Ticker

6/recent/ticker-posts

Nazarin Kurman Da a Wakar “Zuma” Ta Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Citation: Yakasai, M.G. (2024). Nazarin Kurman Ɗa a Waƙar “Zuma” Ta Aminu Ladan Abubakar (ALA). Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, 3(1), 215-223. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.024.

Nazarin Kurman Ɗ a a Wa ƙ ar “Zuma” Ta Aminu Ladan Abubakar (ALA)

Daga

Murtala Garba Yakasai Ph.D .
Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya
Bayero Uni v ersity , Kano , Nigeria
mgyakasai.hau@buk.edu.ng
(+234) 08029458283

Tsakure

Takardar ta yi nazarin wa ƙ ar baka ta ALA inda aka bibiyi amfani da ‘Kurman Ɗ a’ wanda shi ne ya mamaye wa ƙ ar ‘zuma’ ta mawa ƙ in. An fahimci yadda ya yi amfani da hikima da azanci domin isar da sa ƙ onsa ga masu nazari. ALA ya yi ta faman dibilwa ta amfani da harshen Hausa, wadda sai da manazarta suka ci kwakwa kafin fahimtar sa ƙ on mawa ƙ in a cikin sau ƙ i. Dalilin wannan nazari domin masu sauraron wa ƙ a da manazarta sun gaza yin caraf! Domin fahimtar sa ƙ on da ke cikinta, sakamakon haka sai aka nazarce ta, aka fahimce ta, aka kuma tattauna da mawa ƙ in, sannan aka yi fashin ba ƙ inta, domin fahimtar da ɗ imbin masu gurguwar fahimta game da wa ƙ ar. Tunanin rubuta wannan takarada bai wuce fitar da jaki daga duma ba, domin salon sar ƙ a ƙ iyar da sa ƙ on wa ƙ ar yake da shi. An saurari wannan wa ƙ a ne a cikin f aifan m emory, sai aka rubuce ta tsaf domin yin wannan nazarin. Manufar wannan takarda ita ce fahimtar yadda mawa ƙ in ya nuna ƙ warewa ta amfani da harshe, domin kuwa takardar ta binciko yadda manazarta da dama suka wasa ƙ wa ƙ walensu domin gano ha ƙ i ƙ anin sa ƙ on da wa ƙ ar take ƙ unshe da shi, sakamakon yadda sa ƙ on ya dinga zuwa a dun ƙ ule kuma cikin salon tambaya tare da salon waskiya daga mawa ƙ in, har dai daga bisani a ka fahimci bakin ƙ ullin zaren ta yadda mawa ƙ in ya yi amfani da salo irin na ɗ aurin ɓ oye.

Gabatarwa

Ɗ aya daga cikin abubuwan da kan wahalar da masu sauraron wa ƙ a (musamman ma domin nisha ɗ i ko kuma nazari) shi ne rashin fahimtar sa ƙ on da ke cikin wa ƙ a, ba domin komai ba kuwa sai domin yadda mawa ƙ a suka yi amfani da harshe cikin hikima da basira da kuma fasaha wajen ɓ oye sa ƙ onnin da suke son isarwa. Shi mai sauraro domin nisha ɗ i, a irin wannan yanayi yakan dangana ne ga sautin ki ɗ a da raujin amon mawa ƙ i, wato irin abin nan da ake cewa a bi Yarima a sha ki ɗ a. Shi kuwa mai nazari, yakan zurfafa ne cikin tunani domin ganin ko zai kamo tashar mawa ƙ i cikin sa ƙ onsa da ya zuba cikin wa ƙ arsa.

Irin wannan hikima ta mawa ƙ i takan bayyana ne cikin kuramen ɗ iya, kuma tsokaci kan wannan batu ne manufar wannan ma ƙ ala a cikin wa ƙ ar ‘Zuma’ ta Aminu Ladan Abubakar (ALA). Domin cimma wannan manufa, an karkasa ma ƙ alar zuwa gida biyar. Da farko akwai gabatarwa. A kashi na biyu kuma ta ƙ aitaccen bayani kan mawa ƙ in, daga nan kuma sai aka bijiro da ma’anar kuramen ɗ iya a kashi na uku. Kashi na hu ɗ u kuma cikakken tsokaci ne a kan wa ƙ ar zuma. Akwai kuma jawabin kammalawa. Masana wannan fanni na adabin Hausa sun tanadi hanyar nazari ko fi ɗ ar sa (wato bayanin hanyoyin da suke bi domin fi ɗ ar wa ƙ a). Farfesa Ɗ angambo ya fitar da hanyar nazari ta zamani wadda ta bambanta da hanyar nazari ta gargajiya. Ga misali, akwai tarihi ko bayanan share fagen marubuci, wato wanda ya ƙ unshi bayanin diddigi ko salsala da shekarar da aka wallafa wa ƙ ar.

Daga nan kuma sai jigo da warwararsa da furucin gundarin jigo da kuma jigo a gajarce. Wannan ya ha ɗ e jigo da shimfi ɗ arsa da kuma ƙ ananan jigogi. Ta fuskar zubi da tsarin wa ƙ a kuwa, akwai zubi da tsari cikin baitoci da yawan baitoci da layuka a wa ƙ a. Wannan kuma yana biye da amsa - amo ( ƙ afiya) da Karin wa ƙ a da kuma zubi da tsari na gaba ɗ aya. A salo da sarrafa harshe kuwa, akwai salo na gaba ɗ aya da kuma dabarun jawo hankali ko salon sarrafawa. Wato a nan ne ake samun kwatantawa da kamantawa da daidaito da bambanto da kuma ƙ as ƙ anto. Ta fuskar siffantawa kuma akwai gajeriyar siffantawa da kuma doguwar siffantawa. Ita kuwa jinsintarwa ta ƙ unshi mutuntarwa da dabbantarwa da kuma abunta r wa da dai sauransu. A wannan ma ƙ ala ba za a bi hanyar da masana suka tanada ta nazari sau-da- ƙ afa ba, saboda haka ne ma za ta kasance ballagaza.

  Wane ne Aminu Ladan Abubakar (ALA)?

