Ticker

6/recent/ticker-posts

Tsare-Tsare a Shirin Gabatar Da Finafinan Hausa

Citation: Gandu, I.M. (2024). Tsare-Tsare a Shirin Gabatar Da Finafinan Hausa. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, 3(1), 308-314. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.035.

Tsare-Tsare a Shirin Gabatar Da Finafinan Hausa

Daga

Dr Ibrahim Mohammed Gandu
Department of Hausa , Federal College of Education, Kano
Gmail: imgandu0907@gmail.com
Phone No.: 07038520993

Tsakure

Shirya fim babban aiki ne wanda duk mutumin da yake da sha’awar ɗ aukar nauyinsa yake fuskanta. Bayanai a kan yadda shirya fim, yana bu ƙ atar bin wasu matakai da tsare-tsare kafin a kai ga tabbatar gundarin shirin cikin faifai zuwa ga masu kallo. Gabatar da shirya fim yana bu ƙ atar ayyukan ƙ wararrun mutane, masu hikima da basira, kuma wa ɗ anda za su sa ido don ganin an gudanar da aikin da aka sa a gaba. Samar da ingantaccen labari wanda za a iya gabatar da shi a matsayin fim, shi ne mataki na farko. Marubucin labari kan yi tunani n irin abubuwa da ke faruwa a cikin al’umma, wa ɗ anda ake son a nuna domin su fa ɗ akar da al’umma; tare da yin hannunka-mai-sanda zuwa gare su. Dalili na neman samun ingantacciyar al’umma ne yake haifar da tunanin tsara labari wanda zai fa ɗ akar ko ya wa’azantar ko kuma ya ilmantar. An gudanar da wannan nazari ne bisa manufar fito da hanyoyin da masu shirya finafinan Hausa suke bi wajen lura da ƙ a’ i dojin shirin fim. Kazalika, an yi amfani da wasu hanyoyi domin samun bayanai. An duba wasu ayyuka da suka gabata tare da tattaunawa da wasu nmasu ruwa-da-tsaki a harkar shirin finafinai. An le ƙ a zaurukan sada zumunci domin samo wasu bayanai kamar ; Google da Youtube da Wikipedia da Facebook da Opera da Acaemia. An ɗ ora wannan aikin nazari a kan Nazarin Ƙ wa ƙ waf da Ƙ wa ƙƙ wafi, masu ɗ auke da ma’anar ‘Content Analysis’ da ‘Close Reading’, haka kuma nazarin ya gano cewa, a harkar shirin finafinan Hausa, mafi yawanci ba su da takamaiman tsari na gudanarwa.

Gabatarwa

In da za a iya kwatanta fim da gangar jikin ɗ a n’ adam, da za a iya danganta furodusoshi a matsayin ƙ wa ƙ walwa, masu rubuta labara i da daraktoci a matsayin zuciya, sannan ‘yan wasa a matsayin idanuwa, masu harha ɗ a sauti kuma kunnuwa. Sauran masu kula da kayan shirye-shirye a m a tsayin la ɓɓ a masu fa ɗ ar labara i da ado. Wa ɗ annan ƙ usoshi a ƙ ir ƙ ir ƙ ar fim su ne kai na gangar jiki, wato tawagar gudanar da aiwatar da shirin fim. (htpps://infocusfilmschool.com/…).

Shirin fim mataki ne da ake bi wajen gabatar da shi a tsare. Bisa manufa aiwatar da shirin fim tsari ne na ɗ aukar ƙ ir ƙ irarren labari tare da juya shi zuwa hoto mai motsi ta gabatar da shi a tsarin fim na talabijin ko na silima; ko wanda za a na ɗ a a kaset-kaset domin nunawa ta majigi ko talabijin ko bidiyo ko fim ko dai duk wata kafa da za a iya amfani da hoto mai motsi domin a nuna shi. A yanzu lamarin ya ha ɗ a da kafafen sadarwa na zamani kamar zaurikan sada zumunta Instgram da Google da Youtube da Wikipedia da Facebook da Opera da Twitter wa ɗ anda ake gani ta hanyar amfani da yanar gizo.

