Tasirin Musulunci a Kan Auren Hausawa

    Citation: Maikwari, H.U. & Lawan, M.S. (2024). Tasirin Musulunci a Kan Auren Hausawa. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, 3(1), 232-238. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.026.

    Tasirin Musulunci a Kan Auren Hausawa

    Haruna Umar Maikwari
    Department of Hausa Language
    Federal College of Education (Technical) Gusau
    Email. maikwari@fcetgusau.edu.ng
    Phone No. 07031280554.  

    And  

    Muhammad Sani Lawan
    Department of Nigerian Languages and Linguistics
    Sule Lamido University, Kafin Hausa, Jigawa State
    msanilawan@gmail.com
    08063161900

    Tsakure

    Rarrabe tsakanin al’adun aure da Hausawa suka gada kaka da kakanni da abubuwan da addinin Musulunci ya ya zo da su, ba abu ne mai sau ƙ i ba. Idan aka lura da irin tasirin da addinin Musulunci ya yi a kusan dukkan ɓ angarorin rayuwa, za a ga cewa wasu abubuwa da suka shafi aure sun sauya daga abin da al’ada ta zo da shi ya zuwa ga abin da addinin Musulunci ya zo da shi. Musulunci ya zo da dukkan tsare-tsare, kuma rashin bin wannan tsari na Musulunci, kan iya zama barazana ga auren ma’aurata da kuma rayuwarsu ta gaba ɗ aya. Wannan takarda  na da manufar : bayyana auren Hausawa, ta kuma fito da tasirin Musulunci a kan auren Hausawa tare da haskaka alfanun Musuluncin a cikin auren Hausawa. Hanyar da aka bi wajen aiwatar da wannan bincike ta ha ɗ a da hira da wasu mutane da karance-karancen littattafai da kundayen binjcike. An ɗ ora wannan ma ƙ alar a kan ra’in Sauyin al’adu. Ma ƙ alar,  ta fito da irin tasirin da Musulunci ya yi a wasu al’adun Hausawa na aure, tun daga kore wasu, sauya wasu, da kuma samar da wasu al’adun.

    Keywords : Al’ada, aure, Musulunci da tasiri

    1.0 Gabatarwa

    Al’ada aba ce da ta shafi dukkan ɓ angarorin rayuwar al’umma. Wannan ne ya sa kalmar ‘al’ada’ ta da ɗ e tana jan ra’ayin masana da manazarta da dama. Asalin kalmar al’ada ba Bahaushiya ba ce aro ta aka yi. Kuma an are ta daga harshen Larabci. Tana nufin abin da aka saba yi a Larabce. Duk da cewa akwai kininta a harshen Hausa. [1] Akwai rubuce-rubucen ilimi da bincike-bincike da aka gudanar a matakan ilimi daban-daban game da al’adun Hausawa. Masana da manazarta sun yi ƙ o ƙ arin ba da ma anar wannan kalma. A cewar Ibrahim (1982:iii) al ada tana nufin: abubuwan da mutum ya saba yi a cikin rayuwarsa ta duniya . Ɗ angambo, (1984:5) cewa ya yi: Al ada ita ce sababbiyar hanyar gudanar da rayuwa, wadda akasarin jama a na cikin al umma suka amince da ita. Bunza, (2006:7) na da irin wannan ra ayi inda yake cewa: Al ada tana nufin dukkanin rayuwar ɗ an Adam ce tun daga haihuwarsa har zuwa kabarinsa.” Idan aka duba wa ɗ annan ma’anoni da ma wasu da dama makamantansu, za a tarar da cewa, al’ada dai na nufin hanyar rayuwar al’umma ta gaba ɗ aya. Wannan kuwa ya ha ɗ a da dukkan matakan rayuwa da zamantakewa da tattalin arziki da kiyon lafiya da dukkannin abin da ya shafi rayuwar al’umma.

    A ɓ angare guda kuwa, aure na nufin zaman tare tsakanin mata da miji bisa yardar juna da amincewar junansu. Aure na daga cikin manyan matakan rayuwa wanda yake ƙ unshe da al adu baya ga shi kansa. Al’adu su ne suke yin jagorancin tafiyar da shi a zamani dauri.

    Musulunci kuwa, addini ne na Allah (SWA). Haka kuma hanya ce ta gudanar da rayuwa cikin tsari da Allah ya tsara, Annabi Muhammadu (SAW) ya koyar ga al’ummar duniya. Duk irin tanadin da al’ada ta yi wa al’umma, addini ya zo da kwatankwacinsa. Kuma tsarin addinin ya fi sau ƙ i da da ɗ in bi. Wannan ya sa al’ummu daban-daban da kira kan shiriya ya iskar suka kar ɓ e shi hannu biyu-biyu. Kar ɓ an Musulunicin ya taimaka wajen tasirin da Musulunci ya yi ga al’adun da aka gada kaka da kakanni. Wannan ma ƙ ala na da manufar: bayyana auren Hausawa, fito da tasirin Musulunci a kan auren Hausawa da haskaka alfanun Musuluncin a cikin auren Hausawa.

