Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazarin Tsarin Sauti a Wasu Zaurance Na Hausa

Citation: Abdullahi, M.S. (2024). Nazarin Tsarin Sauti a Wasu Zaurance Na Hausa. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, 3(1), 315-321. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.036.

Nazarin Tsarin Sauti a Wasu Zaurance N a Hausa

Muhammad Sulaiman Abdullahi
Sashen Koyar Da Harsunan Najeriya
Jami’ar Bayero, Kano
msabdullahi.hau@buk.edu.ng
+234 806 5846 225

Tsakure

Zaurance yana ɗ aya daga cikin azancin da harshen Hausa ya yi fice da su wanda matasa musamman mata suke amfani da shi wajen sakaya zance ta hanyar sauya masa wasu fitattun kamannin da aka san shi da su a harshe. Hikima ce da ɗ a ɗɗ iya a adabin al’ummar Hausawa wadda matasa suke amfani da ita a harshen Hausa domin isar da sa ƙ wanninsu ba tare da wata matsala ba. Azanci da hikimar z aurance suna da ala ƙ a da ilimin tasarifi da kuma ilimin tsarin sautin Hausa. Wannan takarda ta yi ƙ o ƙ arin bibiyar z aurance a al’adar Hausawa da kuma ala ƙ arsa da ilimin tsarin sautin Hausa. Takardar ta bayyana cewa lallai z aurance wata hikima ce ta harshe wadda harshen Hausa ya yi fice da ita. Kasacewar z aurance ya shafi adabin baka na Hausa kai tsaye, amma takardar ta fito da wasu muhimman lamuran tsarin sauti, kamar sa ɓ a ƙ a’idar tabbatattun ga ɓ o ɓ in kalmomin Hausa ta hanyar wasu ‘yan ƙ are- ƙ are da ake yi a kan ga ɓ o ɓ in a yayin samar da shi. Haka kuma, akwai alamar ƙ ara saurin magana, wadda takan taimaka wajen cikarsa.

Muhimman kalmomi : Zaurance, Tsarin Sauti, Azanci, Harshen Hausa

1.1 Harshen Hausa

Harshen Hausa ɗ aya ne daga cikin muhimman harsunan da ake sadarwa da su a fa ɗ in duniya, musamman a nahiyar Afirka. Harshe ne na kasuwanci da ilimi da fasaha, wanda ya ƙ unshi fasahohi da dama da rubuce-rubuce da yawa wa ɗ anda suke ƙ ara kwarzanta shi a idon duniya. A hasashen wannan bincike za a raba ƙ asashen da suke amfani da Hausa zuwa matakai guda uku. Mataki na farko su ne ƙ asashen da suke da asalin al’ummar Hausawa kamar yadda tarihi ya nuna. A nan za a ga cewa, al’ummar Hausawa sun fi yawa a ƙ asashen Najeriya da Nijar, wanda tarihi ya nuna wa ɗ annan ƙ asashe su ne tushen ƙ asar Hausa.. Sai kuma mataki na biyu, su ne ƙ asashen da ke kewaye da wa ɗ annan ƙ asashe kamar ƙ asashen Ghana da Kamaru da Chadi da Mali da Senegal da kusan dukkanin ƙ asashen Afirka ta yamma. Mataki na uku na ƙ asashen da suke magana da harshen Hausa bayan wa ɗ annan da aka bayyana a baya, su ne, kusan dukkanin ƙ asashen duniya, musamman manyan ƙ asashe, da ma ƙ anana, za a tarar al’ummar Hausawa sun shiga wa ɗ annan ƙ asashe sun fantsama, ko dai a dalilin ilimi ko kuma fatauci ko sauran al’amuran cirani. Al’ummar Hausawa, mutane ne da suka shahara da kasuwanci da kuma neman ilimi.