Bitar wasu ayyuka

Masana da manazarta sun gudanar da ayyuka da suka ji ɓ inci shirya finafinai a Hausa. A inda kowane ya dube shi ta fuskoki daban-daban tare da ba shi ma'ana. Yar ’a dua (2007,p30), ya bayar da ma’anar fim da cewa, “fim wat a hikima ce ta hoto mai motsi da take ɗ auke da mutane, wato hotunansu maza ko mata, yara ko manya ko kuma ma wanin mutane, wanda aka ɗ auka ta hanyar yin amfani da na’urar ɗ aukar hoto ta musamman, tare da bai wa kowane mutanen damar tafiyar da wasu ayyuka ta fuskar kwaikwayo ko waninsa, a wani ɗ an lokaci da aka ke ɓ e. Wanda shi wasan kwaikwayo yana ɗ auke da wani sa ƙ o na musamman kan nisha ɗ i da garga ɗ i da wa’azi da soyayya da tarihi ko wanin haka zuwa ga al’ummar duniya”. A wani ƙ aulin kuma , Mukhtar, (2013), cewa ya yi, “kalmar fim kalma ce ta harshen Turanci wadda take nufin (Drama ko Play) wadda Hausawa suka are ta kuma suke amfani da ita a harshen Hausa; amma a harshen Hausa tana nufin wasan kwaikwayo”. Musa, (2008, p . 55) ya ce, kalmar fim asalinta Turanci ne, wato “film” aka Hausance ta. Jam’in wannan kalma shi ne finafinai. Kalmar fim sabon abu ne a wurin Hausawa, domin kuwa sun fi sanin wasan kwaikwayo kuma sun fi sabawa da shi”. Kalmar fim kamar yadda ma’anar t a ta nuna a cikin Ƙ amusun Hausa tana nufin “dodon ɗ aukar hoto ko hoton silima.” CNHN, (2006). Shi kuwa Sule, (2016), cewa ya yi, “kalmar fim tana da ala ƙ a da silima, idan aka danganta ta da kalma r Turanci ‘motion pictures’, ‘film’ ko ‘mo ɓ ies’. Wadda ma’anarsa a jimlace ita ce hotuna masu motsi”. Haka kuma an gudanar da bincike da ma ƙ alu da dama a kan shirin da suka danganci finafinan Hausa. Abbas (2008), ta gudanar da bincike a kan “Adon harshe a wa ƙ o ƙ in finafinan Hausa”. a inda nazarin ya lalubo yadda adon harshe yake sassar ƙ e a cikin wa ƙ o ƙ in finafinan Hausa. Inuwa (2009), ta yi nazari ne a kan “Kutsen al’adu a finafinan Hausa”. tare da kawo irin nau’o’in finafinan Hausa.

Shi kuwa Chamo (2012), ya yi ‘nazarin yadda ake amfani da harshe a finafinan Hausa’. A inda ya fito da ire-iren ta ɗ i da suke gudana a da, ta fuskar al’ada da suka ji ɓ inci kunya, wa ɗ anda a yanzu babu su saboda canzawar zamani. McCain (2014), ta gudanar da bincike a kan ‘al’amuran da suka ji ɓ inci siyasa a harkar gudanar da shirye-shiryen finafinan Hausa’. Ta yi nuni a kan irin rashin wayewa da masu shirya finafinan Hausa suk e da ita ta fuskar gudanar da shirin fim. Gandu (2006), ya gudanar da bincike a kan “ Tasirin ba ƙ in Al.adu a shirin finafinan Hausa”. A nazarin nasa ya gano cewa, akwai tarin al’adu na Turawa da Indiyawa wa ɗ anda suka yi tasiri a cikin finafinan Hausa. Mustafa (2021), ya gudanar da bincike a kan “Fassara a Fim”. Inda ya yi duba na tsanaki dangane da irin yadda ake fassara maganganun ‘yan wasa a cikin finafinai ta hanyar rubuta fassarar a ƙ asan fim a lokacin gabatar da shi. Adamu (2004), ya rubuta wata ma ƙ ala dangane da irin yadda ya kamata mai shirya fim ya gudanar da bincike a kowane irin shirin fim ɗ in d a ya ƙ uduri aniyar gudanarwa. Ya kawo bayanin irin abubuwan da za a auna a sikeli dangane da labarin da za a mayar da shi zuwa fim. Mohammed (2004), a cikin wannan takarda an yi ƙ o ƙ arin jawo hankalin masu shirya finafinan Hausa. Inda aka nuna bu ƙ atar da su ri ƙ a gudanar da bincike na matakin shirya fim kafin su kai ga gabatar da finafinansu. A cikin takardar Gandu (2010), ya yi nazari a kan ‘asalin wasan kwaikwaiyo da samuwar finafinan Hausa’. M a ƙ alar ta fito da irin gudunmawar da finafinan Hausa suke bayarwa dangane da ci gaban al’umm a; d a kuma irin ƙ alubalen da suke fuskanta.