    1.2 Hanyar Gudanar da Bincike

    Wannan makala za ta bi hanyoyin tattaunawa da wasu masana a kan al’adun Hausawa. Haka kuma za a bi hanyar karance-karancen litattafan da suka yi magana a kan aure da addinin musulunci domin ganin irin tasirin da addinin Musulunci ya yi ga auren Hausawa. Haka kuma an bi hanyar karance-karancen mujallu da ma ƙ alu da kundaye domin samun wani abin dogaro da za a kafa hujja da shi dangane da wannan ma ƙ ala.

    1.3 Ra’in Bincike

    Ma ƙ alar ta yi amfani da ra in Mazhabar Sauyin Al adu . Gusau (2015, p. 51) ya bayyana wannan Mazhaba da cewa; tana kokawa ne da yadda tasirin ba ƙ in al adu na zamananci ko birnanci yake ƙ o ƙ arin mamaye al adun gida na gargajiya masu asali. Abin nufi dai a nan shi ne al ada ta yi tsari ga rayuwar al umma. Addinin Musulunci ya zo da nasa tsarin yadda rayuwa take tafiya cikin tsari. Dukkan Hausawan da suka kar ɓ i Musulunci, sun ɗ auki wannan tsari na Musulunci.

    1.4 Bitar Ma’anar Aure Daga Masana

    Aure ala ƙ a ce ta halaccin zama tsakanin miji da mata, ana yin sa ne domin shi aure sunna ce ta Annabi Muhammada Rasulullahi (S.A.W) domin tsarkaka zuri a. Aure muhimmin abu ne ga al’umma saboda haka akwai hanyoyi da matakai na tabbatar da shi. Mataki na farko shi ne neman aure. Haka kuma akwai wasu matakai na wali, da dukiyar aure da sauransu.

    Rambo, (2013), ya ruwaito, Burgress da Locke, (1953) na cewa “Aure zamantakewa ce ta amincewar mutum ɗ aya ko fiye da ɗ aya ko mace ɗ aya ko fiye da ɗ aya mai dangantakar mata da miji”. Rauf, (1977:78) ya bayyana aure da: “ Ƙ ulla  yarjejeniya da za ta haifar da halaccin saduwa da mace da samun zuri a. Kuma wani ɓ angare ne na mu’amala da ibada”.

    “Auren gargajiya na Hausawa ya danganci zaman tare a tsakanin namiji da mace a bisa yardar juna ko amincewar dangi ta hanyar wasu ƙ a idoji na al ada ko na addini. Ibrahim, (1985:i). Aure muhimmin al amari ne ba kawai a wurin al ummar Hausawa, har ga sauran al ummomin duniya gaba ɗ aya. [2]

    Alhassan, da Wasu (1982:8), Suna ganin “ Aure a matsayin ala Ƙ a ta halaccin zama tare tsakanin namiji da mace. Ana kuma yin sa ne saboda abin da aka haifa ya sami alsali da mutunci, da kiwon iyaye. Haka nan aure shi ne maganin zina da ya ya marasa iyaye, kuma mafi yawanci yaro yakan fara neman aure ne, idan ya kai shekarun balaga. Ibrahim, (1982:22-23) na cwa, Aure shi ne zaman tare tsakanin mace da namiji a bisa yardar juna da amincewar dangi ta hanyar wasu ƙ a idojin al adu ko addini. Saulawa (1986:1) cewa ya yi, “ Aure wani abu ne wanda ake yi tsakanin mace da namiji bisa ga amincewar junansu a ha ɗ a su tare ta hanyar ƙ ulla dangantaka a tsakaninsu da niyyar zaman tare na mata da miji, domin ya ɗ a al’umma da kuma yawaita zuri’a.” A Ƙ amusun Hausa na CNHN, (2006:22) ya kawo bayanin aure kamar haka, Dangantaka tsakanin namiji da mace ta hanyar shari a.

    A gudummuwa irin wannan za a iya cewa: “Aure na nufin ha ɗ uwa ko ratsawar wani abu a cikin wani abu, mutum ko dabba ko tsiri da makamantansu. Domin samun albarkar da ke tattare da abubuwan da suka ha ɗ u ko suka ratsa juna”.

    Idan kuma aka kalli ma’anar a addinance za a iya cewa, “Aure wata hanya ce ta baiwa namiji da macce damar zama tare da saduwa ta hanyar jin da ɗ i da mutunta junansu. Ita wannan hanya ko yarjejeniya ana gabatar da ita ne a gaban shaidu tare da yanka sadaki, kuma yadda addinin musulunci ya ƙ ayyade a kuma zartar da shi ta hanyar da sunnar Manzon Allah (SAW) ta tanada.

