Ticker

6/recent/ticker-posts

Kwatanci Tsakanin Korewa a Jumlolin Hausa da Fulatanci: Tsokaci Daga Jumla Maras Aikaitau

Citation: Sanusi, H. (2024). Kwatanci Tsakanin Korewa a Jumlolin Hausa da Fulatanci: Tsokaci Daga Jumla Maras Aikaitau. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, 3(1), 257-265. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.029.

Kwatanci Tsakanin Korewa a Jumlolin Hausa da Fulatanci: Tsokaci Daga Jumla Maras Aikaitau

Daga

Hariratu Sanusi
Sashen Harsuna da Al’adun Afirka  
Jami’ar Ahmadu Bello, Zaria
harirahamzasanusi4@gmail.com
08030812667

Tsakure

Hausa da Fulatanci harsuna ne mabambanta ta fuskar tarihin tushensu da kuma nahawu. Duk da haka, ba a rasa wuraren da suka yi kama da juna ta fuskar jumlolinsu ba. Manufar wannan mu ƙ ala ita ce ƙ o ƙ arin kwatanta korewa a jumloli marasa aikatau na Hausa da na Fulatanci domin a fito da kamancinsu da kuma bambancinsu ta fuskar gininsu. Hakan zai samu ne ta yin la’akari da ire-iren wa ɗ annan jumloli a harsunan Hausa da Fulatanci. An yi amfani da hanyar hira daga wasu rukunin Hausawa da Fulani tare da nazartar littattafan nahawu na harsunan guda biyu wajen tattara bayanai a wannan bincike. Sannan mai gudanar binciken ta yi amfani da kasancewarta mai jin Fulatanci kuma manazarciyar harshen Hausa wajen ƙ alailaice bayanan da ta samu wa ɗ an da suka kai ga samar da sakamakon wannan bincike. Haka kuma, an ɗ aura aikin a kan ra’in ɗ oriya na Haliday. A wannan mu ƙ ala, an kwatanta ire-iren jumloli wa ɗ anda suka ha ɗ a da jumla ganau da jumla ƙ addamau da kuma jumla rayau. An gano cewa akwai kamanci musamman ta fuskar adadin kalmomin korewa da kuma yadda ake sarrafa su a jumloli marasa aikatau na Hausa da na Fulatanci. Bugu da ƙ ari, an gano bambanci a tsakanin jumla korau ta fuskar kalmomin da suke yin tarayya da ɓ ur ɓ ushin korewa wajen isar da sa ƙ o.

1.0 Gabatarwa

Hausawa da Fulani (Ful ɓ e) suna zaune tare tun da da ɗ ewa har ma ana ikirarin cewa asalinsu guda ne. Johnston (1967:52) ya bayyana cewa sun ha ɗ u ne tun daga ƙ arni na tara, wato shekara kusan dubu daya da ɗ ari biyu da suka wuce. Sun zauna tare suna mu’amala tare kuma sun kasance suna tarayya ta wajen bigire da al’ada da kuma zamantakewa ta yau da kullum. Auratayya ma na kadancewa a tsakaninsu har suka zama tamkar tsatsonsu ɗ aya ne. Asali harsuna ne mabambanta wa ɗ anda suka fito daga tsatso mabanbanta a inda Greenberg (1947) ya bayyana cewa harshen Hausa yana ɗ aya daga cikin harsunan Chadi dangin Afro-Asiatic. Shi kuwa Fulatanci na ɗ aya daga harsunan yammacin Atalantika dangin Niger- kordofanian. Wannan dalili ya sa ake ganin wa ɗ annan harusuna ba su da dangantaka ta tsatso sai dai sun ha ɗ a ala ƙ a ta zamantakewa da kuma aurataya har ma da al’ada ta fuskar abinci da sutura da wasu ɗ abi’u.

