Ticker

6/recent/ticker-posts

Biki na Farar Kaza...: Nazarin Farin Ciki da Godiyar Aliyu Nata a Wakar Aurensa Ta “Na Gode”

Citation: Ayuba, A. & Bugaje, H.M. (2024). Biki na Farar Kaza...: Nazarin Farin Ciki da Godiyar Aliyu Nata a Waƙar Aurensa Ta “Na Gode”. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, 3(1), 205-214. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.023.

Biki na Farar Kaza ... : Nazarin Farin Ciki da Godiyar Aliyu Nata a Wa ƙ ar Aurensa Ta “Na Gode”

Abubakar Ayuba, Ph.D.

Department of African Languages and Cultures
Ahmadu Bello University, Zaria.

0706 089 9737

abuayuba2050@gmail.com / abubakarayuba@abu.edu.ng ,

ORCID : 0000-0003-0178-3548

 

Dr . Hauwa Muhammad Bugaje

Department of African Languages and Cultures
Ahmadu Bello University, Zaria.

0803 640 6803

hhmbugaje@gmail.com

ORCID : 0009-0003-1649-9678

Tsakure

Nazarin wa ƙ ar “Na Gode” ta Aliyu Nata ya tattauna batutuwa ne a kan farin ciki da godiyar mawa ƙ in, saboda irin yadda ‘yan uwa da abokan arziki suka amsa gayyatar da aka yi musu a lokacin aurensa. Ma ƙ alar ta yi tsokaci a kan godiyar Allah daga wa ƙ ar, sannan ta yi magana kan lokacin da mawa ƙ in ya yi godiya da ala ƙ ar godiya da lokaci sai kuma tsokaci kan sosuwar zuciya a godiya. Nazari ya kawo tarihin mawa ƙ in da ta ƙ aitacciyar bita a kan wa ƙ ar baka da nagari da kuma godiya. Manufar yin wannan nazari ita ce, a tarke godiya da farin ciki daga wa ƙ ar auren Aliyu Nata domin a gano irin murnar da ya yi da kalaman da ya yi amfani da su da kuma yadda ya sarrafa su. Binciken ya zavo wa ƙ ar “Na Gode” daga cikin wa ƙ o ƙ in Aliyu Nata saboda wa ƙ a ce da take ɗ auke da murnar cikar dogon gurin mawa ƙ in na yin aure kuma wa ƙ ar tamkar ƙ anwa ce ga wa ƙ arsa ta “Aure Martaba” bakandamiyar Aliyu Nata. Masu bincike sun shifci wa ƙ ar da aka nazarta, suka tantance ɗ iyanta tare da gudummuwar mawa ƙ in, an nemi tarihin mawa ƙ in kuma ya turo da bayanai gwargwado ta WhatsApp, sannan binciken ya sarrafa ɗ an wa ƙ a goma a misalai da ya kawo daga wa ƙ ar “Na Gode”. A dun ƙ ule, ma ƙ alar ta gano godiya a Hausa tana da fa ɗ in gaske, abu ne da ke da ala ƙ a da girmamawa da yabawa da nuna murna da sauransu. Uwa-uba, fa ɗ in Alhamdu lillahi kai wa ma ƙ ura ne a godiya ga Allah (S.W.T.), hakan yana da ala ƙ a da neman ƙ arin ni’ima a wurinsa kuma sunkuyawa ce da mi ƙ a wuya ga mai duka. Binciken ya gano ban gajiyar da mawa ƙ in ya yi na cike da farin cikinsa, inda tarbiyyarsa ta bayyana a wa ƙ ar. Godiya da farin cikin mawa ƙ in na da nasaba da lokaci da sosuwar zuciya, kuma ɗ iyan wa ƙ ar na ƙ unshe da hotancin zucin mawa ƙ in game da yadda taron aurensa ya gudana. Godiyar Aliyu Nata tana fatar ɗ orewar zumunci da abokan zumuncinsa kamar yadda a Hausa, “Na gode!” na nufin, idan mutum ya sami dama zai yi alheri fiye da wanda aka yi masa.  

Muhimman Kalmomi: Aliyu Nata , Aure , Biki , Farin Ciki , Gayya , Godiya , Wa ƙ ar Baka ta Yau

1.1   Shimfi ɗ a

Wa ƙ ar “Na Gode” ta Aliyu Nata ta samu ne mako ɗ aya bayan an ɗ aura masa aure, wa ƙ ar ta ƙ unshi batutuwa da dama da su (ke) bayyana yadda auren mawa ƙ in ya gudana da wa ɗ ansu daga cikin mutane da suka halarci auren. Mawa ƙ in ya bayyana irin farin cikinsa da kuma godiya ga Allah da sauran mutane da suka bayar da gudummuwarsu a lokacin aurensa. Wa ƙ ar tana ɗ auke da sosuwar zuciyar mawa ƙ in game da ranar aurensa kuma tana ƙ unshe da hotancin zucinsa na yadda wa ɗ ansu al’amura suka faru da shi a wurin aurensa da bayani a kan mutanen da suka taya shi murna—mata da maza da yara da sauransu. Aliyu Nata ya yi godiya matu ƙ a a wa ƙ arsa kuma ya yi ƙ udurin zai ci gaba da yin zumunci da jama’a, duk da ya san ba zai iya biyan su abin da suka yi masa ba.

2.1 Manufa da Muradan Bincike

Manufar wannan ma ƙ ala ita ce, ta yi nazari a kan godiya da farin cikin Aliyu Nata daga wa ƙ ar “Na Gode”. Muradun da binciken yake son ya cimma sun ƙ unshi gano yadda wa ƙ ar ta taskace godiya da farin ciki game da gudummuwar da ‘yan uwa da abokan arzikin Aliyu Nata suka ba shi a aurensa. Wannan nazari yana da muradin ya tantance kalaman mawa ƙ in na yin godiya da ya yi a cikin wa ƙ a. Ma ƙ alar tana da muradin ta yi nazarin yadda kalaman mawa ƙ in suka bayyana farin-ciki da jin da ɗ insa saboda karamcin da aka yi masa.

3.1 Hanyoyin Gudanar da Bincike

Wannan bincike ya soma gudana bayan Aliyu Nata ya yi aure a ranar 20 ga Agustan shekara ta 2022. WhatsApp, ɗ aya ce daga cikin hanyar da masu bincike suka yi amfani da ita wajen samo bayanai game da mawa ƙ in, ta wannan kafa binciken ya samo wa ƙ ar “Na Gode” daga hannun mawa ƙ in. A watan Satumbar shekarar 2022, masu bincike sun shifci wa ƙ ar, daga nan suka nemi tarihin mawa ƙ in. Masu bincike sun rubuta kusan duk tambayoyin da suke bu ƙ ata dangane da Aliyu Nata, suka tura masa ta WhatsApp, sannan suka jira na ɗ an lokaci. A ranar 12 ga Disamba, 2022 da ƙ arfe 8:08 na safiya zuwa 8:50 na wannan safiya masu bincike sun amshi sa ƙ on muryar Aliyu Nata ɗ auke da amsoshin tambayoyi da aka yi masa dangane da rayuwarsa. Nan da nan aka saurari bayanan, aka shifta, aka tura wa mawa ƙ in domin ya tabbatar da sahihancinsu a rubuce. Masu bincike sun bi tarihin Aliyu Nata suka tsara shi, suka sake tura masa domin ya tantance (tarihin nasa). Nata ya nuna gamsuwarsa kan abin da aka rubuta da gyare-gyaren da aka yi wajen rubuta tarihinsa kamar yadda yake a wannan ma ƙ ala.