A yanzu harshen Hausa yakan shiga cikin harsuna mafiya muhimmanci guda 10 a duniya, ta fuskar yawan al’umma da fa ɗ a ɗ a, wanda wannan yakan ɗ ora shi a matsayin harshen farko a nahiyar Afirka. Bunza (2019) ya bayyana cewa akwai masu magana da harshen Hausa kusan adadin mutum miliyan 150 a fa ɗ in duniya, wanda idan aka ha ɗ a da masu koyon harshen a yau, adadin zai iya ninka haka.

1.2 Tsarin Sauti a Hausa

Tsarin Sauti, fannin nazari ne da ake bayyana yadda sautukan kowane harshe suke da yadda ake samar da su da kuma yadda za su iya kasancewa a muhallai daban-daban. Wannan fannin ya ƙ unshi wasu muhimman sassa guda uku , Sani (2005);

1)      Tsarin sautin furuci da fatar baki

2)      Ala ƙ ar sauti da ji (kunne)

3)      Ilimin awon sauti

Dukkanin wa ɗ annan fannoni sun ƙ unshi abubuwa da yawa da suka shafi sauti da yadda ake samar da furuci har ɗ an’adam ya ji shi ya kuma fahimce shi. Wasu daga cikin wa ɗ annan fannoni ana karantar su a fahimce su a ɗ akunan gwaje-gwaje na kimiyya ko kuma ta hanyar amfani da kwamfuyutoci da manhajoji ko ma a ha ɗ a duka , Abdullahi (2019, sh.5).

Fannin nazarin Tsarin Sauti ya yi fice a duniya a harsuna daban-daban, kuma fannin yana taimakawa wajen samuwa da daidaitar wasu fasahohin zamani da ake amfani da su a yau, kamar fasahar na’urorin kwamfuyuta da yadda za a koya musu magana, da wayoyin hannu da yadda suke ɗ aukar sauti da karanta magana da fasahar AI, wato ƙ ir ƙ irarriyar basira, wadda ake amfani da ita wajen ƙ o ƙ arin maye gurbin tunani da ayyukan ɗ an’adam ta na’urori, da sauran fannonin fasahar cigaban zamani da yawa.

Haka kuma akwai rubuce-rubuce da aka yi da yawa na ilimi game da wannan fanni, tun daga littattafai da ma ƙ aloli da kundayen digiri, har ma da manyan kundaye na manyan digirin PhD, wa ɗ anda fitattun masana suka rubuta a ɓ angaren ilimin Tsarin Sauti a Hausa.

2.1 Ma’anar Zaurance

Rabi’u (1986), da Yahaya (1992), sun bayyana zaurance a matsayin wata hanya da yara suke wasa da harshe domin nisha ɗ i da kuma samun ƙ warewa gami da isar da wata ɓ oyayyiyar ma’ana a tsakaninsu. Haka kuma sun nuna cewa akan yi amfani da wannan dabara wajen gano wanda ya yi nasara a tsakanin yara gami da bayar da wani lada ga wanda ya yi nasara, ko kuma wani nau’i na u ƙ uba ga wanda bai yi nasara ba. A ta ƙ aice, zaurance wata dabara ce ta sakaya ma’ana da sauya fasalin zance wadda matasa suke amfani da ita domin isar da sa ƙ wanninsu a tsakaninsu cikin gwaninta da nuna ƙ warewar fahimtar harshe. Duk da cewa zaurance da ɗ a ɗɗ en azanci ne a tsakanin al’ummar Hausawa, amma marubuta da yawa sun fi mayar da hankali game da takwarar zaurance, wato ƙ arangiya, wadda ita ma dabara ce da ake amfani da ita wajen koyon iya lallan ƙ wasa zance a harshe. Haka kuma shi azancin Ƙ arangiya ana samunsa a harsuna da yawa na duniya, ta yadda za ma a iya samun Ƙ arangiya a cikin dukkanin harasan duniya, idan aka duba yadda ake samar shi. Amma shi kuwa z aurance, wannan bincike ya lura da cewa ba kowane harshe ba ne na duniya yake iya samar da wannan fasaha da azanci. Misali, ana samun ƙ arangiya a harsuna biyu da suka fi tasiri sosai a kan harshen Hausa, wato Ingilishi da Larabci, amma kuma wannan bincike bai sami misalin z aurance ko ƙ waya ɗ aya ba a cikin wa ɗ annan harsuna.

