Ticker

6/recent/ticker-posts

Dabarun Bayar Da Labari: Nazari A Magana Jari Ce

Citation: Ishaq, R. (2024). Dabarun Bayar Da Labari: Nazari A Magana Jari Ce. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, 3(1), 224-231. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.025.

Dabarun Bayar Da Labari: Nazari A Magana Jari Ce

Ramatu Ishaq
Sashen Harsuna da Al’adun Afrika , Jami’ar Ahmadu Bello Zariya
Ramatuishaq98@gmail.com
09073348091 / 07064832598

Tsakure

Dabarun bayar da labari dabara ce da mawari ke amfani da ita wajen warware labarinsa. Warwara kuwa mawari shi ne yake da dama wajen nuna ƙ warewarsa domin jan zarensa sala-sala ta yadda sa ƙ onsa zai isa ga al’umma, kusan mawara ƙ wararru suna amfani da dabarun bayar da labari wajen yin tasiri a cikin labaransu, kusan mafi yawan labaran suna ɗ auke ne da dabarun bayar da labarai. Saboda haka wannan mu ƙ ala za a yi bakin gwargwado wajen fito da hanyoyin da mawarin wa ɗ annan labarai ya bi wajen gina dabarun ƙ ulla habarcensa, haka kuma mu ƙ alar za ta kawo wasu misalai na dabarun bayar da labarai daga wasu labaran Magana Jari Ce.

Fitilun Kalmomi: Warwara, Salo , Zamani , Kwaikwayo

Gabatarwa

Dabarar bayar da labari wani tsari ne da mawari yake da wu ƙ a-da-nama wajen ganin ya warware labarin ta yadda zaren tunanin ba zai bau ɗ e ba. Haka kuma dabarar nan tana wanzuwa ne a tsakanin taurarin da mawari yake gani za su taimaka wajen bayar da bayani yadda ya dace da abin da mawari yake nufi a tattare da sa ƙ on da kuma taurarin su ƙ ulla zaren tunanin mawarin habarcen.

Su kuwa taurari kusan a iya cewa su ne kanwa-uwar-gami ko kuma abokan tafiya, musamman yadda mawari yake sarrafa su, wajen sauya akalar tauraro daga duniyar mafarki zuwa ta zahiri ko kuma daga kirki zuwa akasin haka . Mawari yana aiwatar da haka ne, domin ya tabbatar da habarcensa ya ƙ ullu yadda ya dace da yanayi da kuma lokaci.

Warwarar labari fanni ne na nazarin habarce rubutacce ko na baka wanda ya shafi salon bayar da labari. A wannan yanayi mawari ne yake gudanar da shi gwargwadon hikima da fasahar shi yana amfani da salo iri-iri, sannan kuma mawarin yana amfani da dabarun bayar da labari a cikin labaransa. Saboda haka wannan mu ƙ ala za a yi amfani da dabarun bayar da labari ne a cikin wasu daga cikin labaran Magana Jari Ce.

1.1 Ma’anar Warwara

Kalmar warwara a luggance tana nufin kwancewa ko sassauta wani abu, musamman abin da ya kasance a ɗ aure, ko dai ɗ aurin igiya ko makamancin haka.Ta wata fuskar kuma kalmar warwara na nufin sasantawa ko sauwa ƙ e ko yaye wani abu. A fannin ilimi ana nufin kwance wani abu a fagen adabi, wanda k almar na nufin ha ɗ awa ko ƙ ullawa ko kuma jerantawa , (Malumfashi, 2019: 124).

Booth (1961) da Stephen (1974) da Newman da Good (1994) da Baldick (2004) da Mukhtar (2004) da Suleiman (2008) sun bayyana ra’ayinsu cewa: Akwai warwara iri uku ko hu ɗ u a cikin labari, mawarin da marubuci ya za ɓ a domin ya bayar da labari, shi za ka samu a kowace warwara, mawari na nan da irin abin da ya sani game da labari da kuma irin matsayinsa a labarin. Stephens (1974) ya bayyana warwara da cewa labari ne da yake magana a kan abin da bai wuce ƙ warewar mai ba da labarin ba. Newman da Good (1994) sun bayyana warwara da wani yanayi ne da ake isar da ƙ ir ƙ irarren labari da ya wuce, wanda muke ɗ auka r s a a kan yanayin mutum ko na wasu, ko kuma wani abin da kake gani. Shi kuwa Baldick (2004) ya bayyana ma’anar warwara da cewa wani ɓ angare ne da ke da ala ƙ a da wani abu da ya wuce fahimta ko abin da kake so, ko gaske ne ko ƙ ir ƙ irarren labari ne. Haka kuwa Mukhtar (2004) da Suleiman (2008) suna da fahimtar warwara aikin mawari ne da yake gudanarwa ga masu sauraro, ta yadda mai aikin warwara yake iya ƙ ulla labari cikin labari. Shi kuwa Tahir (2018) yana nuna cewa warwara aiki ne na mawari, wanda yake gudanar da shi ta hanyar amfani da salo iri-iri. Ta yadda labarin zai ƙ ayatar sannan kuma a fito da tsarin falle-falle, gwargwadon yadda mawarin yake gudanar da warwarar.

