Table of Contents
- Tsakure
- Gabatarwa
-
Mutuwar
H
arshe a Ilimin
Kimiyar Harshe
- Nau’o’in Mutuwar Harshe
- Dalilan Mutuwar Harshe
- Matakan Mutuwar Harshe
- Mizanan Auna Mutuwar Harshe
-
Ko
Akwai Ra’in Nazarin Mutuwar Harshe?
- Hanyoyin Farfa ɗ o da Harshe
- Waiwaye A Kan Ke ɓ a ɓɓ un Kalmomin Nazarin Mutuwar Harshe
- Kammalawa
- Manazarta
Nazari a Kan Mutuwar Harshe
Daga
Isah Abdullahi Muhammad.
Ph.D
Na Sashen Harsunan
Nijeriya
Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato
Email:
amisah2007@yahoo.com
Phon.No: +2347037484144
Tsakure
Batun nazarin
mutuwar harshe,
reshe
na Ilimin Walwalar Harshe,
yana
da
matu
ƙ
ar muhimmanci da ban sha
’
awa. Duk da yake ko a fagen nazarin
kimiyar harshe, batu ne wanda ba ya da farin jini
ga manazarta Ilimin Walwalar Harshe
. Wannan ya sa bai samu
kulawar da ta kamace shi ba, musamman ma wajen
manazarta
harshen Hausa
. Wannan ya sa aka
ƙ
udurci kawo batun a bisa faifan nazari
a wannan takarda
.
Yawancin bayanai da aka yi a wannan nazarin a
n gina
su ne a kan tafarkin bayanin mutuwar harshe
na Crystal (2003,
2014).
Babban abin da wannan takarda ta mayar wa hankali shi ne, fitowa da nazarin
mutuwar harshe a zahiri
a ri
ƙ
a jin
ɗ
uriyarsa a nazarin
Hausa. Sakamakon nazari
na wannan takarda shi ne fitowa da ma’anar
mutuwar harshe da nau’o’insa da matakansa da mizanansa da ra’in nazarinsa da
kuma ke
ɓ
a
ɓɓ
un kalmomin nazarin mutuwar harshe. Nazar
i
n yana da manyan sassa hu
ɗ
u, su ne: Gabatarwa da bayani a kan harshe da mutuwar harshe
a ilimin kimiyyar harshe
,
s
ai sakamakon nazari da kammalawa.
Gabatarwa
Harshe fitacciyar hanya ce kuma tsararriya ta sadarwa ga
mutane. A wata fahinta, halitta ce wadda Ubangiji ya ke
ɓ
anci mutum da ita. Duk
yadda wata halitta
ta
la
ƙ
anci sarrafa harshe abu ne mai wahala ta kai ga mutum. Ha
ƙ
i
ƙ
a Mahalicci, ya mallaka
wa ‘yan’adam harshe.
Akwai ala
ƙ
a ta
ƙ
ud-da-
ƙ
ud a tsakanin harshe da mutum. Saboda haka, yadda mutum
yake da rai wata rana ya mutu. Haka ma, harshe yakan rayu kuma idan lokaci ya
yi, ya mutu. Mutuwar harshe fage ne da ake nazarin halin da harshe yake ciki da
duk wani abin da
ya shafi ha
ɓ
akar
harshe
da dur
ƙ
ushewarsa
.
Mutuwar harshe ba kamar irin mutuwar mutum ba ce, suna da bambanci. A mafi
yawan lokuta, akan sami dalili
ɗ
aya
,
ya yi sanadiyar mutuwar
mutum. Sa
ɓ
anin harshe wanda dalilai da yawa ne suke haifar da
mutuwarsa. Akan ce harshe ya mutu ne, idan babu sauran mai iya magana da shi a
do
ro
n
ƙ
asa ( Crystal, 2014).
Nazarin
mutuwar harshe ko a fagen nazarin kimiyyar harshe bai samu cikakkiyar kulawa
kamar yadda sauran fannoni suka samu ba. Haka ma a nazarin Hausa,
kwata-kwata
ba ka jin
ɗ
uriyar nazarin mutuwar
harshe. Wannan ya sa, a nan, aka
ƙ
udurci
ɗ
auko batun a fito da shi
fili, domin raya shi da
nazari
n sa
da
kuma
tattaunawa a tsakanin
manazarta.
A ta
ƙ
aice, abubuwan da ake son tattaunawa a kan su, su ne:
Harshe da mutuwar harshe a kimiyyar harshe. A
ƙ
ar
ƙ
ashins
u
, akwai
ma
’
anar mutuwar harshe da
nau
’
o
’
insa da matakan mutuwar harshe da mizanan mutuwar harshe
da kuma hanyoyin farfa
ɗ
owa da harshe wanda yake
a kan gararin mutuwa.
Harshe
Abin tambaya a nan
shi ne, mene ne harshe? Ma’anar harshe ana iya kasa ta gida
biyu:
a.
Ma’ana gama-gari
b.
Ke
ɓ
antacciyar ma’ana
Ma’ana gama-gari,
ma’ana ce wadda aka fi samu daga bakunan masana da ma manazarta. Wato dai
ma’ana ce ta kai-tsaye. Da za ka tambayi wani a kan ma’anar harshe zai iya ce
maka ‘harshe shi ne magana’. A wani lokaci kuma, a ce maka tsararriyar hanyar
sadarwa ce. A mizanin wa
ɗ
annan bayanai,
harshe
magana ce kuma sadarwa ce ( Bagari, 1986).
Anyanwu
(2007:7) ya ce:
Language is a type of patterned human behaviour. It is a
way; perhaps the most important way; in which human beings interact in social
situations.
Fassara:
Harshe yana daga cikin halaye na
ɗ
an’adam wanda yake da tsari na musamman. Haka kuma, wata
muhimmiyar hanyar ce wadda
ɗ
an’adam yake
amfani da ita wajen hul
ɗ
ayya cikin
al’umma.