Daga binciken da masana magabata suka gudanar kan wa ƙ o ƙ in ALA (duba ayyukan Gusau 2011, Lawan 2011, Yakasai 2013 da 2014 da 2015 da kuma Yakasai da Sani, 2021 ) mun sami haske dangane da ko wane ne shi cikin tarihin rayuwa da kuma matsayin wa ƙ o ƙ insa a idon al’umma. Tarihi ya bayyana haihuwar Aminu Ladan Abubakar a ranar biyu ga watan Oktoban alif ɗ ari tara da saba’in da uku, a unguwar Yakasai da ke ƙ aramar hukumar birni da kewaye ta jihar Kano. Shi kuwa sunan ALA ha ɗ aka ce ta farkon haruffan da ke ɗ auke da cikakken sunansa. Ita salsala tana da matu ƙ ar muhimmanci wajen bayyana matsayi da kuma ƙ imar mutum, da yake waiwayen shi ne adon tafiya, ga yadda gaskiyar abin yake daga bakinsa:

 

Masarautar Bawa Gwarzo, ku ji salsalar ubana,

Sunana Al-Aminu, da shi aka ra ɗ a suna,

Alhaji Ladan ubana da Abubakari kakana,

Sunan da na sa wa kaina Alan wa ƙ ar yabona,

Sa ƙ andamai na sunayena na cire ciki la ƙ abina,

Asali na garin ubana, Jega Kebbi State ka tona,

Asali na garin uwata, Dabo ta Kano garina,

Shekarar ran haihuwata, ƙ irgen Shari’ar Nabina,

Hijira ta alif dubu ɗ aya da ɗ ari uku da ɗ uguna.

                            

Neman ilimi na Islama da kuma na zamani sun yi tasiri cikin tasowa da tarbiyya da kuma girmansa, har lokacin da ya kai ga matsayin samun takardar karatun Diploma a fannin fasahar zane-zane. Daga iyaye zuwa kakanninsa kuwa, babu wanda ya yi wa ƙ a, to amma kuma ga wa ɗ anda suka na ƙ alci wa ƙ o ƙ insa, suna sane cewa ya yi wa ƙ o ƙ i masu tarin yawa. Ga sauran bayanin yadda ta kasance in ji shi:

 

Ma’anar manufar ɗ uguna, casa’in da hu ɗ u nufina,

Ƙ irge kuma na nasara, 1973 na,

A Municipal Kanawa Yakasai ta garina,

Nan ne aka haihuwata, labarin assalina,

Nai ilimin Islama ma tayassara gwargwadonna,

Nai ilimin zamanina, boko don zamanina,

Gwargwado dai Diploma, nai domin kare kaina,

Nai kan Art & Design, ƙ ir ƙ irar zane fununa,

Daka dangogin fasaha, na fi ƙ arfi lamurana,

Nai rubutu na hikaya, Fikshin shi ne ƙ arin bayana.

 

Kurman Ɗ a a Wa ƙ a

Kafin mu ce wani abu game da kurman Ɗ a , yana da kyau mu ce wani abu game da ita kanta wa ƙ a. Hasali ma, ai sai wa ƙ a ta samu sannan ake tantance sigar ɗ iya. A ƙ aramin ta ƙ adiri, Ɗ angambo (1981) ya bayyana wa ƙ a da wani furuci cikin azanci da ake aiwatarwa ta hanyar rerawa da daidaita kalmomi cikin wani tsari ko ƙ a’ida da kuma yin amfani da dabaru ko salo mai armashi. To idan haka ne (wanda kuma haka ɗ in ne), to ita wa ƙ a tana zuwa ne a sigar gunduwoyin zantuka wa ɗ anda ake kira baitoci ko ɗ iya, kuma ake rerawa da wani sautin murya na musamman (Umar, 1980).

Abba da Zulyadaini (2000) ma sun jaddada cewa wa ƙ a wata tsararriyar magana ce a cikin hikima da fasaha da aka ƙ ir ƙ ira kuma aka rera ta daki-daki (tare da taimakon amo a wani lokacin), kuma ta kasance tana ɗ auke da wani salon burgewa a bisa wata ƙ a’ida ta musamman domin isar da sa ƙ o. A ta ƙ aice dai, wa ƙ a wata ha ɗ aka ce ta kalmomi da ki ɗ a cikin wani tsari mai bayar da armashi ga mai saurare, a inda shi mai sauraren zai iya tantance wannan ha ɗ aka ta ki ɗ a da jerin kalmomi (Mashi, 1986). A irin wannan ha ɗ aka ce ake samun kurman baituka cikin sautin ki ɗ i da kuma raujin amo a wa ƙ a. To idan haka ne, to me ake nufi da kurman Ɗ a?

Domin amsa wannan tambaya, Farfesa Dumfawa (2015) ya ɗ auki kurman baiti a matsayin baitin da ma’anarsa ba ta fito fili ba a wa ƙ a (ko kuma ba a iya fitar da wata ma’ana daga cikinsa). Da yake tur k e a ƙ a’idar manazarta wa ƙ ar baka na nufin sa ƙ o da wa ƙ a take ɗ auke da shi (Gusau, 2008), to kurman Ɗ a kan kawo cikas wajen fahimtar sa ƙ o kan manufar da ta ratsa tun daga farkonta har zuwa ƙ arshenta (wato rashin fahimtar ainahin abin da ake zance a kansa). Ta fuskar samuwa kuwa, wasu na ganin rashin ƙ warewar mawa ƙ i ne kan haifar da haka, a yayin da wasu kuma ke ganin gwanintar mawa ƙ i ce kan kwashe shi ya tsara wa ƙ a ta yadda masu sauraro domin nisha ɗ i da kuma masu nazari za su yi ta bulayi. Domin nazarin kurman Ɗ a cikin sautin ki ɗ i da raujin amon mawa ƙ a, Wa ƙ ar Zuma ta Aminu Ladan Abubakar (ALA) ce ta zamo mana zakaran gwajin-dafi.

Zuma ko Ma ɗ aci?

Kafin mu tsunduma cikin nazari, akwai bukatar yin matashiya dangane da wasu abubuwa da ya kamata a lura da su. Da farko dai “An san ki da Za ƙ i zuma an san ka da Ɗ aci ma ɗ aci”, kalaman da mawa ƙ in ya za ɓ a ke nan a matsayin amshinsa, kuma ya yi ta maimaita su tun kafin ya fa ɗ a cikin wa ƙ ar. Haka ’yan amshinsa ma suka yi ta taya shi maimaitawa. Shin a wane dalili mawa ƙ in ya yi ta maimaita wa ɗ annan kalamai? Wani zai ce ai saboda amshin wa ƙ ar ne. To me ya sa ya za ɓ i wannan a matsayin amshin? Amsa mafi sau ƙ i daga mahanga da za a iya karewa da kyawawan dalilai ita ce, domin jawo hankalin duk wani mai sauraro. Wato domin mai sauraro ya nutsu kuma ya tattara hankalinsa a wuri guda. Dalili kuwa shi ne, ai da ma kowa ya san zuma na da za ƙ i, kuma ma ɗ aci akwai ɗ aci. To me ya sanya mawa ƙ in ya damu da sanar da mu abin da muka riga muka sani? Lallai banza ba ta kai zomo kasuwa.