1.2 Ƙ ulle Zaren Labari da Kwance Shi

Masana irin su Baldick (2004) da Mukhtar (2004) da Uehara (2007) sun bayyana ra’ayinsu kamar haka:

Baldick (2004) ya bayyana dabarar ƙ ulle zaren labari wata hanya ce da mai ƙ ir ƙ ira r labari yake amfani da kalmomi iri-iri wajen bun ƙ asa labari. Shi kuwa Mukhtar (2004: 64) ya bayyana dabarar ƙ ulle zaren labari da cewa dabara c e da marubuci kan yi amfani da ita wajen ta ƙ aita labarinsa a ta ƙ aice. Haka kuma ya ƙ ara da cewa dabarar kwance ƙ ullin labari abu ɗ aya ne, ya bayyana ƙ ulla zaren labari na nufin mawallafi ya ƙ ulle zaren labarin da yake bayarwa domin ya gajarce shi, watau ya kawo shi a gajarce wanda sukan yi hakan ne ta hanyar za ɓ en wa ɗ ansu kalmomi na musamman domin su bu ɗ e kan zance da shi. Shi kuwa Uehara (2007) ya bayyana dabarar ƙ ulle zaren labari da cewa mai warwara yana bayyana hanyar da ake fahimtar abubuwa na rayuwa wajen ba da labari.

Ga misalan kalmomin kamar haka:

a.      A wani gari a ƙ asashen gabas an yi wani … Imam, (MGJ1: 5).

b.      Kwana arba’in ba su cika ba sai da matar Sarki ta … Imam, (MGJ1: 6).

c.       Ana nan ran nan, ina ya Allah babu ya Allah sai Waziri … Imam, (MGJ1: 6).

d.     Cikin daren nan sai ga Barakai ya komo ya gaya wa Waziri … Imam, (MGJ1: 13).

e.      Wata shekara aka yi tsananin yunwa a wani gari, har abinci … Imam, (MGJ1: 22).

f.        A wani gari can ƙ etaren Bahar Maliya a cikin ƙ asar … Imam, (MGJ1: 86).

g.      A wani gari wai shi Kona … Imam, (MGJ2: 140).

h.      Ran nan da dare suna zaune da Sarki, sai wani maro ƙ i ya … Imam, (MGJ2: 142).

i.        A kwana a tashi har ya kai wani ɗ an gidan gona ciki … Imam, (MGJ2: 175).

j.        A wani gari wai shi Randagi akwai wa ɗ ansu mutane … Imam, (MGJ3: 420).

k.      Ana nan kuma, bayan kamar bakwai biyu sai … Imam, (MGJ3: 438).

l.        Can da tsakad dare ashe kuma Telu Ba ƙ i na can … Imam, (MGJ3: 444).

A nan abin lura daga bayanan wa ɗ annan masana shi ne an fahimci cewa dabarun ƙ ulla zaren labari da kwance shi kusan abu ɗ aya suke nufi kuma ana ganin bayanin Baldick (2004) da Mukhtar (2004) sun yi arashi, saboda haka za a ɗ auki wannan fahimtar tasu a matsayin madogara. Domin dabarun ƙ ulle zaren labari da kwance shi abu ɗ aya ake nufi.

Dabarun ba da labari

2.1 Zamani

Zamani shi ne a wani yanayi aka yi labarin. Da d amina ne ko sanyi ko zafi ko dare ko rana, ya kuma bayyana yanayi a cikin labarin muhallin da labarin ya gudanar irin yanayin ƙ asar Hausa, ko kuma an sami bambanci irin wa ɗ anda suka shafi labarin garuruwan ƙ asahen Turawa a labarin , Mukhtar (2004: 76).

