Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazarin Wasu Waibuwar Masunta

Shehu, M. (2024). Nazarin Wasu Waibuwar Masunta. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, 3(1), 302-307. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.034.

Nazarin Wasu Waibuwar Masunta

By

Dr. Musa Shehu
Department of Nigerian Languages,
Usmanu Danfodiyo University, Sakoto , Nigeria
07031319454
yawuri3327@gmail.com

Abstract

Fishing has long been a revered traditional occupation within Hausa society, dating back to ancient times. This paper, titled "The Fishermen's Magic and Wonders," aims to analyze the magical and extraordinary practices exhibited by fishermen in Hausa society during traditional ceremonies, special occasions, or in times of dire predicament. Given the inherent risks and dangers associated with fishing, fishermen have historically sought precautions and protections against the hazards they encounter in rivers. This necessity has rendered them deeply knowledgeable and vigilant in all activities related to water. Additionally, they offer specialized treatments or remedies to individuals afflicted by waterborne diseases or injuries sustained from encounters with dangerous aquatic animals.

1.0 Gabatarwa

Sana’ar su tana ɗ aya daga cikin manyan sana’o’in Hausawa na gargajiya da suke gudanarwa a lokaci mai tsawo da ya gabata. Sana’a ce da ta ƙ unshi yin ta’ammuli da ruwa. Wannan ya sa duk wurin da ruwa ke taruwa masu yawa ko wurin da ruwa ya ratsa a nan ake gudanar da wannan sana’a. Akwai Hausawa da yawa a ƙ asar Hausa wa ɗ anda ba su da wata sana’ar da ta wuce su , ita ce hanyar neman abincinsu da kuma hanyar biyan sauran bu ƙ atun rayuwarsu ta yau da kullum. Samun irin wa ɗ annan sana’o’i ga Hausawa ya sa mutanen kowane sashe suka yi fice a kan abin dogaro. Har ma sukan nuna buwaya da isa da mallakar sana’ar a wajen wani dandali na musamman. Ma ƙ asudin wannan nazari shi ne, za ƙ ulo irin waibuwar da masuntar ƙ asar Yauri kan nuna a wasu lokuta na musamman da kuma taimaka wa mutane da suke yi na samun waraka ga wasu matsalolin rayuwa na yau da kullum, domin nuna isa da buwaya da mallakar sana’ar. Wannan waibuwa da sukan nuna bai tsaya ga nisha ɗ antar da jama’a kawai ba, yakan taimaka ainun wajen ceto rayukan jama’a daga wasu masifu da kan tuzgo a rayuwa kamar matsalar ha ɗ arin jirgi a ruwa ko la ƙ ewar ƙ aya a wuya da makamantansu da dama. Irin waibuwar da masunta kan nuna a wasu lokuta ya sa mawa ƙ a da dama kan yi musu wa ƙ a tare da nuna buwayarsu a kan ruwa da halittun da ke ciki. Ga abin da wani mawa ƙ i mai suna Mansur Muhammadu Maidume ke cewa dangane da masunta:

Jagora: Ni kuma sai ka ban ƙ u ƙ uwa in noce

In tai ƙ asan Teku in yi ziyara

Sarkin ruwa Makwashe Argungu

........................................................

Don na iske dattijo Matanfada

Duba kada ya fito shan iska

Ya gaida manyansa ya gaishe mu

Sarkin ruwa Makwashe dattijo.