Ma ƙ alar ta yi nazarin littafai da ma ƙ alu da kundaye, masu nasaba da kusan duk wani abu da wannan nazari ke da ala ƙ a da shi. Bugu da ƙ ari, masu bincike sun yi nazarin Muhammed (1990) a kan kalmomin sosuwar zuciya da hoton zuci da hotancin zuci da makamantansu lokacin gudanar da wannan bincike. Masu bincike sun bi wa ƙ ar dalla-dalla, suka tsamo ɗ iya da ke da ala ƙ a da muradun wannan bincike domin ƙ alailaice godiya da farin ciki a wa ƙ ar “Na Gode” ta Aliyu Nata. Masu bincike sun bi wa ƙ ar “Na Gode” a yadda take ba tare da sun sauya ba ƙ i ko wasali a ɗ iyan da aka kawo misali da su ba. Duk wata kalma ko suna da ke cikin ɗ iyan da aka kawo misalai a ma ƙ alar haka take, saboda masu binciken sun tattauna da Aliyu Nata, kuma ya fa ɗ a musu yadda suna ko furucin wata kalma yake. Misali “Dabadaba” suna ne na ɗ aya daga cikin mutanen da suka halarci auren Nata, “malmatso” ita ce “marmatso” a Daidaitacciyar Hausa. Masu bincike sun kiyaye karin harshen mawa ƙ in da kuma suna kamar yadda ya tabbatar musu a duk tattaunawa da suka yi da shi bayan an shifci wa ƙ ar.

4.1 Tarihin Aliyu Nata

Aliyu Nata, ɗ a ne a wurin Alhaji Isa Ibrahim da ake yi wa la ƙ abi da Alhaji Ibrahim Soja, sunan mahaifiyarsa Hajiya Binta. Mahaifan Aliyu Katsinawa ne kuma a Unguwar Sullu ɓ awa da ke cikin garin Katsina aka haifi Aliyu Isa Ibrahim, a shekara ta 1995. Aikin soja ya kai mahaifin Aliyu garuruwa daban-daban da suka ƙ unshi Ikko da Zariya da Kaduna da sauransu. Alhaji Isa Ibrahim yana da ‘ya’ya ishirin da biyu, Aliyu Isa Ibrahim shi ne ɗ a na goma sha shida.

La ƙ abin Nata ya samu ne daga soyayya, lokacin Aliyu Isa Ibrahim na aji biyu na babbar sakandare kamar yadda yake cewa : “Akwai wata yarinya da nake son ta (junior ɗ in mu) tana JS Two. To, sai dai irin kunyar nan da kuma yarinta, gaba ɗ ayanmu ni da ita, ba zan iya gaya mata ba. Akwai wata yayarta da take class ɗ in mu, sai na gaya mata saboda muna magana sosai da ita. To, shi ne yayar fa, duk lokacin da na shigo aji sai ta ri ƙ a cewa “Nata, Nata.” ‘Yan aji ba su san wa ake nufi ba, kowa sai ya ɗ auka. Wannan shi ne asalin sunan Nata.”

Aliyu Isa Ibrahim ko Nata ko Aliyu Nata yana da ilmin addinin Musulunci gwargwado, ya yi karatun Ƙ ur’ani da na hadisai da sauransu. Ya kuma halarci Firamaren Ƙ ofar Guga da ke Katsina a tsakanin 2001-2007, ya zarce GDSS Natsinta Army Barrack daga 2007-2013. Aliyu Nata ya yi karatu a Kwalejin Ilmi ta Tarayya da ke Katsina a tsakanin 2015-2019, ya yi karatun share fagen malanta (Pre NCE) daga bisani ya sami horon malanta (NCE) a fannin Biology/Computer. Kafin ya kammala Kwalejin Ilmi ta Tarayya ta Katsina. Nata ya koyar a Firamaren Albarka a Sabuwar Kasuwa da ke Katsina domin cika shara ɗ in samun shaidar malanta ta ƙ asa a shekarar 2019.

Nata ya ce, ya soma yin wa ƙ a bayan ya kammala karatun sakandare a shekarar 2013. Yasir Ubale, maigidansa ne da suka yi harkar decoration tare, da aurensa ya zo, sai Aliyu Nata ya yi masa wa ƙ ar biki, daga nan ya soma yin wa ƙ a kuma da wa ƙ ar aure ya soma wa ƙ a. Aliyu Nata ya ce bai cika sauraron wa ƙ o ƙ in dauri ba, amma idan ta kama yakan saurara, musamman idan ya je wuri, ya tarar ana sauraronsu ko kuma idan gidan rediyo ya sanya ko kuma idan aka kunna wa ƙ o ƙ in a mota yayin da ake yin wata tafiya. Duk da haka, Aliyu Nata ya ce marigayi Mamman Shata Katsina shi ne gwaninsa a cikin mawa ƙ an Hausa na dauri. Nata yana da ra’ayin ya yi wa ƙ a tun yana yaro kuma sha’awar haka ta yi ƙ arfi a zuciyarsa, shi ya sa ya jajirce wajen ganin ha ƙ arsa ta cimma ruwa. Aliyu Nata ya ƙ ara da cewa “… domin Allah babu wani mutum guda ɗ aya da ya koya mun wa ƙ a, ina da burin haka tun ina yaro, na fara jarabawa, to cikin ikon Allah na kuma fahimci zan iya, sai na ci gaba da yi.” Aliyu Nata ya ce bai gaji ki ɗ a da wa ƙ a ba, kuma magabatansa sun san sana’a ce yake yi, tsakaninsa da su sai fatan alheri a sana’arsa. Nata ya ce “Sana’an nan da nike yi ni, babu wani abu da nike fa ɗ a wanda zai sa a ce na lalata tarbiyan da a kai mun, sun yi na’am da abin da nake yi kuma suna yaba man, suna jinjina man, sannan kuma suna taya ni da shwarwari. Ko lokacin da na fara da yardarsu na fara da amincewarsu, cikin ikon Allah ma shi ya sa nake ganin nasara.”