Idan aka ce zamani a dabarun ba da labrai yana ɗ aukar yadda mawari ya yi amfani da zamanin a wajen warware labarinsa, misali wani lokaci za a tarar mawari ya nuna zamani na bazara ko damina a matsayin zamanin da yake gudanar da warwarar labarin. Saboda haka ga misalan labarin da mawari ya warware kamar haka:

  Labarin Banza t a Kori Wofi                                               

Misali:                                                                

Wata shekara aka yi tsananin yunwa a wani gari, har abinci ya zama ba mai ganinsa sai mai dalili. Talakawa da m atsiyata ba su da wani abinci sai rogo, rogon ma bai wadata ba. Saboda haka wa ɗ anda ba su da ko samun rogon sai su ri ƙ a zuwa gonakin rogo da tsakad dare suna satowa. Imam, (MGJ1: 22).

Daga labarin da aka ba da misali za a fahimci mawari ya yi amfani da zamani na kaka watau lokacin zafi musamman a lokacin da ya nuna nau’in abinci watau Rogo wanda ba a faye samun s a ba sai a lokacin kaka, saboda wannan misali mawarin ya yi amfani da bazara a matsayin d abarun ba da labari. Haka kuma ya ƙ ara fito da lokacin da aka gudanar da warwarar wannan labari da kaka ne.

Wannan bayani da aka nuna, mawarin bai fa ɗ i shekara r ba, sai dai ya fa ɗ i abin da ya faru. Sannan ba ya ƙ ulle labarin nasa a cikin watanni sai da aka yi shekara, ya kuma nuna yanayi a cikin labarin inda an fara shi ne a lokacin bazara, saboda mutane ba su da abinci sai mai hali, shi kuwa t alaka ba shi da wani abinci sai r ogo, r ogon ma bai wadata ba. Haka kuma an sami yanayi a lokacin da wa ɗ annan abokai su uku suka yanke shawarar zuwa gonar Madaki sato r ogo ga yadda ta kasance:

Ka san dare in ya yi tsaka, da an yi magana ko da sannu-sannu ce, sai ka ji ta da nisa. Imam, (MGJ1: 22).

Sai dai mawarin ya nuna yanayin aikin wa ɗ annan abokai domin sun kasa ha ƙ ura da yunwa, inda suka yanke shawarar su je gonar Madaki sata in sun ci kuma su ɗ iba har da wanda za su sayar. Haka kuma an nuna cewa a cikin dare ne suka tafi gonar Madaki sata inda suka saki jikinsu tun suna ra ɗ a har su ka koma magana sosai, kamar suna gidajensu.

.Labarin Sarki Abdurrahman

Misali:

A wani gari a ƙ asashen gabas an yi wani babban Sarkin wanda a ke kira Abdurrahman Ɗ an A lhaji , Rabonka da samun ko labarin mai arziki irinsa tun Ɗ an ƙ aruna, mutum ko gidansa ya shiga ya ga yadda aka ƙ awata shi, ya ga kuma irin kayayyakin da ke ciki, sai ya ri ƙ e baki kawai, don abin ya fi gaban mamaki. Imam, (MGJ1: 5).

Daga labarin da aka ba da misali za a fahimci mawari ya yi amfani da ƙ asar Larabawa musamman a lokacin da ya bayyana labarin wani Sarki da Allah ya ba shi arziki mai yawa, kuma rabon da a sami mai ku ɗ i irinsa tun lokacin Ɗ an ƙ aruna, har ma wannan arzikin nas a ba a iya cewa ga yawansa, saboda wannan misalai mawarin ya yi amfani da s u a matsayin d abarun ba da labari.

 2.2 Kwaikwayo

Kwaikwayo dabara ce ta mawari da yake amfani da ita a wajen warware labarinsa, wannan dabara ta kwaikwayo mawari ne kan kwaikwayi ko ya shiga rigar tauraro sai ya yi amfani da muryarsa a lokacin.

Misali , idan za ka ɗ auki cewa magana ta sarauta sai mawari ya mai da kans a ko da shi mawarin ba Sarki ba ne, amma sai sai ya yi murya irin ta Saraki, idan mace ce sai ya yi murya irin ta mata, idan murya ta ban tausayi c e ko ta Y ara sai mawari ya koma da ita irin wannan domin mai ssauraron warwara ya gane cewa a wannan muhallin tauraron ake so a kawo shi a cikin labarin Yaro ne ko sai ya kwaikwayi yadda Yaro ke yin magana. Duk da haka kwaikwayo wani yanayi ne da mawari kan kwaikwayi wata ɗ abi’a da ba tas a ba, wajen aiwatar da ita a fili ko a ɓ oye ta yadda zai jawo hankalin mai sauraro ko karatu. Misali wani lokaci za a tarar da mawari yana kwaikwayon ɗ abi’a ta mutane da dabbobi ko d odanni.