Daga nan kuma sai tambaya da amsa, wato “Alan wa ƙ a me ya faru? Wannan kurman Ɗ a ne” . Haka ’yar amshinsa ta yi ta binsa domin ya fa ɗ a mata me ya faru? Ha ƙ i ƙ a duk wanda ya damu da yadda mawa ƙ in yake ta jaddada abin da kowa ya sani, shi ma dole ya yi irin wannan tambaya, wato me ya faru? Wannan tambaya kuwa da ’yar amshin take yi ta ƙ ara fito da maganar baya a fili cewa ba a banza mawa ƙ in yake ta nanata abin da yake sananne ba. Ke nan kamata ya yi mu yi tunani irin na ’yar amshin mawa ƙ in, wato tunani da ƙ o ƙ arin binciko abin da ya faru. Sai dai kash! A duk lokacin da mawa ƙ in ya yi kalami ba ya ga na tambayarsa, to amsar a sakaye take zuwa (wato kurman Ɗ a). Duk da cewa yana amfani da kalmomi masu sau ƙ i da kuma jumloli marasa sar ƙ a ƙ iya, to amma ma’anarsu a sakaye take. Wannan ma ya kamata ya sake lurar da mu cewa, amsar wa ƙ ar kanta a sakaye take, wato ba zumar da ake sha ko ma ɗ acin da muka sani yake magana ba.

Sai dai kuma kawo yanzu mun rasa makama, domin ko wadda take tambaya ma ba ta samun amsar kai tsaye ba. Ke nan gare mu, dabara ta rage ga mai shiga rijiya, wato ko dai mu bi kurman Ɗ a domin gano ma’anar sa ƙ on da ke tafe ko kuma mu bi Yarima mu sha ki ɗ a. Ƙ ari da ƙ arau ma, mawa ƙ in ya fa ɗ a da kansa cewa “Yau nazari za a yi, ba saurare na ki ɗ a ba.” Ke nan idan ba da idon basira muka kalli wa ƙ ar ba, kuma muka saurara da kunnuwan basira, to ba za mu fahimci komai ba. A yanzu za mu mazaya cikin nazari domin nemo bakin zaren warware ɗ iya, domin tabbatar da “soyayya” a matsayin jigon wa ƙ ar. Idan muka fara daga amshin wa ƙ ar “An san ki da za ƙ i zuma, an san ka da ɗ aci ma ɗ aci”, to da zarar an ambaci soyayya, babu abin da zai zo zuciyar kowa sai jin da ɗ i da nisha ɗ i. Idan kuma gaba ta zo (kishiyar so), to an san cewa akwai ƙ unci da ɓ acin rai da kuma rashin jin da ɗ i. Saboda haka, a ƙ aramin ta ƙ adiri muna iya cewa “An san ki da da ɗ i soyayya, an san ki da ɗ aci ƙ iyayya”. Tambayar a nan ita ce, me ya sa mawa ƙ in ya kawo wannan batu alhali kuwa kowa ya sani? Lallai ruwa ba ya tsami banza! Idan muka duba maganar fari da ke cikin wa ƙ ar, “Kishiya ta maso rigima ta ha ɗ e da mutum maha ƙ urci”. A nan ya kamata mu lura da abubuwa a ƙ alla guda biyu. Na farko, an shiga cikin wa ƙ ar ne kai tsaye ba tare da mabu ɗ in al’ada ba. Ana iya ɗ auka cewa hakan ganin dama ce, to amma a ha ƙ i ƙ anin gaskiya akwai dalilai da kan sanya wasu mawa ƙ a yin haka (wato fara wa ƙ a ba tare da mabu ɗ i ba).

Dalilan sun ha ɗ a da nuna zumu ɗ i da gaggawa da ba ƙ in ciki da farin ciki da dai sauransu. Ga misali idan muka ɗ auki ba ƙ in ciki, mawa ƙ i zai iya fara wa ƙ a ba tare da mabu ɗ i ba a yayin da yake magana akan wani abu da ya ɓ ata masa rai. Sai ya yi nisa kuma ya yi yabon Ubangiji da kuma salati (wato mabu ɗ i a ta ƙ aice). Daga nan kuma sai ya nuna tsabar ɓ acin rai ne ya sanya shi shagala daga yin mabu ɗ in. Wato yanzu ya ɗ an sauko ne ya sanya shi tunawa. Wani mawa ƙ in ma yakan zarce ba tare da yin mabu ɗ in ba. A wa ƙ ar “ Ɗ andaudu”, A ƙ ilu Aliyu ya bu ɗ e wa ƙ ar ne da cewa:

Af jama’a ku tsaya in waigo

In tuna ɗ an rakiyar ta-makwalla 

 

Idan muka lura, za mu ga cewa ya tuno da wata muhimmiyar magana ce wadda tsabar zumu ɗ in ya fa ɗ e ta tare da tsoron mantawa har ya shagala ga yin mabu ɗ i. Ke nan za mu iya cewa mawa ƙ in ya tsunduma cikin wa ƙ ar kai tsaye ne saboda wani dalili babba da ya tsaya masa a rai, wanda kuma ya samo asali ne a dalilin soyayya. Soyayyar kuma tana da fuska biyu, wato ko dai masoyiya ta ɓ ata masa rai ko kuma ainhin yadda ‘so’ kansa ke ɓ ata masa rai ta hanyar shiga masa zuciya da takurawa. Abu na biyu da ya dace mu lura shi ne; maganar na nuna cewa mawa ƙ in na yi wa wani ko wata ko wani abu magana ne cikin rashin jin da ɗ i. Wato kamar mutum ya ce “Duk fitinar ka/ki dai idan na yi ha ƙ uri za mu rabu lafiya”.

