Table of Contents
- Tsakure
- Gabatarwa
-
Shimfi
ɗ
a
- Dabbobin Ƙ asar Hausa a Falsafar Adabin Hausa
- Kura
- Fasalin Kayan Aiki
- Kura a Farfajiyar Nahawu
- Karin Magana d a Zantukan Azanci
- Kura a Farfajiyar Tatsuniya
- Wasannin Yara
- Kura a Addinan Gargajiya
- Labaran Gargajiya, Tarihi da Tarihihi
- Ɗ antauri da Kura
- Ke Kura Sake Dabara na Buwaya
- Kura Cikin Adabin Wa ƙ a
- Kura a Fagen Magani da Warkarwa
- Tsaro
- Sakamakon Bincike
-
Na
ɗ
ewa
- Manazarta
Citation: Bunza, A.M. (2024). Kura Ga Tsoro Ga Ban Tsoro: Yunƙurin Taskace Gudunmuwar Kura Cikin Bahaushen Adabi. Tasambo Journal of Language, Literature, and Culture, 3(1), 191-204. www.doi.org/10.36349/tjllc.2024.v03i01.022.
Kura Ga
Tsoro Ga Ban Tsoro
:
Yun
ƙ
urin Taskace
Gudunmuwar Kura Cikin Bahaushen Adabi
Daga
Aliyu
Muhammadu Bunza
Sashen Koyar
da Harsunan Nijeriya
Jami’ar
Usmanu Danfodiyo, Sakkwato
Tsakure
Adabin baka wani babban kundin tarihi ne, da kowane irin tarihi sai ya dafi kafa ɗ arsa za a ga zatin tsawonsa. Tunanin wannan ɗ an bincike, taskace gudunmuwar dabbobin ƙ asar Hausa ga ha ɓ aka Bahaushe n Adabi. Binciken ya za ɓ i kura a matsayin karan gwajin dahi. An tattaro kayan aikin bincike guda tamanin da uku (83) da aka samo cikin kundayen bincike, wallafaffun ayyuka, hira, da tattaunawa, da rangadi, ta ga-ni-ga-ka, da ta waya, da hanyoyin sadarwa na WASAP da TES, da Yanar Gizo. Bayan tsettsefe bayanai aka ɗ ora takardar a kan fasula (20) da suka ha ɗ a da gabatarwa da na ɗ ewa. An tsara kayan aikin da aka tattaro cikin rukuni tara (9). Rukunin nahawu an samu misalai (6), karin magana (20), tatsuniya (1), wasan yara (1), tarihi da tarihihi (6) labaran gargjaiya (3), an kuma gayyato mawa ƙ an baka (8) da aka sarrafa ɗ iyan wa ƙ o ƙ in su (14). An tattaro sassan magungunan gargjaiya (4), da dabarun tsaro na gargjaiya (4), duk masu ala ƙ a da gudunmuwar kura a adabinmu. An gwada tsawon kura da dabbobi (18) na gida da daji a falsafar adabin baka n Bahaushe. Wa ɗ annan kayan aiki (83) su suka ba mu damar yanke hukuncin cewa, lallai adabin baka ƙ ololuwar falsafar al’umma ce, da sai da shi, za a iya fahintarsu, da ƙ yallaro tunnaninsu. Binciken ya tabbatar da; daga cikin dabbobin ƙ asar Hausa, babu wadda tasirin ta ya yi zara cikin Bahaushen Adabi kamar kura. Ɗ abi’un kura munana sun rinjayi kyawawansu a duniyar adabin Bahaushe. A ƙ arshe, binciken ya zartar da hukuncin na ɗ a wa kura raw a nin sarautar TAURARUWAR BAHAUSHEN ADABI. Ta tabbata matsoraciya ce, amma ban tsoronta ya fi tsoronta yawa. Tunanin Bahaushe a kan hanya yake: “Kura ga tsoro ga ban tsoro”.
Gabatarwa
Dabbobi, da tsuntsaye, da
ƙ
wari, da
kifaye, da iskoki, da ke shawagi a farfajiyar tuddai, da rafuka, da tsaunuka,
da kogunan farfajiyar
ƙ
asar Hausa, sun yi naso matu
ƙ
a a rayuwar
Hausawa. A tarihin mazauna bangon duniyar mutane kowace al’umma tana da nason
ire-iren su a adabi da al’adunta. Farfajiyar
ƙ
asar Hausa
ta yi kusan a kira ta ga
n
dun dabbobi,
domin babu irin nau’in dabbar da babu ita a ciki. A sararin subhananta, da
lemomin bisshiyoyinta, babu nau’in tsuntsaye, da
ƙ
wari, da
babu a ciki, sai dai wa
ɗ
anda
zuriyarsu ta
ƙ
are
[1]
. To,
halittun da muke shawagi a doron
ƙ
asa da su, yadda muke kallonsu, su ma haka suke
kallonmu, sai dai bakin magana muka fi su
[2]
. Don haka,
tunanin wannan bincike shi ne, za
ɓ
o
ɗ
aya daga
cikin shahararrun dabbobin
ƙ
asar Hausa, mai fairn jini, da tagomashi cikin karatun
adabi, a
ɗ
ora ta a
ma’aunin adabi, a ga irin nauyinta. A nawa
ɗ
an bincike,
kura ta fi cancanta da wannan, saboda a cikin karatun adabi, ta zama ko’ina da
ruwanki.
Shimfi
ɗ
a
Daga cikin
dabbobin gida, da daji na
ƙ
asar Hausa, kura ka
ɗ
ai ce ke da
wannan kirari, na ga ta
na
da mugun
tsoro; ga ta kuma da ba da mugun tsoro. Ta shahara wajen razana buwayayyi, ita
kuma an sha razana ta, fiye da yadda
t
ake razana
mazaje. Kura ta samu wani babban gurbi cikin adabin Hausa, da babu wata babbar
dabba daga cikin dabbobin
ƙ
asar Hausa da zai gwada tsawo da ita. A kowane
ɓ
angare na
adabi; in aka ratso da ruhinta, ko hotonta, za a ga, kamar babu wata dabba a
farfajiyar karkarar
ƙ
asar Hausa in ba kura ba. Burin binciken ya fito da
yadda hotonta ke hana a
ɗ
auki hoton
kowace dabba da kyau, cikin Bahaushen adabi. Dalili kuwa shi ne, kura ta yi
kane
-
kane cikin
nahawun Hausa,
[3]
tana da
babbar gona cikin adabin baka da rubutacce
[4]
, kuma ta
mamaye wasu sassa na al’ada, kamar domin ita aka yi su. Ban ce, sauran
dabbobimu ba su da babban gurbi ba, amma idan aka kwatanta gurbinsu, da na kura
cikin adabinmu, dole a ce, ko ba a gwada ba linzami ya fi
ƙ
arfin
bakin
kaza.
Dabbobin Ƙ asar Hausa a Falsafar Adabin Hausa
Halittun da Bahaushe ya yi
tarayyar zama da su a bangon duniya ya kasa su kashi biyu a al’adance:
1.
Halittun Gida: wa
ɗ
anda yake
hul
ɗ
a da su, da
kiyon su, da sarrafa su.
2.
Halittun Daji: Wa
ɗ
anda ke
zaune dawa, sai hul
ɗ
ar farauta,
da ta girshi.
Dukkaninsu ba kallon tsoro
Bahaushe ke yi musu ba, ya tsaya ya karance su sosai, ya yi musu littafin kansu
cikin adabinsa. Hukunce-hukuncen da Bahaushe ya yi wa dabbobi, da
ƙ
wari, da
tsuntsaye, su yake kwatantawa da mutanen da yake hul
ɗ
a da su,
dangane da irin halayyarsu. Ga wani shafi daga cikin littafan adabi da halayyar
dabbobi:
Sunan Dabba |
Bagire |
Ɗ
abi’unta |
Falsafarta |
Rago |
Dabi/
ɗ
aki |
Kunya da nagarta |
Ba ka gardama, ba ka musu |
Akuya |
Dabi/
ɗ
aki |
Raki da tsoro |
Kyalla mai gajeren bindi |
Sa |
Waje |
Ƙ
eta da
ƙ
arfin hali |
Ba ka dariya sai tuni
(tunkuri) |
Ra
ƙ
umi |
Waje |
Wauta da raki |
Afalala kan dabbobi |
Jaki |
Waje |
Nagarta da taurin kai |
Wurin wuya a ja ku a kai ku |
Doki |
Dabi/waje |
Ƙ
arfi da
ƙ
wazo |
Ga
ƙ
arfi ga
iko |
Alfadari |
Waje |
Nagarta da juriya |
Dokin fatake |
Giwa |
Waje |
Ƙ
asaita da
juriya |
Bukkar daji |
Zaki |
Waje |
Ƙ
asaita da
himma |
Mai
ƙ
ashi guda
don
ƙ
arfi |
Biri |
Saman/itace |
Wayo da dabara |
Ya yi kama da mutum |
Gwanki |
Rami |
Ƙ
arfi da fa
ɗ
a |
Dabugi hura
ƙ
asa |
Karkandai |
Waje |
Ƙ
arfi da
gwagwarmaya |
Mai wawan kora |
Cirza |
Waje |
Fa
ɗ
a kawai |
Ba a kallonka kana kallo |
K
a
ren
ɓ
uki |
Rami |
Wayo da fargaba |
Malamin dawa |
Kura |
Rami |
Wauta da kwa
ɗ
ayi |
Ga tsoro ga ban tsoro |
Damisa |
Kogo |
Kwarjini da fa
ɗ
a |
Ba a damisa biyu a fage |
Kada |
Cikin ruwa/tudu |
Shiru-shiru |
Ha
ɗ
e ka koma
gurbi |
Dorina |
Cikin ruwa |
Fa
ɗ
a da hushi |
Dodo cikin ruwa |
Ke nan,
dabbobin da ke kusa da Bahaushe wa
ɗ
anda yake
mallaka, da wa
ɗ
anda suke
nesa da juna; duk ya karance su sosai.