Har wa yau, malamin ya kawo wasu siffofin harshe tara na
ɗ
an’adam. Ga su kamar haka:
1.
Harshe fage ne na
ƙ
ir
ƙ
irar abubuwa (
wato
‘
creative
’
da Ingilishi).
2.
Harshe wakili ne
ba abin da aka furta ba ne. Wato dai, babu ala
ƙ
a ta kamanci a
tsakanin abin da aka furta da abin kansa ( da Ingilishi, shi ne
‘
arbitrariness
’
).
3.
Harshe gamin-gambiza
ne na sautuka daban-daban wa
ɗ
anda asali ba wata
ma’ana suke da ita ba (Wato ‘duality’ da Ingilishi).
4.
Harshe wata hanya
ce
da za a yi amfani da ita domin yin lin
ƙ
aya ga abin da zai
faru. Ko kuma har ya faru, ba dole ne sai in yana faruwa ba (wannan shi ne
Displacement).
5.
Harshe hanya ce ko
kafa ta ya
ɗ
a al’ada (wato
‘cultural transmission’).
6.
Harshe al’amari ne
da ya ginu bisa wani tsari kuma daki-daki, ba kara zube ba. Wato daga matakin
sautuka zuwa kalmomi zuwa jumloli (da Ingilishi shi ne ‘Pattern congruity’).
7.
Akwai ala
ƙ
a ta dindindin a
tsakanin kalmomi da ma
’
anarsu (shi ne
‘
Constancy
’
).
8.
Harshe al’amari ne
da ba a sanya masa shinge ( shi ne ‘Versatality’).
9.
Harshe wata hanya
ce ta bayyana matsayi ko wata
ƙ
warewa (wannan shi ne
‘
Specilazation’).
Bauer & Calude
(2020:1) ga abin da suke cewa a kan muhimmancin harshe:
Language is a powerful tool that help us to think and
make sense of the world, that we use to transmit our cutural histories that we
use to entertain, convince, seduce, inform and misleads.... language is
everyone business.
Fassarar Marubuci:
Harshe wani babban jigo ne da yake sanya mu zurfafa
tunani domin gano hikimar da take
ƙ
unshe cikin duniya, da harshe ake isar da tarihin al
’
adu kuma a nisha
ɗ
antar, a gamsar da mutum, a janyo ra’ayinsa kuma a fa
ɗ
akar, wani lokaci akan yi yaudara da harshe...Ha
ƙ
i
ƙ
a harshe hajar
kowa ce’
Su ma O’Grady
& Dobrovosky & Katamba (1996:1) sun
ƙ
ara jaddada mana haske,
kamar haka:
Language is many things, a system of communication, a
medium for though, a vahicle for literary expression, a social institution, a
matter for political controvesy a catalyst for nation building.
Fassarar Marubuci:
Harshe sirri ne kome-da-ruwanka, kuma kyakkyawan tsari na
sadarwa, kafa ta bayyana fahinta, taska ce da adabi mai
ƙ
unshe da tsari na
rayuwar al
’
umma, hanya ta tafka muhawara ga ‘yan siyasa kuma ginshi
ƙ
in gina
ƙ
asa da kawo
cigaba.
Wannan dai, ya nuna cewa harshe hanya ce ta yin magana
don sadarwa mai siffofi daban-daban.
A ke
ɓ
antacciyar ma’ana wadda ba ta gama-gari ba. Wato dai, ta
ke
ɓ
anta ne ga
fahintar wata mazhaba ko ra’i. A mazhabar Chomsky a karon farko wata halitta ce
da take shimfi
ɗ
e a cikin jikin
ɗ
an’adam wadda take taimaka masa wajen la
ƙ
antar harshe,
cikin
ƙ
an
ƙ
anen lokaci. Kuma la
ƙ
anta ta ha
ƙ
i
ƙ
ani, wadda take sa
idan ka yi kure, ya gyara maka. Wannan harshe ne gama-gari, duk halittar
ɗ
an’adam, tana da shi. Sai kuma,
ɓ
angare na biyu, wanda yake nuni ga harshen da kowa yake
magana da shi wanda mutum ya tashi cikinsa ( Cook & Newson 2007. Carnie
2013).
Mutuwar
H
arshe a Ilimin
Kimiyar Harshe
Ilimin kimiyar
harshe, fage ne wanda ake nazari a kan kimiyar da take cikin harshe
n
ɗ
an’adam (
McGregor,2009). Shi ko mutuwar harshe,
ɓ
angare ne muhimmi a
ƙ
ar
ƙ
ashin nazarin walwalar
harshe, inda ake duba halin da harshe yake ciki, dangane da cigabansa ko
cibayansa.
Za
ncen mutuwar harshe ya fara samun
kulawa ne daga masana harshe daga shekarun 1990. Kamar yadda Crystal (2014: vii)
ya bayyana:
In 1992, linguists attending the
international linguistics congress in Quebec agreed the following statement:
As the disappearance of any one language constitutes an
irretrievable loss to mankind, it is for UNESCO a task of great urgency to
respond to this situation by promoting and if possible, sponsoring programs of
linguistic organizations for the description in the form of grammars,
dictionaries and texts,
i
ncluding
the recording oral literatures, of hitherto unstudied or inadequately
documented endangered and dying languages.