Jumla muhimmiyar aba ce a fagen nazarin harsuna, domin al'umma na sarrafa ta, yau da kullum, a magance da kuma a rubuce. Asali ma ita ce kan gaba a fagen ilimin harshe, domin ta ji ɓ anci nazari a kan furucin kalmomi masu jeren ma’ana. Har wa yau, a fannin nazarin ginin jumla ake duba sigar jumla da tubalan da ke gina jumla ko furuci idan mai magana ya furta ko marubuci ya rubuta. Masana da dama irin su Arnott (1970) da Galadanci (1976) da Zaria (1996) da kuma McIntosh (1984) da Zaruk (2005) da Batagarawa (2019), sun yi ittifakin cewa jumla ta rabu zuwa manyan rassa guda biyu, watau jumla mai aikatau da kuma maras aikatau. Dalilin yin haka kuwa shi ne, a cewarsu, kowace irin jumla na ɗ aya daga cikin wa ɗ anan biyun ne. Jumla mai aikatau, jumla ce wadda aikatau ɗ inta ke aiwatar da aiki. Ita kuwa jumla maras aikatau ba wai ba ta da aikatau ba ne a’a, amma aikatau ɗ in ne ba ya aiwatar da aiki. Asali ma a matsayin mahadi (linking v erb) yake, domin yana sadar da aikau da ita jumlar kanta. Rabe-raben jumla irin su Jumla Sassauka da Har ɗ a ɗɗ iyar Jumla, na iya zama jumloli masu aikatau ko marasa aikatau. Saboda da haka ne wannan mu ƙ ala ta zabi ta yi kwatancin siga da yadda ake sarrafa korewa a jumloli marasa aikatau na Hausa da kuma na Fulatanci domin a gano kamanci da bambancin da ke tsakaninsu a wa ɗ annan harsuna. An yi amfani da hira da wasu rukunin Hausa da Fulani tare da nazartar littattafan nahawu na harsuna guda biyu wajen tattara bayanan wannan bincike. Sannan mai binciken ta yi amfani da kasancewarta mai jin Fulatanci kuma manazarciyar harshen Hausa wajen ƙ alailaice bayanan da ta samu da suka kai ga samar da sakamakon wannan bincike. Dangane da ra'i kuwa, takardar ta yi amfani da Nahawun Ɗ oriya wanda Halliday (1985) ya assasa. Ra’i ne da ya fi bai wa ma’anar yankuna na jumla muhimmanci wajen nazari. Ana bayani ne a kan abin da ya shafi yadda ake gina ma’ana ta hanyar za ɓ a ɓɓ un kalmomi da sauran dabarun nahawu kamar karin sauti  da makamantansa a jumla. Bloor da Bloor (2013:2) da Lamidi (2016:17) sun yi tarayya wajen bayyana cewa, ra’in ɗ oriya hanya ce wadda ke nazarin sa ƙ on da yake ƙ unshe cikin lafazi ko magana. Haka shi ma O’Donell (2012:2) ya bayyana cewa, ra’in ɗ oriya ya danganci yadda ake amfani da harshe domin yin mu’amala tsakanin mutane. Shi ya sa ya ba i wa yin amfani da ma’anar kalmomi a jumla’ muhimmanci a fagen nazarin harshe.

2.0 Jumloli Marasa Aikatau

Jumloli marasa aikatau suna dauke da aikatau wadanda ba su aiwatar da aiki. A cewar Hegedus (2013:58) aikatau da ke bayyana a irin wa ɗ anan jumloli ba su aiwatar da aiki, akasari suna sadar da aikau da jumla ne kawai. Ana kuma iya kiran su da jumloli masu shamaki domin aikatau da ke tattare da su yana kasancewa shamaki ne tsakanin aikau da kuma jumlolin. Stennes (1967) da Arnott (1970) da McIntosh (1980) da Newman (2000) da Jaggar (2001) da kuma Ɓ atagarawa (2013), sun tabbatar da haka.  A cewar Ɓ atagarawa (2013:60), jumla maras aikatau a Hausa tana ɗ auke da aikatau amma ba a mastayin kai yake ba, sai dai a mastayin shamaki, tsakanin aikau da jumlar . S hi ya sa McIntosh (1984:59) ta kira irin wannan jumla da suna jumla mai shamaki. Wato irin wannan jumla na da yanki guda ne maimakon yankin suna da yankin aiki, sai aka sami yankin suna kawai. Ire-iren wannan jumla sun ha ɗ a da jumla ƙ addamau da jumla daidaitau da jumla ganau da jumla nunau da jumla rayau ko zamau da jumla ingantau da kuma jumla motsa rai.

2.1 Jumla Ganau

Jumla ce wadda ta ke bayyana aikau ko kuma yin ƙ arin bayani a kansa. Shi ya sa masana irin su Stennes (1967:225) da Arnott (1970:31) da Jaggar (2001:459) da kuma Hegedus (2013:57) suka ce jumla ce mai nuna kamanni ko kalar abu domin a fahinci abin. A Hausa, masana irin su Newman (2000:545) da Jaggar 2001:457) da Ɓ atagarawa (2013:6-7) sun yi ittifa ƙ in cewa ana amfani ne da dirka (nee/cee) domin sarrafa Jumla Ganau a Hausa. A Fulatanci kuwa, dirka ba dole ba ne, asali ma, irin wannan jumla a Fulatanci na samuwa ne ta yin amfani da Sifa.

2.2 Jumla Ƙ addamau

J umla ce wadda ke gabatar da aikau a cikin jumla. A cewar Newman (2000:181) da Jaggar (2001:468) jumla ce wadda aka gina ta domin jawo ha n kali zuwa ga batu da aka riga da aka ƙ addamar ne kawai. A Hausa, Newman (2000:181) da Jaggar (2001:468) da Ɓ atagarawa (2013:84) sun yi tarayya a kan cewa ana sarrafa Jumla Ƙ addamau ta yin amfani da ɓ ur ɓ ushin ga, wanda Newman (ibid) ya ce ya tsiro daga aikatau ga(ni) → gani. Haka ma a Fulatanci Stennes (1967:155-166) da Arnott (1970:31) sun ce akwai wasu ke ɓ a ɓɓ a ɓ un kalmomin da ake amfani da su domin sarrafa irin wannan jumla kamar ndaa da kuma Hiin. Wannan na nuni da cewa, ɓ ur ɓ ushin ga a Hausa da kuma ndaa ko hiin a Fulatanci na da amfani matuka a gini irin wannan jumla ta Hausa da ta Fulatanci.