Don haka, yawancin rubuce-rubucen da aka ci karo da su, rubuce-rubuce ne da suke bayyana yadda ake amfani da ƙ arangiya wajen koyar da masu koyon harshe yadda za su la ƙ anci wannan harshe, misali akwai Ayom (1987), Luo (2014), Arnott (1957), Ayom, (1987), Luo (2014).

A harshen Hausa, zaurance abu ne da ɗ a ɗɗ e, amma ba a ba shi muhimmanci ba sosai a fagen nazari. Sai dai duk da haka, malamai sukan sanya shi a cikin tsarin koyarwa musamman ga yara ‘yan sakandire, ta yadda ake kawo misalai domin koyar da yara yadda za su ƙ ware a harshe.

2.3 Yadda Tsarin da dabarun Zaurance

Zaurance yana da tsari, kuma ya ƙ unshi wasu dabaru da ake amfani da su a yayin samar da shi. Wa ɗ annan dabaru kuwa sun ha ɗ a da;

1)   Magana da sauri

2)   Saka ɗ a (sa ƙ andami) wasu sababbin ga ɓ o ɓ i

3)   Sakaye ma’anar zance

4)   Rukunin mamallaka

5)   Isar da sa ƙ o cikin nisha ɗ i

2.3.1 Magana da sauri

A daidai lokacin da masu amfani da zaurance suke shirya zancensu, sukan ɗ an ƙ ara saurin maganarsu domin zancen ya ƙ ara wahalar ganewa, sai dai zuwa ga wanda ake maganar dominsa. Haka kuma ƙ arin wasu sabbin ga ɓ o ɓ i da ake yi a cikin zaurance, yakan sanya zancen ya fi sauran magana ta yau da kullum yawa, don haka akwai bu ƙ atar a ɗ an ƙ ara saurin magana domin a iya isar da sa ƙ on a kan lokaci.

2.3.2 Saka ɗ a wasu sababbin ga ɓ o ɓ i

Tsarin kalmomin Hausa ya ginu ne a kan wasu fitattun ga ɓ o ɓ in kalma sanannu. Wa ɗ annan ga ɓ o ɓ i na harshen Hausa su ne kamar haka:

a-      BW

b-     BWW

c-      BWB

A tsarin zaurance, akan ƙ ara sabuwar ga ɓ a ne a cikin ga ɓ o ɓ in da ake da su a kalma, kuma yawanci an fi ƙ ara ga ɓ ar BW da BWBW, sai dai kuma akan samu wata sabuwar ga ɓ a mai ɓ ur ɓ ushin BWB. Dalilin haka kuwa shi ne, ita wannan ga ɓ a, asalinta BW ce wadda aka ƙ ara, amma a sakamakon ƙ warewa da yadda ake tsara zancen, ga ɓ ar takan naso ba ƙ in gabar da ke biye, kamar yadda za a gani a cikin misali mai zuwa;

Za mu zo

1 a – Za da mu da zo da

1 b – Za dam mu daz zo da

A misalin sama, za a ga asalin maganar kamar yadda take a harshen Hausa a 1, sannan kuma da yadda take komawa a zaurance da aka saka ɗ a ga ɓ ar “da” a misali na 1 a , sai kuma yadda salon ƙ warewa yakan sa wannan ga ɓ a ta naso wasu daga cikin ga ɓ o ɓ in da suke biye da ita kamar yadda aka gani a misali na 1 a .