 Labarin Banza t a Kori Wofi

Misali:                                                   

Da ƙ azu m zumi ya ji haka, sai ya ce : K ada ku yi saurin karaya. Ku dai ɗ an jure ka ɗ an, ku ga tawa dabarar.” Sai ya fa ɗ i rica, ya ce , “Wayyo Allah, ya kashe ni! Ashe harbin nan da na ce an yi mini, sai yanzu dafin ya narke. Ku ji ƙ aina, ‘yan’uwana ku yi mini rai.” Imam, (MGJ1: 23).

Daga wannan misalin da aka kawo, za a fahimci yadda mutum idan an ji masa rauni yake kasancewa, inda ya nuna ƙ azumzumi ya fa ɗ i ƙ asa rica, sannan ya nuna yadda yake furta kalamai na karaya da ban kwana, musamman a lokacin da dafi ya fara ratsa jikinsa.

 Labarin Sarkin Busa

Misali:

Da ya kwashe duk, sai ya nufi bakin kogi yana busa suna biye, mutane na kallo na murna. Da isarsa bakin kogi sai ya fa ɗ a cikin ruwa yana busa, ɓ eraye kuma ba su san sa’ad da suka bi shi ba, duk suka mutu cikin ruwa, sai ɗ aya ka ɗ ai ya tsere. Imam, (MGJ1: 87).

Za a fahimci cewa mawarin ya nuna Sarkin Busa ya sa mabusa a bakinsa yana ta busa ɓ eraye na biye da shi har suka shiga cikin kogi ba su sani ba.

Saboda haka nazarin ya nuna mana yadda Sarkin Busa yake da wata baiwa da idan yana busa sai duk wani abu mai rai ya bi shi. Saboda haka ne ma ɓ erayen nan suka fa ɗ a cikin ruwa a lokacin da suka ga Sarkin Busa ya fa ɗ a cikin ruwa.

 Labarin Sarki Abdurrahman

Da bawan nan ya ji haka sai ya ce : “A’a! Da Sarkin za ka yi ba’a? Kana tsammani Sarki ya tambaye ka karin magana ce?’ Bayin da aka zo da su suka tasam masa kamar za su cinye shi ɗ anye, da shi da tsuntsunsa duka. Da dai tsuntsun nan ya ga haka, sai ya ka ɗ a fifike, ya ce, “Allah ya ba ka nasara, kada ka yi hushi bisa ga gaskiyar ubangijina. Ni ma a jaka gudan nan da ya fa ɗ i a ganina ya karya mini daraja ne. Kamata ai bai kamata a sallama ni jaka guda ka ɗ ai ba.” Imam, (MGJ1: 9).

Shi kuwa misalin da aka kawo za a fahimci irin baiwar da Allah ya yi wa ɗ an A dam da kuma yi wa uban gidansa biyayya a lokacin da ya ga Baran Sarki suka tasan wa Balaraben da ya zo da shi kamar za su cin ye shi, da kuma yadda mawarin ya nuna a ku ya kwaikwayi ɗ abi’a ta ɗ an Adam da idan ka yi laifi ka nemi yafiya.

Saboda haka mawarin ya bayyana lokacin da tsuntsunsa ya ga kamar za su cin ye shi, sai aka ga tsuntsu ya ka ɗ a fiffike ya yi wa Sarki magana ya ce : “Kada ran shi ya ɓ aci saboda ubangidansa ya ce a saye shi jaka guda. Inda tsuntsun nan yake gani ma an karya mishi daraja kamata ya yi a ce an saye shi fiye da haka .

Labarin Karen Bana Shi Ke Maganin Zomon Bana

Misali:

Da Bala ya ga abin nasa yau ya wuce a yi ba ƙ in ciki, sai ya yi kuwwa, ya tuma ya buga ƙ afa, ya ce, “Kushewar ba ɗ i sai ba ɗ i. Sai ni na Malami turmi sha kwaranniya!” Ya dubi Nwanko, ya ce, “ Da ma ka ƙ yale shi, in zai dafa ni ne ya dafa ni, mu ga ƙ aryar tsiya.” Imam, (MGJ3: 423).

Haka kuma a wannan misalin da aka kawo, za a fahimci halin da mutum yake shiga a lokacin da ba ƙ in ciki ya same shi, a inda Bala ya yi kuwwa ya buga ƙ afa yana kirari, watau ya mai da kansa wani ta ƙ adari, mara tsoro wanda kome za a yi masa a yi.