Dangane da nazarin da muka gudanar daga bitar ayyukan da suka gabata ; b abu wani aiki wanda ya yi kama da irin wanda muka gabatar.

Ra’in Bincike

Masana da manazarta sun tofa albarkacin bakunansu dangane da ma’anar Ra’i a fagen yin tarke. Shu’aibu (2013), ya kawo bayanin “Ra’i a matsayin tunani ko jerin tunane-tunane wa ɗ anda aka shawarta cewa su ne su ke iya yin bayani a kan wani abu da ya faru ko zai faru”. Ado (2017,p34), ya ce, “Ra’i wani hasashe ne na ilimi, kuma ra’i ya na iya zama kamar wani mizani mai sanya a gane abubuwa n da ba a iya sanin tabbacinsu”. Ra’in nazarin ƙ wa ƙ waf da ƙ wa ƙƙ wafi ne aka ɗ ora wannan nazari a kai.

Ra’in nazarin ƙ wa ƙ waf ya da ɗ e, shekaru da dama ana amfani da shi. “Masana fassara da masu bincike a kan harsuna sun da ɗ e suna amfani da shi, domin fassara littattafan addini da sauran wa ɗ anda suka danganci al’amuran rayuwa domin a gano marubutansu da ingancinsu. Soriki (1937-41), Harold Lasswell (1938), Benard Berelson (1952), Bales (1952), Schneider da Dornbush (1958)”. Kriffendorp, (2004).

Dukkan wa ɗ annan masana sun gudanar da ayyukan nazari da bincike ta hanyoyi da dama wa ɗ anda suka yi amfani da wannan ra’i domin gudanar da ayyukansu. An yi amfani da wannan ra’i saboda dangantakar nazarin ta fuskar adabi, domin yana duba ne ta fuskar adabi ko na harshe wa ɗ anda suke a rubuce, ko abin da ake amfani da shi wajen hanyar sadarwa. Misali, kamar hotuna, murya ko kuma bidiyo da talabijin. “Wannan ra’i an ƙ ir ƙ iro shi ne a cikin ƙ arni na 20, a shekarar 1940. Daga cikin wa ɗ anda suka ƙ ir ƙ iro shi akwai ; I.A. Richards da William Empson da Reuben Brower Stanley Burnshaw Da R.P. Blackmur da Kenneth Bruke da sauran mabiyansu, (Klarer, 2004:312; Encarta Premium, 2009; Blamires, 1991:337). Wannan mazahaba ta faro ne daga Ingila, sannan ta ya ɗ u zuwa Amurka, da wasu ƙ asashen Turai kamar Faransa da Jamus. Har ta fantsama cikin duniyar tarken adabi”. (Shu’aibu, 2013,p43-44).

Tsarin Finafinan Hausa

Idan aka tashi bayani dangane da shirin fim, ana duba irin tawagar mutanen da ke gudanar da shirin ne. Inda a nan ne ake samun fannoni daga cikin tawagar da ke gudanar da ayyuka daban-daban, domin ganin an cimma burin samun aiwatar da ingantacce, kuma kar ɓ a ɓɓ en fim wanda jama’a za su yi na’am da shi.

Duk wani fim da ya kai ma ƙ ura wajen samun kyakkyawan shiri, dole ne ya kasance yana da babbar tawaga ta ma’aikata masu gudanarwa a fannoni daban-daban da suka danganci shirya shi. Olugbodi (2018:27), ya kawo bayani bisa wannan hujja ta samun babbar tawaga a ingantaccen fim da cewa, “ ƙ wararru a wannan fanni, kowanne yana ƙ o ƙ arin ganin ya gabatar da aikin da ya shafi ɓ angarensa, domin ganin an aiwatar da fim ɗ in ba tare da wani ya shiga aikin wani ba’.

Babbar tawagar ƙ wararru ta ƙ unshi:

a.      Furodusa

b.      Mataimakan Furodusa

c.       Darakta

d.     Mataimakan Darakta

e.      Manajan Shirin Fim

f.        Mai Kula da Sashen Ku ɗ i

g.      Mai Lura da Shirin

h.      Mai Gudanar da Shirin

Bayan wannan babbar tawaga ta gudanar da shirin fim. Honthaner (2010,p1).