Fassarar Marubuci:
A taron
ƙ
asa-da-
ƙ
asa na kimiyar
harshe da aka yi a Kyuba shekarar 1992, masana kimiyar harshe, sun yi matsaya a
kan cewa:
Ha
ƙ
i
ƙ
a
ɓ
acewar harshe
ɗ
aya a duniya, hasara ce babba ga
ɗ
an’adam wadda ba ta misaltuwa. Saboda haka,
ƙ
ungiyar kula da
harkokin ilimi da kimiya da al
’
adu ta majalisar
ɗ
inkin duniya ‘UNESCO’ ta
ɗ
aura
ɗ
amarar
ɗ
aukar mataki na gaggawa a kan wannan al’amari ta hanyar
ciyar da harsunan gaba. In zai yiwu hukumar (UNESCO) ta shigo ciki ta hanyar
ɗ
aukar
ɗ
awainiyar gudanar
da aikin. Wanda ya
ƙ
unshi samar da ayuka da suke bayani a kan wa
ɗ
annan harsuna masu rauni, kamar: Littafan nahawu da
ƙ
amu-
ƙ
amus da gundarin
rubuce-rubuce, ha
ɗ
a da taskace
adabin baka na harsunan da suke da
ƙ
arancin
rubuce-rubuce, sannan suke a ga
ɓ
ar shu
ɗ
ewa.
Wannan ya nuna
cewa, akwai matsalar mutuwar harshe a duniya, sannan akwai bukatar
ɗ
aukar mataki. Marubucin (Crystal 2014) ya bayyana cewa
kusan rabin harsunan duniya suna a ga
ɓ
ar mutuwa. A wata majiya ( Newman, 2003) akwai a
ƙ
alla jimillar
harsuna 6000 kafin
ƙ
arshen wannan
ƙ
arni rabin wa
ɗ
annan harsuna za su mutu. Cikin 3000 da suka rage 600
kawai alamu ya nuna za su cigaba da sha
ƙ
ar iskar duniya.
Sauran kuma, za su kwanta-dama. Wannan ya nuna kashi 90% daga cikin harsunan
duniya za su mutu. Wata babbar musiba da take
ƙ
ara rura wutar
wannan matsala shi ne, al
’
ummomin wannan
ƙ
arni hankalinsu
yana karkata ne, ga manyan harsunan duniya kamar Ingilishi. Wanda
in
ba a yi hattara
ba, wata rana za a wayi gari da harshe
ɗ
aya a duniya. Wadda babbar musiba ce da ba a ta
ɓ
a tunani ko ji ba, a doron duniya. Wannan ya nuna, akwai
bu
ƙ
atar al
’
ummar duniya ta mayar da hankali wajen ceto harsuna masu
rauni (Crystal, 2014).
Bayan wannan
shimfi
ɗ
a abin tambaya a
nan, shi ne, wai mene ne ‘mutuwar harshe’
(wato ‘language death’ da
Ingilishi). Janse (2003:viii) ya ruwaito ma’anar Campbell (1994:1961) inda yake
cewa:
The loss of
language is due to gradual shift to the dominant language in language contact
situation
.
Fassara
r
Marubuci
:
Mutuwar harshe shi
ne salwantar harshe a dalilin mayar da hankali kacokan
ga babban harshe
a hali na cu
ɗ
anyar harsuna.
Crystal (2014:1) yana cewa:
‘A language dies when nobody speaks it
any more’
Fassarar Marubuci:
‘
Harshe
yakan mutu ne idan aka kai zamanin da ba sauran
mai
magana da shi’
Can kuma a shafi na 14, ya maimaita
magana mai kama da wannan:
‘A language is said to be dead when no one
speaks it any more’
Fassarar Marubuci:
‘Ana iya cewa harshe ya mutu idan aka
kai zamanin da ba mai magana da shi
.
’
Daga wa
ɗ
annan ma’anoni, ana iya fahintar cewa harshe yakan mutu
idan babu sauran mai magana da shi. Wato dai da zaran al’umma ta yi sakaci har
aka wayi gari, ba wani mai iya magana da harshen, sai dai a yi musu ta’aziyyar
mutuwar harshensu. Makamanciyar wannan ta ta
ɓ
a faruwa ga harshen ‘Kasabe’ a lardin Adamawa. Inda aka
sami shaidun mutuwar ‘Bogon’wanda aka tabbatar shi ka
ɗ
ai ne ya rage, wanda ya iya magana da harshen. An
tabbatar da mutuwarsa a 5 ga watan nuwamba 1995. Haka ma, ga harshen ‘Uboh’ da
yake yammacin
‘Caucasian’ a nahiyar Turai. Shi ma mai iya magana da shi
na
ƙ
arshe mai suna
‘
Ubykh
’
, ya mutu ne
daidai almurun
8 ga watan oktoba ta 1992. Duk wa
ɗ
annan harsuna sun shu
ɗ
e, kamar ba a ta
ɓ
a yin su a duniya ba.
Ka ga an yi hasarar harshen
da adabin da kuma al’adunsu duka sun tafi ba dawowa,
(Crystal 2014)
.
Mai harshe yana
iya samun kansa ci
k
in
ɗ
aya daga cikin wa
ɗ
annan halaye:
a.
Musanya harshensa
(Language shift): Wato a samu yanayin da al’umma take fifita wani harshe da ba
shi kula fiye da nata. Har ta kai, ta bar amfani da harshenta, ta ri
ƙ
e wanda ba nata
ba, tana amfani da shi fiye da nata.
b.
Ku
ɓ
ucewar harshe (Langugae loss): Shi ne a sami yanayin da
mai harshe ya wayi gari, kwata-kwata bai iya magana da harshensa, sai wani
harshen.
c.
Kula da
harshe (Language
maintenance): A nan mai harshe ta kai, yana
ɗ
aukar wasu matakai
na kula da
harshensa
kada
ya ku
ɓ
uce masa.
d.
Ki
shin
harshe (Language loyalty): A nan kuma, an lura cewa
harshe yana fuskantar wata barazana, sai a dalilin haka, a
ɗ
auki matakai na
cigaba da amfani da
shi, (Crystal 2014).
Nau’o’in Mutuwar Harshe
Sasse (1992) ya
kawo nau’o’i hu
ɗ
u na mutuwar
harshe, kamar haka:
1.