 2.3 Hoton Gurbi

Hoton gurbi mawari yana yin amfani da basira ta wajen auna taswirar abin da ke faruwa a zahiri da ka ga zanen abin zai ba ka tabbacin basirar tsinkayar inda mawari ya dosa akan labarin sa . Misali , inda Abubakar Imam yake ba da labarin Telu Ba ƙ i da Telu Fari sai aka yi hoto ga mutum ya ɗ auko kaya a kan jaki yana korawa ko da mutum ba ɗ an nahiyar ƙ asar Hausa ba ne da ya kalli hoton sai ya ga cewa hoton ya ba shi ƙ asar Hausa suna ta’ammali da jaki, to a nan hoton gurbi yana nuna maka abin da ba ka ta ɓ a sanin s a ba ana nuna maka taswirar sa . Kusan mawara ƙ wararru suna ha ɗ awa da hoton gurbi idan ana ba da labari ga kuma hoton da ka ha ɗ a sai ka fahimta.

 Labarin Banza t a Kori Wofi

Misali:

Da Ƙ azuzumin ya ji suna tafe sai ya sake fa ɗ uwa, ya ce, “Wayyo, ni kaina! Da dai na ce ko zan ƙ o ƙ arta in kai gida, don in sami inda za a lura da ni, kada in kumbura kafin safe. Amma na ji dafin ya ci ƙ arfina, ku ku yi ta kanku, ku ƙ yale ni, ashe da ma ƙ asa ke kira na. In kun isa ku ba mata da iyalina ha ƙ uri, su tuna dukan mai rai mamaci ne.” Imam, (MGJ1: 23).

Daga labarin da aka ba da misali za a fahimci cewa mawarin, ya nuna yadda tauraron ya kasance a cikin wannan labarin inda Ƙ azuzumi suka je gonar Madaki suka sato r ogo suna cikin ci suka ji motsin ‘yan gadi hankalinsu ya tashi inda ya ri ƙ a dabara yana ihu yana cewa wayyo, na ji dafin ya ci ƙ arfina ku yi ta kanku, ku ƙ yale ni. Har yana barin wasiyya ga iyalansa domin idan maganar mutuwarsa ya isa garesu to su yi tawakkali da ha ƙ uri domin duk mai rai zai mutu.

 Labarin Sarkin Busa

Misali

Mawarin ya kawo hoton gurbi a cikin labarin Sarkin Busa ga yadda ta kasance:

 Ko da Sarkin Busa ya isa gindin tsauni, sai mutane suka ga tsauni ya bu ɗ e. Sarkin Busa ya kutsa ciki, duk yaran nan suka ɗ uru bayansa. Da suka shige duka, saura ɗ aya da aka bari can baya yana ɗ ingishi, sai tsauni ya rufe. Imam, (MGJ1: 89).

Daga misalin da aka kawo za a fahimci yadda mawarin ya bayyana inda aka nuna Sarkin Busa yana tafe yana busa yara na biye da shi, saboda da ɗ in busan ba su san inda ya kawo su ba, kafin ka ce kwabo har suka kai ga sun shiga cikin tsauni ya kuma rufe da su.

Labarin Rama Cuta g a Macuci Ibada

Misali

Da Telu Ba ƙ i ya ji haka, sai haushi ya kama shi ya ce , “Kai, kada in sake jin ka ce, jakaina! Kai mai jaki ɗ aya, yaya za ka ce jakaina? Mafari ke nan, idan wani ya ji, ya ce gaskiya ne. In nisha ɗ i za ka yi, ka ce , To maza, jakina don a san ɗ aya gare ka.”Imam, (MGJ3: 437).

Daga misalin da aka kawo mawarin ya bayyana abin da ya kasance a cikin labarin inda Telu Ba ƙ i ya nuna yana jin haushin Telu Fari a lokacin da yake tafiya yana wa ƙ a yana maza jakaina a cikin daji, an kuma kawo taswirar hoton jakkai guda hu ɗ u inda yake ri ƙ e da sanda a hannuns a . Wannan wa ƙ a tana ɓ ata wa Telu Ba ƙ i rai saboda duk wanda ya ji zai yi tunanin dabbobin duka na sa ne.