Ya kawo bayanan sauran na wannan tawaga masu tallafa wa lura da sauran ayyuka da wa ɗ anda suka ha ɗ a da:

a.      Daraktoci (masu gayyatar ‘yan wasa)

b.      Manajoji (masu lura da wuraren gudanar da fim)

c.       Masu gudanarwa na fannin tafiye-tafiye

d.     Da sauran fannonin gudanarwa da suka danganci aiwatarwa. Hakazalika, akwai wasu ofisoshi na ha ɗ akar tawagar darakta.   A wannan tawaga ce ake samun sassan gudanarwa da suka ha ɗ a da:

e.      Sashen rubuta labari

f.        Sashen kula da wuri

g.      Sashen ɗ aukar hoto

h.      Sashen lura da sauti

i.        Sashen lura da haske

j.        Sashen lura da tsare-tsaren kayan kwalliya da kuma

k.      Sashen suturu. Honthaner (2010,p31-36).

Kowane daga cikin wa ɗ annan sassa yana da irin nasa ayyukan da zai gudanar domin ganin an sami nasarar shirya kowane irin fim da aka ƙ uduri niyyar gabatarwa.

Rubuta Labari (script)

Labarin fim tsararren rubutu ne mai ƙ unshe da duk wasu maganganu, da sauran nau’o’i da suke ƙ unshe da duk wata ƙ ai’ida ta fa ɗ ar labarai. Rubuta labari ba aiki ne mai sau ƙ i ba, domin yana ɗ aukar tsawon lokaci kuma yana bu ƙ atar mayar da hankali kafin a cimma manufar da aka ƙ uduri aniya.

Lokacin da tunanin rubuta labari ya zo a cikin zuciyar mutum, ba matsala ba ce a kowane irin labari da za a gabatar. Sai dai fito da manufar rubutun labarin shi ne babban aiki. Fahimtar ɓ oyayyun manufofi ko sa ƙ onnin da labaru ke ƙ unshe da su, tare da sanin inda labarin ya dosa ta fuskar kar ɓ uwa shi ne abin dubawa. Wannan yana taimakawa ta fuskar tsara labarin domin samun kar ɓ uwa daga al’umma. “Labari a kodayaushe bayani ne na irin al’amura ko abubuwa da kan faru a cikin al’umma, ko tunani na hasashen faruwar wani lamari; ko al’amuran da a zahiri sukan faru daga cikin mutane da al’amura na nisha ɗ antuwa”. Sule (2016, p6). Marubucin labari babban jigo ne a harkar wasan kwaikwayo, saboda tunaninsa ne ake gabatarwa ko nunawa a aikace. Manufar kowane irin wasa da aka gudanar ita ce sadar da sa ƙ onni ga masu kallo.

  Matakan Rubuta Labari

A zahiri yin ƙ o ƙ arin rubuta labari ko wasa ana ganin abu ne mai sau ƙ i. Saboda kowa yana ganin ya san harshen da ake amfani da shi wajen gabatar da wasanin cikin finafinai. Matsalar rubuta labarin fim ita ce, na ƙ altar finafinai da matakai da suke da bu ƙ atar a san su.

Da farko za a gabatar da ta ƙ aitaccen bayani a kan labarin fim ɗ in gaba ɗ aya, wanda zai kasance a cikin sakin layi da bai wuce ɗ aya ko biyu ba (ana kiran wannan tsari da ‘logline’ a Turance). Za a gabatar da bayani n da ya ƙ unshi ‘yan wasa da tsarin fim. Tilas ya kasance an samar da ‘yan wasa wa ɗ anda za su tallafa wa cimma manufar da aka ƙ udurci a gabatar a cikin shirin. Mataki na gaba shi ne, za a fitar da tsarin labarin gaba ɗ aya a kan takarda. A nan ne za a fitar da duk wani motsi da ake da bu ƙ atar ɗ an wasa zai yi, wato kashe-kashe na sina-sinai (scenes) a cikin fim ɗ in. A mataki na uku kuma za a tsara dukkanin fitowar da ‘yan wasa za su yi a kowane sin (scene). A fitar da irin kalaman da ake bu ƙ atar ‘yan wasa za su yi. Za a kuma fitar da duk irin tsarin tafiyar da fim ɗ in dangane da shigar ‘yan wasa”.

Mataki na hu ɗ u, bayan an tsara ‘yan wasa kowane da matsayinsa da irin rawar da zai taka, ana tsara dukkannin shiga da fita ta fim ɗ in. Daga nan sai a sake gabatar da rubuta cikakken labarin a cikin shiri mai gamsarwa. Samu a kammala rubutun farko cikakke na tsarin labarin fim ɗ in ba ƙ aramar nasara ce ba. Domin tana ƙ unshe da ƙ alubale na bin dukkan irin ƙ a’idojin da aka bayyana kafin a cimma cikakken buri. Daga nan, za a bai wa masana domin su yi masa duba na tsanaki kuma su bayar da shawarwari. Wajibi ne a lura da irin shawarwarin, tare da kar ɓ ar gyararrakin da za su bayar da shawara a kai. Domin hakan yana ƙ ara ingancin labarin shirin da za a gabatar. Honthaner (2010, p79) .