Don haka za a iya cewa tsarin saka ɗ a ga ɓ a a zaurance yana tafiya da wasu fitattun ga ɓ o ɓ i kamar haka;

1)      BW

2)      BWBW

3)      BW(B)

Tsarin zaurance zai iya ɗ aukar wasu fuskokin da yawa, don haka da wahala a iya iyakance irin azancin da ɗ an’adam zai iya ha ɗ awa a cikin zaurance.

2.3.3 Sakay a ma’anar zance

Babbar manufar zaurance ita ce ɓ oye ma’ana. Don haka masu yin zaurance, sukan yi shi da ɗ an sauri-sauri ta yadda za su ɓ oye asalin kalmomin da suke fa ɗ a, kuma ko da wani ya ji kalmomin, to ma’anar abin da suke nufi za ta ɓ uya daga gare shi, domin an hargitsa kalmomin daga asalin tsarinsu da aka san su a harshe. Haka kuma, duba da yanayin yadda ƙ wa ƙ walwa take iya sarrafa zance, kafin mutum ya kai ga fahimtar abin da wata kalma take nufi, an furta wata kalmar. Saboda haka, lokaci ba zai ba i wa mai saurare damar jejjera kalmomin a ƙ wa ƙ walwa har y a fahimce su cikin sau ƙ i ba.

Har’ilayau, masu yin zaurance sukan saka ita wannan ga ɓ a a matsayin wata dabara ta ɓ oye zancensu daga wanda ba ya cikin rukunin wa ɗ anda ake so su fahimci wannan zance. Wato kenan, shi zaurance yana bu ƙ atar wani rukuni na musamman na al’umma da su ka ɗ ai ne suke fahimtar ma’anar abin da aka fa ɗ a, wanda ba ya cikin wannan rukunin ba zai ta ɓ a fahimta ba, sai bayan tsawon lokaci, ko kuma bayan an fahimtar da shi.

2.3.4 Rukunin mamallaka

Wa ɗ annan su ne wani taron jama’a, musamman matasa wa ɗ anda shekarunsu ba su wuce tsakanin shekaru 14 zuwa 19 ba. Za a iya samun zaurance a ƙ asa ka ɗ an ko sama ka ɗ an da wa ɗ annan shekaru, musamman ma a shekarun samartaka. Dalili kuwa shi ne, masu yin zaurance sun riga sun gama iya magana da harshe, sun koyi dukkanin wani siddabaru da harshen ya ƙ unsa ; a cikin sau ƙ i za su iya mammal ƙ waya shi, su sassaka ɗ a abubuwan da suke so su saka ɗ a, domin su ɓ atar da wanda ba ya cikinsu.

Ba a fiye samun magana da zaurance a tsakanin manyan mutane ba, domin manya sun fahimci rayuwa da sanin cewa ɓ oye zance ta wannan hanyar za ta iya ba ƙ antawa wanda ba a so ya gane, su kuwa matasa ba dole ba ne wannan ya dame su.

2.3.5 Isar da sa ƙ on cikin nisha ɗ i

Isar da sa ƙ on cikin nisha ɗ i da ƙ warewa da iya sarrafa harshe yana daga cikin muhimman dabarun da suke sa wa mata su yi amfani da salon zaurance. Iya sarrafa sautukan harshe kuwa , suna taimaka wa mai koyon harshe da ma wanda ya ƙ ware a cikin harshen wajen sarrafa furuci mai sar ƙ a ƙ iya.

3.1 Misalan Zaurance a aikace

Akwai misalan zaurance a cikin maganganun Hausawa da kuma wasu daga cikin irin ga ɓ o ɓ in da ake ƙ arawa. Irin wa ɗ annan ga ɓ o ɓ in kalmar da ake saka ɗ awa a cikin magana domin samar da zaurance sun sha bamban tsakanin wani rukunin mamallaka zuwa wani. Amma akwai fitattun ga ɓ o ɓ in da ake amfani da su wa ɗ anda aka riga aka san su a ƙ asar Hausa sosai, wasu kuma, ƙ ara fa ɗ a ɗ a bincike ne zai iya fito da su. Ga wasu daga cikin ga ɓ o ɓ in;

3.1.1 Zaurancen saka ɗ a “Da”

A wannan nau’i n a zaurance, akan saka ɗ a ga ɓ ar “da”, kamar yadda za a gani a misali masu zuwa.