Mutuwar gaggawa
(Sudden death): Mutuwa ce wadda harshe yake yi a dalilin wata annoba wadda ta
kashe dukkanin al’umma masu magana da harshe.
2.
Mutuwar kisan gilla
( Radical death): Wannan yana da ala
ƙ
a da manufofin
siyasar danniya, inda za a haramta amfani da wani harshe. Duk
wanda ya
yi magana da shi, a kashe shi. Wanda
bisa tilas
,
a daina amfani da ha
r
she, ba don rai ya so ba.
3.
Mutuwa
ta
tsanaki ( Gradual death): Harshe yakan mutu idan al’ummar da take amfani da shi
,
ta
fara
daina amfani da shi, ta rungumi wani harshe daban, saboda dalilai masu ala
ƙ
a da siyasa da
tattalin arziki.
4.
Mutuwa ta musamman
(Bottom to top death): Wannan yana faruwa ne a dalilin ke
ɓ
ance amfani da harshe a wani muhalli na musamman. Kamar
wajen harakar addini ko wasu bukukuwa da ake yi jefi-jefi.
Dalilan Mutuwar Harshe
Dalilan da suke haifar da mutuwar
harshe suna da yawa. To amma, za a kawo
manya-manyan dalilan da suke
haifar
da
salwantar
da harshe. Wa
ɗ
annan dalilai suna
da ala
ƙ
a da: (a) Addini (b) Siyasa (c) Tattalin arziki (d)
Mulkin mallaka (e) Yawaita aro.
A cikin littafan
addinin Yahudawa da na Nasara, an nuna saboda yawan sa
ɓ
on da ‘yan’adam suke yi, sai Allah ya yi fushi da su,
wannan ya sa harsunan mutane suka bambanta sa
ɓ
anin harshe
ɗ
aya. Wannan yana
nuna ke nan samun harsuna daban-daban sharri ne ba alhairi ba ne, ya kamata a
ya
ƙ
e shi. Ta fuskar siyasa kuwa, da yawa ake samun fito da
wasu manufofi da dokoki wa
ɗ
anda suke illa ne
ga
ƙ
ananan harsuna. Sannan suna
ƙ
ara wa harsuna
masu
ƙ
arfi,
ƙ
arfi. Tattalin arzikin masu harshe yana daga cikin abin
da yake
ƙ
ara wa harshensu
ƙ
arfi da matsayi a
cikin al
’
umma. Su kuma harsunan masu
ƙ
aramin
ƙ
arfi ba za su sami
wata kulawa ba. Shi ko mulkin mallaka, tuni ya dasa wa
ƙ
ananan
harsuna
tarko, wanda har wa
yau suna cikinsa ba ranar fit
a
. Wato dai, ‘yan mulkin mallaka suna da hannu dumu-dumu
wajen karya darajar harsunan
ƙ
asa. Sai suka mayar da harshensu a matsayin harshen
mulki. Wannan ya sa a kodayaushe, musamman wurare masu muhimmanci ba za a yi
amfani da kowane harshe ba, sai harshensu. Haka ma, yawaita aro na ba-gaira-ba-dalili,
shi ma yana nakasa harshe, har ta kai wata rana, ya kai ga kashe harshe,
(Crystal 2014)
.
Matakan Mutuwar Harshe
Har wa yau, Sasse
(1992) ya kawo mana matakai uku
na mutuwar harshe, kamar haka:
a.
Musanya harshe
(Languge shift): Al’umma saboda wasu dalilai, suna iya
karkata ga amfani
da wani harshe wanda ba harshensu ba. Sannu a hankali, tun da sun fifita shi
bisa amfani da nasu, sai ya zama sanadiyar ajalin harshensu.Wannan ne matakin
farko.
b.
Gur
ɓ
acewar harshe (Language decay): Wato inda aka sami,
al’umma tana amfani da harshe, yadda ta ga dama, ba tare da kiyaye dokokin
harshe ba, wata
ƙ
ila saboda tasirin wani harshe a kan
nasu. Wannan
ma, yana kai wa ga mutuwar harshe.Wannan ne mataki na biyu.
c.
Mutuwar harshe
(language death): Wannan shi ne mataki na
ƙ
arshe. Da zaran
masu harshe, suka musanya harshensu, saboda ba su yawan amfani da shi, to zai
gur
ɓ
ata. Bayan gur
ɓ
ata, sai lalacewa. Daga nan sai mutuwa.
Mizanan Auna Mutuwar Harshe
Masana harshe, sun
kawo mizanai daban-daban na auna mutuwar harshe. Kodayake dukkansu ana iya kasa
su zuwa manya sassa uku a ta
ƙ
aice. kamar haka:
a.
Harsuna tsayayyu
(Safe languages): Wato harsuna tsayayyu wa
ɗ
anda ba su tsoron wata barazana.
H
arsuna ne da suke cikin ganiyarsu.
b.
Harsuna masu rauni
(Endangered languages): Wa
ɗ
annan rukunin
harsuna ne masu rauni ta fuskoki daban-daban. Harsuna ne da suke fuskantar
barazanar manyan harsuna.
c.
Matattun harsuna (
Extinct languages): Rukunin harsuna ne da suka riga mu gidan gaskiya.
(Crystal, 2014).
Wa
ɗ
annan mizanai an fa
ɗ
a
ɗ
a su, kamar haka:
Akan sami harshe tsayayye mai
ƙ
arfi (viable). Kamar
harshen Ingilishi, domin harshe ne
wanda ya mallaki gida da daji. Sannan kullum aka wayi gari
ƙ
arfi yake
ƙ
arawa. Wannan ya sa ake ganin, shi ne harshe na
ɗ
aya a duniya (Crystal, 2003). Sai masu take masa baya,
wato harsuna tsayayyu amma masu matsakaicin
ƙ
arfi (Small
viable). Daga nan, sai kuma rukunin harsuna masu rauni (Endangered). Daga
cikinsu akwai wa
ɗ
anda masu magana
da su, suna da yawa amma kash! An ta
ƙ
aita amfani da shi
a wurare masu muhimmanci. Akwai wa
ɗ
anda rauninsu ya
yi yawa, tsofaffi kawai ne, suke iya magana da shi, ban da matasa. Da Ing
i
lishi shi ake kira ‘Nearly Extinction’.