Tunanin Marubucin Labari

Kowane fim da za a gabatar ya ta’alla ƙ a ne a kan warware tunanin da marubuci ya yi domin aiwatar da shi ta hanyar sama masa rai. Don haka samun nasarar labari ko tawayarsa tana tattare da marubuci. Matu ƙ ar marubuci bai rubuta abu mai ma’ana ba, tabbas furodusa da darakta da ‘yan wasa ɓ ata lokacinsu kawai za su yi. Don haka ya wajaba kowane furodusa ya sami mai rubuta masa labari da ya san abin da yake yi, kuma tilas shi da marubucin da wasu su zauna su karanta labarin su kuma auna shi a sikelin nazari.

Haka kuma akwai wasu dalilai da ake la’akari da su a lokacin da za a rubuta labari. Wa ɗ anda suka ha ɗ a da:

a.      Tunani a kan irin jinsin mutanen da za a gabatar da fim ɗ in zuwa gare su. Wa ɗ anda ka iya kasancewa maza ko mata, manya ko ƙ anana, samari ko ‘yan mata. Haka kuma ana gabatar da sa ƙ on fim zuwa ga hukumomi ko gwamnati ko kuma al’umma gaba ɗ aya.

b.      Akwai sa ƙ on fim da kan yi duba da irin gur ɓ acewar tarbiyya ko gyaran hali.

c.       Akwai na zamantakewar iyali, musamman lamuran da suka shafi zaman aure, da cin amana da zamba da dai makamantansu. (https://en.m.wikipedia.org/screemplay).

Marubucin labari yana yin la’akari da faruwar lamari gami da sauran fannoni da akan iya rubuta labari a kansu domin ya isar da sa ƙ o.

A wata tattaunawa da muka yi da wani mai ruwa da tsaki a gudanar da shirin fim (Kwabon Masoyi, 2020), ya ba da misalin wani fim mai suna ‘Halin Ɗ an ’a dam’ wanda mai ba da umarni Usman Adam ya gabatar. Ya bayyana cewa , “wannan fim ya samo asali ne daga wata wa ƙ a wadda wani mawa ƙ i Hamisu Breaker ya rera mai suna ‘ Ɗ an ’a dam’’. Bayan fahimtar wa ƙ ar ne dangane da irin sa ƙ onnin da ta ƙ unsa, sai ya ƙ ir ƙ iri labari, kuma ya ba wa wani marubuci mai suna Abba Harara ya zauna ya yi labarin kuma ya rubuta shi. Ya duba ya gyara ‘yan kurkuran da ya gani sannan aka gyara aka kuma tsara fim ɗ in”.

Akwai muhimman abubuwa da marubuci kan yi la’akari da su wajen ganin ba a samu na ƙ asu ba wajen aiwatar da wasan. Wa ɗ annan abubuwa sun ha ɗ a da; tabbatar da ganin cewa zaren tunani da aka gina labarin ya zama bai tsunke ko mur ɗ e ba. Sannan ya tabbatar da ɗ ora kowane ɗ an wasa a kan gurbin da ya dace da shi a cikin shirin. Sannan ya bayyana irin kalamai da ayyukan kowane ɗ an wasa; tare da yin nuni na lokaci da wuraren da suka dace a wasan. Wannan kuwa na faruwa ne a cikin tsarin rubuta wasan. Kwabon Masoyi (2020).

Bayan an gama tsara wasan a rubuce, za a la ƙ aba wa wasan ko fim take na musamman da zai zama sunan yanka. Wanda ya dace da sa ƙ o ko ma ƙ asudin rubuta labarin wasan. Sai a tsara labarin wasan ta sigar shiga-shiga da fitowa-fitowa. Sannan a tsara ‘yan wasa da irin kalaman kowanensu ko ayyukansu kamar yadda aka ambata a sama. Haka nan kuma marubucin zai zama mai shiryawa, ko mai taimakawa ga mashiryin wasan. Ta hanyar bayyana kayayyakin da za a bu ƙ ata da lokuta ko wuraren aiwatar da gudanar da shirin. Don haka ne za a iya cewa marubuci yana taka rawar da ta dace da shi wajen samun nasarar aiwatar da shirin fim. Labarin shirin fim tsararren rubutu ne wanda yake ƙ unshe da tsarin fitowar ‘yan wasa, da maganganunsu da irin motsi da ake da bu ƙ ata daga gare su. Wani lokaci ma tsarin rubutun labarin yana fitar da duk wani tsari na gudanar da ɗ aukar hotuna a cikin shirin. A ta ƙ aice dai kusan komai da ake bu ƙ ata da ya zama a cikin tsarin shirin ana fito da shi fili ƙ arara.