Aliyu Nata ya yi wa ƙ o ƙ i da yawa daga 2013 zuwa yanzu, kusan ya ce ba zai iya tantance adadinsu ba, saboda lokaci ya soma ja, amma ya san ya wa ƙ e mutane daban-daban da suka ƙ unshi sarakuna da ‘yan siyasa da ma’aurata da masoya da ‘yankasuwa da jami’an tsaro da sauransu. Fitattu daga cikin wa ɗ anda ya yi wa wa ƙ a akwai matar Sarkin Katsina da matar Gwamnan Jihar Katsina da Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari da hakimai irin su Durbin Katsina da Galadiman Dokan Katsina da sauransu a ciki da wajen Jihar Katsina. Nata yana son ɗ aukacin wa ƙ o ƙ in da ya yi a rayuwarsa, sai dai ya ce, “amma wacce na fi so, ita ce wacce jama’a suka fi raja’a kanta “Aure Martaba”. Ni na yadda na fi sonta kuma ita ce bakandamiyata, sannan jama’a ma ita suka fi so.” Girman aure da martabarsa suka ja hankalin Nata ya yi wa ƙ ar “Aure Martaba”, sannan ya ce ya lura wa ɗ ansu sun “ ɗ auki auren yanzu, suna yin shi don sha’awa, wasu sun manta ma da bauta ne. To wallahi ka ji babban abin da ya ja hankalina. Duk ɗ an sunna ta silarsa ya zo, na san cewa bi’iznillahi duk ɗ an sunna zai so wannan wa ƙ ar. Shi ne abin da ya sa na jajirce, na tsaya, na yi ta.”

Aliyu Nata yakan rubuta wa ƙ o ƙ insa, amma akwai wa ɗ anda ba rubuta su yake yi ba. Aliyu ya ƙ ara da cewa “Ba wacce ban yi, ina rubutawa, kuma ina yi ban rubuta ba.” Bugu da ƙ ari, Nata ya fi tsara wa ƙ a da daddare, yakan iya samun ilhamin wa ƙ a musamman idan yana barci ko kuma idan yana tafiya a hanya a kan abin hawa ko a ƙ asa (wa ƙ a takan fa ɗ o masa a rai). Aliyu Nata yakan tsaya ya yi nazari a kan abin da zai yi wa ƙ a a kai ko wanda zai yi wa wa ƙ a kafin ya yi ta. Yakan lura da abin sosai kafin ya yi masa wa ƙ a, kuma baiwar wa ƙ a takan fa ɗ o masa a kowane lokaci idan Allah ya kawo ta.

Nata ya yi tafiye-tafiye saboda wa ƙ a, kusan a gida Nijeriya musamman a Arewa babu inda bai je ba. Ya kuma tafi gari-gari a Nijar, musamman Yamai da Mara ɗ i da Tawa ya yi wa ƙ a. Aliyu yana da zumunci da sauran mawa ƙ a a Jihar Katsina da wajenta, suna zaune lafiya, babu fa ɗ ace-fa ɗ ace a tsakaninsu. Sukan ba juna shawara a duk lokacin da bu ƙ atar haka ta taso.

Ƙ alubalen Aliyu Nata a harkar wa ƙ a ba ta wuce irin ta kusan duk wanda Allah ya ɗ aukaka shi ba . Akwai rashin fahimta daga wa ɗ ansu mutane ko abokai, da suke ganin yana wula ƙ anci ko girman kai. Wa ɗ ansu kuma suna kallon ya yanke zumunci da su, ya ɗ auki girman kai ya sa. Nata ya ce “Wani ma ba ka da numbai, to sai su ɗ auka girman kai ne, don ganin cewa, Allah ya ba ka wata dama, sau da yawa wasu mun ɓ ata da su silar haka, wasu in mun ha ɗ u ma sai su ɗ auke kai. To, tsakani da Allah ni ƙ alubalen da nake fuskanta ke nan, amma na ɗ auke shi jarrabawa. Sannan kuma ba kowa ba ne yake haka, wasu in ka zauna ka fahimtar da su suna fahimta.” Aliyu Nata ya ƙ ara da cewa, “Duk wanda Allah ya ba ɗ aukaka kowace iri ce, yana bu ƙ atar uzuri, yana bu ƙ atar uzuri sosai saboda hidindimu ne na jama’a da yawa da dama. Ka ga wancan, wancan ya zo. Ka ga muna da abukkananmu da yawa wanda yanzu sai a da ɗ e ba a ha ɗ u ba, ko kuma su kira kana uzuri ba ka ɗ auka ba, sadda ka gama, call da ka yi missing ya yi yawa, ka rasa wa za ka kira da sauransu, shi ne ƙ alubalena a wa ƙ a.”

Aliyu Isa Ibrahim (Aliyu Nata) ya yi aure ranar ishirin ga watan Agustan shekarar 2022, a garin Katsina, kuma ya ga taron da ba zai iya bayyana adadin wa ɗ anda ya ga ni a wurin auren nasa ba. Nata ya ce shi kam sai dai godiya ga Allah, saboda mutane da Allah ya tara masa su, ya gani, wannan ya sa shi farin ciki har ya yi kukan murna. Burin Aliyu Nata na yin aure ya cika, kuma ya bayyana yadda ya ɗ auki aure kafin ya yi shi, sai ya ga ba haka abin yake ba domin “akwai wasu abubuwa da nake kallon kamar suna da wahala a ciki, domin Allah, sai na samu suna da sau ƙ i. Na samu suna da sau ƙ in gaske, cikin hukuncin Ubangiji da rufin asiri na Ubangiji.” Aliyu Nata ya ce, mai aure da saurayi suna da bambancin tunani sosai, “tazarar ta kai daga nan (garin Katsina) zuwa Saudiyya a ƙ asa. Abu na farko; wanda ya yi aure yakan sami girma da kamala ko a idon mutane, na biyu; kamun kai da fuskantar Ubangiji yadda ya kamata, na ukku; jin da ɗ i da kuma samun kulawa daga ɓ angaren iyali, na hu ɗ u; hankali da natsuwa, na biyar; akwai bambancin bu ɗ i samu yana ƙ ara yalwa da kuma albarka.”

5.1 Wa ƙ a

Abdul ƙ adir (1975) ya ce, wa ƙ o ƙ in baka kafafe ne na musamman da sukan fayyace al’ada a zamantakewar Hausawa da Fulani, inda mawa ƙ a sukan yaba alherin iyayen gidansu har da wa ɗ ansu muhimman al’amuran rayuwa. Manazarcin ya ce, wa ƙ o ƙ in suna ƙ unshe da hoton rayuwa daki-daki, musamman al’amuran fada da ƙ asa baki ɗ aya. Abdul ƙ dair (1975) ya ce, mawa ƙ an baka na Hausa sukan nisha ɗ antar kuma sukan fa ɗ akar, sukan adana tarihi da al’adu da fasahar baka a wa ƙ o ƙ insu. Manazarcin ya ce, mawa ƙ i yakan yabi ubangidansa, yakan shawarce shi, a wani lokaci kuma yakan ba al’umma shawara a wa ƙ a. Masanin ya ce, mawa ƙ i yakan yi zambo a wa ƙ a wani lokaci.