Haka ma, Crystal
(2014) ya ruwaito bayanan Stephen Wurm wanda ya yi a kan
kashe-kashen
matakan harsuna masu rauni:
1.
Harsunan da aka
tauye ( Potentially endangered): Rukunin harsuna ne masu
ƙ
arfi idan aka ba
su dama. Sai dai, manyan harsuna sun tauye su. Ma
’
ana sun nuna musu
ruwa ba sa
’
ar kwando ba ne.
2.
Harsuna masu rauni
( Endangered languages): A nan, ana nuni ne ga harsuna masu rauni, saboda
matasan da suka iya harshen ka
ɗ
an ne ba su da
yawa. Amma tsofaffi da yawa suka iya harshen.
3.
Harsuna masu matu
ƙ
ar rauni
(Seriously endangered languages): Harsunan da kwata-kwata matasa ‘yan asalin
harshen ba su jin harshen
, t
sofaffi kawai suka iya magana da shi.
4.
Harsunan da suke
ga
ɓ
ar mutuwa (
Moribund): Rukuni ne na harsuna, wa
ɗ
anda suka iya magana da su, tsofaffi ne sosai kuma ba su
da yawa, ‘yan ka
ɗ
an ne.
Wato
ko cikin tsofaffin ba kowa yake iya magana da su ba.
5.
Matattun harsuna (
Extinct languages): Rukunin harsuna ne da babu sauran mai magana da su a duniya
( Bunza, 2017).
Dole ne, al’umma
ta ankara a kan matakin da harshenta yake. Shin yana cigaba ne ko yana cibaya
?
Domin kuwa, harshe al’amari ne muhimmi:
a.
Harshe kafa ce ta
ya
ɗ
a
zaman
lafiya da hana tashin hankali cikin al’umma.
b.
Harshe yana
ƙ
ara inganta
tattalin arzikin al
’
umma, domin zai sau
ƙ
a
ƙ
a hul
ɗ
ayyar ciniki.
c.
Samun harsuna
daban-daban a
ƙ
asa, ba musiba ba
c
e, alheri ne kuma
ƙ
awa ce na al
’
ummar.
d.
Kar a manta harshe
tushe ne kuma asali ne na al’umma.
e.
Harshe taska ce ta
tarihi.
f.
Harshe fage ne na
ilimi.
g.
Rumbu na kyawawan halayen al’umma.
h.
Kuma rumbu ne na
al’adun al’umma. (Crystal. 2014).
Idan har wa
ɗ
annan alherai, ana samunsu ta fuskar harshe, ta yaya
al’umma za ta yi wa harshenta ri
ƙ
on sakainiyar kashi?
Ko
Akwai Ra’in Nazarin Mutuwar Harshe?
Haspelmath
(2009:3) ya bayyana ma’anar ra’i (theory) kamar haka: ‘..a sophistacated
metalanguage for describing languages’ ma’ana ‘ingantattun ke
ɓ
a
ɓɓ
un kalmomi masu
zurfin ma’ana da aka tanadar domin bayanin kowane harshe’. Sasse (1992) ya
tabbatar da cewa, ya zuwa yau, babu wani tsayayyen ra’in nazarin mutuwar
harshe. Neman ra’in
ɓ
ata lokaci ne.
Amma duk da hakan, ya yi nasa yun
ƙ
urin na samar da wata sahihiyar hanya ta fito da halin da
harshe yake cikin matsayin ra
’
i. Inda a ta
ƙ
aice, ya kawo abubuwa uku da za a yi la’akari da su.
Domin ya nuna duk akasarin nazarce-nazarcen da aka yi baya a kan mutuwar
harshe, sun
ƙ
unshi abu uku, sannan ana iya amfani da su don fito da
wani ra
’
i na nazarin mutuwar harshe:
1.
Fito da dalilan
mutuwar harshe na waje ( External setting): Kamar dalilai na zamantakewa da
siyaya da tattalin arziki.
2.
Dalilai na
walwalar harshe, (Speech behaviour): Wato dalilai ne na masu nuna halayyar da
mutane suke nuna wa harshensu.
3.
Sai dalilai na
fasalin harshe ( Structural description): Wato dalilai na tsarin harshe wato
kamar tsarin sauti da
ƙ
irar kalma da ginin jumla.
Hanyoyin Farfa ɗ o da Harshe
Crystal (2014) ya
yi bayani mai matu
ƙ
ar muhimmanci da ma
’
ana a kan hayoyin
da za a bi wajen kare harshe daga ta
ɓ
ar
ɓ
arewa da kuma
farfa
ɗ
o da shi.
Na
farko
abin da za a fara
shi ne:
a.
Tattara bayanai a
kan harshe don fayyace inda matsalar take. Wanda ya
ƙ
unshi: Adadin masu
harshe da muhallin mai harshe yake rayuwa da
ɗ
abi’un da masu harshe suke nuna wa harshensu da ra’ayinsu
a kan farfa
ɗ
o da harshensu da
ma yiwuwar farfa
ɗ
owa da harshen da
kuma yanayin la
ƙ
antar harshensu.
b.
Tacewa da fitowa
da manyan matsalolin da harshe yake fuskanta.
c.
Cusa kishin harshe
ga al’umma.
d.
Fitowa da
gangariyar harshe da kare-karensa.
e.
Fahintar da
al’umma cewa harshe babban ginshi
ƙ
i ne na al’ada.
f.