Tsare-Tsare Kafin Gabatarwa (Pre-production)

Wannan shi ne matakin farko a shirin gabatar da tsarin fim. A nan ne ake tara dukkan tunani na abubuwan da ake da bu ƙ ata, mataki ne na tsarawa a kan shirin da za a gabatar. Bayan haka akwai ɓ angarori guda uku a tsarin gabatar da fim. Na farko shi ne (pre-production), sai gabatar da shiri, wato (production), da kuma tsarin kamm a l u war shiri wato (post production).

A gabatar da shirin fim, tsarin tanade-taneden kayan aiki wato (pre-production) yana farawa ne da zarar an haska fitilar gabatar da shirin.   A wannan mataki ne ake ƙ ar ƙ are duk wani tanadi da ake da bu ƙ ata na aiwatar da shirin.

Za a tabbatar da ƙ iyasin adadin kasafi na irin ku ɗ in da za a bu ƙ ata, sannan a tantance irin tawagar da za a nema domin gabatar da shirin, wato darakta da masu ɗ aukar hotuna. Da zarar an kammala da wannan ɓ angare na tanadar kayayyakin aiki, kuma komai ya tabbata daga ɓ angaren masu ɗ aukar nauyi da kuma ruwa-da-tsaki sai a tunkari aikin gadan-gadan. Ana tantance kammaluwar samar da duk abubuwan ɓ u ƙ ata, musamman kayayyakin da ‘yan wasa suke da bu ƙ ata da zai fito da irin shigar da ake son a gan su a cikinta. Ana tsara tanadar ɗ aukar hayar kayan aiki da za a bu ƙ ata a lokacin gudanar da shirin. Za a tsara ranar da za a fara ɗ au ƙ ar shiri da tsarin biyan ku ɗ in ma’aikata da ‘yan wasa da dai sauran tsare-tsare. (https://en.m.wikipedia.org/wiki/pre-production).

Shirin fim na tabbata ne bayan ɓ angaren tsare-tsare sun kammala dukkan tanade-tanaden ayyukansu, na samar da wuri da sauran abubuwan bu ƙ ata domin gudanar da shirin. Tabbatar samar da ingantaccen wuri da ya dace a gudanar da shirin fim, shi ne yake bayar da damar gabatar da kyakkyawa kuma ingantaccen fim ga masu kallo. Hakazalika, wannan na faruwa ne a lokacin da aka sami wanda ya san yadda zai iya daidaita tunanin marubucin labarin fim, gami da hangen tunanin mai gabatar da shirin. Sannan da tunani kan bu ƙ atuwa ta irin ku ɗ in da za a kashe lokacin gudanar da shirin gami da sauran abubuwan bu ƙ atu.

Wurin Ɗ aukar Shiri (location)

Abu na farko da ake bu ƙ ata dangane da samar da wurin da za a gabatar da shirin fim shi ne, karantar labari tare da tattaunawa game da irin wuraren da suka dace a ɗ auki shirin fim ɗ in. Wannan kuwa na samuwa ne ta hanyar gamayyar kamfanin da zai shirya fim ɗ in, da mai ɗ aukar nauyin shirya fim tare da mai gabatar da shirin fim da sauran tawagar da za su tallafawa gudanar da shirin. (https://en.m.wikipedia.org/filming-location).

Watau dai , dole ne a sami amincewar furodusan shiri gami da darakta. Wannan na faruwa ne domin kauce wa sa ɓ ani a kan gabatar da shirin ta fuskar rarrabuwar ra’ayi. Wannan shi yake ba wa manajan gudanar da tsare-tsaren wurin shirya fim haske dangane da inda aka fuskanta game da shirin.

Da zarar an sami amincewa dangane da tattauna yadda za a gudanar da shirin, a nan ne, ake tabbatar da wuraren da za a ɗ auki hoton shirin. A nan za a yi tunanin abin da za a kashe, tsawon lokaci da shirin zai ɗ auka gami da ma’aikatan da za a bu ƙ ata yayin gudanar da shirin. A nan ake ƙ iyasin nawa za a kashe wurin ɗ aukar shiri da wuraren ɗ aukar shiri. Akwai tunani na bu ƙ atar jami’ai domin tallafawa samun nasarar gudanar da shirin idan bu ƙ atar hakan ta faru. Kamar jami’an ‘yan s anda ko jami’an kashe wuta a wuraren da za a bu ƙ aci amfani da su. Sannan da irin abin da za a kashe na ku ɗ i a kansu. Honthaner (2010,p3).