Kura
Za
ɓ
en kura daga
cikin dabbobin
ƙ
asar Hausa domin a
ɗ
an nazarci
yadda Bahaushe ya taskace ta cikin adabinsa ba da gangan aka yi shi ba, an yi
shi bisa cancantar kura, da ficen ta
a
ƙ
asar Hausa,
da tagomashinta a farfajiyar adabin Hausa. Kura na daga cikin manyan dabbobin
dawa na
ƙ
asar Hausa. Dabba ce da ta
ɗ
ara akuya
tsayi, da fa
ɗ
i, amma ba
ta kai zaki cira sama, da
ɗ
aukaka da
ƙ
warjini ba.
Kwankwasonta ya yi
ƙ
asa-
ƙ
asa, gaban nata ya
ɗ
an zabura ka
ɗ
an. Tana da
dabban baki, da
ƙ
aton kai, bisa ga riwayar karin maganan, “ko da ganin
kan kura ya ci mutum”. Bakin
ta
a koyaushe
a bu
ɗ
e yake, sale
ɓ
a na tarara,
jiran
ɗ
anye,
gaskiyar Bahaushe da ke cewa, ka gode wa Allah ko da kana ga bakin kura. Sanin
cewa, duk abin da ya shiga bakinta ma
ƙ
ogoro zai
haura, don haka ake godiya ga Allah, gabanin a yi shahada.
A
launin
fatarta akwai ba
ƙ
a-ba
ƙ
a, akwai kuma mai tamburan ba
ƙ
i-ba
ƙ
i ko’ina a
jiki, akwai fara fes. Mai tambur
a
n ba
ƙ
i-ba
ƙ
i ta fi shawagi
a karkarar
ƙ
asar Hausa, ita Bahaushe ya fi sha
ƙ
uwa da ita.
Farar kuwa ta
ƙ
aranta
ƙ
warai, da wuya a gan ta a karkara, sai dai a dokar daji,
saboda tsoron mutane da take shi ya sa Bahaushe ke da azancin zance, wai, shi,
“tsoro kamar farar kura”.
Ɗ
abi’un Kura
A wajen
Bahaushe, kura na daga cikin manyan dabbobin dawa masu cutarwa. Na farko dai,
abincinta nama
ɗ
anye, da
wuya ta ci ru
ɓ
a
ɓɓ
en nama bale
busasshe. Ga al’ada, ba ta da kama jiki da kiza-kiza irin na zaki, da damisa,
don haka, ba ta cika kashe wa kanta nama mai gamsar da ita ba.
Ƙ
ananan
ƙ
wari/namu
irin su maciji cutar da ita yake yi, gafiya ta fi ta gudu, ma
ƙ
aya ba ta farautuwa
gare ta, biri ya fi ta wayo, ba ta iya sama ba. Damisa kuwa wane mutum! In ji
mutuwa. Wa
ɗ
annan
dalilai su ke sa kura ta matsa wa dabbobin gida na Bahaushe, musamman awaki, da
tumaki, da jakai, da karnai, da mutane su kansu
[5]
. Manyan
dabobin gida irin su ra
ƙ
umi, da doki, sai dai yunwa ta kashe ta, ko kusa ba ta
fara taya su
[6]
. Kare ko ba
su yi arba ba ya gan ta, shi ya tashi aiki. Tsananin fargaba
r
da yake na kura, shi ya haifar da karin maganan, sai
dai kare ya mutu da haushin kura. Tattare da wa
ɗ
annan
martabobi, da kuzari na kura, Bahaushe ya shaide ta da tsoro, da kwa
ɗ
ayi, da
rashin kama jiki, da rashin gaskiya, da zalunci, ga wauta, da rashin iya magana
a duniyar tatsuniya, domin har tsamin baki take yi a riwayoyin tatsuniya.
Fasalin Kayan Aiki
Ban ce, wannan
shi ne bincike na farko a kan dabbobin
ƙ
asar Hausa
ba, musamman kura. Duk da haka, a iya
ɗ
an bincikena ban ci karo da binciken da ya
ɗ
ora kura kan
fitaccen kirarinta ba, da za
ƙ
ulo irin birgiman hankakar da ta yi a cikin adabin
Hausa ba. Kayan aikin da wannan takarda ta tattaro za su nazarci kura a
ƙ
ar
ƙ
ashin
Bahaushen tunani musamman:
a.
A nahawun Hausa
b.
Karin magana da zantukan hikima
c.
Tatsuniyoyin Hausa
d.
Wasannin yara maza ko mata ko duka
e.
Addinan gargjaiyar Bahaushe
f.
Labar
a
n gargajiya,
tarihi da tarihihi
g.
Wa
ƙ
o
ƙ
in baka
h.
Magani da warkarwa
i.
Tsaro
Ina kyautata
zaton idan muka ci nasarar
ɗ
ora kura a
kan wa
ɗ
annan
matakai tara (9) na kayan aiki za mu ci nasarar fito da nagartaccen bincike a
kan kura. Muradin wannan bincike tsaftataccen nazarin hoton kura, bisa sikelin
adabin Bahaushe domin tabbatar da i
ƙ
irarinsa na,
kura ga tsoro ga ban tsoro.
Kura a Farfajiyar Nahawu
Ba magana
kura ke yi ba bale a ji kalamanta, da yadda take sarrafa sautukanta. Duk da
haka,
ɗ
abi’un kura
da halayenta da Bahaushe ya kiyaye, musamman yadda take yi wa awakinsa, da
jakunansa, da yadda ake kwasan ‘yan kallo da ita idan an yi gamon ba zata ya ba
sunanta wani matsayi cikin nahawun ma’ana.
A can da
gabanin saduwar Bahaushe da Larabawa, da Turawa, ba ya da kalmar rashawa,
gulili, zalunci, bale cin hanci. Idan ana son wani abu ga wani mai matsayi, ko
an taka doka, ana son a rufe bakinsa ‘yar
ɗ
awainiya, ko hidima, ko kyautar, da za
a
yi masa sunanta “ci”. Idan ya nemi toshiyar baka aka
ba shi, ko bai nema ba, aka ba shi, ya kar
ɓ
a sunansa “kura”. Da an kira dattjio “kura” an san
bakinsa bu
ɗ
e yake na ya
ci, a ci, a tsarin nahawu kalmar kura a nan tana a matsayin “magu
ɗ
i",
“zurmugu
ɗɗ
u”, da duk
wani rashin gaskiya na ci da ceto, ko ci da mu
ƙ
ami.
A fassara ta
biyu “kura” na nufin makami. Ga al’adar Hausawa, gari ba ya zaunawa
b
abu rijiya. Ita kuwa rijiya ba ta shiguwa a yi yason ta,
sai da katausa. Idan ruwa sun samu da “guga” kawai za a ci moriyar su. Guga
tana da wani suna wai shi “wasaki”. Ana yin guga da fata, ko
ƙ
warya, ko
garwa, ko roba ko langa da dai sauransu. To, idan
ɗ
aya daga
ciki
n
abubuwna da
aka yi guga ya fa
ɗ
a rijiya
gaba
ɗ
aya, ko ya
tsinke ya fa
ɗ
a cikin ba
katausa za a nema a fitar da ita ba, “kura” za a nema. Ana yin kura da itace,
ko da
ƙ
arfe, a tsara ta yadda an zura cikin rijiya zai shiga
bakin wasaki, a fito da shi. Ana yi wa
ƙ
arfen “kura”
kirari da kura ba ki tsoron rami
[7]
. Wannan ya
tabbatar da kurar ce aka yi wa takwara.
Na uku,
akwai
ƙ
arfen “magana
ɗ
iso”
[8]
da a
tantagaryar Hausa sunansa “kura”. Da ya kusanci
ƙ
arfe zai
jawo
ƙ
arfen ya ma
ƙ
ale shi, tamkar
yadda kura ke yi wa
ɗ
an akuya, in
ya yi kuren hanya. A
ƙ
asar Hausa, ‘yan wasan tauri da yawa ana yi musu
kirari da “kuran
ƙ
arfe”
[9]
wato kamar
yadda kura ke yi wa nama raga
-
raga, haka
suke yi wa
ƙ
arfe kaca
-
kaca
[10]
. An ce, a
zamanin jamhuriyya ta farko an jarraba wannan sunan a Kaduna
[11]
. Na biyar,
tasirin kalmar “kura” a nahawun Hausa ya zarce tunanin na bayan fage. Irin
ƙ
aurin sunan
da kura ta yi, ya sa ba a sarrafa sunanta a yi wata kinaya ta yabon wani, na
ƙ
wazo, ko
alheri. Da an shaidi mutum da cewa, ku
ɗ
in kowa yana iya cinyewa, ko ba ya wasa da amana, ana
ba shi ita yana cinye ta, sunansa “kura”. Ai shi ne dalilin Bahaushe na yi wa
kura sunan “duhu” wai, kura a yi miki duhu yanzu abin wani ya
ɓ
ata. Idan amana
aka ba maras ri
ƙ
on ta sai a ce: “an ba kura hi
ɗ
a”. Ga wasu
jimloli da sunan “kura” ya ta
ɓ
i ruhin
nahawun ma’anarsu:
a.