King (1980) ya ce, akwai dangantaka tsakanin wa ƙ a da amshi, ya kuma fito da rawar ‘yan amshi wajen gina ɗ an wa ƙ ar da mawa ƙ i ya fara. Manazarcin ya ce, ‘yan amshi sukan ɗ ora daga inda mawa ƙ i ya fara gina ɗ an wa ƙ a, kuma sukan yi tankiya da uban wa ƙ a su cika masa ɗ an da ya fara. A kusan kullum, ‘yan amshi sukan maimaita amshi a ƙ arshen ɗ an wa ƙ a. King (1980) ya ce, amshin wa ƙ a yana turke karin wa ƙ a, ya taimaka wajen daidaita jigonta. Masanin ya ce, tsawon amshin wa ƙ a yakan bambanta daga wa ƙ a zuwa wa ƙ a, amma amshi bai cika sauyawa ba a wa ƙ a, kodayake amshi yakan sauya, ana iya samu n amshi fiye da ɗ aya a wa ɗ ansu wa ƙ o ƙ i. Manazarcin ya ce, kar ɓ i yana da tasiri a ginin ɗ an wa ƙ a kuma ya bambanta da amshi , domin a kan cika ɗ an wa ƙ a da kar ɓ i ko a yi ƙ arin hasken manufar da aka faro a ɗ an wa ƙ a da shi (kar ɓ i). King (1980) ya ce, akwai nau’i biyu na kar ɓ e ɓ eniya; na farko akan yi tankiya tsakanin uban wa ƙ a da ‘yan amshi kuma ‘yan amshi ne sukan kammala ɗ an wa ƙ ar, na biyu kuma amshi yakan biyo bayan kar ɓ i. A dun ƙ ule, manazarcin ya ce, amshi yakan na ɗ e sa ƙ on da wa ƙ a ta ƙ unsa cikin hikima kamar yadda ya nuna a turken Bakandamiyar Naramba ɗ a. Masanin ya ce, a yawancin lokaci, mawa ƙ i yakan bu ɗ e wa ƙ arsa da turke, masu amshi su yi ta maimaita shi a ƙ arshen kowane ɗ an wa ƙ a.

Kusan duk wani nau’i na adabi yakan sanya mai sauraro nisha ɗ i sannan ya ilmantar da shi. Wa ƙ ar “Na Gode” ta Aliyu Nata ta ƙ unshi wa ɗ annan muhimman batutuwa kuma tana cike da rayuwar Hausawa da tadodinsu duk da kasancewarta wa ƙ ar baka ta yau. Wa ƙ ar tana da turke kuma shi ne amshinta, amma mawa ƙ in bai ambaci turken a kammale ba a farkon wa ƙ ar kamar yadda yawancin wa ƙ o ƙ in baka na dauri suke bin wannan tsari. Turken wa ƙ ar da amshinta sun na ɗ e murna da godiyar Aliyu Nata ga Allah da ya nuna masa ranar bikinsa da kuma arzikin jama’a da ya yi masa. ‘Yar amshi ta soma ambaton wani ɓ angare na turken wa ƙ ar kafin ambaton turken wa ƙ ar “Na Gode” da amshinta. Uban wa ƙ a shi ma ya ambata wani ɓ angare, ki ɗ a ya biyo baya daga nan jagora ya furta “Na gode!” da “Allah na gode!” Wa ƙ ar “Na Gode” tana da ragaggen amshi da ‘yar amshi ta yawaita maimaitawa bayan uban wa ƙ a ya ambaci kusan kowane ɗ ango a kusan kowane ɗ an wa ƙ a, inda “Na gode!” da “Ya gode!” da “Mun gode!” da “Nata ya gode!” suka wanzu a gurabe daban-daban na cikin kusan kowane ɗ an wa ƙ ar. Uban wa ƙ a shi yake bu ɗ e ɗ an wa ƙ arsa kuma shi yake rufewa a wa ƙ ar “Na Gode”, amshi ya biyo bayan kowane ɗ a, illa a ɗ an wa ƙ a na ƙ arshe ‘yar amshi ta bu ɗ e ɗ an kuma ta rufe shi , uban wa ƙ a kuma ya yi ta maimaita “Na gode!” a tsakanin kusan kowane ɗ ango sai ‘yar amshi ta biyo da amshi.                              A dun ƙ ule, ‘yar amshi ta bu ɗ e wa ƙ ar “Na Gode” kuma ita ta rufe ta, sa ɓ anin a wa ɗ ansu wa ƙ o ƙ in baka na dauri da kusan uban wa ƙ a yake bu ɗ e wa ƙ arsa kuma ya rufe ta. Duk da haka, wa ƙ ar “Na Gode” ta bi tsarin wa ƙ o ƙ in baka na dauri, inda aka bu ɗ e ta da ki ɗ a kuma aka rufe ta da shi.

5.2 Godiya

Bargery (1993:395) ya ce, gode tana da ala ƙ a da shu ɗ a ɗɗ en al’amari da halin da ake ciki, kalmar tana da nasaba da godewa ko godiya. Ƙ amus na CNHN (2006:169) ya ce, godiya tana nufin nuna murna ko yabawa bayan an aiwatar da wani kyakkyawan abu. Ƙ amus na Newman (1997:278-9) ya bayyana godiya da gode suna da ala ƙ a da alhamdu lillah, kuma madalla da na gode suna nufin godiya. Ƙ amusun ya ce, akwai wa ɗ ansu zantuka da suke cike da godiya irin su “ya gode wa masu sauraronsa don goyon bayansu da na yi masa godiya don taimakonsa da ‘na gode, Allah ya amfana da ‘ina matu ƙ ar godiya… da ‘godiya ta musamman da ‘isar da godiya da ‘ka isar mini da godiyata= ka mi ƙ a musu godiyata da ‘sannu da ƙ o ƙ ari da ‘sannu da wahala da ‘mun gode wa Allah= mun gode Allah da ‘albarkacinka suka yi nasara da ‘sun sami albarkacina.” Ƙ amus na Abraham (1978:330-331) ya ce, godiya tana da nasaba da jin da ɗ i, kuma akwai hanyoyin godiya a Hausa kamar a ce, “muna godiya da ‘mun yi godiya bisa ga wannan.” Ƙ amusun ya ce, mu ƙ arrabai na Sarki ko basarake sukan ce “godiya yake yi” idan kyauta ta fito daga hannun basarake zuwa na talaka. Haka kuma, Hausawa sukan ce, ‘godiya ke sa ƙ arin kyauta.”

Godiya ɗ abi’a ce mai kyau da akan yabi alheri da ita, akan yi amfani da kalmomi irin su madalla da na gode da godiya nake da alhamdu lillahi da sauransu yayin da aka cimma gaci a rayuwa. Galibi mutum yakan yi godiya ga Allah (S.W.A.) saboda ni’ima da ya yi masa, halin kirki da yake gudana tsakanin mutane kan zama sanadin wani ya gode w a wani a rayuwa. Kusan duk inda godiya ta faru, to, wani ya yi w a wani abin kirki. Godiya tana iya ɗ aukar ma’anar nuna jin da ɗ in ko farin ciki da murna ga wanda aka yi wa halin ƙ warai . Wannan farin ciki da annashuwa kan faranta zuciyar mutum ya ce, “Na gode!” Wannan furuci a Hausa yana da ala ƙ a da yau da gobe, wato kusan duk wanda aka yi masa ya gode, to yana da burin mayar da biki ga wanda ya yi masa halin kirki. Idan hali ya samu akan iya yin abin da ya zarce alherin farko ba yankewa har muddan rai.