2.0 Su Wane Ne Masunta

Calvin (1991) ya bayyana ma’anar su da cewa “su (kamun kifi) wata farauta ce ta ruwa wadda ake yi domin a kama kifi da wasu halittun ruwa . [1] Alhassan da wasu (1982) cewa suka yi “su sana’a ce da ake shiga ruwa da hannu biyu ko da taru ko da koma da mamari ko ma da fatsa, don a kama kifi don a ci ko don a sayar. Sana’ar su sana’a ce da ake gudanarwa a cikin koguna da gulabe da tekuna a duk fa ɗ in duniya baki ɗ aya. Masunta kuwa mutane ne da sana’arsu ta danganci kamun kifi da sauran halittun ruwa. Masunta ba su da wata sana’a da ta wuce ta shiga ruwa, sai dai akan sam i ‘yan ƙ alilan da sukan ha ɗ a da noma wanda bai taka kara ya karya ba. Galibi akan kira masuntar ƙ asar Hausa da suna sarkawa. Sarkanci kuma sunan sana’arsu ta kamun kifi. [2] Dangane da asalin wannan sana’a a ƙ asar Hausa kuwa, wani ra’ayi ya nuna cewa, wasu mutane ne arna mabiya addinin Gundari wa ɗ anda suka fito daga ƙ asar Firzan tare da Muhammadu Kanta. Bayan da aka sauya hedikwatar Kabi daga Surame zuwa Birnin Kebbi, sai wani mutum da ake kira Magaji Alfa wanda ya fito daga ƙ asar Songai tare da jama’arsa ya shigo ƙ asar Kabi wa ɗ anda su ne a yanzu ake kira “Sarkawa”, kuma mabiya addinin Islama ne. A nan suka ci gaba da rayuwarsu tare da arnan da suka iske a wurin suna kamun kifi ba tare da tilasta musu musulunta ba. Ra’ayin ya ci gaba da cewa, kalmar “Sarkawa” wadda ake kiran masu sana’ar da ita ta samo asali ne daga kalmar “Sorko s ” wato sunan ƙ abilar da suka fito daga ƙ asar Songai suka zauna a ƙ asar Kabi, inda daga baya suka watsu a sassa daban-daban musamman a yankin arewa maso yammacin Nijeriya.Yau da gobe har kalmar ta koma Sarkawa a Hausance. Ra’ayin ya ƙ ara da cewa, wannan ƙ abila ta Sorko s su ne asalin Kabawa. Wato daga Sarkawa aka samu Kabawa. [3]

 Fitattun masuntar ƙ asar Yauri su ne Kabawa wa ɗ anda suka fito daga ƙ asar Argungu suka zauna ƙ asar ta Yauri domin ci gaba da sana’arsu ta gado (su). Sai kuma wasu ƙ ungiyar Hausawa da suka fito daga ƙ asar Taraba suka za ɓ i su zauna a ƙ asar ta Yauri, su ma don su ci gajiyar da ake iya samu a wannan ruwa na kwara. Wa ɗ annan Sarkawa ne (kabawa da ‘yan Taraba) suka shahara wajen kash e manyan dabbobin ruwa kamar su Dorina da Kada da Ayyu da makamantansu. Sauran sarkawan kuwa sun ta ƙ aita ne kawai ga kamun kifi manya da ƙ anana . [4]

3.0 Makaman Su (Kamun Kifi)

Kowace sana’ar Hausawa ta gargajiya akwai kayayyakin da akan tanada wa ɗ anda ake amfani da su domin samun sau ƙ in gudanar da sana’ar kamar yadda ya kamata. Haka ma masu sana’ar kamun kifi ba a bar su a baya ba wajen tanadar makamai ko kayayyakin da ake amfani da su wajen kamun kifi. Daga cikin makaman da ake amfani da su wajen su sun ha ɗ a da gwangu ko saran ɗ amba da dalan tcereke da ƙ awuri da taru da birgi da gura da ɗ ankara da mamari da ƙ ugiya da bilili da makamntansu. Kusan kowane daga cikin wa ɗ annan makamai da nau’in kifin da ake kamawa da shi. Akwai wanda kowane nau’in kifi ya ci karo da shi yana kamawa. Akwai kuma zago ko mashi wanda da shi ne ake kashe dorina ko kada da makamantansu. [5]

4.0 Amfanin Sana’ar Su/Masunta

Kamar yadda kowace sana’ar Hausawa ta gargajiya ke da ayyukan da take gudanarwa masu amfanin jama’a, masunta ma suna da irin nasu gudummuwa da suk e bayarwa na amfanin jama’ar da suke rayuwa a cikinta da suka ha ɗ a da:

a.      Samar da abinci ko maha ɗ in abinci (kifi) ga al’umma.

b.      Samar da magungunan waraka da kariya daga wasu cututtukan da kan dam i mutane, kamar maganin sanyi da maganin fitar da ƙ ayar kifi idan ta ma ƙ ale wa wani a wuya da sauransu.

c.       Samar da ayyukan yi ga sauran jama’a, kamar sana’ar bankwai da sana’ar ɗ anyen kifi da sayar da kayan kamun kifi da sauransu.