Kare ya farauto kura.
b.
Awaki sun hana kura haura ganuwa.
c.
Ku yi yarjejeniya a rubcue ka san Hassan kura ne na
ƙ
arshe.
d.
Musa ka kula da aljihunka,
kasuwar Kano akwai kuraye.
Yadda kura
ta yi tasiri ga yi wa tumaki, da sauran raunanan dabbobi ta’adi, haka nan
Bahaushe ke kallon kowane azzalumi. Ai a nahawu jimlar farko, daidai take
domin: yankin suna da yankin aikatau daidai suke. Idan za mu yi wa jimlar nazarin
gwari-gwari sai mu ce:
a.
Kare: shi ne ma’aikaci wanda ya yi farauta
b.
Ya: wakilin sunan kare ne, kuma mai tabbatar da jinsinsa “namiji”.
c.
Aa: jan wasalin da aka yi “a” ta li
ƙ
e ga “y” ya
nuna shuda
ɗɗ
en lokaci,
don haka, tuni kare ya gama aikin farauta.
d.
Farauta: aikin da kare ya aikata, samunta da wasali “o” a
ƙ
arshe ya
nuna shu
ɗ
a
ɗɗ
en aiki ne,
an yi an gama.
e.
Muzuru: shi aikin da kare ya yi “farauta” ya fa
ɗ
a wa, don
haka ya zama “shawuya”.
Babu hazi
ƙ
in
ɗ
alibin nahawu da zai musanta
wannan gwari-gwari amma wurin da gizo ke sa
ƙ
a shi ne, nahawun ma’ana bai yi
canjaras da al’ada ba
[12]
.
Dalili shi ne, kare na iya farauto kura? Misali irin
haka suna da yawa. Maka
ɗ
a Sani Aliyu
Dandawo ya raba wannan takaddamar nahawun cikin wa
ƙ
arsa ta. “Mu
zo mu ga Ma
ɗ
awaki” ya
ce:
Jagora: Kare
bai ja da kura
,
Yara : Don
ba
ƙ
arfinsu
ɗ
ai ba
.
Gindi : Mu
zo mu ga madawaki
,
: Bai
ɗ
au warga ba
Audu.
Maka
ɗ
a
Walga Bunza ya yi irin wannan hasashe a gindin wa
ƙ
arsa da ke
cewa:
Jagora/Yara:
Kare bai zuwa ramen kura
: Don ba gaskiyan Allah na ba.
Idan nahawun
jimla ya yi fito-na-fito da al’ada, ko a
ƙ
ida, ko
addini,
ko wani
sanannen ilmi gama
-
gari,
ma’anar na haifar da ta
ƙ
addama
[13]
.
Karin Magana d a Zantukan Azanci
Karin magana da zantukan hikima,
wasu fitattun nau’ukan adabi ne da kowace al’umma ke bugun gaba da nata. Haka
kuma, sun ratsi al’adu, da addinai, saukakki da na gargjaiya.
Ƙ
unshiyoyin
hikimomin karin magana, da zantukan hikima, sun fi amo, da fice, da kama
zuciya, idan suka kakkamo halittun da
ɗ
an Adam ke shawagi tare da su, a sararin duniya
musamman dabbobi, da tsuntsaye, da
ƙ
wari, da
tsirrai, da iskoki, da ake taho-mu-gama da su
[14]
. Sifofin
kura, da
ɗ
abi’unta, da
halayenta, da waibuwarta, da kasawarta, sun yi naso sosai a karin magana, da
zantukan hikima na Bahaushe. Ga ka
ɗ
an daga
cikinsu domin misalan da za a tattauna.
1.
Karambanin akuya gai da kura
.
[15]
2.
Jigji
[16]
mai shan
ruwa kwatarnin kura
.
3.
Maraba da gasasshe kura ta ga ba
ƙ
in jaki
.
4.
“Ba gyaran-gyaran ba a yi mai”, kura ta ga jaki mai goda
[17]
.
5.
Laifin kura goma ban da satar wa
ɗ
ari
.
[18]
6.
Kura da shan bugu Gardi da kar
ɓ
e ku
ɗ
i
.
7.
Tsoro kamar farar kura
.
8.
Gaba kura baya saya
ƙ
i
.
[19]
9.
Bismillahi ba shi yankan kura, sai an gama da “wayyo Allah”.
10.
Ba a cin bashin kura a yi dare daji
.
11.
Kulkin jifan kura sai gobe a
ɗ
auko
.
[20]
12.
Mui! Kukan kura
.
13.
Kura ga tsoro ga ban tsoro
.
14.
Ko da ganin kan kura ya ci mutum
.
15.
Kowa da bukin zuciyarsa, ma
ƙ
wabcin mai akuya a sayo kura
.
16.
Kura ke ci da gashi
.
17.
Kura gare ku masu awaki!
18.
Ƙ
assan kura sai gara
.
19.
Kashin guiwan kura ba lasan karnai ba.
20.
Kura ta san kada tudu shika
kwana.
Na
ɗ
an tsakuro
ka
ɗ
an daga
cikin karuruwan magana da zantukan azanci, da kura ta mamaye a farfajiyar
adabin baka, na wannan fanni. Karuruwan magana na 1-4 suna bayyana irin
halayyar kwa
ɗ
ayi da
ɗ
okin nama na
kura, ga dabbobin da Bahaushe ke kiyo. Haka kuma, idan muka nazarci lambobi na
15, 16, da 17, za mu ga da kare, da akuya, su ne tumun kura
[21]
. A fannin
tsoro da Allah Ya halicci kura da shi, lambobi na 7, 12, da 13, sun fayyace shi
sosai. Abin
ban sha’awa,
ko an shaidi kura da tsoro, ita ma dai wanda ya shaide ta da tsoro, shi ma
tsoron
ta yake yi.
Dangantakar tsoron da
ɗ
an Adam
(Bahaushe) ke yi wa kura a bayyane yake,idan muka kalli lambobi na 8, 9, 10 da
11 duk sun tabbatar da cewa, kura ta san Bahaushe tsoron ta yake yi. Sau nawa
ta sa shi hauka? Da kuwwa shi ka
ɗ
ai? Da
magangannun sa
ɓ
ari na bar
wa na baya abin fa
ɗ
i? A
ma’aunin karin magana, da zantukan hikima, da kura da Bahaushe, duk matsorata
ne, sai dai a fagen kwa
ɗ
ayi, kura ta
zarce Bahaushe nesa ba kusa ba. Don haka, tunanin Bahaushe na, “kura ga tsoro”
ya tabbata a lambobi na 6, 7, 12 da 13. Tabbatar da fashin ba
ƙ
in “ga ban
tsoro” a bayyane yake a lambobi 8, 9, 10, 11 da 14. Ga alama, a farfajiyar
karin magana, Bahaushe ya fi tsoron kura fiye da yadda kura ke tsor
o
n sa. Hankalin da Bahaushe ya fi ta, da da
ɗ
in baki ya
sa, ya sa ta gaba a karin magana, kura ga tsoro ga ban tsoro
[22]
.
Kura a Farfajiyar Tatsuniya
Ba
ƙ
asar Hausa
ka
ɗ
ai ke da
kuraye ba, amma ga alama a farfajiyar Afirka ta Yamma
ƙ
asar Hausa
ta fi saur
a
n
ƙ
asashe ma
ƙ
wabtanta
abin da kura ke so. Abin nufi, mu muka tara awaki, da tumaki, da karnuka, da
jakuna, da ra
ƙ
uma, da kura ke
ɗ
okin gani da takaicin kamawa
[23]
. To, wannan
shi ya haifar da samun jirway
e
n kura da
yawa a cikin tatsuniyoyin Bahaushe. A cikin turakun tatsuniya na wauta, da kwa
ɗ
ayi, da
raki, da zalunci, da nadama, da gaggawa, da tsoro, da ban tsoro, kura ke
jagorantar wuraren. Bugu da
ƙ
ari, hatta da wurin magana Bahaushe kura “tsamin baki”
ya ba ta, wai don tsananin wauta. Ga wata tatsuniya wai ita “Muduka”:
Wai kura ta
ɓ
oye ‘ya’yanta a wani rami domin ta ciyar da su a
shekara ta ga yada za su kasance. Da zomo ya ji labari ya je ya shiga ramin
tare da ‘ya’yanta ba ta sani ba. Da ya shiga, ya gaya musu cewa, sunansa
“Muduka”. Da ta zo ta wurgo nama cikin ramin da ‘ya’yanta suke ciki sai ta ce:
“Ga shi nan, ku duka”. Da jin haka, sai zomo ya ce: “Ai ni ake nufi domin
sunana aka fa
ɗ
a”. Haka aka
cigaba da yi har tsawon shekara. Zomo na cinye nama, yana bai wa ‘ya’yanta
ƙ
assa su
lashe. Da shekara ta cika, ta nemi su fito ta gan su. Kowane ya fito sai iska
t
a buge shi ya fa
ɗ
i domin
tsananin rama, yunwa ta ci ta cinye. Ta ce, “me ke faruwa?” Suka ce “Ai abincin
da kike turo muna duka Muduka ke cinyewa”. Ta ce “waye Muduka”? suka ce: Yana
can ciki”. Kura ta
ƙ
wala murya ta ce: “Muduka! “ya ce: “E” ta ce: “Fito in
gan ka”. Ya ce “To, ga ni zuwa”. Can, sai ya ce: “Ga takalmana ki ri
ƙ
a mini, sai
ya turo kunnuwansa fankan-fankan biyu”. Cikin haushi, kura ta kama su, ta yi
jifa da su nesa, ta tsura wa rami ido, zom
o
ya fito a yi watanda da shi. Tana haka, ‘ya’yan suka
ce “Ai mama shi ne kika jefar waje ga shi can ya tsere”. Kura da ‘ya’yanta suka
kwana cikin takaici.