A nan zai zamo ne ko dai yana magana ne da wata masoyiya da ta ɓ ata masa rai ko ma ta saka shi a rana, yana fa ɗ a mata cewa idan ya yi ha ƙ uri shi ke nan ha ƙ arta na ganinsa a rana ba za ta cimma ruwa ba. Ko kuma yana magana ne da ‘so’ kansa cewa duk yadda yake takura masa a zuciya kan dole ya so wata ko wani abu, to idan ya yi ha ƙ uri zai iya ku ɓ uta. Mawa ƙ in kuma ya ce: “Idan ka ga ruwa rahama, idan ka ga wuta kai takaici”. Wannan kuma ya yi daidai da amshin wa ƙ ar tasa, kai za ma a iya cewa ya sako maganar tsakiyarsu ne (wato kishiya ta maso rigima ….) domin ya ɗ an gusar da hankalin mai sauraro, ya zamana bai danganta ma’anarsu ba. Ke nan zai zama yana ƙ ara nanatawa ne cewa “So an san shi da da ɗ i, ƙ iyayya kuma da rashin da ɗ i” . Haka kuma dole mu sake gamsuwa cewa mawa ƙ in ba a banza yake maimaita maganar da kowa ya sani ba. Domin ga shi ya nuna zumar da aka sani da za ƙ i ta koma sa ɓ anin haka, kuma ruwa ya zama ba rahama ba. Inda ya ce ya sha zuma da zafi, to shi soyayya da ke da da ɗ i ba da ɗ in ta zamo ba a gare shi. Wannan kuwa ba abin mamaki ba ne, musamman idan mutum ba zai iya samun abin da yake so ba.

A ɗ an kuma da yake cewa, “Idan ka ji amo an gama, idan ka ji shiru akwai ka ɗ aici” , idan a zahiri ne ai wanda bai ji amo ba babu labarinsa. Ga misali, harbin bindiga ko tashin bom da sauransu. Amma mawa ƙ in sai ya ce, “Idan ka ji shiru akwai ka ɗ aici”, wato shi hankalinsa ya karkata ne da cewa idan zuciyar mutum ta zauna lafiya, to tana da ka ɗ aici ne, (ba ta samu abin da take so ba).               

A gaba kuma ya ce:

Idan ka zo da salon sallama,

Ka zo da salo managarci,

Wanda ya ƙ i ya ma sallama,

Ya zo da zubin mamugunci.

 

A nan ma idan muka dube shi ta fuskar yana magana da mai neman saka shi a rana, za mu ga yana nufi ne da cewa idan masoyiya ta sanar da masoyi cikin salama dalilan rabuwa, to ta zo da managartan salo. Amma kuma da ta zo kai tsaye ta ce ba ta son sa (watakila ma da nuna rashin mutunci), to wannan mugunta ce take yi masa tare da neman cutar da shi (haka ma abin yake ga namijin da ya yi wa mace hakan). Idan kuma mun dube shi ta fuskar mawa ƙ in yana magana ne da ‘so’ kansa, to za mu ga cewa yana nuni ne ga yadda so yake shiga zukata ba tare da sallama ba. Wato ba sai da izinin mutum ba ne so kan mamaye shi, kuma ya takura wa rayuwarsa (wanda ya kira hakan da salon mugunta). A gaba mawa ƙ in ya fa ɗ i yadda ya sha zuma da zafi, wato dai soyayyar da ya kamata ta zama nisha ɗ i ta zame masa ƙ a ƙ a-ni-ka-yi. A sanadiyar hakan, ya kuma fa ɗ i yadda jikinsa ya zama kumama har ya kasa yin bacci. Wannan ba sabon abu ba ne domin akwai da dama wa ɗ anda ‘so’ ya yi masu illa fiye ma da haka. Maganganunsa na gaba kuma, ya jero su ne ta hanyar siffanta abin da yake ta magana akai amma cikin kurman Ɗ a, inda ya kira lamarin da rashin lafiya. To dama ai ‘so’ ya cancanci a kira shi da rashin lafiya, domin kuwa duk wani abu mai hana sukuni da walwala da jin da ɗ i tare da dugunzuma              

Ɗ an’ a dam ai rashin lafiya ne. Sannan so ya tara dukkan wa ɗ annan halaye. Baya ga haka, ai mun san cewa duk cututtukan da ke akwai a duniya ko da ba su da magani ai suna da rigakafi. Amma bari mu ji yadda mawa ƙ in ke siffanta wannan cuta da ta wahalar da shi, wadda kuma daga siffar zai sake tabbatar mana cewa ‘so’ ne wannan cutar. Ga abin da yake cewa:

Rashin lafiya wacce Malam ko Likita,

Boka da matsafa duka, a daina batun Likita,

Yahudu-Nasara duka sun gaza da rigakafinta.

 

To ga shi daga abin da ya fa ɗ a, duk wa ɗ annan sun rasa maganinta kuma sun ma rasa yadda za a yi Ɗ an ’adam ya iya guje mata domin ya ƙ ara da cewa “Don ba ta gano ko da miscrocope…”. Ko ba komai dai mun san babu cutar da ba a iya bincike kan sinadaran da suka samar da ita ba kuma an gan su, to amma shi ‘so’ fa? A gaba kuma sai ya kawo maganar ha ƙ uri inda ya ce “Komai tsanani anka ce ha ƙ uri shi ne mafita” . Ke nan duk abin da mutum yake so ba zai samu ba, to ya ha ƙ ura shi ne mafita. To fa yanzu ya kamata wasa da hankalinmu da ake yi ya ƙ are. Ta yaya za a kwatanta mana cuta mai tsananin illa marar magani daga Malam ko Boka ko Likita ko Nasara ko Yahudu ko matsafi amma kuma a ce maganinta ha ƙ uri ne? Mai tsananin amai da gudawa ya yi ha ƙ uri ke nan sai ya warke? Wato dai wannan cuta ‘so’ ne, kuma idan aka rarrashi zuciya kuwa sai a warke.

A gaba mawa ƙ in ya fa ɗ a “Ga ba ƙ on zuciya wanda ba sallama shi yake ba” . Wato dai kamar yadda so yake shiga zuciyar mutum ba sallama, to ƙ in ƙ arawa ma sai ya kwatanta saurin shigarsa. Ya nuna cewa shi fa farat ɗ aya yake shiga ta yadda duk saurin abu bai kai saurin yadda yake shiga zuciya ba. Ga yadda ya ce:

Shigar bacci a ido, bai kai shi fita da gudu ba,

Fitar Kibiya a baka, ba ta kai shi fita da gudu ba,

Fitar harsashi sani na, bai yi ya shi a gudu ba,

Kai ƙ ifta ido Ɗ an ’ a dam, bai kai shi saurin gudu ba.

 

Idan muka duba duk abubuwan nan da mawa ƙ in ya kawo, to wacce cuta ce muke tsammanin take da saurin da za a kwatanta da wa ɗ annan? Ebola? Ke nan ‘so’ ne. Wato daga kallon abu sai son ya shiga. A nan sai ya kawo maganar da muka yi a baya, cewa nazari za mu yi ba sauraren ki ɗ a ba. Idan muka lura, ai sai da ya gama mana kwatancensa sannan ya yi maganar nan. Don haka, yana rayawa a zuciyarsa ne wani ya ɗ auki wa ɗ annan ɗ iya kawai maganar nisha ɗ i, shi kuma yake jan hankalin mutane cewa a fa yi nazarin ɗ iya n ƙ warai. A ta ƙ aice dai a yi nazarinsu domin suna da ma’anonin da sai an kula sosai. A gaba yake cewa “Sa ƙ ona yau ba akala da zuci nake sarrafawa” , wannan ma ya kai ya nuna cewa tsabagen yadda zuciyarsa take rashin jin da ɗ i bai ma damu da sama wa zantukansa akala ba. Don haka yake zubo su kamar yadda zuciyar ta so ko za ta samu sarari.