2.3 Jumla Rayau

J umla ce mai ishara ga rayuwa. Jespersen a shekarar (1924:155) ya ƙ ir ƙ iro irin wannan jumla, a inda ya ce jumla ce mai ishara ga rayuwar abu ko rashinta. Shi ya sa Ƙ uirk da Greenbaum (1980:419) suka ce jumla rayau, kawai, jumla ce mai nuna rayuuwar abu ko rashinta. Shi kuwa Newman (2000:176) ya ce ana furta jumla rayau ne ta yin amfani da kalmomin maha ɗ i akwai da kuma da. A Fulatanci kuwa Arnott (1970:32) ya ce a amfani ne da ɓ ur ɓ ushin ɗ on domin sarrafa irin wannan jumla. Saboda haka, za a iya cewa a kan sarrafa jumla rayau ta yin amfani da ɗ aya ko ma duka biyun kalmomin maha ɗ i domin furta irin wannan jumla a Hausa, a Fulatanci kuwa, ana amfani ne da ɓ ur ɓ ushin ɗ on .

3.0 Korewa

Korewa, ƙ wayar ma’ana ce gama-gari wadda take da muhimmaci sosai a nahawu kuma ana sarrafa samunta a kusan duk k an harsunan duniya. Dalili kuwa shi ne kowac e hanyar sadarwa ta ɗ an adam ta na ɗ auke da tunanin kalmar korewa. A cewar Jackson (2007:43) , k almar korewa na nufin furucin hani ko soke wani al’amari ko matsayi. Shi kuwa Crystal (2008:323) cewa ya yi, hanya ce ta ginin ma’ana wadda ta a’ anta wani ɓ angare na jumla ko kuma ɗ ungum ɗ in jumla. Shi ya sa Forest (1993:50-64) ya ce , kalmar korewa ƙ wayar ma’ana ce mai canza daraja r furuci daga gaskiya zuwa akasin hakan. Ha ƙ i ƙ a, haka maganar take, tun da ita kalmar korewa ba wai tana gabatar da sab o n batu ba ne a’a, ana amfani da ita ne a muhallin da muhawara ta riga ta kafu. Shi ya sa Mohsen (2011:1) ke cewa , amfanin korewa a bayyane take, domin tana kore wa ni al’amari na ɓ angaren jumla ko ma na jumlar baki ɗ aya. Hageman (1996:71) ya bayyana cewa , ana samun korewa a ya n kin aiki na jumla korau domin ita korewa ɗ in ta na da ala ƙ a ta ƙ u t- da - ƙ u t da aikatau a jumla . Amma , a jumla wadda ta kore ɓ angare guda k a wai, korewar na ala ƙ an cewa ne da ganga wadda take korewa ka ɗ a i. Saboda haka, ana iya cewa , korewa a b u c e mai muhammanci a f a gen ginin jumla dangane da nahawun harsunan duniya

Sigar korewa ta kasance ta sha bamban a harsuna, a yayin da wasu harsuna k an yi amfani da ɓ ur ɓ urshin kalma, wasu kan yi amfani da ɗ afi, a yayin da wasu kuwa sukan yi amfani da kalmar aikatau ta musamman domin nuna kore wa a cikin jumla. Hakan ne ya sa Dahl (1979:3) da Payne (1985:1) suka raba harsuna bisa ga irin sigar korewa da k o wane ya ke amfani da ita . Wato rukuni uku ke nan. Kodayake , wa ɗ a n nan nau’o’i n sigar korewa su ake samu a mafi akasarin harsunan duniya, Hausa da Fulatanci ma ba a bar su a baya ba tun da ɓ ur ɓ ushin korewa a wa ɗ a n nan harsuna biyu kan yi amfani da ɗ aya ko ma biyun cikin ukun.

A Nahawun Hausa, masana da manazarta da dama irin su Galadanci (1976) da Skinner (1977) da Newman (2000) da Jaggar (2001) da Zegelmeyer (2009) da kuma Ɓ atagarawa (2019) sun bayyana cewa, Hausa takan yi amfani da ɓ ur ɓ urshin korewa wajen kore jumla marasa aikatau. Har wa yau, jumloli marasa aikatau na Hausa suna amfani da ɓ ur ɓ urshin korewa guda biyu domin kore jumla, wa ɗ anda suka ha ɗ a da ra ɓ au baa…ba da kuma korau baabu/baa. Haka ma a Fufulde, masana da manazarta da dama irin su Taylor (1953) da Stennes (1967) da McIntosh (1984) da Ahmed (2011) da Aminu (2017) sun bayyana cewa, jumla korau maras aikatau a Fulatanci tana amfani ne da sigar ɓ ur ɓ urshin korewa guda biyu wa ɗ anda suka ha ɗ a da naa da kuma korau walaa/ngalaa.

4.0 Ƙ alailaicewa

Game da sarrafa korewa a jumloli marasa aikatau, ya dogara ne ga irin jumlar da ake sarrafawa. Domin, kowace jumla korau maras aikatau tana da irin ɓ ur ɓ ushin kalmar korewa da ake sarrafawa. Wato, wannan mu ƙ ala ta ta ƙ aita ne a kan misalai daga jumla ganau da ta ƙ addamau da kuma jumla rayau .