A wannan
tatsuniyar mun fahinci rami ne gidan kura. Kura kwa
ɗ
ayi gare ta,
ba ta da abincin da ya fi nama
[24]
. Wanzam ba
ya so a jikinsa don haka ta
ɓ
oye
‘ya’yanta cikin rami ka da wani ya farauce su, amma ta je farautan
ɗ
iyan wasu.
In ba wauta ba, wa ke share shekara yana kiyo bai je ya ga abin da yake kiyo
ba? Wanda ya yi irin cutar da zomo ya yi, da wace hujja za a jira ya fito rami,
tun da
ƙ
ofa
ɗ
aya ke ga
ramin, ai sai a je, a riske shi? Me ya hana shiga a riske shi? “Tsoro’. Me ya
sa Muduka ya ce: “Ga takalmansa a ri
ƙ
a?” Tsoron kura
yake yi. Haka kuma, ya fi ta wayo. Da aka wurgar da shi, me ya hana a bi shi, a
kamo? Kura ba ta iya gudu, bale daka tsalle irin na zomo. Har dai yanzu da yake
gudun fitan rai. I
ƙ
irarin Bahaushe na, kura ga tsoro ga ban tsoro ya
tabbata a wannan tatsuniya, tare da tabbacin wautan kura, da ita da ‘ya’yanta
[25]
, tare da
fayyace kwa
ɗ
ayin da
Bahaushe ya tabbatar ga kura. A Bahaushiyar tatsuniya, babu dabbar da ta kai
zomo, da dila, da biri, wayo
[26]
. Haka kuma,
babu wadda ta kai kura da ra
ƙ
umi wauta. A wannan riwayar, an yi wahalar shekara ana
neman abinci, wauta
t
a hana a ci
moriyarsa. Abin da aka yi nema ana tarawa shekara
ɗ
aya, wayo ya
tserar da mayaudarin da ya cinye shi duka
[27]
.
Wasannin Yara
Dabbobin da
yara ke hul
ɗ
a da su
cikin gidajensu, da su ake gina musu tatsuniyoyinsu, da wasanninsu. Wasannin
yara maza da mata na
ƙ
asar Hausa ana aiwatar da su a dandali
[28]
na unguwa,
ko a cikin gidaje, lokac
i
n tashe
[29]
. Wannan
ɗ
an bincike
ya yi iya
ƙ
o
ƙ
arinsa na nemo dabbobin da yara ke kwaikwayo a
wasanninsu, bai samo ko
ɗ
aya ba, face
na “kura”. Wata
ƙ
ila, saboda takaicin kura na cin amanar iyayensu ya sa
suka
ƙ
ir
ƙ
iro wasan tashe da sunanta. Ga yadda wasan ke tafiya:
Tashen kura yaki kura
Jagora : Kura yaki kura!
Yan amshi : Damashere
Jagora : Ba don farin wata ba
Yan amshi : Damashere
Jagora : Da buru ta yi
ɓ
anna
Yan amshi : Damashere
Wannan wasar
rukuni uku gare ta, rukuni na farko shi ne,yaro za a yi wa shiri irin na kura
da wutsiya da kunnuwa, jikinsa a
ɗ
i
ɗɗ
iga
karmatako, da ba
ƙ
in tukunya, ya ri
ƙ
a sanda,
yana ‘yar rawa, irin yadda kura ke tattakawa na farauta. Abin mamaki da kare,
da akuya, da sun ga yaron sai rugawa aguje, ka ce sun ga kurar gaskiya. Rukuni
na biyu shi ne mai bayar da wa
ƙ
a. Shi ka
ɗ
ai ke ba da
wa
ƙ
a kura na rawa. Rukuni na uku, su ne ‘yan amshi, yayin
da suka amshi suna ‘yin rawa irin ta yaron da aka yi wa shirin kura. Ita kurar
za ta cigaba da rawa, amma nesa da nesa da sauran yaran. Hoton kura na tsoro a
bayyane yake, domin an ce: “ba don farin wata ba”
[30]
yadda duk
ake tsoronta haka take tsoron hasken farin wata a gan ta, a je kamo ta. Idan da
farin wata da ta shiga gari, ko gida, neman awakai, za a gan ta. Ashe zancen
kwa
ɗ
ayi a fili
yake cikin w
a
nnan wasan
domin jagora ya ce: “Da buru ta yi
ɓ
anna”.
Ɓ
annan me? “
Ɓ
annar kama
dabbobin mutane”. Duk fa abin da ba nama ba, babu ruw
a
n kura da shi, d
a
lilin B
a
haushe ke nan na fa
ɗ
ar, “laifin
kura goma ban da satan wa
ɗ
ari”. A farfjaiyar
tatsuniya tsoro, da tsoratarwa, da kwa
ɗ
ayi na kura wani babban tubalin gina tatsuniya ne.
Kura a Addinan Gargajiya
Addinan
gargjaiyar
ƙ
asar Hausa gabanin bayyanar saukakkin addinai su ne,
camfi
[31]
, tsafi
[32]
, da bori
[33]
. Ga alama,
bori ya haifar da camfi, camfi
ya haifi
tsafi. Cikin hidimomin bori, akwai “kangida” wadda za ta kasance dabba, ko
ƙ
waro, ko
wani tsuntsu, ko kifi, da za a haramta wa zuriya ci, da kisa, da mallaka. Daga
nan ne, za a camfa wani abu ga sa
ɓ
a wa
dokokin. Idan wasu abubuwa sun wakana dole a kauce hanya a samo yadda za a
fuskance su. Neman agajin “Kangida” da za a yi, nan “Tsafi” zai shigo. To, ita
kura Bahaushe ba ya “kangida” da ita. A fassarar Bahaushe ita kanta iska ce,
mai zama cikin iskoki, mai waibuwa, da
ƙ
u
ƙ
uwa, irin na
iskoki. A kundin jerin sunayen isko
k
in ‘yan bori
akwai iska mai suna Kure
[34]
. Taken iska
kure a ki
ɗ
an goge da
garaya shi ne:
: Gobe daji muka kwana
,
: tun da kure muka aure
.
Haka kuma, a cikin kirare
-
kiraren da ake yi masa akwai:
Na Inna mai rabon fa
ɗ
a da ta
ɓ
arya,
Ga wanda ya yi kwari ya yi baka,
Yac ce wa kasuwa: “kulleru”!
Mai girbi gona
r
surukai
Tun bai fitar da kai ba
[35]
.
Ai ko bayan
da Musulunci ya bayyana, kura ba ta daina tasiri cikin adabin baka ba, musamman
idan aka yi duba ga zantukan hikima, da kirari, da karin magana irin su:
a.
Bismillahi ba shi yankan kura sai an gama da wayyo Allah!
b.
Kura mai shiga gari da attahiyatu
c.
Birgi-birgi sallar kura, salla takai tana waiwaya.
A kula,
dabbobin
ƙ
asar Hausa ana kangida da su, da ‘yan camfe-camfe, da
taje-taje, amma babu wadda ke cikin jerin iskokin
ƙ
asar Hausa
hatta kyanwa, da macizai, ba sa ciki, kura ka
ɗ
ai ke da
wannan mats
a
yin
[36]
. A cikin
wannan fasalin, barazanar kura, da ban tsoron ta, da tsoron ta, sun bayyana. Da
kwana dawa, da aure dawa, duk Bahaushe na ce musu, dawa mai ban tsoro. Wai a
ce, ko da Malam ya ce, bismillahi ya
ɗ
ora yu
ƙ
ar yanka, da wayyo! Zai
ƙ
arasa
addu’ar yanka, me ke sa haka ba tsoro ba? Dabbobin da take ci cikin gari suke,
dole wata rana sai an shiga gari, to me ya kawo “attahiyatu”?