2) a- Yadaroda yada cida adabindacida

b- Yáaròo yá a cí abincí

A misalin 2 a da ke sama, za a ga j u mlar “yaro ya ci abinci”, j u mlar da take ɗ auke da kalmomi hu ɗ u, wato , yaro da ya da ci da kuma abinci . Amma kalmar farko wadda take da ga ɓ a biyu, ta komai mai ga ɓ a hu ɗ u, wato daga BWBW zuwa BW(BW)BW(BW), saboda ƙ arin da aka yi wa ga ɓ o ɓ in kalmomin da sa ƙ andamin “da - BW”.

Don haka za a iya amfani da wannan salo a cikin zance wanda yake da tsayi, wato cikakkiyar magana ko hira, kamar yadda matasan suke aiwatar da maganganunsu da suaran hirarrakinsu na rayuwa a cikin zaurance. Ga misali na gaba .

3) a- Wadatada radanada munda jeda madakadarandatada saida mudakada gada wadasuda badakida sunda shidagoda dodaminda tatdataudanada madatsadalodalinda idalidamida ada madakadarandatardamuda. Ada cidakinda bada ƙ inda nanda adakwaida mandayanda mudatadaneda wada ɗ andadada sudakada hada ɗ ada madazada dada madatada. Munda yida murdanada ƙ wadaraida dada jinda idarinda adabinda dada sudakada zoda dada shida. Kudamada muda mada munda yida niydayarda kodayonda idarinda wandananda hadalinda kirdakida nadasuda. Munda kodayida dadabida’arda taidamadakonda alda’umdamada dadagada wadajendasuda.

b-  Wata ráanáa mun jée makaranta a sai muka ga wasu bá a ƙ i i sun shigo o do o min tattauna matsalo o lin ilimi i a makarantarmu. A cikin bá a ƙ in nan akwai manyan mutá a e wa ɗ anda suka ha ɗ a a mazá a da má a a . Mun yi murna ƙ warai da jin irin abin da suka zo o da shi i . Kuma mu u a mun yi niyyar ko o yon irin wannan há a lin kirki ná a su. Mun kó o yi ɗ abi’ar taimakon al’umma a daga wajensu.

3.1.2 Zaurancen saka ɗ a “Wala”

A wannan nau’in zaurance kuma, ana saka ɗ a ga ɓ ar “wala”, ga misalai kamar haka;

4) a- Suwalanawala zuwalawawala mawalakawalaranwalatawala awala kanwala lowalakawalaciwala.

b-  Sunáa zuwa makaranta a kan lóokaci.

5) a- Niwala zawala kawala cewala wawala bawala niwala dawala wawalayowala? Towala walwalalawalahiwala zawala kawala sanwala wanwaladawala kawala gawalayawala wawala mumwalamuwalanarwala mawalagawalanawala iwalarinwala wanwalananwala dowalaminwala niwala mawala aiwala bawala kanwalawarwala lawalasawala bawala newala, kuwalamawala karwala tawala sanwala karwala awala ciwalakinwala harwalakarwala nanwala. Donwala hawalakawala dukwala awalabinwala dawala awalakawala yiwala minwala saiwala nawala rawalamawala.

b- Ní i a ka cé e wa bá a ni da w aa o ? Tó o wallahi zá a ka san wanda ka gaya a wa mummunar magana a irin wannan do o min ní i a ai b aa kanwar lá a a ba ne e , kuma kar tá a san kar a cikin harkar nan. Don haka duk abin da aka yí i min sai ná a a ma a .