Sannan, dangane da wuraren da za a ɗ auki shirin; akwai wuraren da sai an nemi izinin mazauna wurin, idan ya kasance ba bu ɗ a ɗɗ en wurin da kowa ka iya shiga a duk lokacin da ya so ba ne. Akwai wurare da ba sa bu ƙ atar hayaniya, watau ke ɓ a ɓɓ un wurare, wurin da dole ana bu ƙ atar amincewar masu muhallin. Akwai la’akari da irin abubuwan da za a yi amfani da su a wuraren, wa ɗ anda tilas sai da amincewar hukuma da mazauna wuraren; kamar idan akwai sarrafa abu mai sauti ko ƙ ara da suka ha ɗ a da harbe-harbe saboda tsoro. Ko kafe-kafen alamomi da wuraren ajiye ababen hawa na jami’an gudanar da shiri da dai sauran muhimman al’amura. Duk wa ɗ annan suna da bu ƙ atar tattaunawa domin tabbatar da gudanar shirin fim a wuraren da aka ware cikin nasara.

A harkar gudanar da shirin fim a finafinan Hausa, mafi yawanci ba su da takamaiman tsari na gudanarwa a inda za ka sami tawaga ta musamman da za su gudanar da tsare-tsare. Da yawa babu maganar neman ƙ wararren mai gabatar da shiri saboda matsalar ku ɗ i, ko don neman sau ƙ i na kashe ku ɗ i a lokacin da ake aiwatar da shirin fim. Sannan, ragowar tsare-tsare na neman wurin da za a gudanar da shirin shi ma babu wani ingantaccen tsari na bin dukkan ƙ a’idojin da suka shafi neman wurin aiwatar da shirin fim. Suna neman mutumin da yake kamar dillali ne mai nemo wuraren da za a shirya fim, wanda yake kamar wannan ɓ angare aikinsa ne. Kasancewar wasu finafinan ba sa bu ƙ atar kashe ku ɗ i da yawa, a irin wannan ba a shan wuya wurin nemo wuri. Amma wanda labarin shirin yake da bu ƙ atar manyan wurare, a nan ne ake da tunanin kashe ku ɗ i da yawa. Domin a nan ne ake da bu ƙ atar manyan wurare. Sai dai kuma a mafi yawan lokuta wasu wuraren ba sa dacewa da irin muhallin isar da sa ƙ on shirin.

Sakamakon Bincike

A dun ƙ ule wannan nazari ya gano cewa, masu gudanar da shirin finafinan Hausa, mafi yawanci ba su da takamaiman tsari na gudanarwa. Ma’ana, babu cikakkiyar tawaga da za su gudanar da tsare-tsaren. Da yawa babu neman ƙ wararren mai gabatar da shiri. Saboda matsalar ku ɗ i ko don neman sau ƙ i na kashe ku ɗ i a lokacin da ake aiwatar da ɗ aukar shirin fim ɗ in. Sannan ragowar tsare-tsare na neman wurin da za a gudanar da shirin, shi ma babu wani ingantaccen tsari na bin dukkan ƙ a’idojin da suka shafi neman wurin aiwatar da ɗ aukar shirin.

Kammalawa

Wannan ma ƙ ala tana ƙ unshe ne da bayanai wa ɗ anda suka danganci shirin aiwatar da finafinai a Hausa. Bayan bayanin gabatarwa, ma ƙ alar tana ƙ unshe da bayanai da suka danganci gabatar da finafinai a Hausa. Akwai bayanai da suka shafi rubuta labarin shirin fim da kuma bayanai na tunanin marubucin labarin dangane da irin matsalar da ya duba a cikin al’umma, wadda ita ce dalilinsa na rubuta labarin. Bayan an ka m mala rubuta labarin da fim ɗ in zai isar da sa ƙ onsa a kai, sai kuma bayanin tanadin gabatar da shirin a zahiri. Akwai bayanan da suka danganci tanadar wuraren da a gudanar da shirin fim ɗ in (locations). Daga ƙ arshe an kawo bayanan ma’anar wasu kalmomi da aka yi amfani da su a cikin ma ƙ alar.

Bayanan wasu kalmomi

1.                   

Aiwatar da shirin fim

Production

2.                   