[37]
Labaran Gargajiya, Tarihi da Tarihihi
Labaran
gargajiya sun sa
ɓ
a wa
tatsuniya domin akwai da
n
sh
i
n wuraren da suka wakana. Tarihi riwayar abubuwan da
suka gabata ne, ko su maimaita kansu, ko wasu su tsira cikinsu. Tairhihi ya fi
kusantar tatsuniya, amma ya fi
ƙ
arfi, da sahihanci, domin shi na da mafari, da bagire,
da lokaci, wasu lokuta har da sahihan sunaye a ciki
[38]
. Wa
ɗ
annan
abubuwa uku sun kakkamo abubuwa da yawa cikin tarihin Bahaushe, da
ƙ
asarsa, da
ma
ƙ
wabtansa. Yadda kura ta yi malkashi a cikinsu abin
nazari ne sosai ga
ɗ
aliban ilmin
al’ada da adabi.
A cikin wasa
ƙ
wa
ƙ
walwar wasannin labaran gargajiya akwai:
An ba ka ku
ɗ
i fam uku, ka je ka say
o
akuya
ɗ
aya fam
ɗ
aya, kura
ɗ
aya fam
ɗ
aya, da buhun wake
ɗ
aya fam
ɗ
aya. Bayan
ka sayo su an ri
ƙ
o maka su, kun iso bakin kogi, za ka
ƙ
etara babu
jirgi, yaya za ka tsallake da su? Ka tuna, ana son ka
ƙ
etar
ar
da su
ɗ
ai bayan
ɗ
ai, kuma kada
ɗ
ai ya cuta
wa
ɗ
aya.
[39]
Idan ka fara
ɗ
aukar wake,
ka bar kura da akuya, gayya na gama aiki. Idan kura ka
ɗ
auka, ka bar
akuya da wake, an yi rufin kan uwar da
ɗ
i
[40]
. Ko da ka
ƙ
etare da
akuya, ka bar wake da kura, idan ka dawo
ɗ
aukar na biyu, wane za ka
ɗ
auka? Me ya
kawo kura ciki? Kwa
ɗ
ayi da ban
tsoro, da zalunci.
Ɗ antauri da Kura
Wannan
labari ba
ƙ
age ba ne ya auku zahiri a
ƙ
asar Gobir,
yadda na samu labarin shi ne:
A wani
ƙ
auye wani
ɗ
an tauri ke
kawo wa
a
bokinsa wani
Hakimin
ƙ
auye hira, wani lokaci har duhu ya shiga sannan ya
wuce
ƙ
auyensu. Wata rana ya yi dare, sai Hakimin ya hana shi
komawa gida cikin dare domin gudun masu dagi (musamman kura). Hakimi ya ba shi
wurin da zai
ɗ
an huta, da
safe ya wuce gida, sai ya gaya wa Hakimi cewa: “Ina! Ai arne bai tsoron arne.
Wace kura ‘yar fatar uwa, ai maye ba ya cin maye sai dai ya ci kurwa”. Hakimi
ya ce: “A’a, karen daji waibuwa gare shi, yi ha
ƙ
uri ka
kwana, ai ba kasawa ba ne, kowa ya san ka”. Ya ce: “Ina! Hakimi sai da sahe, na
wuce”. Bisa
ƙ
addara, yana rabuwa da garin da nisa, kura ta kwararo
shi haukace, ba ji ba gani. Ya yi ‘yan dabarunsa duk ta ce: “Ina! Sai ya zama
nama”. Da ya ga ba mafita, ya dawo gidan Hakimi
.
Hakimi, ya ce: “Lafiya Sarkin Karma”! Ya ce: “Hito ka
gani, wallahi kura ba ta da kyawo, ni ko ba ni da kyawo! Sai dai a hwa
ɗ
i hullar
jirge, koko lahirar maza ta yi
ƙ
ura! Wallahi
yau bala’i ya gamu da bala’i. Wane mutum ta haukata shi, ta tafi abin ta, ta
bar shi nan yana yada abin fa
ɗ
i ga ‘yan
uwa
[41]
.
Babu wai!
Sarkin Karma ya tsorace ya gigice ya ci moriyar dugadugansa. Me ya hana, ya
tsaya can daji arne ya kashe arne? Wa yake yi wa kirari
ƙ
ofar Hakimi?
Me ya hana ya zo da gawarta, in gaskiya ne, kafiri ba ya tsoron kafiri? Haba!
In ka ji
ƙ
i gudu, sa gudu ne bai zo ba. A nan, “kura ga ban
tsoro”, ya tabbata. A wajen kura ita kuma, gudun da Sarkin Karma ya ti
ƙ
a, da ‘yan
koke-koke, da kuwwace-kuwwace, na ru
ɗ
ewa, da neman agaji, da ‘yan tusoshi na isa barka, su
suka ba ta tsoro ta ruga abin ta, ta koma dawa. Ai ko da ya shigo cikin gari, ba
tare suk
a
shigo ba,
tuni tsoro ya kama ta, ta gudu. Wannan
ɓ
angare ya tabbatar da “kura ga tsoro”.
Ke Kura Sake Dabara na Buwaya
Wannan shi
ma tarihi ne mai tabbatar da cewa, kura na da
ƙ
u
ƙ
uwar
ɓ
atar da hankalin
mutum. Hausawa na ba da shawara cewa, wanda duk kura ta koro, ya ruga ya kama
wani ice ya hau, da ta ga zai hau saman kowane irin ice, za ta ruga. In ya hau,
za ta dawo, ta ga ko zai fa
ɗ
o
ƙ
asa irin na
ƙ
adangare. In
bai fa
ɗ
o ba, za ta
ɗ
aga kai ta
dube shi, in ya dubo ta, zai fa
ɗ
o
ƙ
asa.
Da ta koro
wani Barade, ya haye sama. Kura ta da
ɗ
e ba ta ga ya fa
ɗ
o ba, ta duba sama bai dubo ta ba, sai ta ji tsoro ta
ruga. Shi kuwa an neme shi gida, ba a gan shi ba, sai da asuba. Da aka ga
safiya ta waye, aka shiga daji, da maka
ɗ
a, da mahaya dawaki, bi
ɗ
arsa. Aka ci
nasara aka tarar da shi saman wata itaciya doguwa. Aka lura a
ƙ
ar
ƙ
ashin
itaciyar sun yi artabu sosai, an malkashe ciyawa, ga iri na wanda ta koro.
Babban yayan
ɗ
akinsu ya
ɗ
aga kai ya
gan shi, ya ce:
“
Wane barka
da arziki, Alhamdu lillahi, Allah Ya sa da shan ruwa a gaba”.
Jama’a an taru tinjim ana kallon ikon Allah. Sai ya ce
wa yayansa. “Ke kura sake dabara, wallahi na buwaya,
ƙ
ara gwada
sa’a ki gani”. Ai sai da aka hau sama aka
ɗ
a
ɗɗ
aure shi aka
sako
ƙ
asa, jama’a na
ƙ
asa suka kar
ɓ
a, shi kuwa
yana a kan bakinsa: “Wayyo! Ta yi halin ta! Makashi
n
maza maza ka kashe shi”
[42]
!
Tarihi na
gaskiya, da
ƙ
agagge, irin wannan game da kura suna da yawa. A wannan
ma, za a ga, taken takarda
y
a fassara
kansa. Kura ta ba da tsoro har na fitan hankali, ta tsere saboda tsoro, ta
tabbata, kura ga tsoro ga ban tsoro.
Kura Cikin Adabin Wa ƙ a
Mawa
ƙ
an baka na
kowane
ɓ
angare, suna
aro kura su saka cikin turakun
wa
ƙ
o
ƙ
insu, ko cikin
fan
ɗ
ararrun wa
ƙ
o
ƙ
i (wa
ƙ
o
ƙ
in sata) muhalli
biyu ke ga kura a turakunsu. Kura tana iya wakiltar masu ku
ɗ
i, kuma tana
hawa turken
ƙ
wari (
ɓ
arayi). Da
aka yi artabo da Bawa Makau a kasuwar Gumi har aka kai shi
ƙ
asa Gambo
mijin Kulu cewa ya yi:
Jagora: Ana ta bugun mugu shina
tsaye,
: Mugu har yak kai ga kwance,
: Dan nan sai nak kau da kaina,
:Nac ce: Kaicon na kaina!
”
: Bunsurun ga da kuraye ka tsoro
,
: Ga shi mutane sun kashe shi.
A nan, Bawa
Makau (
ɓ
arawo) shi
ne “bunsuru”, masu ku
ɗ
i su n
e
“kuraye”, ‘yan kallo na gayyan wayyo! Su ne “mutane”.
Da aka yi wa
ɗ
aya daga
cikin taurarinsa irin yadda aka yi wa Makau Bawa, ga shi kwance matacce, amma
babu mai isa kusa don tsoron da ak
e
yi masa.
Nan ne Maka
ɗ
a Gambo ya
kira shi kura, da fa
ɗ
ar:
Jagora: Ashe Kura ko ta yi kwance,
: Ko an
yanke ba ta motci,
:
Ɗ
an akuya bai
ƙ
etarat ta
,
: Shi na aza
kura lahiya take
,
: Ba shi isa
kusa ba shi yarda
,
: Aradu!
:
Kwab bi daren banza da yohi,
: Ya sha
kashin banza da yohi.