Kwa
ɗ
aitar da al’umma wajen yi wa harshensu hidima.
g.
Ɗ
aga darajar harshe ta hanyar ya
ɗ
a shi da amfani da shi.
h.
Masu harshe su du
ƙ
ufa wajen ha
ɓ
aka tattalin arzikinsu. Wato su shiga harkar kasuwanci
ka’in-da-na’in, su zama masu
ƙ
arfin fa
ɗ
a-a-ji a cikin
al’umma.
i.
Masu harshe su
kasance
masu fa
ɗ
a-a-ji a harakar zartar da dokoki. Wanda zai taimaka
ƙ
warai wajen samar
da dokoki masu
ɗ
aga darajar
harshensu.
j.
Masu harshe su yi
ƙ
o
ƙ
arin wajen samun
ƙ
arfin-fada-a-ji a
harakar ilimi.
k.
Masu harshe mafi
yawansu su kasance suna iya karatu da rubutu.
l.
Masu harshe su
ƙ
ara
ƙ
aimi sosai wajen
yayata harshensu a kafafen ya
ɗ
a labarai na
zamani.
Abin da yawa,
mutuwa ta shigo kasuwa! Malamin (Crystal, 2014), ya tabbatar da cewa muddin
masu harshe suka yi amfani da wa
ɗ
annan shawarwari
to ba shakka, harshe zai sami
ɗ
aukaka da cigaba a
cikin tsaransa sauran harsunan duniya. Kamar yadda wasu harsuna suka samu,
kamar harshen Ingilishi.
A yau harshen
Ingilishi, ya zarce duk wani harshe a duniya. Saboda ko, a yau wasu manazarta
suna ganin Ingilishi ya wuce ya zama mallakin wata ke
ɓ
antacciyar al’umma tilo. Sai dai a
ɗ
auke shi a matsayin harshe na alummar duniya (Wato
‘global language’). Wasu suna ganin, in ba a yi hattara ba, za a kai ga lokacin
da harshe ‘Ingilishi’ ka
ɗ
ai zai rage a
duniya. Dalilin wannan hasashe, shi ne duba da yadda harshen yake
ƙ
ara samun
ƙ
arfi da kar
ɓ
uwa a duniya. A ta
ƙ
aice Ingilishi,
harshe ne wanda:
a.
Ya mamaye yankin
Turai da na ma
ƙ
wabta, sannan ya fa
ɗ
a
ɗ
a
ƙ
arfinsa a sauran
ma
ƙ
wabta na nesa.
b.
Harshe ne da
ƙ
asashe a
ƙ
alla saba’in suke
amfani da shi a matsayin harshen
ƙ
asa.
c.
Harshe mai
ƙ
arfin fa
ɗ
a-a-ji a siyasar duniya da tattalin arziki da
ɓ
angaren ilimi da harkonin kimiya da fasaha da sauransu
(Crystal, 2003).
Abin da yake da
muhimmanci a nan shi ne, gano hanyoyin da harshen Ingilishi ya bi, ya kai ga
wannan nasara. Wata
ƙ
ila, wata rana zai yiwu Hausa ta sami makamancinsa.
Wannan ba zai ta
ɓ
a samuwa ba, sai
in al’ummar Hausawa ta saukar da nauyin da yake a kanta na nuna kulawa ga harshenta.
Waiwaye A Kan Ke ɓ a ɓɓ un Kalmomin Nazarin Mutuwar Harshe
A nan kuma,
za a kawo ke
ɓ
a
ɓɓ
un kalmomi da fassararsu na wucin-gadi a kan batun nazarin mutuwar harshe
a Hausa. Ga su kamar haka:
1.
Harshèe
(
H
)
‘Language’:
Tsararriyar hanya ce ta
sadarwar
ɗ
an’adam. Akwai fahinta
gama-gari a kan harshe. Watau shi ne kallon harshe a matsayin ‘magana’. To,
amma akwai ke
ɓ
antacciyar ma’ana, inda
ake kallon harshe a matsayin wata ke
ɓ
antacciyar halitta ta
ɗ
an’adam. Wadda da ita ce ta sa ya zama gagarabadau ta
fuskar harshe, wadda ba ya bu
ƙ
atar wani dogon koyo, kai-tsaye zai iya gane kure har ya
yi nufin gyara, sabada la
ƙ
antar harshe da ya yi ( Cook & Newton, 2007, Carnie
2013).
2.
Mutuwàr harshèe (M.H)
‘
Language death
’
:
Idan aka wayi gari babu mai iya magana da harshe, to,
harshe ya mutu.
Ko
kuma, a sami al’umma saboda wasu dalilai ta juya wa harshenta baya zuwa wani
harshe can daban.
Misali kamar harshen ‘Ubykh’ ya mutu a 1992, Kasabe ma,
ya mutu a 1995. Yau a duniya kaf! Babu mai iya magana da su (Crystal 2003).
Masana harshe, sun nuna a
ƙ
alla akwai harsuna 6000 a duniya, rabinsu sun
ɓ
ace
ɓ
at! Harsuna 600 suke
raye, wa
ɗ
anda suka sami gata na
rubutu da nazari
ba su kai 300 ba (Thomas 1997, Bauer 2007). A fagen nazarin
mutuwar harshe, ake fayyace matsayin harshe ta fuskar cigabansa da ya
ɗ
uwarsa da kuma ta
ɓ
ar
ɓ
arewarsa.
3.
Mùsanyan harshèe (M.H), ‘Language
shift’:
Inda al’umma ta fara ba harshenta baya, saboda wasu
dalilai masu ala
ƙ
a da ilimi ko siyasa ko tattatlin arziki zuwa wani
harshe.
4.
Ɓ
acèewar harshèe (
Ɓ
.H)
‘
Language loss
’
:
A wayi gari kwata-kwata
mai harshe bai iya magana da harshensa ba, sai dai wani harshen daban.