Sannan ya sake cewa : “Sa ƙ o daga can zuciya, fa ɗ arsa ake ba kawarw a”. Kamar dai idan ran mutum ya ɓ aci yake fa ɗ an komai barkatai yadda ya so. Gaba ya ce : “Mai mai da fasihi balidi, fagen fa ɗ akarwa” . A nan dai mun san yadda fasihi ke zama takwalli saboda ‘so’. A wata magana makamanciyar wannan sai ya ce “Mai sa malam mantuwa, ya manta sanin a gidansu”. Wannan kuwa haka take, wato yadda ‘so’ yakan ja hankalin wasu masu ilimi har su yi aiki irin na marasa ilimi. Ɗ iya na gaba ma irin sa ƙ on ne ya isar inda yake cewa “Mai sa sarki ɗ imuwa ya manta sarautar kansa” , kamar dai yadda za a ga shugaba amma mace ke juya shi (ka gagari maza, mata sun gagare ka). A gaba kuma ya nuna har ma ana sanya talaka ya yi ƙ unar bakin wake da ransa (talaka ya ga abin da ba shi yiwuwa a gare shi ya samu, amma ya ƙ wallafa rai yadda har cibi zai zama ƙ ari). Lamarin bai bar mata ba ma, domin ya ce sukan yi bulayi ko a samu ko a rasa, (wato dai a rasa abin da zuciya ke marari). Daga nan ne kuma mawa ƙ in ya koma ga Allah:

Allah abin dogara, taimaka mani kan zuciyata,

Tsare ni da bin sha’anin da soye-soyen zuciyata,

Tsare ni da bin mararin ganin sha’awar zuciyata.

 

Wa ɗ annan kalamai duka suna bayyana ro ƙ onsa ne ga Allah, wanda hakan na nufin idan Allah ya amshi ro ƙ on, to ya tsira daga wannan cutar. Wace cutar? Cutar ‘so’ ke nan. Kamar yadda ya nemi Allah ya tsare shi daga marari da soye-soyen zuciya da kuma sha’awar da zuciya za ta yi, wato ka da ma ya so abin da zai wahalar da shi.

Walwala da Harshe

Daga abin da ya gabata, mun yarda cewa wa ɗ annan kuramen Ɗ a ne sosai, musamman ma idan muka yi la’akari da yadda ɗ iyan kan wahalar wajen fayyacewa. Ke nan bayan fayyace ma’anoninsu, sai kuma batun tabbatar da abin da ya mayar da su ‘kuramen Ɗ a’ (wato masu wuyar ganewa). Ha ƙ i ƙ a kuwa akwai ɗ in.  A’a to ko ba komai ma, idan babu rami me ya kawo maganar rami? Yanzu za mu juya akalar nazarin domin gano dabarun da mawa ƙ in ya yi amfani da su wajen mayar da wa ƙ ar mai tsauri ta fuskar fayyace ma’ana. Hasali ma, ai irin rawar da mawa ƙ a ke takawa wajen bun ƙ asa harshe da kuma al’adun da suke ƙ unshe a cikin harshen ba ƙ arama ba ce. Wannan shi ne ya sa a kowane harshe, mawa ƙ a sukan kasance tamkar gishiri a miya (wato fasaha da zala ƙ a irin na harshe duk a wurin su ake jin su). Bugu da ƙ ari, su ne rumbun ajiyar kalmomin harshe da hikimominsa da kuma al’adunsa (Yakasai, 2012).

Da farko yadda ya zo da amshinsa “An san ki da za ƙ i zuma, an san ka da ɗ aci ma ɗ aci” , sai kuma ya yi ta rangaji da rausayar murya yana maimaita zancen. Da a ce sau ɗ aya ya fa ɗ a ya wuce, to da hankalin mai sauraro zai yi saurin ha ɗ a ma’ana ko manufar amshin da maganar da ke biye. Duk da cewa maimaitawar da ya yi ta yi na zaman jawo hankalin mutane ne cewa akwai abin dubawa a ciki, lallai maimaicin ya taka rawa wurin sa hankalin mai tunani ya ta’alla ƙ a bisa wancan amshi. Wato ke nan lokacin da ya yi farat ya kawo zance na farko sai ya zama ba-zata. Hakan ya sa danganta ma’anar ya zama aiki. Abu na biyu da mawa ƙ in ya sanya shi ne, duk da cewa akwai ɗ iya mai magana ɗ aya da amshi (mai fa ɗ in abin da amshi ke fa ɗ a), mawa ƙ in ya ƙ i kawo shi kusa da amshin saboda kada a yi saurin ganewa inda ya ce “Idan ka ga ruwa rahama, idan ka ga wuta kai takaici”

Da a ce ya kawo wannan bayan amshinsa ne, to da za a gane ma’anar amshin da wuri. To amma sai ya ƙ i kuma ya kawo wani abu na daban, wurin da ya ce “Kishiya ta maso rigima, ta ha ɗ e da mutum maha ƙ urci” . Wannan wani abu ne na daban ya kawo, kafin kuma ya bari mu gama tunani game da abin da yake nufi, sai ya yi farat ya kawo wani ɗ a da ke fassara amshinsa (kamar yadda ya bijiro a sama), idan muka yi duba ga ɗ an da ya sako tsakanin amshinsa da kuma ɗ a mai kama da amshin, za mu ga cewa zance ne kammalalle kuma na gaskiya ga ma’ana. To amma me ya sa ya yi shi, kuma bai yi wata magana ba da za ta fayyace me ɗ an yake nufi? A maimakon haka sai ya kawo ɗ a madangancin amshinsa. Wannan ya nuna ke nan shi ɗ an da ke tsakanin tamkar wani ɓ ad-da-bami ne. Da kuma ya ci gaba da cewa “Idan ka ji amo an gama, idan ka ji shiru akwai ka ɗ aici” , wannan har yanzu yana nuna akwai fa wani abu da ke faruwa. Tamkar dai yadda ake danganta bindiga da idan mutum ya ji amo to ta wuce kansa, haka yake nunawa idan fa mutum ya ji shiru to akwai ka ɗ aici. Wato dai da ka ji amo an gama – ta faru ta ƙ are…. Idan muka lura, da so yake yi wa ƙ ar ta yi saurin fahimta to da zai kawo d an da ke can gaba me cewa “Ni na sha ta da zafi zuma….” Idan da ya kawo na bayan amshi da kuma ɗ an da ya fayyace amshin, to da kuwa za mu gane lallai wani abu na nisha ɗ i ko jin da ɗ i ya zame masa wahala da jidali. Har ma za mu gane ai hakan ne ya sanya ya damu da maimaita wa ɗ annan kalamai a matsayin amshi. Wato ya nuna ta yaya mai da ɗ i yau ga shi ya zama mai ɗ aci?