5.0 Waibuwar Masunta

Ƙ amusun Hausa na Jami’ar Bayero, Kano, an bayyana ma’anar waibuwa da yin wani abu wanda ya shallake tunanin mutane. [6] Waibuwa wata hanya ce da mutum ko wata halitta kan yi wani abu na ban mamaki kamar canzawa daga yanayin da aka san shi zuwa wani yanayi ko kuma ya   ɓ ace sam. [7] Kenan waibuwa na nufin nuna buwaya ko siddabaru ko sihiri a kan wani abu ko wata sana’a domin nuna isa da mallakar wannan abin ko sana’ar. Galibi waibuwa aiki ne na sihiri wanda ake ha ɗ awa da iskoki domin su biya wa ɗ an Adam wata bu ƙ ata, shi kuma ya ri ƙ a yi musu wata hidimar da suka bu ƙ ata. Masu gudanar da sana’o’in Hausawa na gargajiya musamman irin su ma ƙ era da manoma da wanzamai da mahauta, sukan nuna buwayarsu a fagen sana’arsu a wajen wani taro kamar bukin na ɗ in sarautunsu ko makamancinsa. Su ma masunta ba a bar su a baya ba wajen nuna irin nasu waibuwar da ta shafi sana’arsu ta su. Ana iya kallon wannan waibuwar masunta ta fuskoki daban-daban dangane da yadda suke aiwatar da su.

5.1 Ɗ aure Ruwa Da Kwance Shi

Wannan na daga cikin manya-manyan waibuwar da masunta kan nuna. Galibi sarkin ruwa ya fi aiwatar da irin wannan waibuwa na ɗ aure ruwa da kwance shi musamman a lokacin bukin kamun kifi. Yadda wannan waibuwa ke gudana shi ne, idan za a yi wani bukin kamun kifi, sarkin ruwa kan taho ya yi wasu ‘yan surkulle na tsafe-tsafe da ‘yan siddabaru kafin a fara su a cikin ruwan da za a gudanar da bukin. Sukan yi haka ne domin a ɗ aure duk wani mugun dabban ruwa da suka san zai iya cutar da masunta da kuma samun sa’ar kama kifi. Don haka, idan ya yi wannan ɗ aurin ruwa, duk wani mugun dabba kamar dorina da kada ko wani mugun kifi ba zai motsa a wannan lokacin ba idan an ci karo da shi. Idan aka ƙ are buki sai sarkin ruwa ya kwance ɗ aurin da ya yi domin samun walwala ga halittun ruwan da aka ɗ aure. Su ma ɗ ai ɗ aikun masunta suna da irin nasu waibuwa na ɗ aure ruwa idan za su fita su musamman ‘yan gora wa ɗ anda ke lalabe a ƙ asan ruwa. Yadda nasu ɗ aurin ruwan yake shi ne, duk wani abu mai rai da suka ta ɓ a ba zai motsa ba balle ya cutar da su. [8]

5.2 Kira

Idan aka ce kira ana nufin kamar a kira wani abu don ya zo a tattauna da shi ko a aike shi ko saboda wani dalili na musamman. Kira a sana’ar su yana daga cikin manya-manyan buwaya ko waibuwar da masunta kan nuna musamman idan rana ta   ɓ aci, ko wani halittan ruwa ya yi musu ba daidai ba. A nan, za a kira wata dabban ruwa ne ta fito da kanta daga cikin ruwa zuwa bakin ganga ta kwanta sai yadda aka ga dama aka yi da ta. An nuna misalin wannan ya ta ɓ a faruwa a wani ƙ auyen Yauri, inda wani kada ya kama ɗ an wani basarke a bakin K uwara. A nan ne mahaifin yaron (basarke) ya nuna irin nasu waibuwa na sarkawa, ya zo bakin Kuw aran ya yi sihirce-sihircensu na masunta. Daga nan ya fara kiran kadoji ɗ aya bayan ɗ aya suna fitowa daga cikin ruwa suna zuwa ganga suna kwantawa, har wanda ya kama ɗ ansa ya fito sai ya sa zago (mashin ruwa) ya soke shi, nan take shi ma kadan ya mutu. [9]

5.3 Kirari

Kirari a nan yana nufin a wasa makami don ya shiga jikin dabba ba tare da an wahala ba. Wannan wata waibuwa ce da masunta kan nuna musamman a lokacin da suka zo kashe manyan dabbobin ruwa kamar su k ada ko d orina. A lokacin da aka caka wa dabban zago ya ɗ an kama jikinsa ko yaya, daga nan za a fara yi wa zagon kirari yana shigewa jikin dabbar har sai zagon ya ci ƙ arfin dabbar saannan a koma gefe ana kallonta. Sai dai abin lura a nan shi ne, kirarin da ake yi wa zagon ba kirari ne wanda aka saba da shi kamar wanda ake yi wa mutane ba. Kirari ne na surkulle wanda ba a iya fahimtar abin da ake fa ɗ i kai tsaye. [10]