5.3 Nagari

Muhammad, (1997) ya ce, jama’a suna ƙ aunar mutum nagari, wanda duk ya san nagari zai so shi, saboda mutum ne da yake da fahimtar Allah ya yi wa bayinsa baiwa. Masanin ya ce, mutum nagari yana ba kowa girma kuma yana karrama kowa kamar yadda kusan shi ma na kowa ne. Kirk-Greene (1973) ya ce, mutumin kirki a Hausa, shi ake kira nagari , wato mutum mai halin ƙ warai da fara’a ga mutane. Kirk ya ce, mutumin kirki yana da gaskiya da ri ƙ e amanar mutane, yana da karamci da ha ƙ uri da hankali da natsuwa da takatsantsan a rayuwarsa. Kirk-Greene (1973) ya ce, ladabin mutumin kirki a wurin manya da duk na gaba da shi abin a yaba ne. Manazarcin ya ce, kunya takan wanzu a zantukan mutumin kirki da ayyukansa, yana da mutunci da ƙ o ƙ arin kauce wa cin mutuncin kowane mutum. Mutumin kirki yana da hikima da adalci da haiba da kwarjini ga kuma farin jini a idon mutane. Muhammad, (1997) ya ce, mutum nagari yana da gaskiya da ƙ aunar mai gaskiya, kuma ba ya munafunci. Nagari, mutum ne mai cika al ƙ awari da ri ƙ on amana da son adalci da kamanta shi. Nagari yana da ƙ wazo da ƙ o ƙ arin baza alheri (ga kowa) gwargwadon iko, saboda lafiyar zuciyarsa da ta jikinsa. A kusan kullum, nagari; mutum ne mai kuzari da kazar-kazar da yawan walwala da raha da barkwanci da fara’a da ɗ imbin jimirin aiki da ƙ wazo wajen biyan bukatun alheri da ya sa gaba. Muhammad, (1997) ya ce, nagari gwani ne a fagen rayuwarsa kuma yana da fasaha da haza ƙ a a ɗ abi’unsa da ayyukansa, ga shi da zurfin tunani da hangen nesa kuma yana da naci da sanin ya kamata da kishin al’ummarsa da na ƙ altar harshe. Muhammad ya ce, natsuwa da ladabi suna cikin sifofin mutum nagari. Muhammad ya na ɗ e da cewa, halin mutumin kirki, jigo ne wajen gina gari da al’umma, da halin mutum nagari ake gina al’umma, ta kafu, rayuwa ta ɗ ore a kan gaskiya da aminci.

Nagari shi ne mutumin kirki, mai nagarta wanda ya san mutunci da karamci da kusan duk wani abu mai kyau a rayuwa. Mutumin kirki yana da na ƙ altar yadda ake sarrafa nagarta domin ɗ orewar aminci a zamantakewa. Duk da ba manufa da muradin wannan ma ƙ ala ce a yi nazari a kan mutumin kirki ko nagari ba, amma ma ƙ alar tana da muradin yin nazari a kan godiya, wadda ta kasance ɗ aya daga cikin ɗ abi’un mutanen kirki.

6.1 Godiya ga Allah

Godiya ɗ abi’a ce mai kyau, mafalsafa da suka yi tsokaci a kan kyautayi sun bayyana ɗ abi’a nau’i ce ta falsafa a aiwace, ita ce takan yi wa mutum jagora ya gane abin da ya dace da dalilin da ya sa ya kamata a yi wannan ɗ abi’a (mai kyau). Kyawon ɗ abi’a a hangen mafalsafa yakan yi wa mutum ƙ aimi, ya iya kiyaye doka sau-da- ƙ afa. Da nagarta mutum yakan jagoranci rayuwarsa ta yau da kullum. Mafalsafa kyautayi sun ƙ arfafa magana a kan cewa kusan duk wani ra’in nagarta yana da wa ɗ ansu sharu ɗɗ a da suke zama abin koyi ga mutum saboda ya tsira da mutuncinsa, kusan a kodayaushe (Bennett, 2011:57). Tarihin Aliyu Nata yana cike da kyautayi saboda irin tarbiyya da ya samu a hannun mahaifansa da malamansa. Domin burin kusan ɗ aukacin iyaye ne a Hausa, ɗ iyansu su zama mutanen kirki su san abu mai kyau; su ri ƙ e shi, su san illar mugun abu; su guje shi. Hausawa sukan cusa ɗ abi’un kirki a gida da waje , shi ya sa sukan ce : Ɗ a na kowa ne.” Kusan har yanzu wannan al’ada ba ta mutu ba duk da rauni n da tarbiyya take fuskanta saboda halin yau.

Godiya a wurin Bahaushe tana ci gaba da wanzuwa a duk lokacin da wani ya taimaki wani ko kuma wani ya yi abin alheri kamar yadda godiyar ta kasance fitacciyar ɗ abi’ar Aliyu Nata da yadda ya cusa ta a wa ƙ ar “Na Gode”. Yawan ambaton “Na gode” a rayuwar Aliyu Nata yana da nasaba da ganin girma da kuma kimanta abin alheri komai girmansa ko ƙ an ƙ antarsa a rayuwa. Wa ƙ ar “Na Gode” ta fito da kalaman godiya a bakin Aliyu Nata, musamman yadda Hausawa sukan yaba alherin da aka yi musu ko kuma sukan girmama wata baiwa da Allah ya yi musu. Turken wa ƙ ar “Na Gode” ya na ɗ e tunani n Hausawa game da godiya ga Allah da cewa:

Turke: Lallai biki bidiri haka nan take na ga taron al’umma,

: Ashe ina da rabon na ga ranar nan da za a yi mun murna,

: Alhamdu lillahi, Allah kai mini jamma’a haka na gode!

 

Turke na wa ƙ ar “Na Gode” ya na ɗ e cikakkiyar godiya da girmamawa ga Allah saboda da ɗ in da mawa ƙ in yake ji a zuciyarsu, sai ya furta “Alhamdu lillahi, Alla kai mini jamma’a haka na gode!” Batun nasa yana cike da yarda ga Allah da nuna tsantsar soyayyarsa ga mahaliccinsa da jin babu wata magana da ta dace ta fito daga bakinsa sai godiya ga Allah saboda kalmar tana da sau ƙ in fa ɗ i da kuma da ɗ in ambato a daidai lokacin da yake murnar aurensa. Tunanin da yake ƙ unshe a zuciyar mawa ƙ in yana yin yabo ga Allah da godiya a gare shi da nuna yarda da cancantar Allah ne abin godiya. Kalaman mawa ƙ in suna nuna irin yadda ya mi ƙ a wuyansa ga Allah, ya nuna sakankancewarsa da babu wani wanda ya cancanci a gode masa sai Allah. Batutuwan mawa ƙ in suna fitowa ne daga zuciya zuwa ga Allah da ya yi masa ni’imomi, a wannan ga ɓ ar ya cika masa burinsa na yin aure. Har ila yau, Aliyu Nata yana godiya ga Allah ne da fatan ya ninka ni’imar da ya ba shi. Wa ƙ ar “Na Gode” ita ce hanyar da Aliyu Nata ya bi ya yi wa Allah godiya a zuci da bayyane. Abu na biyu da mawa ƙ in yake ƙ ara girmama Allah cikin godiya shi ne irin taron jama’a da (Allah) ya ha ɗ a masa a wurin ɗ aurin aurensa, musamman inda yake cewa:

Jagora: Idan Allah ya ma arzikin jama’a sai ka ga warraka,

Yarinya: Ya gode!