5.
Kùlaa dà harshèe (K.H) ‘Language
maintenance’: Watau inda
masu harshe suka wayi gari rauninsu ya bayyana, alamomin mutuwar harshe ta
bayyana
ƙ
arara ga hrashensu, daga nan sai a fara
‘
yan kame-kame da sunan
kula da harshen, wata
ƙ
ila, idan an yi nasara sai su cuce shi.
6.
K
i
ishìn harshèe (KSH.H) ‘Language loyalty’:
Ɗ
aukar matakan yawan
amfani da harshe saboda barazanar wasu harsuna. Sai a yawaita amfani da shi.
7.
Mutuwàr gagg
a
aw
a
a (M.G) ‘Sudden death’:
Nau’i ne na mutuwar
harshe
a dalilin wata annoba da ta kashe dukkanin masu harshe.
8.
Mutuwàr gillà ( M.H) ‘Radical death’:
Shi ma, nu’i ne na mutawar harshe, wanda yake da ala
ƙ
a
da mulkin
danniya, wato inda za a hana amfani da harshe, wanda ya yi kuma, sai a kashe
shi.
9.
Mutuwàr tsànaakii (M.Tsnk) ‘Gradual
death’:
Nau’i ne na mutuwar harshe, inda aka sami al’umma da
kanta ta ba da baya ga harshensu saboda wasu dalilai.
10.
Mutuwàa ta mùsammàn (M.M) ‘Bottom to top death’:
Nau’i ne na mutuwar
harshe wanda aka ke
ɓ
ance amfani da harshe,
sai a wurare na musamman ( kamar na ibada).
11.
Tsàyàyyun harsunàa (Ts.H) ‘Safe languages’:
Matsayi ne na cigaban
harshe, misali Ingilishi, tsayayyen harshe ne, saboda ya mamaye yankin Turai,
harshe ne na
ƙ
asa a
ƙ
asashe a
ƙ
alla saba
’
in (70). Yana da matu
ƙ
ar fa
ɗ
a-a-ji, a siyasar duniya da tattalin arziki da ilimi.
Akwai matsakaita masu
ƙ
arfi musamman a yankunansu. A ta
ƙ
aice, Ingilishi a yau,
shi ka
ɗ
ai ne
harshen
duniya watau ‘Global language’.
12.
Raun
i
i (R) ‘Endangered language’:
Matsayi ne na rukunin
harsuna masu rauni, saboda dalilai daban-daban. Masu ala
ƙ
a da manyan harsuna da
halayyar al’umma ga harshensu da sauransu.
13.
Sàlwàntàttun harsunàa (S.H) ‘Extinct languages’:
Shu
ɗ
a
ɗɗ
un harsuna ne da suka
kwanta-dama.
14.
Harshèn dà akà ni
i
sànt
a
a (H.A.N) ‘Abandoned language’:
Harshe ne wanda masu
harshe suka yi fatali da shi, saboda wani dalili.
15.
Harshèn dà àl’ummàa ta rùngumàa (H.A.R) ‘Target
langauage’:
Harshen da al’umma ta mayar wa hankali, ta jingine nata.
16.
Madarar harshèe (M.H) ‘Primary language’:
Wannan cikakkiyar
kamala ce ta harshe.
17.
Harshè nùunar ra
a
n
a
a (H.N.R) ‘Second
a
ry language’:
Wannan kuma, ragaggiyar
siffa ce ta harshe.
18.
M
u
sànyà harshèe (M.H) ‘Language Replacement’:
Inda al’umma ta sauya
harshenta ta za
ɓ
i wani.
19.
Sadar dà harshèe (S.H) ‘Language transmission’:
Matakin koyar da harshe
ga masu tasowa wato
ƙ
anana. Babbar garkuwa ce ga mutuwar harshe.
20.
Màtàakan sadar dà harshèe (M.S.H) ‘ Langauge Transmission
Strategies’:
Matakan da ake
ɗ
auka don hana mutuwar harshe da
koyar da shi ga
ƙ
anana.
21.
Gaa
ɓ
àr mutuwàa (G.M)
‘Moribund’:
Rukunin harsuna ne wa
ɗ
anda suke gab da mutuwa, masu jin sa ‘yan
ƙ
alilan ne.
22.
Gur
ɓ
àacêwar harshèe (G.H)
‘Language decay’:
Inda aka sami saboda rashin kulawa, al’umma harshenta ya
gur
ɓ
ace a dalilin ma
ƙ
wabataka da wasu
harsuna.
23.
Mài raunin harshèe
(M.R.H) ‘Semi-Speaker’:
Wanda bai la
ƙ
anci harshe da kyau ba.
24.
Mài màganàa na
ƙ
àrsh
e
e (M.M.N.
Ƙ
)
‘
Terminal Language
’
:
Wanda shi ka
ɗ
ai ya rage a duniya wanda yake iya magana da harshe.
25.
Nàkasàr harshèe (H.L) ‘Reduction’:
Amfani da Harshe
wanda
yake nakasasshe mai matu
ƙ
ar rauni, marar gar
ɗ
i.
26.
Harshèe gàmà-gàr
i
i (H.G) ‘Global language’:
Ba duk harshe yake
samun kai wa wannan matsayi ba. Sai wanda Allah ya yi wa wannan
ɗ
aukaka. Watau harshe ne, wanda a duniya babu inda bai
sami matsayi na musamman ba. Bayan ya mamaye yankinsa ko nahiyarsa. A wasu
sassan duniya ma, yana a gaba. Sannan harshe ne, wanda ya fi
ƙ
arfin a jingina shi ga
wata
ƙ
abila
ɗ
aya, saboda ya
ɗ
uwarsa. Kuma a kullum
ƙ
ara
ƙ
arfi yake yi. Zuwa yau,
harshen Ingilishi kawai ya kai wannan matsayi. Domin wa
ɗ
annan dalilai:
a.