Ba za a iya ƙ ayyade adadin sa ƙ andaman da masu zaurance su ke iya kawowa ba. Masu zaurance za su iya kawo ga ɓ o ɓ i mabambanta iri-iri wa ɗ anda za su isar da sa ƙ on da ake so na zaurancensu.

3.2 Ala ƙ ar Tsarin Sautin Hausa da Zaurance

Kamar yadda aka bayyana a baya, tsarin ga ɓ ar Hausa ya yi tasiri wajen samar da ala ƙ a tsakanin zaurance da tsarin sautin Hausa. A nan za a kawo misalan yadda wannan ala ƙ a take musamman ta fuskar saurin sauti da kuma ga ɓ ar kalma

3.3 Tsarin ga ɓ ar kalma a Hausa

Zaurance yana da ala ƙ a ne ta kai tsaye da tsarin ga ɓ ar kalma a tsarin sautin Hausa, sai kuma yadda ake ɗ an ƙ ara saurin magana domin a ƙ ara samar da hanyar sakaye zance da kuma yin sa a kan lokacin tun da an ƙ ara wa zancen adadin ga ɓ o ɓ i da ƙ arin tsayi a kan tsayinsa na asali.

Ita ga ɓ a a kalma tana nufin dukkanin inda mai magana zai iya tsayawa ya huta. Za a iya ɗ aukar ga ɓ a kamar ga ɓ ar rake, wato wani wuri ne da yake kamar maha ɗ i na wannan kalma, domin haka ga ɓ a ma wuri ne da yake tamkar maha ɗ i a jikin kalma. Amma a ilimin tsarin sautin Hausa, za a iya ƙ arawa ga ɓ a ma’ana da cewa ita ce ha ɗ uwar ba ƙ i da wasali ko ba ƙ i da dogo wasali ko tagwan wasali, ko kuma ba ƙ i da wasali da ba ƙ i (BW/BWW/BWB) har su bayar da wani sauti mai ma’ana mai zaman kansa. Кamusun Cambridge ya bayyana ga ɓ a da cewa;

“a single unit of speech, either a whole word or one of the parts into which a word can be separated, usually containing a v owel”,

A wata ma’anar ƙ amusun ya ƙ ara cewa:

“a single unit of speech, in English usually containing a v owel, consisting of either a whole word or one of the parts into which a word is separated when it is spoken or printed”.

A wannan bincike, za a iya bayyana ga ɓ ar kalmar Hausa da cewa, shi ne wurin da mutum zai iya tsayawa ya huta a cikin kalma, wanda yakan ƙ unshi ba ƙ i da wasali ko ba ƙ i da wasali da ba ƙ i, kamar yadda za a nuna a misalai. A harshen Hausa ga ɓ a ta kasu zuwa kashi biyu, bu ɗ a ɗɗ iya da rufaffiya, ga bayaninsu kamar haka:

Bu ɗ a ɗɗ iyar ga ɓ a : wannan ga ɓ a ta kasu zuwa gida biyu, ta ƙ unshi gajeriya da doguwa. Bu ɗ a ɗɗ iyar ga ɓ a gajeriya ita ce ga ɓ ar da ta ƙ unshi ba ƙ i da wasali kawa. Ana wakiltarta a rubuce da – BW –. Sai kuma ta biyu ita ce bu ɗ a ɗɗ iyar ga ɓ a doguwa, wadda ita kuma ta ƙ unshi ba ƙ i da dogon wasali ko kuma ba ƙ i da tagwan wasali. Ana wakiltarta a rubuce kamar haka – BWW –. Ga misalansu kamar haka;

a-      B+W   = Ba

b-     B+WW = Baa/Bai

Rufaffiyar ga ɓ a: ita kuma ga ɓ a ce wadda take farawa da ba ƙ i kuma ta ƙ are da ba ƙ i a karshenta. Ita wannan ga ɓ a, dole ne a magana ta yau da gobe, ta ƙ unshi gajeren wasali, domin dogon wasali ba ya shiga cikinta, sai dai a tsarin zancen da ya kauce kar ɓ a ɓɓ iyar ƙ a’ida ko kuma yake nuna shau ƙ i. Ana nuna wakilcin irin wannan ga ɓ a kamar haka;

B+W+B.