Jagora: Na gode wa Rabbu da yai mini al’umma na ɗ aukaka,

Yarinya: Mun gode.

Jagora: Jama’a suka taru gun aurena sai hidimar ta haskaka,

Yarinya: Nata ya gode!

Jagora: Babu abin da zan iya ce muku sai dai um fa ɗ a muku na gode!

 

Ɗ an wa ƙ a na sama ya da ɗ a fito da godiyar Allah da mawa ƙ in yake ta yi saboda taron jama’a a wurin aurensa, wanda ni’ima ce cikin ni’imomin Allah kuma godiya ga mutanen wani ɓ angare ne na godiyar Allah. Tarbiyyar mawa ƙ in ce take haska masa rayuwa kuma take da ɗ a yi masa ƙ aimi ya gode wa Allah domin shi ne silar duk wata ɗ aukaka da ya samu na ƙ aruwar aure da kuma jama’a da suka yi masa karamci. Idan aka lura da kyau, godiyar ta biyo bayan karamci da ya samu a wurin Allah da kuma karamci na mutane duka suna da ala ƙ a da abin da ya shu ɗ e da kuma da ɗ in rai da mawa ƙ in yake ji na abin alheri da ya same shi da kuma yadda mutane suka ba shi goyon baya da taimako a halin da yake godewa. Aliyu Nata ya ci gaba da bayyana dalilai da suka faranta masa rai a lokacin aurensa. ‘Yar amshin Aliyu Nata ta bi sawunsa a fagen godiyar Allah da ya cika masa (Aliyu Nata) dogon gurinsa kamar yadda take cewa:

Yarinya: Alhamdu lillahi an ɗ aura ta zamma matarka,

Jagora: Na gode!

Yarinya: Gurinka ya cika sanya ruwa ƙ asa, sha da bakinka,

Ki ɗ a

: Kullum kana ta batun aure yau ka ga ranarka,

Jagora: Na gode!

Yarinya: Ku rayu tare da Zainabu Abu ta zamma matarka

Jagora: Na gode!

Yarinya: Nata banna zai yi jiki, ya yi ɓ ul ɓ ul kuma yai hasken fata.

 

Yayin da ‘yar amshi take taya mawa ƙ in godiya ga Allah, sai ya tsaya a gurbin ɗ an amshi yana maimaita “Na gode” kamar yadda ‘yar amshi ta yawaita maimaita ‘Ya gode da Mun gode da Nata ya gode da sauransu a cikin wa ƙ ar baki ɗ aya. Kusan babu wata kalma da mawa ƙ in zai fa ɗ a face wa ɗ annan kalmomi na godiya da ya yi ta fa ɗ insu, tare da ‘yar amshinsa. Yin hakan yana yin nuni da dogaro ga Allah a kowane yanayi da mi ƙ a masa wuya a kodayaushe, musamman a yanayin auren da aka ɗ aura masa da irin farin ciki da jin da ɗ i da suke tattare da shi da kuma mutanen da Allah ya tara masa.  

6.1.1 Lokacin Godiya

Jama’a ta ha ɗ u a lokacin auren Aliyu Nata kamar yadda wa ɗ ansu ɗ iyan wa ƙ ar suka nuna haka, kuma mawa ƙ in ya bayyana wa wannan bincike ya rera wa ƙ ar “Na Gode” mako ɗ aya bayan an ɗ aura masa aure. Lokacin auren Aliyu Nata muhimmi ne a rayuwarsa kuma abin tunawa a rayuwarsa , musamman da yake auren fari ne. Godiyar mawa ƙ in ga Allah da shau ƙ in abin da ya auku a wannan rana kusan abin a-zo-a-gani ne a tarihin wannan ango, wannan ya sa zuciyarsa ta tuna, cikin murnar abin da ɗ imbin jama’a ta yi masa musamman wa ɗ anda suka halarci ɗ aurin aure. Mawa ƙ in ya shaida wa duniya irin yabon da yake yi wa mutane cikin murna da farin ciki kamar haka:

 

Jagora: E, wa ƙ ar ta ban gajiya ce, zan muku um fa ɗ a muku,

Yarinya: Ya gode!

: Abin da duk kuka yi mini tilas in yaba muku,

Yarinya: Mun gode.

Jagora: Allahu Sarki ya nuna mun ranar da zan muku,

Yarinya: Nata ya gode.

Jagora: Irin dubun hidimar da kukai mini mai yawa haka na gode!

 

Ɗ an wa ƙ a na sama da mai bi masa a ƙ asa suna maganar godiya kuma suna lura da lokaci, duka ɗ iyan sun shafi shu ɗ a ɗɗ en lokaci; ɗ an wa ƙ a na sama yana zance a kan ranar auren Aliyu Nata bayan cikar burin mawa ƙ in kuma yana tuna irin ɗ imbin alherin da jama’arsa ta yi masa. Ɗ a na ƙ asa kuma yana cewa:

Jagora: E, Alhamdu lillahi, mun yi kira an amshi gayyarmu,

Yarinya: Ya gode!

Jagora: Ku malmatso, ku ji yadda akai taro na aurenmu,

Yarinya: Mun gode!

Jagora: Wurin bukin muka gane irin dubban mutanenmu,

Yarinya: Nata ya gode!

Jagora: A gurin shiga da fita duk inda mukay yi hanyar ta da ɗ e!

 

A nan, mawa ƙ in yana tuna lokacin da aka gayyaci jama’a ne a ɗ a na saman wannan kuma batun ranar biki da karamcin da kowa ya nuna masa duk sun faranta zuciyarsa. Lokacin godiyar ya dace da sa ƙ on da mawa ƙ in yake magana kuma abu ne da mafalsafa kan nagarta suke dubansa yana da ala ƙ a da irin ƙ aunar da zuciya take yi wa nagarta da yadda zuciyar take bayanin ƙ aunar da kowa ya gwada wa nagarta da tasirinta ta fuskoki daban-daban ko kuma irin alherin da ya gudana a wani lokaci na musamman saboda farin cikin wani. Ba nagarta ce ka ɗ ai hankalin mutumin kiriki ya fi so ba, yakan fi duban ala ƙ arsa da rayuwa da yadda zai ri ƙ i halin kirki kuma ya aiwatar a duk lokacin da yake gogayya da jama’a (Bennett, 2011 shf. 74).