4. 1 Korewa a Jumla Ganau

Jumla ganau jumla ce wadda take bayyana aikau ko kuma yin ƙ arin bayani a kansa. Ƙ ara wa jumlar ganau ɓ ur ɓ ushin korewa yana kore gaskiyar al amarin da jumlar ta bayyana. A Hausa ana amfani da korau ra ɓ au baa…ba tare da dirka nee ga jinsin namiji da kuma jam’i sai kuma cee ga jinsin mace.   Mu dubi wa ɗ annan jumloli:

Misali na 1:

Lamba

Jumla Ganau

Jumla Korau

        i.             

i ta cee.

baa ita cèe ba.

      ii.             

gwado nee.

baa gwado nee ba.

   iii.             

mataashi nee shi.

baa matashi nee shi ba.

   iv.             

doguwa cee.

baa doguwa cee ba.

 

A wa ɗ annan misalai, an ga amfanin ɓ ur ɓ ushin korau baa…ba, a inda yake kore aikau da jumlar ta bayyana. A nan, amfanin korau baa…ba a wannan jumla, shi ne ta kore ko a’anta ko kuma soke aikau da jumlar ta bayyana. Hakan na faruwa ne idan aka ha ɗ a ɓ ur ɓ ushin korewa ra ɓ au baa…ba da dirka cee ko kuma ga namiji ko jam’i ana amfani da nee.

Misali na 2:

Lamba

Jumla Ganau

Jumla Korau

        i.             

s uu nee.

b aa su nee ba .

      ii.             

f arare nee.

b aa farare nee ba .

   iii.             

ƙ onannu nee.

b aa ƙ onannu nee ba

   iv.             

d oogaye nee su

b aa dogaye nee su ba.

 

A nan, kalmar dirka nee tare da korau ra ɓ au ba a …ba (wato korau mai ƙ a f a biyu, a farko da ƙ arshen jumla) duk a ka n sarrafa su ne a yayin kore jumla ganau ta Hausa. A wa ɗ anan misalai, za a ga cewa , kor au tare da dirka su suka n gina yankin aiki a jumlar kuma suka ba i wa jumlar ma’anarta ta jumla korau. Kodayake dirka a irin wannan jumla, ba dole ne ba , tun da a ka n iya sarrafa jumlar kuma ta ba da ma’ana ba tare da an yi amfani da dirka ba , kamar yadda za a gani a misali na 3.

Misali na 3 :

Lamba

Jumla Ganau

Jumla Korau

        i.             

i ta cee.

b aa ita ba.

      ii.             

s hi nee .

b aa shi ba.

   iii.             

f ara cee .

b aa fara cee ba.

 

Wa n nan ya na nuni cewa , yin amfani da dirka a jumla ganau ta Hausa ba dole ne ba . Wato, jumlar ta na sarrafuwa ne ko da ta kasance babu dirka a cikinta.

A Fulatanci kuwa, kodayake ba a tantance jinsi, amma ana amfani ne da wakilin suna wanda yake nuna ajin kalmar da kuma adadi tare da ɓ ur ɓ ushin korewa naa domin kore jumla ganau. Misali na 4:

Lamba

Harshe

Jumla Ganau

Jumla Korau

        i.             

Ful ɓ e

n du sonndu.

ndu naa sonndu.

 

Hausa

(wannan + tsuntsuu)

(wannan + korau + tsuntsuu)

 

Jumla

wannan tsunstuu nee.

wannan ba tsuntsuu nee ba.

A wannan misali na 4 da yake sama, an ga yadda harshen Fulatanci , kamar dai a Hausa, yake sarrafa ɓ ur ɓ ushin korewa wajen kore jumla. Bambamci tsakanin tsarin harsunan kuwa ya bayyan ta fuskar kalamomin da su ke ha ɗ uwa da ɓ ur ɓ ushin korewa domin kore tabbacin alamari. Ɓ ur ɓ ushin korewa a harshen Fulatanci na ha ɗ ewa da kowane azuzuwan wakilin suna nunau guda ashirin da shida da ake da su a harshen domin samar da irin wannan jumla . Wannan ya bambanta da ta Hausa a inda ɓ ur ɓ ushin korewa ke ha ɗ ewa da dirka domin kore jumla. Saboda haka, za a iya cewa kalmar dirka a harshen Hausa da kuma wakilin suna nunau a Fulatanci na taimakawa wajen kore tabbacin alamari a jumla na nau. Haka ma idan wakilin suna a Fulatanci na nuna jam’i, ta yin amfani da wakilin suna ɗ i a maimakon ndu na misali da ya gabata.

Misali na 5:

Lamba

Harshe

Jumla Ganau

Jumla Korau

        i.             

Ful ɓ e

ɗ iya colli .

ɗ iya naa colli.

 

Hausa

(wa ɗ ancan + tsuntsayee + nee)

(wa ɗ ancan + korau + tsuntsayee)

 

Jumla

wa ɗ ancan tsuntsayee nee.

wa ɗ ancan ba tsuntsayee ne ba.

A nan, an ga cewa wajen furta jumla ganau a Fulatanci, ana amfani da jam’in wakilin suna nunau tare da ɓ ur ɓ ushin korau. Ita wakilin suna nunau kan iya zama tilo ko jam’i, wanda ya sha bamba n da dirka na Hausa wanda yake nuna bambamcin jinsi. Haka kuma idan aka dubi amfanin wa ɗ anan kalmomi a irin wannan jumla za a ga cewa suna kore jumlar ne.

Ana koma iya yin amfani da ɓ ur ɓ ushin korau naa da kalmar abin da aka kora kawai a misalai kamar haka:

Misali na 6:

Lamba

Harshe

Jumla Ganau

Jumla Korau

        i.             