To amma da ya kai kan ɗ a mai cewa “Ni na sha ta da zafi zuma….” Can cikin wa ƙ ar, sai ya zamana ya gusar da hankalin masu sauraro wajen la’akari da dangantakar ɗ an da amshin wa ƙ ar. Hakan ya taimaka wajen mayar da ɗ iyan ‘kuramen Ɗ a’ . A cikin wani salo na walwala da harshe, mawa ƙ in ya ba wa abin da yake magana a kai siffofi da dama. A wasu wurare ya kurwanta ko mutunta, a wasu wuraren kuma ya ba da wata siffar ta daban. Ga misali “Kishiya ta maso rigima ta ha ɗ e da mutum maha ƙ urci” . A nan ya mutuntar da ‘so’ tun da ya kira shi da mai son rigima. Mai son rigima da ta da hankali kuwa mun san abu ne me tunani. To ta yaya ‘so’ ke da rai ma balle ya yi tunani?. Ke nan ba shi wannan siffa ya taimaka wajen kautar da hankalin mai sauraro daga gano asalin abin da mawa ƙ in yake nufi (wato mai sauraro zai koma tunanin abin mai rai ne).

In da kuma yake cewa “Idan ka zo salon sallama….”, wannan ma mutuntawa ne. Domin wanda zai zo kuma a yi tunanin ya yi sallama sai dai mutum ko aljani. Ke nan da mawa ƙ in ya ba shi wannan siffar to ya kawar da tunanin nai sauraro ba zai kawo cewa wannan ana magana ne da abu marar rai ba. Hasali ma, ai duk siffar da mawa ƙ in ya bai wa ‘so’ a wa ƙ ar sun dace da shi, kuma ba ƙ arya ya yi ko kuskure ba. Da ya ce ‘ba ya sallama’ ai dama duk abu mai shigar bagatatan ba da sanin mutane ba, to babu sallama ke nan ya shiga. Bayan ya gama da siffar mutum, sai kuma ya ƙ ara siffanta shi da cuta. Kai ba ma siffantawa ba, har ya kira shi da cutar. Sannan kuma ya nuna cewa babu masanin maganinta a duniya. A nan mawa ƙ in ya sanyo ru ɗ ani a zukatan masu sauraro. Mutane na farko da ya ru ɗ a su ne, wa ɗ anda za su yi zaton wannan ‘cuta’ da mawa ƙ in ke nufi abu daban ne da abin da yake nufi a baya. Ke nan ma sun zata ya saki layin farko ne ya kama wani zance na daban. Kashi na biyu na wa ɗ anda ya ru ɗ a kuma su ne wa ɗ anda za su ce ta yaya aka ba cuta siffar mutum? Ta yaya mutum ya zama cuta? Duka wannan mai sau ƙ i ne idan aka gane takun. Kamar yadda muka ambata a baya, ai duk abin da ke sa rashin nutsuwa da jin da ɗ i to cuta ce ko kamar cuta yake. Ga shi kuma ita tana shiga ba sallama kamar yadda ya ba ta siffar mutune.

Lokacin da ya fara siffanta tsantsar saurinta, sai ma ta sake zama wata aba daban, domin duka cututtuka da muka sani da wuya a samu wadda za a iya cewa ta kai wannan sauri haka, tun da kuwa ya ce, ta fi ma sartse ko bindiga. Wannan ba ƙ aramar hikima ya sanyo ba wajen canza wa abin da yake magana a kai kamanni. Hakan ya sanya mai sauraro ya yi ta buguwa kamar ƙ wallo daga nan zuwa can a ƙ o ƙ arin gano me ake magana a kai, kurman ɗ a kuwa ke nan. Haka kuma da ya ƙ irgo masu magani ya ce sun kasa magance ta, sannan ga shi ba a ganin ta ko da ‘microscope’. A nan mai sauraro zai ce yauwa yanzu kawai zai duba wace cuta ce a duniya take haka?. Da ya yi haka kuwa an tafi an bar shi, domin mawa ƙ in ya yi hakan ne da nufin ya kai hankalin mai sauraro nesa. Hakan ya taimaka wajen mayar da ɗ iyan ‘Kuramen Ɗ a’.

Gaba kuma sai yake nuna “…. ha ƙ uri shi ne mafita” . A nan mutum zai ce wace irin cuta ce wannan wadda ha ƙ uri ne maganinta? Sai mawa ƙ in ya sake ɓ atar da masu sauraro inda ya ce a samu ko a rashi ha ƙ uri ne mafita. Mutum na iya cewa ai dama game da samu da rashi ake magana? Dabarar kuwa a nan ita ce, ya sakaya cewa ha ƙ uri da abin da zuciya ta ‘so’ shi ne mafita, amma sai ya ce samu da rashi. Ke nan wani salon sakayawa ya yi ga asalin abin da yake magana a kai. Hakan kuwa ya mayar da ɗ iyan kuramen ɗ a. A gaba ma ai cewa ya yi cutar na mayar da:

Fasihi ya zama balidi,

Malami ya manta malunta,

Sarki ya manta sarauta.

 

Idan wani mai sauraron ya ji wannan zai ce ai dama game da ‘hauka’ yake magana, sai dai idan ya duba siffofin baya zai ga akwai siffofin da hauka ba shi da su. Ke nan zai sake shiga ru ɗ ani, amma ‘so’ fa? Sai a ga komai ya tafi daidai - gishiri ya ji, barkono ya ji! A lokacin da kuma ya koma ga Allah (SWT) cikin addu’ar neman tsari daga sharrin zuciya, mai sauraro zai yi kasa ƙ e domin mene ne dangantakar zuciya (kyau da muninta) da kuma wannan cuta ko abin da mawa ƙ in yake magana a kai? Amma kuma sai mawa ƙ in ya yi wani wanka mai kama da jurwaye ya ce ai manzo ne ya fa ɗ a idan zuciya ta ɓ aci to jiki ma ya ɓ aci.