6.1.2 Sosuwar Zuciya a Godiya

Aure ya ɗ arsu a zuciyar Aliyu Nata, hakan na daga cikin dalilin yin wa ƙ ar “Aure Martaba” bakandamiyar mawa ƙ in, mai ƙ unshe da sosuwar zuciya a kan aure ta fuskoki mabambanta. Sosuwar zuciyar Aliyu Nata a kan aure ba ta rasa nasaba da horon da addini ya yi na a yi auren da ilmin da mawa ƙ in yake da shi a kan auren da kuma halin da yawa-yawan matasa ke tsintar kansu saboda ƙ alubalen da yake yi wa wa ɗ ansu daga cikin matasan ƙ arni na ashirin da ɗ aya kamar yadda matsalar take a ƙ arnukan da suka shu ɗ e. Masu nazarin ƙ awa (nci) a adabi sun tofa albarkacin bakinsu a kan sosuwar zuciya, musamman Richards (2001 shf. 83 da 89) inda yake ganin akwai nasaba tsakanin sosuwar zuciya da lura, wato yadda jiki yakan kiyaye faruwar wani abu da kan iya haifar da tsoro ko damuwa ko murna da ɓ acin rai da sauran sabubba da sukan sosa zuciya dindindi ko kuma na wucin gadi. Yanayin mutum yakan canja idan zuciyarsa ta sosa. Idan abu ya ɗ arsu a zuciyar mutum yakan ji a jikinsa, hotancinsa yakan bayyana yayin da yanayin murna ko damuwa sukan bayyana a ɗ abi’un mutum. Shiga yanayi na murna ko akasinta jakadu ne da ke nuna wani abu yana faruwa g a mutum.

Graham (2004 shf. 31 da 32) ya ce, sosuwar zuciya fitaccen al’amari ne a kowace ƙ ir ƙ ira ta fasaha domin mai karatu ko saurare ko mai gani yakan ji tasirin abin da ya ɗ arsu a zuciyar fasihi ne daga fasahar fasihi. Idan marari shi ne yake fito da kimar fasaha, to lallai kam bayyana sosuwar zuciya na fito da yanayin kimar fasaha. Har ila yau, sosuwar zuciya ta sabbaba wa Shakespeare da Haydn da Leonardo da Christopher Wren da sauran fasihai suka yi ƙ ir ƙ ira daidai da fasaharsu. Aliyu Nata bai kauce wa sosuwar zuciya ba musamman a wa ƙ arsa ta “Na Gode”, inda abubuwa dadan-daban suka ɗ arsu a zuciyarsa musamman idan aka yi nazarin wannan ɗ an wa ƙ a da yake cewa:

Jagora: E, lallai ba ka gane masoyi sai hidimarka ta zaka,

Yarinya: Ya gode!

Jagora: Nan za ka rarrabe wanda suke burin su yi maka,

Yarinya: Mun gode!

Jagora: Ko da a ce ka fi ƙ arfin ko ma mi akai maka,

Yarinya: Nata ya gode!

Jagora: Gudummuwar hidima mai da ɗ i al’umata na gode!

 

Ɗ an wa ƙ a na sama yana cike da jin da ɗ in Aliyu Nata, a kan gudummuwar da masoyansa suka ba shi a lokacin aurensa, wannan gudummuwa ta sa shi farin cikin da ba ya misaltuwa, idan aka yi duba da kalmomin da ya furta a ciki har da godiya. Yawaita yin godiyar kanta, abu ne da ke nuna zuciyarsa ta sosu saboda al’amura daban-daban da suka ƙ unshi son yin auren da fa’idar yin auren da samun matar auren da goyon bayan mutane da ya samu da sauransu. Sosuwar zuciyar mawa ƙ in ta sanya shi ya ɗ ungume duk wata gudummuwa da ƙ auna da dangi da abokai da masoyansa na cikin Katsina suka nuna masa da cewa:

Jagora:  E, a ɓ angare na tsatsona Kattsina na ga al’uma,

Yarinya: Ya gode!

Jagora: Abokanai da masoyana duka akka ɗ unguma,

Yarinya: Mun gode!

Jagora: Rana ta ɗ aurin aure duk mun ɗ auki harrama,

Yarinya: Nata ya gode!

Jagora: Ba ƙ i da duk ‘yan gari tun kan ya zuwanmu titin ya da ɗ e!

Susuwar zuciyar mawa ƙ in na ƙ unshe da hotancin zucinsa na taron jama’a da suka ha ɗ u a wurin ɗ aurin auren nasa da yadda aka ɗ unguma zuwa wurin ɗ aurin aurensa ba ƙ i da ‘yangari. Ɗ a da yake tafe ya ci gaba da nuna hotancin zucin mawa ƙ in ha ɗ e da sosuwar zuciyarsa kamar haka:

Jagora: E, da zuwanmu kowa ya tunkaro murna yake mini,

Yarinya: Ya gode!

Jagora: Kai ku ji har da mata wurin su ma barka suke mini,

Yarinya: Mun gode!

Jagora: Duk inda nai jama’a ne sai fara’a suke mini,

Yarinya: Nata ya gode!

Jagora: Dan da nan ido ya cika da hawayena na murna na ru ɗ e!

 

Kusan babban abin da ya sosa zuciyar Aliyu Nata a wannan ɗ an wa ƙ a ya ha ɗ a da ganin mata a wurin ɗ aurin auren da yadda kowa yake zuwa wurinsa; ana yi masa murna da barka cikin fara’a da nuna jin da ɗ i. Yanayin da mawa ƙ in ya tsinci kansa na al’ajabi, tunaninsa ya fa ɗ a ɗ a, farin cikinsa ya kai matu ƙ a, mamaki ya kama shi saboda shau ƙ in komai na wannan rana. Ɗ an yana cike da batutuwa na godiya ta kowace fuska, inda a ƙ arshe kalma ta ƙ are wa Aliyu Nata sai hawaye na godiya ga Allah ke gudana. Yanayin sosuwar zuciyar mawa ƙ in ya sanya shi ya fito da hotancin zucinsa na al’amuran da suka faru da shi a lokacin aurensa, a cikin mamaki ya ri ƙ a cewa:

Jagora: Ashe ina da mutane manya da yara ƙ an ƙ ana,

Yarinya: Ya gode!

Jagora: Daga ran Fulani zuwa ƙ wallo aka je akai diner,

Yarinya: Mun gode!

Jagora: Ga jaruman Hausa Film da mawa ƙ a dole in tuna,

Yarinya: Nata ya gode!

Jagora: Muna ta facing da Mummy Gombe cikin gilashi ta da ɗ e.