3.4 Saka ɗ a ga ɓ ar kalma a zaurance

A tsarin sauti, saka ɗ a wani sabon sauti abu ne sananne a wasu muhallai domin cimma wani yanayi na samar da sauti. Akan saka ɗ a sautin wasali ko ma ba ƙ i a wasu wurare domin samar da wasu sautukan.

Kamar yadda aka bayyana a baya, a zaurance, cikakkiyar ga ɓ a ake saka ɗ awa wadda shigarta yakan sauya fasalin zancen zuwa wani abu da ba kowa ba ne zai iya ganewa sai wanda ya san me ake magana a kai. Misalan inda ake saka ɗ a wasali a kalmomin Hausa shi ne a cikin kalmomin aro domin su dace da yanayin furucin kalmomin harshen Hausa. Misali;

a-      Table – Tebur

b-     Cable – Kebur

c-      Le v el – Lebur

d-     Candle – Kyandir

e-      Bundle – bandir

f-       Android – andiroy

A zaurance, kuwa, akan ƙ ara cikakkiyar ga ɓ a ne guda ɗ aya ko biyu, ko ma fiye, domin samar da yanayin zancen da mamallaka zaurancen suke so su yi amfani da shi.

4.1 Muhimmancin Zaurance

Zaurance yana da muhimmanci sosai a tsakanin al’ummar Hausawa, kuma musamman a wajen masu yin sa. Wasu daga cikin muhimmancin da zaurance yake ɗ auke da su, sun ha ɗ a taimaka wa wajen ɓ oye ma’anar abin da ake magana a kai ga wanda ba ya cikin rukunin masu zaurance. Yakan ba wa masu magana da shi damar la ƙ antar magana da harshen da jujjuya shi yadda suke so.

Haka kuma, z aurance yana ba wa masu amfani da shi damar zama hazi ƙ ai masu ƙ ir ƙ irar azanci, ta yadda duk wanda ya iya wani nau’in zaurance, to zai iya fahimtar wani nau’in ko da kuwa ba nasa ba ne a cikin sau ƙ i. Haka kuma, zaurance yana ƙ ara nuna hikimar ta ke tattare da harshen Hausa, ta yadda za a ga cewa harsuna da yawa ba su da wannan fasaha ta zaurance a cikinsu.

5.1 Kammalawa

Zaurance yana cikin hikimomi da fasahohi da azancin al’ummar Hausawa wanda hikima ce da matasa suke amfani da ita domin sakaye zancensu ta yadda wanda ba ya cikin rukuninsu ba zai fahimci abin da suke fa ɗ a ba. Akwai lamuran da suka shafi tsarin sautin Hausa a cikin zaurance musamman tsayin zance da kuma ga ɓ ar kalma. A yau, zaurance yana ƙ ara ɓ acewa daga cikin al’ummar Hausawa, musamman ma a birane. Domin binciken nan ya gano cewa, yawancin wuraren da ake amfani da zaurance a yanzu sun fi yawa a karkara, a yay in da kuma da yawa daga cikin mazauna birni ba ma su san shi ba.

References

Abraham, R.C. (1959). The Language of the Hausa People London: University of London Press

Abubakar, A. (1983). Generative Phonology and Dialect variation: A study of Hausa Dialects, PhD. Thesis, University of London.

Abdullahi, M.S. (2019). Acoustic analysis of vowels in Hausa dialects, Phd. Thesis, Bayero University, Kano, Nigeria.

Arnott, D. W. (1957). Proverbial lore and word-play of the Fulani. Africa, 27(4), 379-396.

Ayom, E. B. (1987). A linguistic analysis of Dinka tongue twisters. Anthropological linguistics, 170-180.