    Haka kuma Allah Ma ɗ aukakin Sarki ya ambaci aure a cikin littafinSa Mai Tsarki wato Al ƙ ur ani cewa, (Ku auri abin da ya fi maku da ɗ i daga mata biyu-biyu ko uku-uku ko hu ɗ u-hu ɗ u, amma idan ba za ku iya adalci ba ku auri ɗ aya) [3] . Sannan kuma Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce, (Mafi yawancin aure mai albarka shi ne, auren da yake da ƙ arancin sadaki kuma babu riya a cikinsa.) [4]

    Shi kuwa Bergery, (1934) da Roxana, (1997) da Abraham, (1962) dukkansu ba su bayar da ma’ana wadda za a gane aure ba. Sai dai sun yi maimaicin kalmar sun saka a cikin jimla wasu kuma sun yi fassara daga Hausa zuwa Ingilishi. A ƙ amusun Jami ar Bayero kuwa, an bayyana cewa, Aure dangantaka ce tsakanin namiji da mace ta hanyar shari a, ko mace da namijin tattabara, ko ha ɗ a wani tsiro da wani don samun ingantaccen iri”. CNHN, (2006:22). “Aure wani tsari ne wanda Allah ya shirya wa mutum musulmi, wanda ya ba shi damar ya nemi matar da ta dace domin su zauna tare a matsayin miji da mata bisa wasu sharu ɗɗ a da Allah ya shimfi ɗ a masa”. Auta, (2017:279). 

    Daga ma’anonin da suka gabata za a iya cewa: “Aure hanya ce ta ha ɗ a ko ƙ ulla dangantaka tsakanin mace da namiji wa ɗ anda za su zauna tare kuma a wuri guda a matsayin mata da miji, wadda kowace irin al’ada ta duniya ta amince da ita a kan dangantaka ta din-din-din domin yawaitar al’umma da kuma ci gabanta.”

    1.5 Bitar Ma’ana Aure Musulunci

    Musulunci wata rayuwa ce da Allah Ya shar'antawa bayinSa ta hanyar Annabi Muhammadu (SAW), shi kuma ya koyar ga al’ummar duniya. Duk wanda ya bi wannan rayuwar cikin dukkan alamuransa na ibada da mu’amalansa to shi ne musulmi, kuma shi ne wanda ya ri ƙ i Allah a matsayin Ubangijinsa kuma maji ɓ incin al'amuransa. [5]

    Musulunci shi ne yarda da sa ƙ on da Allah Ya aiko Annabi Muhammadu (SAW) da shi, da kuma aikata abin da sa ƙ on ya ƙ unsa daidai da karantarwar Annabi Muhamadu (SAW) [6] . Musulunci shi ne addinin gaskiya wanda babu wannan addini in ba shi ba. [7] Musulunci shi ne tsarin tafiyar da rayuwa da bautar Allah Ma ɗ aukakin Sarki. [8] Musulunci shi ne zaman lafiya, ku ɓ uta daga aibubbuka. [9] Musulunci shi ne sanin ƙ a idojin shari a wanda annabi Muhammadu ya zo da shi daga wajen Allah. [10] Musulunci shi ne mi ƙ a wuya ga Allah da jawuwa gare Shi, da yi maSa ɗ a’a, da tsalkake Shi da barin yi masa shirka. [11] Duk wanda ya ri ƙ i wani addini wanda ba Musulunci ba, Allah ba zay amsa masa ba, ranar Lahira suna cikin masu hasara. [12] Ha ƙ i ƙ a addini a wurin Allah shi ne Musulunci. [13] Musulunci shi ne sanin dokokin shari’a wa ɗ anda annabi ya zo da shi tare da sharu ɗɗ a ke ɓ antattu da suka danganci Sallah, Azumi Hajji, Zakka. [14]

    Aure a Musulnce shi ne shi ne ƙ ulla ala ƙ ar zama na har abada tsakin namiji da macce ta hanyar sadaki, waliyai, siga da kuma shaida [15] .

    Aure wani zama ne halastacce tsakanin mace da namiji a matsayin mata da miji wanda addini ya yarda da shi. Aure sunna ce mai ƙ arfi daga cikin sunnonin addinin Musulunci. Allah (SWA) ya ambaci aure a ayoyin Al’ ƙ ur ani Mai tsarki misali: Ha ƙ i ƙ a Mun aiko Manzanni (da yawa) kafin ka zo (Ya Muhammad SAW) kuma muka sanya a gare su, mataye (da yawa) da zuriya.... (Q, Ra’ad 38). A wata ayar kuma Allah (SWA) yana cewa; “ku auri daga abinda ya yi maku da ɗ i daga mata biyu-biyu ko uku-uku ko hu ɗ u-hu ɗ u, to amma idan kuna jin tsoron ba za ku iya adalci ba, to ku auri ɗ aya tak” (Q. Nisa’i 3). Ya zo a hadisi cewa Annabi (SAW) ya hana wasu sahabbai su fidiye (dadda ƙ a) kansu kamar yadda Sa ad bin Abi Wa ƙ as (RA) ya yi bayani. (Bukhari, 1467) haka kuma a wani hadisin Annabi (SAW) ya ce, Aure sunnata ce, duk wanda ya ƙ yamaci sunnata, ba ya tare da ni (Bukhari, 5063, Muslim, 1501).