Ful ɓ e

l eeso on.

naa leeso.

 

Hausa

(gado nee)

(korau gado)

 

Jumla

gado nee.

baa gado nee ba.

      ii.             

Ful ɓ e

ɗ erewol on.

naa ɗ erewol.

 

Hausa

(tak ά rdaa cee)

(korau tak ά rdaa)

 

Jumla

takardaa cee.

baa takardaa cee ba.

Wa ɗ anan jumloli d ake misali na 6, sun nuna cewa ana iya kore jumla nunau a Fulatanci ba tare da yin amfani da k almar dirka on ko kuma wakilin suna nunau ba. Wan n an ya bambamta da yadda jumla nunau yake a Hausa inda ya zama tilas a yin amfani da dirka domin yin nuni . W a ɗ a n nan harsuna biyu sun nuna bambanci ta fuskar kalmomi da suke ha ɗ uwa da k almar korewa domin su samar da korewa a jumla nunau . A yayin da Hausa take amfani da korewa ra ɓ au baa…ba tare da dirka nee/cee, Fulatanci na amfani da ɓ ur ɓ ushin korewa naa da kuma wakilin nunau suna wa ɗ anda suke zuwa a bisa azuzuwan suna guda ashirin da shida da ake da su a harshen tare da ƙ wayar korewa naa.

4. 2 Korewa a Jumla Ƙ addamau

Irin wanan jumla na ƙ addamar da aikau a jumla . K ore irin wannan jumla a harshen Hausa da Fulatanci na bu ƙ atar amfani da ɓ ur ɓ ushin korewa. Har ila yau, Hausa na amfani da ra ɓ au baa…ba a yayin da Fulatanci ke amfani da naa. Kodayake masana da dama na gan in cewa ba a kore jumla ƙ addamau, domin sai abin da ke akwai ake ƙ addamarwa. Duk da haka, ana iya amfani da korau a irin wannan jumla domin ci m ma w ani buri n a daban. A Hausa, ana amfani ne da ɓ ur ɓ ushin korewa ra ɓ au da kuma alamar motsin rai.

Misali na 7:

Lamba

Jumla Ƙ addamau

Jumla Korau

        i.             

gaa dookin.

baa gaa dookin ba!

      ii.             

gaa shi.

baa gaa shi ba!

   iii.             

gaa ni

baa gaa ni ba!

A wa ɗ annan misalai na Hausa, ɓ ur ɓ ushin korewa baa…ba, a nan, ba ta kore jumlar amma tare da alamar motsin rai da kuma ɓ ur ɓ ushin ga, sun ha ɗ u ne don ƙ arfafawa da ƙ ara ƙ addamar da aikau a cikin jumlar, ba don a kore ma’anar jumlar ba. Ana kuma iya amfani da iyalin bayanau nan da can tare da ɓ ur ɓ ushin korewa a irin wannan jumla.

Misali na 8:

Lamba

Jumla Ƙ addamau

Jumla Korau

        i.             

gaa littafin can.

baa gaa littaafin can ba!

      ii.             

gaa su nan.

baa gaa su nan ba!

   iii.             

gaa ni nan

baa gaa ni nan ba!

 

A nan, amfanin da ɓ ur ɓ ushin korewa a wa ɗ annan jumloli ba yana nufin sun kore jumlar ba, a’a, sun dai ƙ ara wa jumlar bayani ne. Yin amfani da ɓ ur ɓ ushin korewar ƙ addamau tare da ɓ ur ɓ ushin ga da kuma alamar mosin rai, na ha ɗ ewa ne domin su ƙ ara kaddamar da aikau jumla. Wannan na nuni da cewa ba a kowace jumla ɓ ur ɓ ushin korewa ra ɓ au ba a …ba a harshen Hausa ke kore tabbacin alamari ba.

Haka ma a Fulatanci, amfanin ɓ ur ɓ ushin korewa naa a jumla ƙ addamau kamar a Hausa ne, ba ta kore jumlar, sai dai ta ƙ ara ƙ arfafa jumlar da aikau da ke cikin jumlar.

Misali na 9:

Lamba

Harshe

Jumla Korau

Jumla Ƙ addamau / Ƙ arfafau

        i.             

Ful ɓ e

n daa defte ma.

n aa ndaa d efte ma!

 

Hausa

(korau + ga + littatafan + ka/ki)

ba a ga a litatta a f a nka/ki ba!

A nan, in an lura za a ga cewa an yi amfani da ɓ ur ɓ ushin ndaa tare da ɓ ur ɓ ushin korewa amma hakan bai sa jumlar ta z ama korau ba. Asali ma kalmomin na ƙ arfafa jumlar ne. Har wa yau, Fulatanci shi ma ya na amfani da iyalin bayanau d o n ƙ ara ƙ arfafawa da kuma ƙ addamar da aikau da ke cikin jumlar.

Misali na 10:

Lamba

Harshe

Jumla Korau

Jumla Ƙ addamau /Nunau

        i.             

Ful ɓ e

ndaa defte ma haa ɗ o!

n aa ndaa defte ma haa ɗ o!

 

Hausa

korau + ga + litattafan + ka/ki a + (manuni nan)

b a a ga a litattafanka/ki a nan ba!