A nan mai sauraro idan bai kula ba zai yi tunanin ai mawa ƙ in ya yi addu’a game da zuciya ne kawai saboda maganar manzo, ba wai saboda cutar da yake nufi na tasiri a zuciya ba. Wannan kuwa ha ƙ i ƙ a zai iya taka rawar gani wajen janye hankalin mai tunani daga ma’ana ta asali. A ta ƙ aice dai ya mayar da ɗ iya ɗ in kuramen ɗ a. Bugu da ƙ ari, sai kuma ya kawo cewa Allah ya kare shi daga soye-soye da kuma mararin zuciyarsa, amma kafin ya bar wani mai sauraro ya yi nazari game da zancen, sai ya yi saurin kawo maganar Manzon (SAW). Ke nan ya gusar da tunani da nazarin mai sauraro, wato ya dai fi son mai sauraro ya yi zaton yana addu’ar ne saboda wannan maganar ta Manzo kuma farin jakada.

Abokan Tafiya

Kafin zuwa ƙ arshen wannan nazari, ya kamata mu yi magana game da ainihin abin da zai zo zukatan wasu, wato dai tunanin cewa nazarin ya karkata ne kawai a kan ‘so’. Shin babu wani abu da za a iya tsinta a cikin ɗ iya na wa ƙ ar idan ba so ba? A wa ƙ o ƙ i da dama (musamman masu sar ƙ a ƙ iya) akan samu abubuwa mabambanta. A wasu lokuta ma akan samu wa ƙ o ƙ i da mutane kan fitar da mabambantan manufofi da wa ƙ ar ke da su. A wasu lokutan kuma, haka ake tashi kowa na da ra’ayinsa game da abin da wa ƙ ar ke magana a kai. Kamar kullum, za ka samu kowa yana da hujjoji da zai iya kare i ƙ irarinsa daga cikin wa ƙ ar. Duk da haka, a wasu lokutan kuma, masu bincike da nazarin wa ƙ a suna kaiwa wani gaci da shi kansa mawa ƙ i hankalinsa bai kai wurin ba. Wato a ƙ o ƙ arin mawa ƙ i na fitar da wani sa ƙ o har ya fitar da wani sa ƙ on na daban wanda bai shirya masa ba. Wannan kan zama abin burgewa ga mawa ƙ in, a duk lokacin da aka sanar da shi hakan.

A cikin wa ƙ ar ‘zuma’ ma akwai wasu na daban wa ɗ anda idan aka ɗ ora su bisa ɗ iya na wa ƙ ar, za a ga sun yi daidai (duk da cewa daidai ɗ insu bai kai na ‘so’ ba ) . Ga misali, akwai (i) hassada da kuma (ii) munanan halayen zuciya. Su wa ɗ annan abubuwa biyu suna kama da abin da wa ƙ ar ke magana a kai. Idan muka ɗ auki munanan halayen zuciya, sai mu ga cewa amshin wa ƙ ar da yake cewa ‘An san ki da za ƙ i’ zuwa baitin da ya ce amma ya shata da zafi, sai mu ga ai yana nuni ne da yadda muradi na zuciya (abubuwan da ke faranta mata) suke wanzar da wahala a gaba. Wahalar nan kuwa ko dai a duniya ko a lahira. A duniya misalin ɓ arawon da ya sha bugu ko mashayin giyar da mota ta ka ɗ e.

Idan muka duba kwatancen da ya yi game da abin da yake magana a kai, nan ma za mu ga ya daidaita da munanan halayen zuciya. Domin kuwa lokacin da yake kwatanta saurin abin, ai mun san yadda abubuwa munana ke ƙ idartuwa a ranmu cikin gaggawa. Ga misali, wanda zai kalli kayan wani amma farat ɗ aya ya ji zai sace. Lokacin ma da yake cewa Allah (SWT) ya kare shi daga soye-soyen zuciyarsa, sai mu ga ai kamar ba ƙ a ƙ en halayen zuciya yake nufi, domin ai Allah (SWT) ne ya fa ɗ a cewa ya zagaye wuta da abin da zuciya ke so. Hassada ma a ɗ aya ɓ angaren, tana iya hawa kan da dama daga cikin ɗ iyan, musamman inda yake nuna ba ta sallama. Mun san kuwa hassadar ba ta yi. Hasali ma, wasu sukan yi ƙ o ƙ arin daina hassada amma lamarin ya zamo mai wuya.

A wurin da yake kwatanta saurin ta ma, ai sai mu ga hassada na da matu ƙ ar saurin tasiri a rayuwar Ɗ an ’ a dam, domin tana shiga ne farat ɗ aya. Ga misali, fa ɗ a wa mutum cewa ma ƙ wabcinsa ya gina sabon gida ko kuma a fa ɗ a masa wane ya samu ƙ arin matsayi. Lokacin da kuma yake magana game da marari ko soye-soyen zuciyarsa da yake so Allah (SWT) ya yaye masa, ai dama yawanci mararin zuciya ne ke kawo hassada. Misali idan wani ya samu irin abin da kake son samu ko kuma wani ya samu wani abu mai amfani wanda ka san abin soyuwa ne. Wani kuma na iya cewa me ya sa duk da cewa nazari ya nuna haka amma kuma aka ɗ auki so a matsayin abin da mawa ƙ in ke nufi? Amsar kuwa mai sau ƙ i ce, domin ‘so’ ne ka ɗ ai abin da idan ka ɗ auka ba za ka samu wani ɗ iya da ba ya magana kansa ba. Wato ba za ka samu wani ɗ a da idan aka yi masa fassara, ba za ka samu ta inda yake taimakawa wurin bayyana wani abu game da so ba. Saura duk akasi ne kawai.

Idan ka ɗ auki hassada, ai ba za a ce malam ya rasa maganinta ba, domin akwai addu’a da Musulunci ya zo da ita da ke kare mutum daga yin hassada. Haka kuma idan ka ɗ auki sauran munanan halaye na zuciya, za ka samu kusan kowane na da maganinsa ko dai ta hanyar malam ɗ in da ya ambata ko kuma sauran da ya lissafo (boka da matsafa da likita da nasara da kuma yahudu). Sannan sai mu lura, ta yaya hassada za ta sa mutum ya manta gidansu? Abin da kamar wuya wai tsohuwa ta tauna ƙ wallon goriba. Kamar yadda mawa ƙ in ya ce ma, har sarki ya ɗ imauce ya manta sarautar kansa. Ta yaya hassada za ta sa haka? Mun ga dai ke nan ‘so’ ɗ in ne ake magana a kai.