 2.4 Aiwatarwa

Aiwatarwa a duniyar mafarki mawari ke aiwatar da wani yanayi daga duniyar mutane ya koma duniyar dabbobi ko ta ƙ wari da sauransu. A wani bagire yakan yi amfani da wata halitta wadda ba da ita aka fara ba. Sannan kuma ya shigo da wata ɗ abi’a wadda ta sa ɓ a wa tunanin mai sauraro, ko kuma ya aiwatar da duniyar mafarki a kan duniyar zahiri, mawari yana aiwatar da warwara zuwa duniyar Aljannu da ta dabbobi wannan hanya ce da mawari ke amfani da ita wajen bayyana wani abu da ya faru kai tsaye a cikin labari ta hanyar aiwatarwa. Misalin yadda Telu Ba ƙ i da Telu Fari yake cewa mu tafi mana jakaina wannan duniyar mafarki ce inda aka nuna wannan hikima ce ta mawari da yake amfani da duniyar zahiri zuwa duniyar mafarki watau ta dabbobi.

  A Labarin Banza t a Kori Wofi

Misali:

Ko da ɓ arayin nan suka ji haka fa, sai suka kwashe ‘yan kayansu suka runtuma. Suna cikin shawarar inda za su bi, sai suka ji ɓ arawon nan na kwance, ya fara kakarin mutuwa, yana sha ƙ uwa ƙ i ƙ af- ƙ i ƙ af, can sai ya ja wani kakari mai ƙ arfi, ya yi shiru, sauran ɓ arayin suka buga salati baki ɗ aya, suka ce, “Ya cika.” (MGJ1: 24).

Da gudu . ‘Yan Gadi kuma suka dafo su suna cewa,

 “Kada su kai!” Imam, (MGJ1: 22).                                         

Daga misalan da aka bayyana za a fahimci yadda ɓ arayin nan suka ji tafiya sai suka kwashe kayansu suka runtuma a guje, domin suna gudun kada masu gadi su yi ram da su . Mawarin ya nuna mana cewa wannan ɓ arawon yana gargara r mutuwa ce, saboda yana ta sha ƙ uwa, inda har ta kai ga ya yi kakarin mutuwa tare da sha ƙ uwa, alamun cewa yana gab da mutuwa, har ta kai ga ya ja wani kakari mai ƙ arfi alamun ya mutu ke nan. Inda sauran ɓ arayin suka rafka salati gabaki ɗ ayansu suna fa ɗ in ya mutu, a lokacin da ‘yan gadi suka biyo su da gudu domin ganin sun dam ƙ e su.

A Labarin Sarkin Busa

Misali:

Sarkin Busa ya ce, “To madalla.” Ya sa wata irin mabusa bakinsu, ya yi ta busa, yana yawo cikin gari rariya-rariya. Sai ɓ erayen nan suka yi ta fitowa ko ina, suna bin sa tururururu, wa ɗ ansu manya, wa ɗ ansu ƙ anana, wa ɗ ansu tultul, wa ɗ ansu ƙ yamas- ƙ yamas. Imam, (MGJ1: 87).

A wannan misalin da aka bayar za a fahimci cewa mawarin ya nuna inda Sarkin Busa ya sa mabusa a bakinsu yana yawo cikin gari yana busa rariya-rariya, sai aka ga ɓ eraye kala-kala suna fitowa, saboda tsananin baiwar da Sarkin Busa yake da ita ne ya saka ɓ eraye yin tururuwa sa ƙ o da lungu na cikin garin wannan ya bayyana cewa daga duniyar asali an koma duniyar mafarki .

  Labarin Jimrau ɗ an Sarkin Noma n a Biyu

Misali:

Da ganin ta zama ɓ era sai Jimrau ya yi farat ya saki kyanwarsa yadda Yaron nan ya gaya masa. Ko da kyanwa ta ga ɓ era sai ta yi tsalle ta kama shi ta kashe ta cinye. Ko da ta cinye Dodanniya, sai ya ji gidan ya ɗ auka “ Haa! Jimrau, babu kuskure, ka yi nasara.” Imam, (MGJ2: 177).

Daga labarin da aka ba da misali za a fahimci Jimrau yana ɗ aya cikin ‘ya’yan Sarkin Noma inda ya yarda musu da su shiga duniya domin kowa ya kama sana’ar da za ta fisshe shi , inda ya ce ya sallame su ranar ɗ aya ga wat a n Salla Babba, ba ɗ i kuma ga wannan wata in Allah ya sa muna numfashi ina so duk a taru nan mu ga abin da sana’ar kowa ta ba shi . Mawarin ya yi amfani da inda aka nuna Jimrau ya saki kyanwarsa, sannan ya ba da labarin yadda take yi idan ta ga ɓ era ta yi tsalle ta kama shi ta kashe ta cinye, ko da ta cinye Dodanniya sai gidan ya ɗ auka Haa ! Jimrau, babu kuskure ka yi nasara.