Ya mamaye yankin Turai da na ma
ƙ
wabta, sannan ya fa
ɗ
a
ɗ
a
ƙ
arfinsa a sauran ma
ƙ
wabta na nesa.
b.
Harshe ne da
ƙ
asashe a
ƙ
alla saba
’
in suke amfani da shi a
matsayin harshen
ƙ
asa.
Harshe ne mai
ƙ
arfin fa
ɗ
a-a-ji a siyasar duniya da tattalin arziki da
ɓ
angaren ilimi da harkokin kimiya da fasaha da sauransu
(Crystal, 2003)
27.
Harsunàa
màasu rauni (H.M.R) ‘Endangered language’: Harsuna ne wa
ɗ
anda suka kasance masu rauni ko ta fuskar siyasa ko ta
tattalin arziki
ko saboda wasu dalilai.
28.
Farfa
ɗ
o dà Harshèe (F. H) ‘Language
Revitalization’:
Matakai ne da za a
ɗ
auka wajen farfar
ɗ
o da harshe daga gararin mutuwa ko salwanta ko kuma da
ƙ
ushewa.
Kammalawa
Wannan nazari ya
yi magana ne, a kan batun mutuwar harshe a Hausa. Domin sau
ƙ
a
ƙ
a tattaunawar an
kasa nazarin zuwa sassa bakwai: Ma’anar mutuwar harshe da nau’o’in mutuwar harshe
da matakan mutuwar harshe da mizanan mutuwar harshe da kuma ra’in mutuwar
harshe da hanyoyin farfar
ɗ
o da harshe da
kuma jerin gwanon ke
ɓ
a
ɓɓ
un kalmomin fashin ba
ƙ
in mutuwar harshe
a Hausa. Babban gurin wannan nazari shi ne, ya
ƙ
ara fitowa da
batun mutuwar harshe a Hausa, a ci gaba da jin
ɗ
uriyarsa kamar yadda ake jin muryar sauran fannoni na
nazarin harshe a Hausa. Haka ma ya zama silar janyon hankalin masana zuwa
wannan fanni, daga nan har ta kai ga al’umma ta fa
ɗ
aku ta rungumi harshenta da kyau, a ha
ɗ
a hannu da manazarta da sauran jama’a wajen ciyar da
Hausa gaba, ya yi sanadin fitar Hausa daga
ƙ
angin rauni.
Manazarta
Anyanwu,
O.
(2007)
. Languages of
Nigeria. Basic Linguistics for Nigerian Languages
Teachers
(ed) Ore Yusuf.pp.1-28.
Argungu, D.M. (2021). Hausa
and the National Language Question in Nigeria: Privilages, Prospects and Predicaments.
23rd
Inaugral Lecture, Usmanu Danfodiyo University, Sokoto.
Bagari, D.M. (1986). Bayanan
Hausa:Jagora ga Mai Koyon Bayanin Ilimin Harshe. Maroco: Almaarif eljadida.
Bauer, L.(2021).
The Linguistic Student’s Handbook. Edinburgh: Edinburgh University Press.
Bauer, L & Calaude, A. S. (2020). Questions About Language: What Everyone
Should Know
About Language in the 21st Century. London: Rouledge.
Bunza, A.M. (2017).
Language Endangerment, Status and
Extinction: The Linguistic Balance
Sheet of Kyangawa. Endangered Language in Nigeria Policy, Structure
& Documentation
. (eds) Yusuf, M.A., Salim, B.A.,
Bello, Vol.2. pp
.
467-476.
Brenzinger, M.,
Dimmendaal,
G. (1992). Social Context and Language
Death. Language
Death: Factual and Theoretical Explorations with Reference
to East Africa
(ed) Brezinger, M.
pp
.
1-3.
Carnie, A. 2013. Syntax:
A Generative Introduction Third Edition. USA: Wiley-Blackwell.
Cook, V., Newson, M. (2007). Chomsky’s Universal Grammar:
An Introduction. USA: Blacwell Publishing.
Crystal, D.
(2003). English as a Global Language.
Cambridge: Cambridge University Press.
Crystal, D.
(2014). Language Death. Cambridge:
Cambridge University Press.
Dixon, R.M.W. (1997). The
Rise and Fall of Languages. Cambridge:
Cambridge University.
Ikara, B. (1991). Hausa Language Studies: A Projection
for Future. Nigerian Language Yersterday,
Today and
Tomorrow. (ed) Rufa’i, Abba. Pp. 26-51.
Janse, M. 2003.
Introduction: Language Death and Language Maintenance: Problems
and Prospects. Language
Death and Language Maintenance: Theoretical, Practical and Descriptive
Approaches. (eds) Janse, M., Tol, S. vii-ix.
McGregor, W. (2009). Linguistics:
An Introduction. Newyork: Continuum International Publishin Group.
Muhammad, I.A. (2021). Ko Harshen Hausa Zai Mutu?
Ma
ƙ
alar da Aka Gabatar a Taron
Ƙ
ara wa Juna Sani na Tsangayar Fasaha da
Nazarin Addinin Musulunci.
Newman, P. (2003).
The Endangered Languages Issues as a Hopeless Cause. Language Death and Language
Maintenance:
Theoretical, Practical and Descriptive Approaches
. (eds) Janse, M.,
Tol, S. Pp
.
1-14.
Sasse, Hans-Jurgen
(1992). Theory of Language Death. Language
Death:
Factual and Theoretical
Explorations
with Reference to
East Africa
(ed) Brezinger, M.
Pp
.
7-31.
William, O & Dobrosvosky, M & Katamba, F. (1996).
Contemporary Linguistics: An
Introduction.
London: Longman.
Yakasai, S.A. (20
20
). Jagorar Ilimin
Walwalar Harshe. Sokoto: Garkuwa Media Services LTD.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.