5.4 Su (Kamun Kifi) Bisa Fa ƙ o

Wani waibuwa ne da masunta kan nuna musamman a lokacin wani ƙ asaitaccen buki kamar bukin na ɗ in sarkin ruwa ko sarkin gari gaba ɗ aya. Masunta za su sa homa ne a fa ƙ o jama’a sun taru suna kallo, sai kawai a ɗ ago homan sai a gan shi cike da kifaye masu rai tamkar dai yadda ake yi a cikin ruwa. An nuna irin haka ya ta ɓ a faruwa a lokacin na ɗ in Sarkin Yauri Abduulahi mahaifin Sarkin Yauri Dr. Zayyanu Abdullahi wanda ke mulki a yau. [11]

5.5 Baduhun Ruwa

Baduhu wani magani ne da ake yi na tsafi ta fuskar amfani da tayin dabbobi, da kyanwar da ba ta bu ɗ e ido ba, da suturar makaho ko makauniya.(Bunza 2006). Mai baduhu yakan   ɓ ace ga ganin mutane gaba ɗ aya, ko da ga shi ga su yana magana ana jin sa. Ba kowane masunci ke da baduhun ruwa ba, sai wa ɗ anda suka shahara wajen kashin dorina ko kada ko ayyu da makamantansu. Baduhun ruwa baduhu ne da ake yi a lokacin da aka zo kashe wani mugun dabban ruwa. Sau da yawa idan aka zo kashe dorina ko bayan an daka mata zago, takan yun ƙ uro ta nufo mutum da nufin kashe shi, to a wannan lokacin ne baduhun ruwa yakan yi aiki ta hanyar   ɓ acewa ga barin ganin dabban ruwan. Wato da ta yun ƙ uro ba za ta ga mutum ba sai dai ta yi ta haukarta har dafin zago ya kama ta , ta gaji ta mi ƙ a wuya. [12]

5.6 Basanyi

Basanyi wani sihiri ne da ake yi na karya lagon abokin fa ɗ a. ‘Yan dambe da ‘yan kokuwa da maharba da maya ƙ a su suka fi amfani da basanyi. Abin da basanyi ke yi shi ne, ya saka wa jikin abokin adawa sanyi, jikinsa ya yi la’asar, ya ji ba shi da sauran kuzari ga ga ɓ ɓ ansa da tsokokinsa. Bahaushe ya yi imani da samuwar basanyi, kuma yana ganin da jinin ɗ an Adam da fitsarinsa ko kashinsa ake ha ɗ a shi. (Bunza 2006). Basanyin masunta ba ga mutane yake aiki ba, yana aiki ne a lokacin da masunci ya nuta cikin ruwa wajen lalaben kifi. Duk kifin da ya ta ɓ a ba zai motsa ba sai an jefa shi cikin gora sa’annan ya yi motsi. Haka ma duk wata dabban ruwa da aka ci karo da ita aka ta ɓ a ta cikin rashin sani ko ma ana sane, ba zata motsa ba balle ta cutar da mutum. [13]

5.7 Nuta

 Nuta na nufin shiga cikin ruwa a nutse ƙ asa ga barin ganin mutane. Sau da yawa masunta kan nuna wata waibuwa ta hanyar nuta cikin ruwa musamman idan an samu ha ɗ arin jirgin ruwa mutane suka nutse a ciki ko wasu kaya. A irin wannan yanayi, masunta sukan nuta cikin ruwa na ƙ imanin awa ɗ aya suna neman gawar mutum ba tare da sun taso sun nunfasa ba. A wasu lokuta har gasa ma akan yi na nuta a lokacin wasannin bukin kamun kifi musamman na Argungu domin a ga wanda zai fi da ɗ ewa idan aka yi nuta. [14]

5.8 Gyandi/Gindi

 Gyandi kalma ce da ke nufin wasu addu’o’i na gargajiya da masunta ke yi ta hanyar furta maganganu da sassar ƙ a su, suna kuma sauka ɗ aya bayan ɗ aya cikin sauri, sai dai babu wata ma’ana da mai sauraro zai iya kamawa balle ya ƙ arar. Gyandi tamkar surkulle ne wajen ƙ umshiya da yadda ake sarrafa shi, sai dai yana iya kasancewa a bayyane ko a asirce. Masunta sukan sarrafa gyandi gwargwadon irin waibuwar da suke son nunawa. Ga dai yadda suke sarrafa shi kamar haka :