  Labarin Karen Bana Shike Maganin Zomon Bana

Misali:

Suna nan kwance, zuwa asuba sai wani ɓ arawo ya shigo wurin fataken nan da ke cikin rumfa, suka yi kuwwa, su Bala da ke bisa rufi suka diddiro. Abin ka da ƙ addara, Bala ya diro bisa kan wannan da sauro suka kora waje, abu ya iske ƙ arar kwana, asalatu ba ta yi ba, ya ce ga garinku. Imam, (MGJ3: 424).

Har ila yau, an bayyana inda tsautsayi ya faru a lokacin da Bala suka ji kuwwa r ɓ arawo, da inda ya nuna yadda Bala wajen dir k owa ashe akwai mutum a kwance bai sani ba ya dirko a kansa abin ka da ƙ arar kwana bai kai asuba ba ya mutu.

Daga misalin da aka bayar za a fahimci cewa , mawarin a cikin wannan labarin inda ya ri ƙ a kawo su daki-daki, idan aka yi la’akari da wa ɗ annan misalai:

  Labarin Hassada g a Mai Rabo Taki

Misali:                                                                

Muka shiga jirgin ruwa, yarana duk na bar su a gida, ban tafi da kome ba sai ɗ an k aren nan da kuke zargina a kansa, sai da suka bari mun yi nisa cikin Bahar Maliya, gaba ruwa baya ruwa, sa’an nan suka tura ni ciki. Imam, (MGJ3: 498) .

Hari la yau an nuna yadda Azlamu da Zalimu suka same shi suka tura shi cikin ruwa, inda k aren sa yana san ya taimake shi ya fito da shi daga cikin ruwa.

Da muka isa, Dogaran nan suka ɗ auke ni suka jefa ciki kamar dutse tim, suka wuce. Abin da aka tabbata, duk wanda aka jefa cikin ramin nan kafin ya kai ƙ asa numfashinsa ya ɗ auke. Imam, (MGJ3: 499).

Za a fahimci cewa Dogarai suka ɗ auki Farke suka jefa shi cikin rami ya fa ɗ a tim kamar an jefa dutse.

Suka tasam mini k aren nan kuwa ya dage, sai ya sa ƙ irji ya banke wannan, ya bar shi ya tasam ma wannan. Suka yi ta sukar k aren nan. Imam, (MGJ3: 506) .

 Labarin Rama Cuta g a Macuci Ibada

     Misali:

Matar ta ce, “ Maza shiga cikin akwatin nan, kada ka yarda ka ko yi motsi.” Ya yi farat ya shige, jiki na rawa, ta sa marufi ta rufe shi. Imam, (MGJ3: 439).

Daga wanan Labarin Rama Cuta g a Macuci Ibada an bayyana inda Telu Ba ƙ i ya fito ya daka wa jakin Telu Fari mashi, aka ga jaki ya fa ɗ i ya mace da kuma inda Telu Fari ya tsuguna bayan ya gama kuka ya fe ɗ e fatar jakin ya busar da shi ya sa ɓ a a kafa ɗ a ya tafi cikin gari domin ya samu mai siya.

Misali

Da suka isa bakin kogi, suka ajiye gadon kara, suka cicci ɓ o gawan nan suka ƙ unduma ta ciki ƙ undum, ruwa ya tafi da ita tun suna kallonta har ta nutse. Imam, (MGJ3: 445).

Da zuwan Telu Ba ƙ i ya shiga cikin rigiza da takardar a kara. Telu Fari ya sami kirtani ya ɗ inka rigizar ram, ya ƙ unduma shi cikin ruwa. Ya ce. “Alhamdulillah! Imam, (MGJ3: 449).

Har ila yau an bayyana yadda Telu Ba ƙ i ya nuna wautarsa na cewa akwai zumunta tsakanin Sarin ruwa da Telu Fari inda yake san ya je ya gaishe shi, ko sa saba don gaba. Saboda san abin duniya inda ya kai kansa ga halaka ya shiga cikin rigiza shi kuma Telu Fari ya ɗ auki zaren kirtani ya ɗ inke buhun, saboda kada ida n sun jefa Telu Ba ƙ i a cikin ruwa ya fita daga ciki . Wannan warwarar ya nun a cewa Telu Ba ƙ i kuwa ya isa sakarai an koma duniyar mafarki saboda maganar Sarkin kogi domin shi ya shuka w a kansa mugunta, d o min an ce , in za ka gina ramin mugunta ka gina shi gajere.             