Ruwayar
tauraron, da waibuwarsa, ya sa aka kira shi “kura”. Abin lura a nan, ga kura
kwance ta yi bu
ƙ
u ta lahe don tsoro, wai a ce, ta mutu a rabu da ita
[43]
. A ge
f
e
ɗ
aya kuma ga
makasa kowa ya sha jinin jikinsa babu mai isa kusa don tsoro.
Wasu maka
ɗ
an jama’a,
sukan aro sunan “
k
ura” su
dabbantar da kansu, domin isar da wani sa
ƙ
o, ko mayar
da martani, ga wani, ko ga wasu. Idan aka dabbantar da mutum aka ba shi sunan
kura, ko sa
ƙ
on da ake son a isar da sunanta, za a ga ya yi daidai
da bu
ƙ
atun kura, ko halayyarta. Da Alhaji Muhammadu Gawo
Filinge ya ji irin ra
ɗ
e-ra
ɗ
in da ake a
kansa, cewa ga shi Malami kuma yana wa
ƙ
a da ‘yan
mata, dole da walakin goro cikin miya. Da zai mayar da martani sai ya kira kura
ya ha
ɗ
a ta da raguna,
ya ce, su ba da bayani:
Jagora: Kura cikin gar
k
en rago
,
: Ko sau
ɗ
aya
n
ba ta hwasa gar
g
en ba
,
: In ta hwasa ku h
w
a
ɗ
i ga ku
.
Yara : A a Malam, ba ka kutsa ba
.
Jagora: Haka nika tammaha!
Gindi : Ya Allah gyara, Wahabi
: Ka taimaki ‘yan Nijar.
A dubi kura,
da za ta
ƙ
are rayuwa ba ta ga rago ko sau
ɗ
aya ba, sai
dai awaki, da jakkai, da karnuka. Wai yau, ga ta cikin gar
k
en rago kuma ko
ɗ
aya ba ta ta
ɓ
a ba. Ragunan da kansu suka ce: “Ko sunsunar su bai yi
ba, bale ya fasa su,”
[44]
a wata
rerawa shi da kansa ke cewa: “Haka nan na”. A ha
ɗ
a kura da
rago wuri
ɗ
aya akwai ha
ɗ
ari, kamar
yadda Bazaura ta yi wa Sani Danbal
ɗ
o a wa
ƙ
arsa ta “Zaura”
ya ce:
Jagora: Irin wada zaura tay yi wa
Ɗ
anbol
ɗ
o!
: Tamkar Kura ta iske farin
rago an
ɗ
aure.
: Yamma garai darni ya hwa
ɗ
i,
: Mi kika shakka, ai ke ad da
.
Yadda Mamman
Gawo ya kalli kura, haka nan Sani
Ɗ
anbol
ɗ
o ya kalle
ta, na tsananin kwa
ɗ
ayi ga
tumaki musamman masu mai irin rago. Lallai gaskiyar Bahaushe da ke yi wa kura
kirari mai “a ci wawai” domin an san, da ta ha
ɗ
u da tumaki,
ko awaki, labari ya
ƙ
are. Maka
ɗ
a Ibrahim Naramba
ɗ
a a wa
ƙ
ar Sarki
Ɗ
ankulodo na
Mara
ɗ
i mai suna “Ciwon
Cikin Maza
Ɗ
ankulodo” yana cewa:
Jagora:
Magatakarda tsohon kare na
.
Yara : Gudu
shikai shina yar da
ƙ
ashi
.
Jagora:
Magatakarda da bunsuru na
.
Yara : Da na
sayo shi na kai ma kura,
Gindi: Ciwon
cikin maza
Ɗ
ankulodo
: Na Yari mai halin Tcagarana
A ta
ƙ
aice, yadda
tatsuniya da karin magana, da sauran sassan adabin Hausa, ke kallon kura da
raaki, da tsoro, da kwa
ɗ
ayi, haka
nan mawa
ƙ
anmu ke sarrafa ta. A wa
ƙ
o
ƙ
in fada, ba
a cika yabo da sunan kura ba sai dai a yi zambo da
ita
. Dubi yadda Sani Aliyu
Ɗ
andawo ke yi
wa wani zambo cikin wa
ƙ
ar: ‘Hashimu
ɗ
an Abdullahi’
Jagora:
Kurar Gardi kwa
ɗ
anki ka ja
miki
,
Yara : Ko
jiya nan kis sha kashi
.
Gindi :
Hashimu
ɗ
an Abdullahi
,
: Ka
ƙ
ara ri
ƙ
o sai ka sarki.
Kura a Fagen Magani da Warkarwa
Daga cikin
tussan magungunan Bahaushe, akwai dabbobi, da
ƙ
wari, da
tsuntsaye
[45]
. Mutanen
duniya a tsarin magungunansu na gargajiya, akan yi la’akari da sifar abu, ko
halayensa, ko abincinsa ko sunansa, idan ana son a yi maha
ɗ
in magani da
shi
[46]
. Tunanin
Bahaushe kan kura abubuwa hu
ɗ
u ya zo da
su:
a.
Tana da tsoro sosai ba ta bari a kai ga jikinta
.
b.
Tana da ban tsoro ga mutane da dabbobi har na fitan hankali
.
c.
Tana da
ƙ
u
ƙ
uwa mai razanar da duk halittar da take cin namanta
.
d.
Tana da raki mai haddasa, zawo,
da kashi, da ta razana, don haka ake da karin magana
r
, “in kura na da magnain zawo da ta yi wa kanta
.
”
Magani da
bokayen
ƙ
asar Hausa, ke bayarwa suna tsaraka da “kan kura” don
haka suke yin jakar saka magani da shi. Idan ana tallar magani yana jawo kasuwa.
Haka kuma, sukan yi walki da fatan kura domin buwayar abokan gaba da iskoki.
[47]
A
gargajiyance, ana rataya kan kura
a
ƙ
o
far
ɗ
aki, wai a
kori miyagun iskoki
.
Fata
r
goshin kura, ana ha
ɗ
a wa sarakai
magani da shi na
k
warjini da
ban tsoro. Gardawa na amfani da kashinta, da kitse, da fitsarinta, da sale
ɓ
anta, a ha
ɗ
a magungunan
zaga (duk wani mai ha
ƙ
ora ba zai iya ya ciji mutum ba). A gaskiyar al’amari,
Allah Ya saka wasu abubuwa cikin kura na sa tsoro ga duk wani abin da ya
kasance abincinta. Na gani da kaina an
ɗ
auko fatar kura
ɗ
anya, aka wurga wa kare ya ruga aguje yana kuka na
ɗ
aukar
hankali da fitan rai
[48]
. Haka kuma
an gaya mini cewa, kare na cikin murhu kwance kura ta
ƙ
etari
murhun, ba ta san da shi ba, amma nan ya mutu. Na samu wani labari
da
aka ce:
A barikin sojojin Kwantagora akwai wani mugun kare a
wani gida kowa tsoransa yake yi, saboda shi yara dole suka
ƙ
aurace wa
gidan. Wata rana, wani Gardi ya biya can tallar magnai, tare da kurarsa, yana
buga tamburansa. Da karen ya ji hayaniyar tambura, da bai saba ji ba, ya rugo
aguje wai ya tarwatsa taro. Yara na ganin kare suka hau
ƙ
afafunsu.
Kare na
ɗ
auko zambiya
ya dako hari, ya mi
ƙ
a, suka arba da kura, ai nan ya ce: “ga garinku” ba
zancen gudu, bale kuka, ko shure-shure
[49]
.
Ire-iren wa
ɗ
annan
labarai tsakanin kura da kare suna da yawa. Za a ga karen bai ta
ɓ
a ganin kura
a rayuwarsa ba, amma da sun yi idonki-idona nan zai mutu. A wasu lokutan kurar
ba ta ma gan shi ba. Haka kuma, za a ga, ba wani kuka ta yi ba, ko gurnani,
amma kare ya mutu. Dole mu mayar da al’amari ga mai shi (Allah) Shi ka
ɗ
ai Ya san
abin da Ya sa tsakaninsu. Don haka kura babban maha
ɗ
in magani ce
katta’u
[50]
.
Tsaro
Adabin bakan
Bahaushe ya tabbatar da irin dangantakar da ke akwai tsakanin kura da Bahaushe.
Duk da haka, a
ƙ
asar Hausawa, babu mai wasa da kura, sai Gardawa ‘yan
gado. Abin mamaki, cikin
ƙ
asa, ko gunduma gaba
ɗ
aya da wuya
a samu Bagarde fiye da
ɗ
aya. Wanda
ya nuna ba kowa ke da asirin kura ba, sai ‘yan gado. Gidajen Gardawa kura ce ke
yi musu gadi, batun wani
ɓ
arawo ya
shiga gidajensu, ko na ma
ƙ
wabtansu, bai taso ba, domin kura jin warin mutum take
yi ta dinga bin iska har sai ta kai gare shi. Mafarauta na amfani da
ƙ
assan kura,
ko kitsenta, wajen adana naman da suka gyara, aka shanya, domin ya bushe a sa
rumbu
[51]
. Idan aka
shafa masa kitsen kura, ko aka ajiye
ƙ
assanta kura,
da kare, da ita kusa kanta, ba sa isa kusa
[52]
. Ba wani
ƙ
waron da zai
kusanci wurin, in ba gara ba, ai shi ya haifar da karin maganan, “
ƙ
assa
n
kura sai gara”. Dubi taken Gobirawa a fagen ya
ƙ
i yadda
tamburansu ke cewa:
:
Ƙ
ashin guiwan
kura ba lasan karnai ba
,
: Ai ba manya hili ba don Allah
ne ba
,
: Kai! Ina mutuwa tay yi? Ina mutuwa
tay yi?