    A musulunce, aure baya cika sai da wasu rukunnai da suka ha ɗ a da; waliyyai, sadaki, siga da kuma shaidu. Duk wanda ya kutsa wa wata mace ba tare da cika wa ɗ annan sharu ɗ a ba, to lallai ya sa ɓ a wa shari’a. Kuma hukunci ya hau kansa.

    1.6 Tasirin Musulunci a Kan Auren Hausawa

    Addinin Musulunci ya yi tasiri kusan dukkan al’amurran rayuwar Hausawa wa ɗ anda suka kar ɓ e shi. A fannin aure Hausawa kuwa Musulunci ya yi tasiri tun daga nema, zuwa zance, baiko, shiga lalle, hidimomin buki, tarewa, da zaman aure. Akwai wasu abubuwa da yawa da ake yi wa ɗ anda idan ba ilmi ke ga mutum ba, zai yi wuya ya iya rarrabe su. Ra’in sauyin al’ada da aka za ɓ a don ɗ ora wannan aiki, ya tabbatar muna da cewa ana samu tasirin wasu ba ƙ in al adu su mamaye ko su sauya wasu ko ma su kore su al adun. Addinin Musulunci ya yi irin wannan tasiri ga al adun Hausawa na aure. Yayin da ya sauya wasu, ya mamaye wasu ya kuma kore wasu al adun.

    1.6.1 Tasirin Musulunci a Kan Al’adun Da ɓ e

    Da ɓ e dai shi ne aikin daddale ƙ asan ɗ aki da ma wajensa domin gusar da tur ɗ a. Ana yin da ɓ e da ƙ asar ɓ urji da ruwa da makuba da sauran kayan ha ɗ i. [16] Kafin zuwan Musulunci wannan lalura ta da ɓ e ta ta’alla ƙ a ne a kan amarya. Iyakar miji ya gida ɗ aki, su kuma dangin amarya su ke da alhakin yin da ɓ e da balgen ciki da wajen ɗ aki [17] . Da Musulunci ya zo sai ya zo da tsarin tanadin muhalli da gyaransa duk sun ta’alla ƙ a a kan miji. Yanzu da Hausawa suka kar ɓ i Musulunci sau-da- ƙ afa sai waccan al adar ta da ɓ e da ta ta’alla ƙ a a kan mata (amarya da danginta) ta koma a muhallinta na asali. Miji ne zai gyara komai, ita mata zuwa ta shiga ɗ ai an nata.

    Akwai tattaro da ‘yan uwa da abokan arziki daga dangin amarya tare da dafe-dafen abinci, da gayyato masu aikin da ɓ en su zo da ɓ e suna yin wa ƙ o ƙ insu na arashi da batsa da sauran abubuwan da suke son su fa ɗ a ko isar duk a wannan da ɓ e, duk zuwan Musulunci ya sauya wa ɗ annan al’adun. Yanzu ma da tsarin ginin zamani ake yi, sai a ƙ are komai na gyaran gida amarya da dangi ba su ma san an yi ba. Sai dai kuma idan an gama ko an tanada akan kai su su gani domin su san irin kayan ƙ awar da za su saka. Muhallin shahid dai yanzu Musulunci ya dakatar da da ɓ e da shagulgulan da ake yi cikin yinsa.

    1.6.2 Tasirin Musulunci Kan Neman Aure

    Addinin Musulunci ya tsara yadda ake neman aure. Idan namiji ya ga wadda yake so da aure, yakan nemi iyayen yarinyar a ba shi dama ya nemi so ga yarinyar. Idan ya samu dama sai a tsayar da magana. Za a tanadi wali (wakili) sannan kuma za a dakatar da duk wanda ke neman yarinyar bayan shi ka ɗ ai. Idan zai zo hira (zance) kuma, yarinyar takan zo masa tare da ‘yar rakiya. Ba za a bari su ke ɓ anta su ka ɗ ai ba a wani waje ɓ oyayye. Musulunci ya hana zuwa tsarance kuma ya hana cire. A wancan lokaci al’ada ta yadda da zuwa tsarance domin kuwa babu wani abu na lalata a cikinsa. Zuwan Musulunci ya hana wannan al’adar duk kuwa da cewa babu wani abu mai kama da lalata a cikin wannan tarancen.