Bargery, G. P., & Westermann, D. (1951).A Hausa-English Dictionary and English-Hausa Vocabulary: O x ford: O x ford University Press.

Bello, A. (2014). Sabon Nahawun Hausa. Zaria; Ahmadu Bello University Press, Ltd.

Carnochan, J. (2015). The Vowels of Hausa. Studies in Hausa; Language and Linguistics, 17.

Fatriani, N. (2017). The effect of Applying tongue Twister technique on students’ English consonants pronunciation (Doctoral Dissertation).

Galadanci, M. K. M. (1976) An Introduction to Hausa Grammar. Ibadan: Longman, Nigeria.

Greenberg, J H (1942). Some problems in Hausa phonology. Language 17 316-23

Jinju, M. H. (1980). Rayayyen Nahawun Hausa (Current Hausa Grammar). Zaria: NNPC.

Ladefoged, P, (1971). Preliminaries to linguistic phonetics, Chicago: Chicago University Press.

Ladefoged, P., & Maddieson, I. (1990). Vowels of the World Languages. Journal of Phonetics, 18(2), 93-122.

Ladefoged, P. (Ed.). (1993). A course in phonetics (3rd ed.). Fort Worth: T ɗ Harcourt Brace College.

Ladefoged, P., & Maddieson, I. (1996). The Sounds of the World's Languages. O ɗ ford: Blackwells.

Leben, W. R., & Newman, P. (2002). The Hausa Language: An Encyclopedic Reference Grammar.

Lindau-Webb, M. (1985). Hausa vowels and diphthongs. UCLA working papers in phonetics, 60, 75-92.

Luo, J. (2014). A Study of Mother Tongue Interference in Pronunciation of College English Learning in China. Theory & Practice in Language Studies, 4(8).

Lutfiani, D. (2017). Using Tongue Twister to Improve Students’ Pronunciation. ELLITE: Journal of English Language, Literature, and Teaching, 2(2), 110-115.

Mu’in, F., Amrina, R., & Amelia, R. (2017). Tongue Twister, Students’ Pronunciation Ability, and Learning Styles. Arab World English Journal (AWEJ), 8(4).

Newman, P, and R M Newman (1977). Modern Hausa English Dictionary Ibadan 6 Zaria O ɗ ford University Press.

Newman, P. (2000). The Hausa Language.An Encyclopedic Reference Grammar. New Haven.

Newman, R. M. (1990). An English-Hausa dictionary: Yale University Press New Haven.

Newman, P. (1991). A century and a half of Hausa language studies. Centre for the Study of Nigerian Languages, Bayero University, Kano.

Rabi’u, M.Z, A Abubakar, Bello SY. (1986). Sabuwar hanyar nazarin Hausa: don kananan makarantun sakandare. University Press.

Sani, M.A.Z. (1989). Ilimin Tsarin Sauti Na Hausa. Published by T.P.C. Ltd., Kano.

Sani, M.A.Z. (2011). Tsarin Sauti da Nahawun Hausa. University Press, Ibadan.

Sitoresmi, U. (2016). Tongue twisters in pronunciation class. In International Conference on Teacher Training and Education. SebelasMaret University.

Yahaya, I.Y. (1992); Darussan Hausa don manyan makarantun sakandare . (Vol. 3), University Press PLC.

Yahaya, I. Y. (1988). Hausa A Rubuce: Tarihin Rubuce-rubuce Cikin Hausa. Zaria: NNPC.

Zaria, A. B. (1981). Nahawun Hausa (Hausa Grammar). Lagos: Thomes Nelgos.

( https://arabiconline.eu/can-you-say-these-arabic-tongue-twisters/ )

( https://dictionary.cambridge.org/dictionary/english/tongue-twister )

( https://www.rumbunilimi.com.ng/HausaZaurance.html#gsc.tab=0 )

Post a Comment

0 Comments