Jawabin Kammalawa

Ɗ an abin da ya gabata ballagazar nazarin kurman ɗ a ne a wa ƙ ar zuma ta Alan wa ƙ a. Ba shakka mawa ƙ in ya yi wasa da hankula sosai, kai ka ce ya samu wuri ne ya zauna domin ya sha dariyar wahalar da ya ba masu sauraro da kuma masu nazari. A cikin wa ƙ ar akwai maganganu da dama wa ɗ anda za su fito da ma’anoninta a fili amma sai ga shi ta wahalar. Ba ma wannan ba, ai maganar farko da ya fara yi ta isa ta warware wa ƙ ar, domin cewa ya yi “An san ta da za ƙ i zuma….” Me za mu gani a nan? Mun manta da abin da ake yawan fa ɗ a “Soyayya ruwan zuma”? shin kuma kowa ne ke amfani da haka? A wa ƙ o ƙ i da dama har ana cewa “Soyayya ruwan zuma ce, idan ka sha ka ba masoyi”. A nan ke nan mawa ƙ in kamar ya ajiye sunan yanka ne (soyayya) ya yi amfani da wakilin suma (zuma).

Daga amshin wa ƙ ar na “Alan wa ƙ a me ya faru, wannan kurman ɗ iya ne” , haka ’yar amshin ta yi ta damuwa da sai ta san “Me ya faru” amma da an ba ta amsa sai ta ce ai kurman ɗ iya ne. Ma’ana dai tana son ƙ arin bayani. Wannan tamkar daidai yake da yadda lamarin zai kasanc e ga duk mai sauraron ta a karo na farko (wa ƙ ar), domin zai yi ta tambayar wa ƙ ar ne daga zuciyarsa da cewa me ya faru? A sau ƙ a ƙ e ko ba komai dai mai sauraro zai za ƙ u da ya ji me mawa ƙ in ke son bayyanawa. Ke nan da masu sauraro da nazari a gabansa suke, to da tambayar da za su yi ita ce me ya faru? Wato dai tamkar yadda ’yar amshin ta yi.

Gaskiyar maganar ita ce, al’ummar Hausawa al’umma ce wadda ta ginu a bisa fasahar harshe (Gusau, 2013), saboda haka wannan ne ya sanya ko a harshen ma mawa ƙ a na da tudun dafawa na musamman. Wannan kuma shi ne ya haifar da samuwar baiwa ga mawa ƙ a ta sarrafa hikima da basira cikin Hausa wadda take ƙ unshe da kalmomin fannu (daidaitattu kuma nagartattu) domin isar da sa ƙ onni.

Nazarin da ya gabata ya ƙ ara tabbatar da matsayin wa ƙ a na sarrafa tunani da yadda zukata kan sami kansu a yanaye-yanaye daban-daban, Ita dai wannan wa ƙ ar ‘zuma’ ta ɗ auki zuciyar mai sauraro da kuma mai nazari ta mi ƙ a wa duniya. A irin wannan yanayin ne aka bar w a mai sauraro da ɓ igewa cikin tunani na nisha ɗ i. A nazarce kuwa, an ga cewa ‘so’ shi ne ƙ ashin bayan sa ƙ on da wa ƙ ar take ƙ unshe da shi.

Manazarta

Abba, M. & Zulya daini, B. (2008). Nazari Kan Wa ƙ ar Baka ta Hausa . Kaduna, Nijeriya: Gaskiya Coporation Limited.

Abubakar, A. L. (2015). Alfiyyar ALan Wa ƙ a (Shahara Sanadi). Kano: Taskar ALA Global Ltd.

Barista, M. L. (2011). Wa ƙ o ƙ in Aminu Ladan Abubakar (Alan Wa ƙ a) V ol. 1.   Kano: Iya Ruwa Publishers .

Ɗ angambo, A. (1981). “ Ɗ aurayar Gadon fe ɗ e Wa ƙ a”. Takarda Wadda ya Gabatar a Taron Argungu. Sakkwato: Hukumar Fasaha da Al’adun Gargajiya ta Jihar Sakkwato. 

Ɗ angambo, A. (2007). Ɗ aurayar Gadon Fe ɗ e wa ƙ a. Zaria: Amana Press.

Dunfawa, A. (1981). Ma’aunin Wa ƙ a . Sakkwato: Garkuwa Publishers

Gusau, S. M. (1993). Jagoran Nazarin Wa ƙ ar Baka. Kano: Benchmark Publishers Limited.

Gusau, S. M. (2011). Ta ƙ aitaccen Tar ƙ e a kan Wa ƙ ar Jami’a ta ALA, T aron ‘Wa ƙ a a Bakin mai ita’, CNHN, Kano: Jami’ar Bayero.

Lawan, M. B. (2011). Wa ƙ o ƙ in Aminu Ladan Abubakar , V ol.1, Kano: Iya Ruwa Publishers  

Mashi, A. B. (1986). “ On the Poem Alkaiyah by Al-Ustaz Al-Mukasaf Muhammad Ibn Al-Sbbabgh Al-Kashnawy ( Ɗ anmarina).

Thrall, H. (1936). A Handbook of Literature. New York: Odyssey Press.

Umar, M. B. (1980). Dangantakar Adabin Baka da Al’adun Gargajiya. Kano: Triumph.  

Yakasai, S. A. & Sani, A-U. (2021). Diwanin Wa ƙ o ƙ in Aminu Ladan Abubakar (ALA). Kaduna: Amal Printing & Publishing Nigerian LTD. ISBN: 978-978-57624-9-0

Yakasai, S. A. (2012). Jagoran Ilimin Walwalar Harshe. Sokoto: Garkuwa Media Se ɓ ices Ltd.

Yakasai, S. A. (2014). “Nazarin Harshen Farfaganda Cikin Siyasar Kudanci da Arewancin Nijeriya a Wa ƙ ar ALA ta Rajista”, a GARKUWAN ADABIN HAUSA: A Festschrift in Tribute to Abdul ƙ adir Ɗ angambo, S. M. Gusau (ed), Zaria: ABU Press.

Yakasai, S. A. (2014). “ Some Major Themes in Hausa Reponsorial Songs in Aminu ALA’s Performance”, Current Persfecti v e of African Folklore: A Festschrift for Professor Ɗ andatti Abdul ƙ adir. Zaria: ABU Press .

Yakasai, S. A. (2015). “Memory in Oral Tradition: An E x cursion in to the History and Culture of City-State in Aminu ALA’s MASHIGAN KANO”, 1st International Conference on Hausa People, Language & History, DNL, Kaduna State University.   

Post a Comment

0 Comments