    Musulunci ya tsara yadda komai ya dace ya tafi a cikin sha’anin neman aure. A yau, bin wasu al’adun ya zama wani abin ƙ yama. Da wuya a iske mai neman mata ya je tsarance. Amma yana iya ke ɓ ancewa wannan kuma ba ya nuna wani abu. Kawaci da ke ga Hausawa na nuna yarda da mutum ya sa ake barin wanda ya je zance ke ɓ ancewa da wadda yake nema kar ya zargi ba a yarda da shi ba.

    1.6.3 Tasirin Musulunci Cikin Shiga Shagalin Aure

    A dauri al’ada ta yadda da kafin shiga shagalin aure, a sa yarinya ta ɓ oye sai a nemo tsohuwa mai sa amarya lalle. Ana kiran wannan tsohuwar da arwanka. A dauri idan za a sa amarya lalle, akan nemi ta je ta ɓ oye a wani gida daban. Sai a nemi arwanka ta shiga nemanta. Ita dai arwanka, takan nemi run tulun matar da ta tsufa ba ta ta ɓ a yin yaji (tashi) ba. Sai wannan arwankar ta ɗ ebi wannan ruwan a gyan ɗ ama (gora) sai ta ri ƙ a yawon gari unguwa-unguwa, gida-gida tana neman wannan amaryar. Kuma tana da damar shiga ko ina na gida idan ta shiga. Tana iya shiga har ban ɗ aki ta kuma duba har cikin ɗ aki har bayan gambu da ƙ ar ƙ ashin gado. Ba wanda zai hana ta. Idan ba ta gani ba sai ta yi sallama da masu gidan ta fita zuwa wani gidan daban da ake tsammanin yarinyar ta je. Daman amaryar za ta iya zuwa gidan da ba a tsammanin ganinta. Wannan neman amaryar don sa mata ruwa ta shiga lalle yana iya ɗ aukar makonni biyu ko fiye. Ya danganta da lokacin da aka gane amaryar. Daga ta gane ta za ta zuba mata wannan ruwan a kai ko fuska ta ce mata ga ruwan aurenki nan. Sai amaryar ta fashe da kuka, ita kuma da mutanen gidan da aka gane ta sai su ɗ auki gu ɗ a. Daga nan a kama amaryar zuwa gidan ubanta domin shiga shagulgulan aure.

    Daga an je gida kuma sai arwankar ta shiga hidimar yi wa amarya wanka. Akan yi wannan wankan a tsirara, kuma a saman turmi a tsakar gida a gaban mutane dangin amarya da na mijin. Bayan wankan kuma akwai al’adar ɗ aurin la ɗ e da ake yi wa amarya wanda abokanta ke yi. Akan yi ka ɗ e-ka ɗ e da luguden turame da ki ɗ an ƙ warya da shantu da dai makamantan wannan.

    Wannan al’adar Musulunci ya sauya ta. Ya dakatar da wannan ɓ oyon, ya kuma hana yin wankan lalle tsirara a saman turmi da kuma ɗ aurin la ɗ e da aka saba. Haka kuma, ya zo da saka rana da gayyata da gyaran jiki ba tare da an fita cikin bainar jama’a ba. Haka kuma Musulunci ya dakatar da cu ɗ a ga shi kansa ango da yi wa angon ko amaryar wata al’ada da za ta bayyanar da tsiraicin wani daga cikinsu. 

    1.6.4 Tasirin Musulunci Wajen Ɗ aurin Auren Hausawa

    Tun kafin zuwan Musulunci Hausawa na yin aure. Akan saka rana a tara mutane musamman a ranar kasuwa ko a cikin kasuwa sai a ɗ aura aure. A lokacin Maguzanci, lokacin da Hausawa ba su kar ɓ i addinin Musulunci ba. Idan za a yi ɗ aurin aure, aka nemi wani tsoho ya ɗ aura aure. A wajen wannan aure dai tsohon kan tara ƙ asa ya ɗ auki ɓ ota ya tara ƙ asa a gaban mutane ya bugi (doki) wannan tarin ƙ asar ya furta cewa Ya ɗ aura auren wane da wance ya ga ɗ an kaza-kazar uban da ya isa ya kwance. [18] Haka kuma wannan auren ana iya ɗ aura shi a cikin kasuwa ko ƙ ofar gidan uban yarinya.

    Da Hausawa suka kar ɓ i Musulunci sai wannan lafazi ya sauya daga na ashar zuwa na abin da Musulunci ya zo da shi (addu’a). Haka kuma a madadin a nemi tsoho ya ɗ aura sai abin ya koma sai limamai ke daura aure da malaman addinin Musulunci. Har ila yau, a madadin a ɗ aura a kasuwa, sai abin ya sauya zuwa ɗ aurawa a cikin masallacin dai ba ƙ ofar wani ba ko uban yarinya.