 Idan ƙ aya ta ma ƙ ale wa mutum a wuya aka yi juyin duniya ta ƙ i wucewa, da zaran suka yi gyandi a ruwa aka ba mutum ya sha sai dai wata ƙ ayar ba wannan ba. Wannan ya faru ga wata mata da ƙ aya ta kama ta a wuya har aka tafi asibiti amma abin ya faskara. Da aka kai ta wani ƙ auye da ake kira “Bunzawa” wajen wani masunci ya yi gyandi a ruwa ya ba ta ta sha, kafin ka ce kwabo ba ƙ aya ba labarinta.

 Haka ma wasu masunta suna i ƙ irarin cewa, idan mutum ya mutu a ruwa matu ƙ ar ba a yi masa kuka ba kuma bai yi amai a ciki ba, ko shakka babu rayuwarsa za ta dawo idan aka yi masa gyandi. Wannan ma ya sha faruwa ba sau ɗ aya ba. Haka kuma za a iya ɗ ebo ruwa a kwanu ko a wani abu a tofa gyandi a ciki, sai a rufe da ƙ yalle. Da zaran aka bu ɗ e za a ga kifaye masu rai da lafiya suna yawo a ciki.

 Akwai wani gyandi da ake yi domin a hana mutum shan ruwa, ko a hana shi ha ɗ iye yawu. Wannan yakan faru ne idan ana wasannin raha tsakanin masunta da mahauta. A duk lokacin da mutum ya ɗ auko ruwa zai sha sai kawai ya ga ƙ ananan kifaye na yawo a ciki, tilas ya fasa shan ruwan. [15]

6.0 Sakamakon Bincike

Bisa bayanai da misalan da aka gabatar, za a iya fahimtar cewa, wannan bincike ya samu nasarar gano abubuwa da dama da suka shafi masunta da waibuwar da suke da ita ga sana’arsu ta su. Daga cikin abububwan da binciken ya gano akwai cewa:

a.      Yadda masu sana’o’in gargajiya kamar ma ƙ era da mahauta da ma’aska da sauransu suke nuna isa da mallaka da buwaya a sana’o’insu na gado, su ma masunta suna da irin waibuwa da isa da mallaka ga abin da ya shafi ruwa da halittun da ke cikinsa.

b.      Haka ma binciken ya gano cewa, masunta na da irin nasu gudummuwa da suke bayarwa ga al’umma da ta shafi magungunan waraka, kamar tayar da wanda ya mutu a cikin ruwa matu ƙ ar ba a yi masa kuka ba, da fitar da ƙ ayar kifi a wuyan mutum da maganin sanyi da sauransu.

c.       Har wa yau, binciken ya gano cewa, a yayin da wata dabbar ruwa ta addabi mutane, masunta su ke taimakawa wajen kawar da ita don samar da natsuwa da kwanciyar hankali ga jama’a.

7.0 Kammalawa

Ba da gaskiya da bugun gaba da Hausawa suka yi wa sana’o’insu na gargajiya, shi ya haifar da matsayi da ƙ imar da suke da shi a idon ma ƙ wabtansu na gida da ma sauran ƙ asashe na duniya. Wannan ne kuma ya ba su damar shiga da fita wajen ganin sun mallaki sana’o’in nasu ciki da wajensa. ƙ o ƙ arin yin hakan ne ya haifar da waibuwoyin da sukan nuna a lokuta daban-daban. Sai dai wani hanzari ba gudu ba, kusan mafi yawan abubuwan da aka bayyana a wannan nazari baya na waibuwa sun gushe ainun a sakamakon tasirin addinin musuluncia rayuwar masuntar.‘Yan ƙ alilan ne daga cikin ire-iren wa ɗ annan waibuwa suka saura da rayuwa musamman wa ɗ anda ke da alfanu ga jama’a, kamar gyandin da ake yi idan ƙ ayar kifi ta kama mutum da ire-irensu. Duk da yake cewa wani lokaci masuntan kan tayar da tuba idan rana ta   ɓ aci, ko wani ya ta ɓ a su, kamar dai yadda ya faru ga masuncin da kada ya kama ɗ ansa .

Manazarta

Argungu, I. A. (2007) “Samuwar Wa ƙ ada Kirari a cikin Bikin Kamun Kifi na Argungu” Kundin Digiri na Biyu, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗ anfodiyo.

Bawa, I. (2004) “Dabarun Kamun Kifia ƙ asar Argungu”. Kundin Digiri na Ɗ aya, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗ anfodiyo.

Bunza, A. M. (2006) Gadon Fe ɗ e Al’ada . Lagos: Tiwal Nigeria LimitedSurulere.

Garba, C. Y. (1991) Sana’o’in Gargajiyaa ƙ asar Hausa . Kaduna: BarakaPress Limited.

Harris, P. G. (1930) “Notes On Yauri” (Sokoto Province, Nigeria). The Journal of the Royal Anthropological Institute of Great Britain and Ireland Vol. XL

Harris P.G. (1942) The Kebbi Fishermen (Sokoto Province, Nigeria) . The Journal of the Royal Anthropological Institute of Great Britain and Ireland. Voloume 72.

Jelani A. (2005) “The Socio-Economic Development of Fishing in Yauri Emirate” B.A. Project, Department of History, Sokoto:Usmanu Ɗ anfodiyo University.

Ƙ amusun Hausa (2006) Wallafar Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya . Kano: Jami’ar Bayero .

Ƙ ofar Soro, S. S.(2007) “Dabbobin Ruwa a Idon Bahaushe”. Kundin Digirina Ɗ aya, Sakkwwato: Jami’ar Usmanu Ɗ anfodiyo.

Madabo, M. H. (1979) Ciniki da Sana’o’i a ƙ asar Hausa . Printed in Great Britain Thorbay Press Limited Rayleigh Essex.

Sanda, U. M. (1999) “Sana’ar Su a Madatsar RuwataKanji”. Kundin Digiri na Ɗ aya, Sakkwato: Jami’ar Usmanu Ɗ anfodiyo.

Yahaya, I. Y. (1992) Darussan Hausa Don Makarantun Sakandare . Ibadan: University Press.

Tattaunawa

Tattaunawa da Alhaji Usman, unguwar ‘yan Taraba a garin Yauri, a watan February, 2010.

Tattaunawa da Alhaji Ibrahim, unguwar ‘yan Taraba a garin Yauri, a watan February, 2010.

Tattaunawa da Ataka-sisi da abokansa a ƙ auyen Bunzawa na garin Yauri, a watan March, 2010.



[1] Garba, C. Y. (1991)Sana’o’in Gargajiya a Ƙ asar Hausa . Kaduna: Baraka Press Limited. Shafi na 12.

[2] Alhassan, da wasu. (1982) Zaman Hausawa Na Biyu. Zaria: NNPC. Shafi na 23.

[3] Harris, P. G.(1930) “Notes On Yauri” (Sokoto Province, Nigeria). The Journal od the Royal Anthropological Institute of Great Britain and Ireland Vol. XL shafi na 74.

[4] Dubi lamba ta 3 shafi na 72 domin ƙ sarin bayani

[5] Tattaunawa da Alhaji Usman, unguwar ‘yan Taraba a garin Yauri, a watan February, 2010.

[6] Ƙ amusun Hausa (2006) Wallafar Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano. Shafi na

[7] Argungu, I. A. (2007) “Samuwar Wa ƙ a da Kirari a C ikin Bikin Kamun Kifi na Argungu” na Argungu”, kuundin Digiri na Biyu, Sakkwato: Jami’ar Usmanu [anfodiyo. Shafi na 24.

[8] Tattaunawa da Ataka-sisi da abokansa a ƙ auyen Bunzawa na garin Yauri, a watan Maris na shekarar 2010.

[9] Tattaunawa da Alhaji Usman, unguwar ‘yan Taraba a garin Yauri, a watan Fabrairun shekarar 2010.

[10] Tattaunawa da Alhaji Ibrahim, mai ƙ imanin shekaru 62, a unguwar ‘yan Taraba a garin Yauri, a watan Fabrairun shekarar 2010.

[11] Tattaunawa da malam Umaru mai geme, mai ƙ imanin shekaru 65, a unguwar ‘yan Taraba a garin Yauri, a watan Maris na shekarar 2010.

[12] Dubi lamba ta 10 don ƙ arin bayani.

[13] Dubi lamba ta 11 domin ƙ arin bayani.

[14] Dubi lamba ta 9 domin ƙ arin bayani.

[15] Dubi lamba ta 7 domin ƙ arin bayani.

Post a Comment

0 Comments