A nan , za a ga cewa ɓ ur ɓ ushin kalmomin nan guda biyu, ndaa da kuma korewa naa suna taimakawa wajen jaddada sa ƙ on da jumlar ke ƙ o ƙ arin isarwa. Wannan na nufin sarrafa irin wannan jumla a Hausa da Fulatanci a na amfani da ɓ ur ɓ ushin korewa iri ɗ aya a yayin da harsunan suke sarrafa k almar n u nau da kuma ɓ ur ɓ ushin korewa domin gabatar da irin wannan jumla. Har wa yau, aukuwar wa ɗ an n an kalmomi a irin wannan tsari ba ya nufin jumlolin a harsuna biyun sun zama jumloli korau ne ba , a a, kawai suna tabbatar wa da kuma nuna gaskiyar al amari.

Saboda haka, ana iya cewa akwai kamanci na ku t- da - ku t t a yadda harshen Hausa da na Fulatanci suka yi kamanceciniya ta fuskar sarrafa ɓ ur ɓ ushin korewa da kuma sauran ɓ ur ɓ ushin kalmomi da suke ha ɗ uwa da korau wadda suka ha ɗ a da ɓ ur ɓ ushin ga a Hausa da kuma ndaa a Fulatanci, sai kuma alamar motsin rai wa d da harsunan su k an yi amfani da ita wajen isar da sa ƙ o da kuma nuni da cewa wa ɗ anan jumloli ƙ addamau ne. 

4. 3 Korewa a Jumla Rayau

Jumla rayau, jumla ce mai ishara ga rayuuka ko kuma mallakarsa ga wani abu a cikin jumla.   Ɗ afa wa jumlar ɓ ur ɓ ushin korewa na nuni da cewa aikau da ya ke cikin jumlar ba sh i da ala ƙ a da kar ɓ au ko kuma shi aikau ɗ in bai mallaki abin ba. Saboda haka, tsarin kore irin wannan jumla a harshen Hausa da na Fulatanci sun yi tarayya a kan turba guda. Abin da ake nufi a nan , shi ne, harsunan Hausa da Fulatanci suna sarrafa ɓ ur ɓ ushin korewa na musamman (wanda ake kira da negati v e e x istential markers ) domin kore irin wannan jumla.

A Hausa, ana amfani da kalmar korewa baabu da baa ta domin kore irin wannan jumla. Wa ɗ a n nan kalmomi guda biyu, wani lokaci suna na fitowa a mastayin ɗ aya, a wani lokaci kuma guda ɗ aya kawai ake bu ƙ ata.

Misali na 11:

Lamba

Jumla Rayau

Jumla Korau

        i.             

da shi a cikinsu.

baabu shi a cikinsu.

A wa ɗ annan misalai da suka gabata, sun nuna cewa za a iya amfani da kowace kalmar korau kuma ta ba da cikakkiyar ma’ana a jum la. Ana iya cewa ba ya

 cikinsu ko kuma baabu shi cikinsu, na da cik a kkiyar ma’ana. Korewa a jumloli duka biyu anan na kore gaskiyar alamari. Har ila yau, idan aikau din jumla ya na iya z uwa a farkon jumla, ɓ ur ɓ ushin k almar korau baa ya bin sa.

Misali na 12:

 

Lamba

Jumla Rayau

Jumla Korau

        i.             

baabarmu tana gida.

baabarmu ba ta gida.

 

A wannan misali, an yi amfani da baa a maimakon baabu domin aikau ya zo a gabanin shi kalmar korau ɗ in. Duk da hakan korau a wannan jumla ya na kore gaskiyar jumlar ne . Haka kuma , idan jumlar ta na kore abin da aikau ya mallaka, korau ɗ in da za a yi amfani da shi ya kan daganci irin wakilin sunan kalmomin da aka yi amfani da su .

  Misali na 13:

 

Lamba

Jumla Rayau

Jumla Korau

        i.             

yana da komai.

ba shi da komai.

      ii.             

suna da gida

ba su da gida.

   iii.             

yana cikin wa ɗ anda suka ci jarrabawa

ba yaa cikin wa ɗ anda suka ci jarrabawa.

 

A wa ɗ annan misalai, za a g a korewa r ta zo da jer i n kalmomi daban daban. A na farko, za a ga jumlar ta zo da maha ɗ i da wanda ke karbar korau ba kawai da kuma wakilin suna mutum na uku. Jumla ta uk u kuwa na iya ɗ aukar kowane cikin korewa r tun da ba y a zuwa da mah a ɗ i da. Don haka, ana iya cewa korau da za a yi amfani a jumla ya danganci irin kalmomin da suka zo cikin jumla.

A Fulatanci kuwa, jumla rayau ta na amfani da kalmar korewa walaa g a tilo ko ngalaa g a jam’i domin nuna kore wa a cikin jumla.

Misali na 14:

Lamba

Harshe

Jumla Raya u

Jumla Korau

        i.             

Ful ɓ e

ɓ inngel (ngel) mari pa ɗ e.

ɓ inngel (ngel) walaa pa ɗ e.

 

Hausa

(yaro/yarinya + (wannan) + korau + takalmi.)

yaron/yarinyar (nan) ba shi/ta da takalmi.

 

 

 

 

      ii.             

Ful ɓ e

mi mari saare mau ɗ ee

mi walaa saare mau ɗ ee.

 

Hausa

(ina + da + gida + babba )

( ni + korau + gida + babba)

 

 

 

baa ni da babban gida.