    1.6.5 Tasirin Musulunci Ya Haifar da Walima a Shagalin Bukin Aure

    A lokacin Maguzanci, idan aka yi aure akan yi shagali a ci a sha a yi ka ɗ e-ka ɗ e. [19] Da Musulunci ya bayyana ga al’ummar Hausawa, sai wannan ya sauya daga abin da aka sani a Maguzanci zuwa walima. A duk lokacin da aka yi hidamar aure, akan ke ɓ e rana ta musamman domin yin walima. A wannan lokaci aka saka wannan walima daga jerin tsare-tsaren da ake yi na shagalin buki. Walimar aure dai ta danganta daga masu yinta. Wasu sukan gayyato malaman addini maza kuma fitattu. Wasu kuma sukan gayyato malaman wannan amaryar na Islamiyya. Wasu kuma malamai mata da suke da ilimin addinin Musulunci suke gayyata. Idan suka zo, sukan yi wa’azi da jan kunne a muhallin da aka tanada. Wasu sukan tanadi wata makaranta ta Islamiyya wasu kuma gidansu ko na danginsu.

    Galibi a wannan rana ta walima, kayan da amarya ke sakawa dole akwai alkyabba. Wannan alkyabba ta samo asali ne daga suturar Larabawa. Su kuma Larabawa Bahaushe ɗ aukar yake dukkansu Musulmai ne. Duk abin da Larabawa suka zo da shi Bahaushe ɗ auka yake addini ne. Yanzu wannan walima ta zama wajibi cikin sha’anin auren yau. Ko da ba za a yi komai ba, akan fitar da rana da ake yin walima. Kuma galibi wannan ranar takan zama ko dai Alhamis idan za a ɗ aura ranar Juma’a. Ko kuma ranar Juma’a idan za a yi auren ranar Asabar.

    1.6.6 Tasirin Musulunci Wajen Ɗ aukar Aure Ibada ba Sharholiya ba

    Kafin zuwa Musulunci a ƙ asar Hausa aure al ada ce ta zama da mace ko mata a matsayin matan aure. Ana yinsa don kamala da ribar aure da makamantansu. Da addinin Musulunci ya samu ga Hausawa sai kuma aure ya tashi daga al ada zuwa ibada. Tsarin Musulunci ake bi wajen aiwatar da shi. Idan aka samu matsala, matsarin Musulunci ake bi, wajen gyaransa. Tsarin Musulunci ake bi idan aka samu sa ɓ ani aka yi saki. idan za a koma, abin da Musulunci ya tsara ake amfani da shi wajen yin kome.

    1.6.7 Tasirin Musulunci Cikin Kai Amarya

    A rayuwar baya ta Maguzanci, akan kai amarya ta ka ɗ e-ka ɗ e da bushe-bushe da wa ƙ e-wa ƙ e. A kan hanyar zuwa akwai zabaya ita ke shiga gaba ta rera wa ƙ a su kuma yan rakiya suna amsawa har a isa. Yanzu kuma da Musulunci ya zo sai aka bar gayyatar zabaya, sai dai a zo da abin hawa a ɗ auki amarya a kama hanya zuwa kai ta gidan ango. Idan Musuluncin ya ƙ ara tasiri ma a yau shi ne wasu iyaye su ke kai yarsu da kansu. Ma ana uba kan ɗ auki ‘yarsa ya kai ta gidan miji domin yin koyi da Sabin nan da ya kai ‘yarsa. An bayyana cewa sunna ce uba ya kai ‘yarsa gidan miji ya yi mata hu ɗ u ba [20] . An kuma samu wasu da dama suna ɗ abba ƙ a wannan sunna.

    1.6.8 Musulunci ya yi Tasiri Wajen Ƙ ayyade Yawan Mata da Za a Aura

    Kafin zuwan Musulunci Bahaushe na iya auren mata fiye da hu ɗ u. domin kuwa a wancan lokaci, wanda yake da yawan ‘ya’ya shi ne mai arziki. Domin kuwa da ‘ya’yan ne ake zuwa gona wajen aiki. Su ne ke tara abinci. Yawan ‘ya’ya kuma yana samuwa ne idan akwai mata da yawa a gida. Kenan kowace za ta haihu, kuma abin da aka haifa yakan zama jarin gida. Da musulunci ya samu a ƙ asar Hausa, sai aka samu shara ɗ in ƙ ayyade mata. Musulunci ya ƙ ayyade cewa dukkan Musulmi kar ya wuce mata hu ɗ u. Musulmi kan iya auren mata biyu, uku, ko hu ɗ u. Idan kuma ba za su iya adalci ba suna iya tsayawa ga auren guda. [21] Wannan karantarwa ta addinin Musulunci, ita ce ta sa Bahaushe yanzu ba ya auren matan da suka wuce wannan ƙ a ida ta mata hu ɗ u da aka shata.

