ahmadu Bello University Press.

Crow, B. (1983). Stud y ing Drama , Nigeria, Longman.

 

Ɗ angambo, A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmanci n sa ga Rayuwar Hausawa.

Ma ɗ aba ar Kamfanin Triumph Gidan Sa adu Zungur, Kano.

 

Ɗ angambo, A. (2008) . Mata a Adabin Zamani, Nazari Kan Wasu Litattafan Ƙ agaggun Labarai n a Hausa Ci kin Mujallar Cibiyar Nazarin Harshe da Al’ada da Adabi .

Gusau, S.M. (2008) . Dabarun Na zarin Adabin Hausa , Kano: Benchmark Publishers Limited

Kofoworola, E. O. (1978). A Comparative Analysis of the Development of Drama in Kaduna   State and in Medieval and Early Renaissance Europe. Unpublished M.A. Thesis. Zaria:  Department Of Theatre and Performing Art. Ahmadu Bello University.


Malumfashi, I . A. M. (1990). Madubi Ɗ aya Fuska Biyu: Nazari da Sharhi kan Rubutattun  Wasannin Kwaikwayon Hausa. Sokoto : Takardar da aka gabatar a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo.

Mustapha, S. (2013) . Tasirin Mazhabobin Adabi Kan Tarken Adabin Hausa. Kundin Digiri Na Uku, Kano: Jami’ar Bayero.

Sambo, A. (2012). Sake Leka Rabe- ra ben Wasan Kwaikwayon Hausa. A cikin Amfani, (ed)

       Champion Of Hausa Cikin Hausa: A Festschrift in Honour Of Dalhatu Muhammad. Zaria: Ahmadu Bello University Press.

 

Umar, A. U. (2020) . Wasannin Kwaikwayon Hausa: Tushensa da Kashe-Kashensa da Kuma Muhimmancinsa. A cikin Hausa Drama, Films and Popular Culture in the 21st Century. Malumfashi da wasu (Ed). Kaduna: Gakuwa Publication.

      

Yar’aduwa, T.M. (2007). Wasan Kwaikwayo na Hausa, Nau’o’insa da Sigoginsa. Kano:

       Benchmark Publishers Limited, Nigeria.

Post a Comment

0 Comments