Finafinan Hausa

Kannywood films

3.                   

Gabatar da labarin fim a taka ƙ aice

Logline

4.                   

Labarin fim

Script

5.                   

Tsare-tsare kafin gabatar da shiri fim

Pre-production

6.                   

Tsarin kammala gabatar da shiri

Post-production

7.                   

Sina-sinai

Scenes

8.                   

Wuraren ɗ aukar shirin fim

Locations

  Manazarta

Abbas, U.A. (2008). “Sassar ƙ uwar Adabi Cikin Adabi: NazarinAdon Harshe A Wa ƙ o ƙ in Finafinan Hausa” Kundin Digiri n a Uku. Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

Adamu, Y.M. (2004). Muhimmancin Bincike a Shirin Fim. A Cikin Adamu A.U,, Jibril,   U.F., (Ed) Centre for Hausa Studies. P462.

Ado, A. (2017).Ra’o’inBincike Kan Al’adun Hausawa. Katsina-Nigeria : Kanki Classical Media Enterprises.

Adamu, Y. M. (2004). Muhimmancin Bincike a Shirin Fim. In Adamu A.U., Adamu Y.M., Jibril, U.F. (Ed). Centre for Hausa Studies. Pp. 462.

Chamo, I.Y. (2012). “The Changing Code ot Communication in Hausa Fiilm”. Doctoral Dissertation. Facultyof Oriental Studies, Uni v ersity of Warsaw Poland.

CNHN, (2006). Ƙ amusun Hausa na Jami’ar Bayero . Zaria: ABU Press .

Gandu, I.M. (2006). “Tasirin Finafinan Indiya a kan na Hausa”. Kundin Digiri n a Biyu. Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya. Jami’ar Usmanu Ɗ anfodio. Sokoto.

Gandu, I.M. (2010). Matsayin Adabi d a Ci Gaban Al’umma: Gudunmawar Finafinan Hausa. WAZOBIA: A Journal of Hausa Department. FCE: Kano. V ol.5 No. 1.Pp255-263.

Gandu, I. M. (2023)  “Nazarin Matakan Shirya Fim a Masana’antar Kannywood”.Doctoral Dissertation. Department of Nigerian Languages. Umaru Musa Yar ’a dua Uni v ersity, Katsina.

Honthaner, E.L. (2010). The Complete Film Production Handbook (Fourth Edition). Elserier INC. UK: O x ford.

Inuwa, U.A. (2009). ”Kutsen Al’adu Cikin Finafinan Hausa”. Kundin Digiri n a Uku. Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya. Jami’ar Bayero: Kano.

Kriffendorp, K. (2004). Content Analysis: An Introduction to its Methodology. 2nd Edition. USA: Sage Publications Inc. Uni v ersity Press.

McCain, C.R. (2014). “The Politics of E x posure: Contested Cosmopolitanism: Re v elation of Secrets and Intermedial Refle x i x ity in Hausa Popular E x pression”. Doctoral Dissertation. Uni v ersity of Wisconsin Madison.

Muhammad,A. (2004). In Adamu Y.M., Jibril, U.F. (Ed). The Need of Research in Hausa V ideo Film Production. (297). Kano Centre for Hausa Studies.

Musa. B.K. (2016), “Tranformation in the Production and Consumption Strategies of Hausa V ideo Films 1990-2014”. Doctoral Dissertation. Department of Mass Communication. Bayero Uni v ersity: Kano .

Musa, A. (2008). Tasirin Niganci A Finafinan Hausa. Harsunan Nijeriya V ol. XX I (Pp. 55-62).

Olugbodi, Y. (2018). About V ideo Production (Directing). Benue: SE V AGE, Publishers.

Shu”aibu, M. (2013).”Tasirin Mazahabobin Adabi Kan Tarken Adabin Hausa”. Kundin Digiri n a Uku. Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya. Jami’ar Bayero : Kano.

Sule, B. (2016). Rubutun Fim. Kano : Gidan Dabino Publishers .

Yar’adua, T.M. (2007). Wasannin Kwaikwayo Na Hausa. nau’o’insu da Sigoginsu. Kano: Usmaan AL-Amin Publishing Company.

Yanar Gizo

https;//en.m.wikipedia.org/wiki/screenplay

https:/en.m.wikipedia.org/wiki/filmmaking

https;//en.m.wikipedia.org/wiki/filming-location

https;//en.m.wikipedia.org/wiki/pre-production

https://indiefilmhusle.com/5-stages-indie-film/production/

https://getinmedia.com/career/script-super v ision

Post a Comment

0 Comments