    1.6.9 Tasirin Musulunci Cikin Ƙ ayyade Ƙ arancin Sadaki

    A lokacin Maguzanci, babu ƙ ayyade ƙ arancin sadaki. Kenan komai mutum ya bayar a matsayin dukiyar aure za a amsa. Da Musulunci ya samu kar ɓ uwa, sai ya zo da mizani (ma’auni) cewa mafi ƙ arancin sadaki rubu in dinari (rub u Dinar) wato kwatankwacin naira dubu sittin da ɗ aya da ɗ ari tara da tamanin da biyar a yanzu. (N61,985.00). [22] Yanzu idan za a yi sadaki sai an tabbatar da cewa ya kai wannan adadi kar a sa ɓ a wa umarnin Musulunci. Haka kuma Musuluncin ne ya zo da a rage ku ɗ in sadaki, sai dai kar ya kasa wannan ƙ a ida da aka shata.

    1.6.10 Tasirin Musulunci Cikin Zamantakewar Aure

    Kafin zuwan Musulunci, Hausawa al’adu suke bi sau da ƙ afa. Matan Hausawa a wancan lokaci suna suna zuwa gona, sukan yi ayyukan ƙ arfi domin ri ƙ on gida. Da Musulunci ya zo sai ya zo da tsarin yadda zamantakewar aure take a shari ance. Musulunci ne ya zo da yi wa mace gata cikin sha anin aure [23] . Musulunci ya yi umarni ga maza su ciyar da matansu da suka aura. Kuma wannan ciyarwa ma tana daga cikin ginshi ƙ an aure. [24] Musulunci ne ya samar da gado ga mace koda tana a wani gida tana aure idan mahaifinta ya mutu tana iya gadonsa. Haka kuma idan maigidanta ya mutu, tana iya gadonsa. Idan ma ɗ anta ne ya mutu, tana iya gadonsa. [25] Ko shakka babu Musulunci ya tsara duk yadda ya dace zamantakewa tsakanin ma’aurata ta kasance.

    1.7 Kammalawa

    Tasirin Musulunci a kan al’adun Hausawa ba bau ne da za a iya ƙ ayyadewa ba. Rabe tsakanin al adu da umarnin addinin Musulunci ba abu ne mai sau ƙ i ba. Idan mutum ba ya da ilimin addini zai yi wuya ya iya rarrabewa. Akwai auren sadaka da aka sani ana yi domin Musulunci. Yadda ake yinsa, kuma ake ɗ auka Musulunci ne idan ba ilimin addinin Musulunci ke ga matum ba, sai tunaninsa ya tafi kan cewa Musulunci ne. Ciyarwa da ba da wajen kwana ha ƙƙ i ne da ya rataya a kan namiji, amma yanzu wasu gani suke kamar al ada ne. Dafa abinci da mata ke yi ganinsa ake tamkar haka addini ya tanadar. Musulunci ya yi tasiri kusan dukkan ɓ angarorin rukunnan aure.

    Manazarta

    Abraham, R. C. (1962). Dictionary of the Hausa Language. London: Hodder Sydney.

    Alhassan da Wasu (1982) Zaman Hausawa. Institute of  Education ABU, Zaria.

    Argungu A.I da Sanyinnawal. (2022) “Kutsen Zamani Kan Suturar Hausawa”. Takardar da Aka Gabatar A Taron ƙ ara Wa Juna Sani A Tsangayar Nazarin Harsuna Ta Kwalejin Ilmi Ta Adamu Augie, Argungu.

    Auta, A. L. (2017). Fa ɗ akarwa A Rubutattun Wa ƙ o ƙ in Hausa . Kano: BUK Press.

    Bargery, G.P (1934). A Hausa English Dictionary & Hausa Vocabulary, London: Oxford University Press.

    Burgress, and Locke, (1953). The Family, 2nd (ed): New York. American Book. Co.

    Bunza, A. M. (2006) Godon Fe ɗ e Al’ada , Lagos Tiwal Nigerian Ltd.

    CNHN (2006) Ƙ amusun Hausa Cibiyar Nazarin Harsunan Nijeriya Kano: Jami ar Bayaro.

    Ɗ angambo, A. (1984). Rabe-Raben Adabin Hausa da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa . Kano:Triumph’, Gidan Sa’adu Zungur.

    Dogondaji N.B (2021) Takarda Mai Taken Farin Kan Da Musulunci Ya Sanya Wa Aure. Takardar Da Aka Gabatar a Ajin Masu Neman Digiri Na Uku a Darasin HAU: 933

    Ibrahim M.S (1982) Auren Hausawa: Gargajiya da Musulunci. Publications Center.

    Gusau, G. U. (2012), Bukukwan Hausawa. Gusau: Ol-Faith Publishers.

    Gusau, S. M. (2015). Mazhabobin Ra’i da Turke a Adabi da Al’ada na Hausa. Kano: Century Research and Publishing Limited.