Sakamakon Bincike
Na
ɗ
ora wannan
binciken bisa ga tunanin Bahaushe na kura ga tsoro, ga ban tsoro. Manufa ita
ce, a fe
ɗ
e karin
magana
r
bisa ga
sassan adabi daban-daban, domin a ga tsawonsa, da fa
ɗ
in sa, a
tabbata tunanin ya yi c
a
njaras da
tunanin Bahaushen adabi. Binciken ya yi yun
ƙ
urin yin
haka, tare da hujjojin da aka farauto wurare
daban-daban nagartattu. Binciken ya kuma kwakkwahe sassan karin maganan biyu,
wato ya
ƙ
yallaro: “Kura ga tsoro” ya tabbatar. Ya nemo, “ga ban
tsoro” ya tabbatar. Don haka, binciken ya ci nasarar hango:
Lallai adabin mutane a ko’ina suke shi ne madubin
ƙ
yallaro
halittun da suke tare da su, masu rai da marasa rai. Binciken ya tabbatar da
tarsashin dabbobin da ke
ƙ
asar Hausa, na gida, da daji, babu wanda ya yi suna
irin na kura, kuma babu mai farin jininta a farfajiyar adabin Hausa. Wannan ya
tabbatar da kasancewar kura dabbar
ƙ
asar Hausa,
kuma sunanta Bahaushe ne, dukkanin
ɗ
abi’un da Bahaushe ya ba ta, sun dace da ita. Ashe ba
tunaninmu, da fasaharmu, kawai ta gina adabinmu ba, a aha, har da gudumuwar
halittun da muke rayuwa da su a
ƙ
asashemu,
kura ta cancanci a na
ɗ
a mata
rawanin: “Tauraruwar Bahaushen Adabi”.
Na
ɗ
ewa
Dabbobin
gida, da dajin Bahaushe, kowane da irin gurbinsa cikin Bahaushen adabi. A girma
ba a kai giwa ba, don haka take zama bukkar daji
[53]
. Gaba
ɗ
aya sun mi
ƙ
a wuya ga
zaki ya kasance Sarkinsu
[54]
. A fagen
wayo da dabara dila
shi ne
kan gaba
;
sarakunan fada
rsa
su ne biri
da zomo
[55]
. Sarkin ya
ƙ
insu zai
kasance cirza amma maza wajensu damisa
[56]
. Da dorina,
da kada, da ayyu, da tsari,
ɗ
an
ƙ
iliu suke
yin shawagi a adabinmu
[57]
. Jaki, da
ra
ƙ
umi, da kare, sai a zambo, da arashi, ake jin
ɗ
uriyarsu a
sassan adabi
[58]
. Hatta da
mutanen
ɓ
oye, da ake
yi wa hidima cikin bori, sai sun riki
ɗ
a zuwa kura za su yi tasiri. Da
z
a
a
ɗ
auko
dabbobin
ƙ
asar Hausa,
ɗ
aya bayan
ɗ
aya, babu wanda ya yi naso mai yawa cikin adabin baka
kamar kura. A kwakkwafafiyar magana, kura matsoraciya ce, kuma makwa
ɗ
aiciya,
azzaluma, da wauta irin ta ta
ɓ
uwar
hankali. Da ta yi rutsi, aka mayar da gami, nan take ana gane rakinta. Garba
Maitandu Shinkafi a wa
ƙ
arsa ta: “Ya hito ma kusa hausance…..”. Ya ce, da
Nababa ya kara da namun daji, makamai suka
ƙ
a
ƙƙ
ale, aka
koma ga kokuwa, babu dabbar da ta fito da kwa
ɗ
ayin ta, da
rakinta, da wautarta a fili, sai kura, domin sai da ta
ɗ
aga murya,
kowa ya ji tana cewa:
Jagora:Daga yau ba ni koma
halinci
.
Yara : Kowa ba ai cin abinci Shinkahi
.
Gindi: Ya hito ma kusa hausance
,
: Nababa ya saba da gina.
Manazarta
Abdullahi,
A. (1980) “Camfi a
Ƙ
asar Hausa”, Kundin BA, Zaria:
Jami
’
ar Ahmadu Bello.
Abubakar,
S.Y. (1997) “Bori a Zariya”, Kundin MA, Kano: Jami’ar
Bayero.
Ado, A.
(2009) “Gardancin Hausawa Jiya da Yau”, Kundin MA,
Sokoto:
Jami’ar Usmanu
Ɗ
anfodiyo.
Ahmed, S.A.
(2011) “Gurbin
Ƙ
wari a Magungunan Gargajiya na
Hausa”,
Kundin MA, Sokoto: Jami’ar Usmanu
Ɗ
anfodiyo.
Aminu, N.
(2002) “Adabin Hausa a Zamanin Mulkin Mallaka: Nazari
a Kan
Ayyukan Frank Edger”, Kundin MA, Sokoto: Jami’ar
Usmanu
Danfodiyo.
Aminu, N.
(2012)
“
Nazarin
Kirarin Madugan Ra
ƙ
ummai na Illon
Geza
”
, Cikin Dun
ɗ
aye Journal of Hausa Studies Vol. 1. No.4
,
shafi 158-
174.
Bada, B.D.
(1995)
“
Literary
Study of the Theme, Fu
n
ctions and
Poetic
Divices of Hausa Karin Magana
”
, PhD Thesis, Sokoto: Usmanu
Danfodiyo
University.
Badejo, P.
(1980) “Bori Sprit Possession Religion as
a Dance Event: A
Pre-Islamic Hausa Phenomennon”
MA
Dissertaiton Califonia:
University of Califonia, Los Angeles.
Bello, M.
(2011) “Maha
ɗ
in Dabbobi a
Magungunan Gargajiya na
Hausa”, Kundin MA, Sokoto: Jami’ar Usmanu
Ɗ
anfodiyo.
Bunza, A.M
(1990) “Haya
ƙ
i Fid da Na Kogo: Nazarin Siddabaru da
S
i
hirin Hausawa”, Kundin MA, Kano: Jami’ar Bayero.
Bunza, A.M.
92019) “Kurar Gardi” cikin Dundaye
Jorunal of Hausa
Studies Vol.2 No.2
Shafi 1-12.
Bunza, A.M.
(2003) Hausa Medicine: its Relevance and
Development
in Hausa Studies
, The Second
Inaugural Lecture, Sokoto:
Usmanu
Ɗ
anfodiyo University, Thursday 18th
Decmeber, 2003.
Bunza, A.M.
(2009) Naramba
ɗ
a
, Ibrash, Lagos: Surulere.
Bunza, A.M. In Ba Ka San Gari Ba Saurari Daka: Muryar
Nazari Cikin
Tafashen Gambo
. Cairo:
Elkudus Printing and Publishing House.
Bunza, D.B.
(2014) “The Hyene in Hausa Folktale”, in Folktale
in
Nigeria
, Zaria: Ahmadu Bello University
Press, pp. 100-107.
Dahiru, I.
(2012) “Nuni Cikin Rayuwa da Labaran
Da
bbobi”,
Kundin
MA, Sokoto: Jami’ar Usmanu
Ɗ
anfodiyo.
Darma, A.Y.
(2014) “Farauta a
Ƙ
asar Hausa”, Kundin MA, Sokoto:
Jami’ar
Usmanu
Ɗ
anfodiyo.
Greenberg,
J. (1941) The Infleucne of Is
l
am on a Sudanese Religion
,
New York:
J.J. Augustine Publishers.
Kudan, M.
(
2015) “Gurbin Dabbobi a Tunanin Bahaushe”, Kundin
PhD, Sokoto:
Jami’ar Usmanu
Ɗ
anfodiyo.
Ibrahim, A.
(2014) “Fashin Ba
ƙ
in Tarihin Karin Maganan Hausawa”,
Kundin MA,
Sokoto: Jami’ar Usman Danfodiyo.
Ibrahim,
M.S. (1982) “Dangantakar Al’ada da Addini: Tasirin
Musulunci
a
Al’adun Hausawa”, Kundin MA. Kano: Jami’ar
Bayero.
Imam, A.
(1933) Ruwan Bagaja, Zariya: NNPC.
Lewis, W.
(1988) Hausa Medicine: Illness and
Well-Being in a West
African Culture
, Durham:
Duke University Press.
Mu’azu, A.H.
(2012) “Tasirin Dabbobi a Adabin Baka na Hausa”,
Kundin MA,
Sokoto: Jami’ar Usmanu
Ɗ
anfodiyo.
Sani, A.
Gobir, Y.A. (2021) Wasanni a
Ƙ
asar Hausa
, Kaduna:
Amal
Printing Press.
Sanyinna,
Y.L. (2012) “Dabbobi da
Ƙ
wari a Karin Maganar Hausa”,
Kundin MA,
Sokoto: Jami’ar Usmanu
Ɗ
anfodiyo.