 

Zuciyar Aliyu Nata ta sosu matu ƙ a a ranar ɗ aurin aurensa da kuma sauran al’amura da suka gudana a lokacin auren. Wannan ya sanya ya yi mamakin ganin tarin jama’a da bai yi zaton ganinsu ba , yara da manya a wurin dina da ƙ wallo da kuma ranar Filani. Yayin da Aliyu Nata yake mamaki, ‘yar amshi tana ta jaddada godiyarsa ga mutane. Har ila yau, mawa ƙ in ya ambato ka ɗ an daga cikin gogayen fim na Hausa da mawa ƙ an Hausa na zamani da suka ƙ awata bikinsa kamar yadda ɗ angon ƙ arshe a ɗ a na sama ya soma ambaton ɗ aya daga cikinsu. Da ɗ in da ɗ awa, Aliyu Nata ya ambato sunan Abdul Amart da Hamis Breaker da Ado Gwanja da Sadik Mafia da Sadik Sani Sadik da Ari Baba da Jamilu Roja da Alfazazi da Fresh Emir da Ali Haidar da Abdulsamad Horo da Mahmud Abnur Dabadaba da Sarki Audu Boda da Ali Show da Malam Carki da Sadi ƙ u artist da Kamakazi da Umar da Shehu Jaha da Teema Yola da Mummy Gombe da Maryam da Minal Ahmad da Zainab Zee Hanan da Khadija Daddy Hikima duk sun halarci dinar aurensa. Godiya cikin sosuwar zuciya ba ta ƙ are a wa ƙ ar “Na Gode” ta Aliyu Nata ba har sai da ya dangana da bayyana walimar da aka yi, kwana ɗ aya bayan an ɗ aura masa aure da matarsa inda yake cewa:

Jagora: An ɗ aura aure a washegari muka shirya wallima,

Yarinya: Ya gode!

Jagora: Wani hall da ke Dutcin Safe ya ɗ auki al’umma,

Yarinya: Mun gode!

Jagora: Mata, maza cincirindo yadda ka san ruwan sama,

Yarinya: Nata ya gode!

Jagora: Ina ta so mu fita ko a mota ba space ɗ in da zan bu ɗ e.

 

Wannan ɗ a yana ɗ auke da hotancin zucin mawa ƙ in game da yanayin ɗ akin taron da aka yi walima, inda ɗ an yake nuna wurin ya cika ma ƙ il da mutane maza da mata. Hakan ya sosa zuciyar Aliyu Nata, musamman yadda ya ƙ osa ya fita daga cikin mota domin su jera da amaryarsa amma mutane sun cike wurin babu hali. Kusan a wannan yanayi ba murna ce ka ɗ ai a zuciyar mawa ƙ in ba, domin akwai gajiya da ƙ osawa su tafi su zauna amma ana dakatar da su saboda ana ƙ o ƙ arin tsara komai yadda zai yi kyau, wa ɗ ansu kuma suna dama al’amari a ƙ o ƙ arin su faranta masa rai. Biki ya gaji haka, kuma ba wani abu ya jawo sosuwar zuciya ba a wannan ga ɓ a sai shau ƙ in yin auren da yake cikin zuciyar Aliyu Nata da kusan duk wani abu da ya biyo baya, tun daga gayyata har zuwa ranar ɗ aurin aure da kuma yin taron walima. Kusan a lokacin da mawa ƙ in ya gudanar da wa ƙ ar yana cike da sosuwar zuciyar abin da aure ya haifar masa, idan aka yi la’akari da ɗ iyan wa ƙ ar duka. Tarbiyyar Aliyu Nata ita ce jagora wajen yin godiya da yabo ga duk wanda ya haskaka aurensa, tare da fatan idan ya sami dama zai ci gaba da baza alheri a tsakaninsa da mutane, ita ce godiyar da zai yi musu.

7.1 Na ɗ ewa

Wa ƙ ar “Na Gode”, wa ƙ a ce ta godiya da ban gajiya da Aliyu Nata ya wallafa. Ma ƙ alar ta yi nazarin godiyar Allah da mawa ƙ in ya yi, a wani gefen, ma ƙ alar ta tarke nasabar lokaci da godiya da kuma yadda sosuwar zuciyar mawa ƙ in ta yi tasiri lokacin da godiya take gudana a cikin wa ƙ ar “Na Gode”. Ma ƙ alar ta gano tasirin da tarbiyya take da ita ga mutum kamar yadda son nagarta da halin kirki suka sanya mawa ƙ in ya gode wa Allah a sakamakon ni’imar da ya yi masa. Binciken ya gano tasirin da shu ɗ a ɗɗ en lokaci yake da shi da na lokaci mai ci da lokaci mai zuwa , inda mawa ƙ in ya nuna sun yi gayya an amsa da kuma burin ri ƙ e zumunci domin nuna godiya mara yankewa tsakaninsa da jama’arsa. A dun ƙ ule, ma ƙ alar ta gano tasirin kusan duk abin da ya shafi rayuwar mawa ƙ in a sosuwar zuciyarsa da yadda hakan ya haifar da hotancin zucin mawa ƙ in yayin da yake yin godiya a wa ƙ ar “Na Gode”. Har ila yau, yin godiya ko fa ɗ in “Na gode” a Hausa na nufin idan mutum ya sami dama zai yi fiye da alherin da aka yi masa kamar yadda Aliyu Nata ya taskace haka a wa ƙ ar “Na Gode”.   

Manazarta

Abdul ƙ adir, Ɗ . (1975). The Role of An Oral Singer In Hausa/Fulani Society: A Case Study Of Mamman Shata. Unpublished Ph.D. Thesis. Indiana: Folklore Institute, Indiana University.

Abraham, R. C. (1978). Dictionary of the Hausa Language 4th Edition. London: Hodder and Stoughton Ltd.

Al-Hilali et al (Ed.). (1996). Interpretation of the Meaning of The Noble Ƙ ur’an In English Language: A Summarized Version of Al-Tabari, Al- Ƙ utubi, and Ibn Kathir with Commentary from Sahih Al-Bukhari Summarized in One Volume. Riyadh, Saudi Arabia: Darussalam Publishers and Distributors.

Bargery, G. P. (1993). A Hausa – English Dictionary and English – Hausa Vocabulary 2nd Edition. Zaria: Ahamdu Bello University Press Limited.

Bennett, F. J. (2011). The Virtuoso Human: A Virtue Ethics Based on Care. Unpublished M. A. Desssertation. Florida: Department of Philosophy, University of South Florida.

 

CNHN (2006). Ƙ amusun Hausa , Zaria: Ahmadu Bello University Press.

Graham, G. (2005). Philosophy of the Arts: An Introduction to Aesthetics Third Edition. New York: Routledge.

King, A.V. (1980). Chorus Form and Function in Hausa Professional Songs. Zaria: Department of Nigerian and African Languages, Ahmadu Bello University.

Kirk-Greene, A. H. M. (1973). Mutumin Kirki: The Concept of Good Man in Hausa. (Hans Wolf Memorial Lecture) Bloomington Indian. African Studies Program.

Muhammad D. (1997). Nagari Na Kowa: Nazarin Tunanin Hausawa da Adabinsu. Laccar Tunawa da Marigayi Farfesa Ibrahim Yaro Yahya.

Muhammed, D. (1990). (Ed.) Hausa Metalanguage Vol. 1. Ibadan: University Press Limited.

Newman, R. M. (1997). An English-Hausa Dictionary. Zaria: Longman Nigeria PLC

Richards, I. A.  (2001). Principles of Literary Criticism. New York: Routledge and Kegan Paul.

Post a Comment

0 Comments