    Muhammad Siddiqal Minshawi (1134AH) Karantar da Ma’amala tsakain ma’aurata. Madina: Darul fadilati Wat Tazayyin. Shafi na 16.

    Rambo, R. A. (2013), “Gwagwarmayar Kamancen Neman auren Hausawa Da Na Dakarkari”. Takardar da aka gabatar a taron ƙ arawa juna Sani a Sashen Nazarin Harsunan Nijeriya. Jami ar Usmanu Ɗ anfodiyo, Sakkwato.

    Rauf, M. A. (1977). Islamic View On Women and Family: New York: Cambrige Press.

    Roxana, (1997) Dictionary of the Hausa Language. London: Cambrich

    Saulawa I.A (1986) Yanayi da Tasirin Al’adun Aure a Ƙ asar Katsina. Kundin Digiri Na Farko,    Jami ar Usmanu Danfodiyo , Sakkwato.



    [1] A dubaBunza (2006) Gadon Fe ɗ e Al’ada , a shafina XXV

    [2] Ahmad Magaji ya bayyana Aure a matsayin wata yarjejeniya ce a tsakanin namiji da mace da kuma bin wasu ƙ a’idoji da dokoki da wannan al’umma ta tanada domin samun zuri’a ta gari.

     

    [3] Suratul Nisa’I. aya ta 4. A cikin Al}ur’ani mai girma

    [4] Hadisi na 22, a cikin Zadul Muslimat. Haka kuma akwai shi a Buguyatul Muslimin, da kuma Bulugul Maram Min Adillatul ahkam.

    [5] An samu a shafin ZAUREN SUNNAH DA TAMBAYOYI. Kuma an yi wannan ɗab’i a ranar 17 ga Febrairun 2016 a shafin Internet.

    [6] An samu wannan bayani daga shafin Internet na Sayyada Suhaila. Ta kuma buga shi a ranar 13 ga Mayu, 2020.

    [7] Tattaunawa da Malam Aminu Ibrahim Mailemu a gidansa da ke Gusau, unguwar Samaru Phese II, a ranar 15 ga Ogusta 2023 da misalin ƙarfe biyar na yamma (5:00)

    [8] Hira da Malam Sanusi Mai Almajirai a gidansa da ke Samaru Bayan S.S, a ranar 15 ga Ogusta, 2023 da misalin ƙarfe 6:00 na yamma.

    [9] Tattaunawa daga Dr. Abbas Abubakar Bunza. Dean School of Languages, HOD Arabic Department. A ziyarar da na kai masa a ranar 16 ga Ogusta, 2023 da misalin ƙarfe 4:30 na yamma.

    [10] A cikin Durusil Awwaliyya Babul Ƙawa’idul Islam.

    [11] Bayanin Imamu Nawawi a cikin Usulus Salasa.

    [12] Aƙur’ani Maitsarki. A cikin suratul Ali Imran.

      [13] Alƙur’ani Suratul Baƙra.

     

    [14] Hadisin Durusul Awwaliyya, Babin ƙawa’idul Islam.

    [15] Tattaunawa da malam Aminu Ibrahim Mailemu a ƙofar gidansa da ke Samaru Phase II Gusau jihar  Zamfara, a ranar Juma’a 12 ga Junairu 2024 da misalin ƙarfe biyar na Yamma.

    [16] Hira da Malam Ɗahiru Sankalawa, malami a Kwalejin Ilmi da ƙere-ƙere ta gwamnatin Tarayya da ke Gusau, a ofishinsa ranar 16 ga Ogusta 2023 da ƙarfe 12:00 na rana.

    [17] Hira da Malama Hauwa’u a gidanta da ke Gusau Unguwar Saminaka a ranar 17 ga Ogusta 2023 da misalin ƙarfe 5:00 na yamma.

    [18] Laccar ALH 308 Thougth and Believe. 2011.

    [19] Laccar ALH 308 Thougth and Believe. 2011

    [20] A zamanin Manzon Allah (SAW) an samu Sahabi  Sa’id Bn Musayyid ya kai ‘yarsa gidan miji domin ya kauce wa taron nan  na bidi’a da ake yi wajen kai amarya.

    [21] Alƙur’ani: Suratul Nisa’i

    [22] Wata sanarwa da Sarkin Musulmi Muhammadu Sa’ad ya fitar a watan Juli da ya gabata 30 ga Juli, 2023.

    [23] Hadisin Durusul Awwaliyya, Babin ƙawa’idul Islam

    [24] Hadisi ya zo a littafin Riyadus Salihin kan maza su riƙa ciyar da matansu, kuma alhakin ciyarwa a kan mazan yake.

    [25] Allah (SWA) ya faɗa a cikin Alƙur’ani Mai Tsarki cewa mata suna gadon iyayensu da mazansu da kuma ‘ya’yansu idan sun riga su mutuwa.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.