 

A wa ɗ annan misalai za a ga cewa korau di n jumloli ne ka ɗ ai a mastayin yankin aiki kuma suna kore abin da ak a mallaka. Haka ma yin amfani da korau mai nuna jam’i na abu ko mutum fiye da ɗ aya, ana amfani da ngalaa kuma shi ma korewa ce ko kuma nuna rashin abin da aikau ya mallaka yake yi.

Misali na 15:

Lamba

Jumla Rayau

Jumla Korau

        i.             

ɓ e mari ndiyam yarugo.

ɓ e ngalaa ndiyam yarugo

      ii.             

(suna + da + ruwan + sha

su + korau + ruwan + sha)

   iii.             

 

baa su da ruwan sha.

 

A nan korau na nuna jam’i da kuma kore abin da aikau ya mallaka. Wannan na nufin cewa, lallai, korau da ke zuwa a jumla rayau na kore jumla ko ma a ce kore abin da aikatau n a jumlar ya mallaka. Don haka a iya cewa, kalmar korau baabu/baa da kuma walaa/ngalaa suna zuwa ne a jumla rayau domin kore abin da jumlar ta gaskanta.

Jumla rayau a Hausa da Fulatanci na da kamanci masu yawa saboda irin jumlar a harsuna biyun na amfani da korau na musaman wanda kowane harshen na da guda biyu. Haka kuma , suna yin aiki iri ɗ aya wagen kore gaskiyar jumlolin. Bambamcin korewa a wainan harsuna biyu shi ne amfaninsu ta wajen mu amala da jumla a inda baabu da baa a Hausa ke mu amala da juna ta fuskar zamowa mawakilta juna , walaa da ngalaa a Fulatanci kuwa na mu amala ta fuskar adadi.

5. 0 Ta ƙ aitawa da kuma Kammalawa

Idan aka yi la’akari da bayanan da suka gabata za a iya fahimtar cewa akwai kamanci masu dama a jumloli korau marasa aikatau na Hausa da Fulatanci. Kamancin ya shafi adadin ɓ ur ɓ ushin korewa da ake sarrafawa a irin wa ɗ anan jumloli. A yayin da harshen Hausa ke sarrafa da guda biyu wato, korau ra ɓ au baa…ba kamar a misalai na 1 zuwa na 3 da kuma korau rayau baabu/baa, a misalai na 11 zuwa na 13, haka ma Fulatanci, korau guda biyu yake sarrafawa, wa ɗ anda suka ha ɗ a da ɓ ur ɓ ushin naa kamar a misalai na 4 da na 6, da kuma korau rayau walaa/ngalaa a misalai na 14 da kuma 15. Har wa yau, idan aka dubi aikin da ko wacce siga ke yi a harsuna biyun, za a ga cewa suna kore jumla iri ɗ aya ne. Korau ra ɓ au baa…ba kamar a misalai na 7 da na 8 a Hausa da ɓ urbushin naa na Fulatanci da yake kore jumloli ganau da ƙ addamau a misalai na 9 da na 10. Haka lamarin yake tsakanin korau baabu/baa na Hausa da walaa/ngalaa na Fulatanci da suka kore jumla rayau a harsuna biyun kamar yadda aka kawo a misalai na 11 zuwa na 15. Har ila yau, ta yin amfani da ra’in Halliday, an gano cewa akwai bambamci da kamanci a yadda ake sarrafa ɓ ur ɓ ushin korewa a jumloli marasa aikatau na Hausa da Fulatanci. Ta fuskar kamanci, an gano cewa, a jumla ƙ addamau , Hausa da Fulatanci sun yi tarayya ta fuskar yin amfani da ɓ ur ɓ ushin korewa tare da ɓ ur ɓ ushin ga, sai kuma alamar motsin rai. Wato a nan, harshen Hausa da Fulatanci suna yin amfani da ƙ wayoyin kalma iri guda domin furta irin wannan jumla. Wa ɗ anan ɓ ur ɓ ushin a Hausa da Fulatanci, ba sa kore jumla ƙ addamau, maimakon haka, suna tabbatar da sa ƙ on da jumlar ke isarwa ne. Haka ma a jumla ganau, Hausa da Fulatanci sun yi tarayya wajen sarrafa ɓ ur ɓ ushin korewa. A yayin da ɓ ur ɓ ushin korewar ke fitowa a farkon jumla, ko kuma a tsakiya idan wakilin suna ne a farko. Wannan na nufin ɓ ur ɓ ushin korewa a harsuna biyun na aiwatar da aiki iri ɗ aya; ko su kore jumla ko kuma su jaddada ta, ko kuma tabbatar da aikau ɗ in jumlar.

Duk da yawan kamanci, ba za a rasa bambamci ba, a inda korau rayau baabu da baa kan iya bambanta, shi kuwa walaa da ngalaa a Fulatanci ana amfani da su ne domin nuna bambamcin adadi. Haka ma ana samun bambamci wajen ƙ wayoyin kalma da ake sarrafawa, kamar yadda aka nuna a jumla ganau, inda Hausa ke amfani da dirka, a Fulatanci kuwa, ana amfani ne da azzuzuwan wakilin suna ashirin da shida da ake da su a harshen. Daga ƙ arshe, duba ga tarin kamanci a tsarin korewar jumlioli marasa aikatau na Hausa da na Fulatanci, ana hasashen cewa, idan aka tattara irin wa ɗ anan bayanai, za su iya ba da haske wajen sake bibiya, ko a ce za a iya samu dangantaka ta jini a tsakanin wa ɗ anan harsuna guda biyu da ake ikirarin ba su da ala ƙ a ta jini.