 Kammalawa

Dabarun bayar da labari marubuta kan yi amfani da dabaru daban-daban domin ganin sun isar da sa ƙ onninsu. Wannan nazarin ya fito da wasu dabarun mawari a warwarar dabarun bayar da labari, inda aka za ɓ i wasu daga cikin labaran domin fito da ire-iren dabarun. Saboda haka wannan nazarin ya gano yadda Abubakar Imam ya yi ƙ o ƙ ari wajen yin amfani da dabarun bayar da labari a cikin warwarar labarinsa na Magana Jari Ce, inda ya yi amfani da z amani ya nuna wani yanayi aka yi labarin, da d amina ne ko sanyi ko b azara ko dare ko rana da kuma irin yanayin ƙ asar. Har ila yau , mawarin ya yi amfani da k waikwayo inda ya nuna cewa yanayi ne da mawari kan kwaikwayi wata ɗ abi’a da ba ta sa ba wajen aiwatar da shi a fili ko a ɓ oye. Duk da haka mawarin ya yi amfani da a iwatarwa inda salo ne da mawari ke amfani da shi wajen waske tunanin masu sauraro wajen jan hankalin mai sauraro daga duniyar asali an koma duniyar mafarki . Ko kuma daga duniyar mutane an koma duniyar mafarki, inda nazarin ya lura da cewa mawarin ya yi amfani da hoton gurbi wajen warware labarinsa inda yake kawo hoton bayani kai tsaye a kan wani aiki da mawari ke san isar wa ta yadda ake taswirar wani ɓ angare na daga cikin labari da kuma bayani game da yadda yake ƙ ulle labaransa.

MANAZARTA       

Abrahams, M. (1999). A Glossary of Literary Terms, 7th Edition. New York: Harcourt Brace College Publishers.

Baldick, Ch. (2004). Oxford Concise Dictionary of Literary Terms. London: Oxford University Press.

Bidemi, A. (2009). A Practical Guide to Terms Literature a nd Criticism Graphael Printing and Publing Company Osun State.

CNHN. (2006). Ƙ amusun Hausa . Kano: Cibiyar Nazarin Harsunan Nigeriya. Jami’ar Bayero.

Gagan, G. (1990). Dictionary of Literary Terms . Amol Publication, New York Delhi India

Genette, G. (1980). Narrative Discourse. An Essays in Method. (Translated by Jane E Lewin) Oxford: Blackwell.

Gray, M. (1994) . Dictionary of Literary Terms, London: Longman Group

Hassan, S . (2012). Ba a Mugun Sarki Sai Mugun Bafade: Tsokaci Daga Magana Jari Ce na Uku. A Cikin Champion of Hausa Cikin Hausa . A Festschrift i n Honour of Ɗ alhatu Muhammad . Sashen Harsuna d a Al’adun Afrika, Jami’ar Ahmadu Bello, Zariya.

Imam, A. (2010). Magana Jari Ce 1-3: Northern Nigerian Publishing Company Limited.

Lawrence, S (1979). The Revival of Narrative: Reflections on a New Old History, Past and Present.

Malumfashi, I .A. (2009). Adabin Abubakar Imam. Garkuwa media Services. Sokoto.

Mora, A . (ed) (1989). Abubakar Imam Memoirs. Zariya: Nothern Nigerian Publishing Company Limited.

Mukhtar, I. (2004). Jagoran Nazari n Ƙ agaggun Labarai . Kano: Benchmark Ltd.

Pweddon, N. (1977). Thematic Conflict and Narrative Technique in Abubakar Imam’s Ruwan Bagaja. Unpublished Ph.d Thesis. Madison, University of Wisconsin, U.S.A.

Tahir, R. M. (2018). Habarcen Nigeriya d a Nijer: Tsokaci a Kan Tatsuniya. Unp ublished Ph.D Thesis Zaria: Department of African Languages and Cultures. A h madu Bello University.

Tahir, R.M. (2020). Warwara a Taskar Habarcen Tat s uniyar Hausa : Journal of Arts an Education. Vol. 3: No. 3. Bauchi State University, Ga ɗ au.

Uehara, E.S. (2007). Disturbing Phenomenology” in the Pain and Engagement Narratives of Cambodian American Survivors of the Killing Field . Culture, Medicine and Psychiatry.

Post a Comment

0 Comments