Manazarta

Ahmed, A. I. (2011) . Introduction to Fulfulde Syntax. Muenchen: Lincom Europa Academic Publications .

Aminu, A. (2017). Morphosyntactic Analysis of Fulfulde Voice and Tense in Adamawa Dialect: A Case Study of Yola South. In Journal of Linguistics Association of Nigeria Vol. 20 No. 2 p.21-27 .

Arnott, D. W. (1970). Nominal and Verbal Systems of Fula Oxford: Clarendon Press.

Bagari, M. D. (1986) . Bayanin Hausa. Rabat: Imprimerie El Maarif Al Jadada Press.

Bargery, G. P. (1934) . Hausa-English Dictionary and English-Hausa Vocabulary London: Oxford University Press.

Bloor, T. and Bloor, M. (2013) . The Functional Analysis of English: A Hallidayan Approach USA: Routledge.

Ɓ atagarawa, A. G. (2013) . Movement Operations in Hausa Non-verbal Sentences Unpublished Ph.D. Thesis Zaria: Department of African Languages and Cultures, Ahmadu Bello University.

Dahl, O. (1979) . Typology of Sentence Negation Linguistics p.17,79-106.

Forest, R. (1993) . Negation : Essai de Syntax et de Typologie Linguistique Collection Linguistique LXXVII Paris: Klincksieck.

Galadanci, M. K. M. (1976) An Introduction to Hausa Grammar Kano: Longman Nigeria Abdullahi Bayero College,

Greenberg, J. H. (1948) . The classification of African Languages America: New series Vol. 50 No. 1 Part1 American Anthropologist Association

Haegeman, L. (1995) The Syntax of Negation Cambridge: Cambridge University Press.

Halliday, M. (1985) . Introduction to Functional Grammar . London : Arnold .

Halliday, M. (1994) . Introduction to Functional Grammar ( 2n d ed ). London : Arnold .

Halliday, M. & Matthiessen, C. ( 2004 ) . Introduction to Functional Grammar (3rd ed). London : Arnold .

Hegedus, V. (2013) . Non-Verbal Predicates and Predicate Movement in Hungarian Netherlands: LOT Trans 10 .

Horn, L. (1989) . A Natural History of Negation Chicago and London: University of Chicago Press.

Jackson, E. (2007) . Weak and Strong Negative Polarity Items: Licensing and Inter ɓ ention Linguistic Analysis p.25-181

Jaggar, P. J. (2001) . Hausa. London: London Oriental and African Language Library

Johnston, H. A.S ( 1967) . The Fulani Empire of Soko Nairobi: West African Graphic Company Ltd.

Kyambo, B. S. (2019) . Kwantancin Yankin Aiki a Hausa da Fulfulde. Unpublished Ph.D. Thesis

McIntosh, M. (1984) . Fulfulde Syntax and Verbal Morphology Great Britain: Routledge & Kegan Paul PLC.

Moscati, V. (2010) . Negation Rising: Logical Form and Linguistic Variation Cambridge: Cambridge Scholars Publishing.

Mohsen, K. H. (2011) . Negation in English. Unpublished MA Dissertation Department of Foreign Languages and Translation University of Agder.

Newman, P. (2000). The Hausa Language: An Encyclopedic Reference Grammar London: Yale University Press.

O’Donnell, M. (2012) . Introduction Systemic Functional Linguistic for Discourse Analysis-Language Function & Cognition http://docplayernet

Payne, J. (1985) . Negation: Language, Typology and Syntactic Description of Clause Structure Cambridge: Cambridge University Press

Ƙ uirk, R. & Greenbaum, S. (1985) . A Comprehensive Grammar of the English Language. London: Longman

Sani, M. A. Z. (1999) . Tsarin Sauti da Nahawun Hausa Ibadan: University Press PLC.

 Skinner, N. (1977) . A Grammar of Hausa Zaria: Northern Nigeria Publishing Company Ltd.

 Speranza, J. L. & Horn, L. R. (2010) . A Brief History of Negation Journal of Applied Logic V ol.8 www.else ɓ ier.com/locate/jal

Stennes, L. H. (1967) . A Reference Grammar of Adamawa Fulani Michigan: Michigan University.

Taylor, F. W. (1932) . Fulfulde – English Dictionary Oxford: Oxford University Press.

Taylor, F.W. (1953) . A Grammar of the Adamawa Dialect of the Fulfulde Language Oxford: Oxford University Press.

Yusuf, M. A. (2011) . Hausa Grammar: An Introduction Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

Zaria, A. B. (1981) . Nahawun Hausa Lagos: Thomas Nelson Nigeria Limited.

Zarru ƙ , R. M. (2005) . Bishiyar Li’irabi: Nazarin Jumlar Hausa Zaria: Institute of Education Ahmadu Bello University.

Ziegelmeyer, G. (2009) . Negation of non-indicative mood in Hausa, Fulfulde and Kanuri Negation Patterns in West African Languages and Beyond. Amsterdam: John Benjamins Publishing Company P. 7-20.

Post a Comment

0 Comments