Sayaya, A.S.
(2011) “Wasan Tauri a
Ƙ
asar Hausa”, Kundin MA,
Sokoto:
Jami’ar Usmanu
Ɗ
anfodiyo.
Shinkafi,
R.H. (2012) “Garba Maitandu Shinkafi da Wa
ƙ
o
ƙ
insa”.
Kundin MA,
Sokoto: Jami’ar Usmanu
Ɗ
anfodiyo.
Umar, M.B.
(1987) Dangantakar Adabin Baka da Al’adun
Gargajiya,
Kano: Triumph Publishers.
Usman, B.
(2018) Peopole, Animals, Spirits and
Objects 1000 Folk
Stories of Nigeria
, Abuja: Klamidas
Communciation.
Usman, B.
(2018) A selection of Nigerian Folktale
Themes an Settings,
Abuja: Klamidas Communciaiton Ltd.
Wushishi,
B.J. (1998) “Adabin Baka: Sigoginsa da Muhimmancinsa”,
Kundin MA,
Kano: Jami’ar Bayero.
[1]
. A
ɗ
an namu bincike (mu
ɗ
aliban al’ada), muna ganin zuriyar angulu, da maiki, da
jemage, da
jaki, da alfadari, da
ƙ
waron damina, da dole-dole, da buzuzu, suna kan hanyar
ƙ
arewa.
[2]
. Daga cikin manyan dabbobin daji, in ba ra
ƙ
umin daji ba, babu mai yarda da mutum (
ɗ
an Adam). Kowanensu da ya ga
ɗ
an
Adam sai neman wurin gudu. Ayyukanmu ke ba su labarinmu.
[3]
. Da ma’aikatan hukuma, da malaman addini, da an
danganta sunansu da kura, fassarar a bayyane take.
[4]
. A
ɗ
an dubi irin rawar da kura ta
taka cikin littafin da ya cinye gasar
ƙ
agaggun
labarai na shekarar (1933) watau Ruwan
Bagaja na Alhaji Abubakar Imam.
[5]
. Kura tana cin naman mutum, sai dai da wuya ta kama
mutum in yana tafiya. Wai, in ta ga yana motsi da hannuwansa, za ta dinga bin
sa, tana jiran su fa
ɗ
i ta
ɗ
auka. Idan ta ga an yi kusan shiga gari, ba su fa
ɗ
i ba, to, za ta ce, yanzu kan bari ta cire su da kanta. Ai
wannan shi ne dalilin da, da yawa, kura ba ta artabu da mutum sai a
wajen ga
r
i. In a daji ne kuwa, sai ya ruga
ta ga hannun ba su cire ba, sai ta bi shi ta cire.
[6]
. Da kura, da zaki, da sun ji kukan doki sai ru
ɗ
ewa, ba sa iya ta
ɓ
uka komai. Shi kuwa ra
ƙ
umi
abokin
ya
ƙ
inta ne, zama
ɗ
aya zai shure ta, ta gaba, ko ta baya, ya kashe ta. Farfesa
Ibrahim Mukoshy ya tabbata mini wannan, a gamon da ya yi da kura yana kan ra
ƙ
uminsa a Sudan, ya ce yana kan ra
ƙ
uminsa dole kura ta nemi agajin dugaduganta. Hira da
shi a gidansa na Runjim Sambo, shekarar (2000).
[7]
. Wannan kinaya ce, yadda kura ke gina rami ta yi gida,
haka nan
ƙ
arfen ke shiga cikin ramin
rijiya ya ciro guga. Ko mai tsoron da ake yi wa rijiya, ba ya
hana a zura kura a ciro guga/wasaki.
[8]
. Ina ganin “magana
ɗ
iso” ba kalmar Hausa ba ce,
kalmar Ingilishi ta magana
ɗ
iso ce aka hausantar.
[9]
. Yanzu haka a garin Bunza ta jihar Kabi, a Unguwar
Malammai akwai wani
ɗ
an tauri sunansa “
Ɗ
antalata kuran
ƙ
arhe”.
[10]
. A lan
ƙ
wasa
shi, a karya shi, a tsage shi, a ruguza shi, a mayar da shi tuka, ko tsaki, ko
ruwa. Mafi yawansu dabaru ne kawai.
[11]
. An ce, a zamanin siyasar salama (NPC) a Kaduna aka yi
taron wasan tauri. Aka yi gina mai zurfi, aka sa
ƙ
arafan rodu ciki, aka bizne, aka shafe da siminti, aka ce
wanda duk ya cika, ya yi ihu! Ya kira rodun su tsago
ƙ
asa su fito.
[12]
. Ba Bahaushen da zai yarda da kai, idan ka ce ka ga, “
ɓ
era ya farauto muzuru” ai a nahawunce, jimla ta cika,
kuma ta ba da ma’ana; sai dai
ma’anar na takin sa
ƙ
a da al’ada.
[13]
. Don haka ne malaman a
ƙ
ida sahihiya ke ganin kuskuren Imam Gaz
a
li da aka ce, ya ce, wai a cikin
littafinsa Ihyaa ul uluumiddi, ya ce: Innii ra’aitul laahaa ma’ana, wai, “Ni
na ga Allah”. Wannan ya sa
ɓ
a wa sahihiyar
a
ƙ
idar Musulunci, ko da Larabcin ya yi daram! Ma’ana kuwa ta yi
baram-baram!.
[14]
. A dubi, Bello D.B. (1995) Literary study of the
themes, functions, and poetic divices of Hausa karin magana, PhD Thesis, UDUS.
[15]
. Babban karambani ne mutum ya gamu da mutuwa, ya gan
ta, ita ba ta gan shi ba, kuma shi take nema, wai
ya gaishe ta.
[16]
. Shi ne bunsurun tsafi wanda ba a yi wa wanka, ko’ina
ya bi ana jin war
i
n jikinsa.
[17]
. Goda (gwarje) watau
ƙ
araurawar da ake yi wa jaki laya da ita a wuya.
[18]
. Wa
ɗ
ari fari ne kamar kitse, amma
zare ne da ake sa
ƙ
a shi.
[19]
. Shaya
ƙ
i
(sayaki) wani mugun dabba ne, wasu su ce “kyarkeci” ne.
[20]
. Tsoron da ake yi na kura, ko kulki aka jefe ta da shi
ta ruga, ba ya
ɗ
aukuwa a ranar, sai dai gobe, in
gari yawaye. Ana tsoron a je ta dawo a gamu.
[21]
. Tumu ne matsayin abincin marmari. Ai a “wa
ƙ
ar Jaki” ta Garba Maitandu Shinkafi wajen yabon
“Jaki”
ya ce masa: Jagora: Katagore tumun kura
Gindi: Sai na yi mai ki
ɗ
i sarkin cicci
ɓ
ar kaya
: In jida akai jaki ba a tausainai.
[22]
. Kamata ya yi a fara gabatar da abin da ke gaba, watau
a ce: “Kura ga ban tsoro, ga tsoro” domin
ban
tsoronta ya fi ts
o
ronta yawa.
[23]
. Ba kamar sauran ma
ƙ
wabtanmu da ba su da irin su ba.
[24]
. Ai a tatsuniyar nama kawai take kasowa tana kawo wa
‘ya’yanta, an ce, wata rana kura ta ga
ɗ
anta da wani
ƙ
ashi ya sungumo aguje ta ce: “Wa ya ba ka wannan”? Ya
ce “Baba” ta ce: “Ya jifar da shi ko yassuwa”. Wai domin ta san in ubansa ne ya
ba shi
ƙ
ashin, to ba sauran tsoka a li
ƙ
e, duk ya cinye,
ƙ
ashin
banza kawai ne. Gaskiyar kirarin Bahaushe da ke ce wa, “
ɗ
an kura baya
n
gidanku duk
ƙ
assa
ne”.
[25]
. Wace wauta ya yi tsawon shekara
ɗ
aya, daga cikinku babu wanda ya fito ya gaya wa mamarsa cewa,
ta yi ba
ƙ
o ba?
[26]
. Da zomo, da dila, da biri, ba sa rami a matsayin gida,
babu wanda zai tantance muhallinsu bale a je a yi tarkon kama
su a can, ko a rutsa da su a
ramin.
[27]
. Da bai ce, a ri
ƙ
a
masa takalminsa ba, da wace dabara zai tsira? Ba don wauta ba, ba ki cewa, fito
da kai da shi waje? Hausawa sun ce, ba a rama gayya da hushi. Kura ta yi, ba ta
ci riba ba.
[28]
. Idan gida na da yawa, cikin gida yara ke wasannin.
Idan ba ya da yawa, sai yaran unguwa su taru a
ɗ
an
hilin unguwa su yi. Sai an
ɗ
an tsatsanta akan je wata babbar
mararrabar hanya ko masha
ƙ
ata
a yi
wasannin.
[29]
. Tashe da wasanninsa, cikin azumni ake gudanar da su.
Yara gida-gida suka bi suna yin wasannin tashe. An fi gudanar da wasannin tashe
a kwanakin azumi goma na tsakiya wa
ɗ
anda Bahaushe ke ce wa: “Goma na
tilas”.
[30]
. Kura tsoron haske take yi, ai shi ya sa ake yi mata
kirari da, “a yi miki duhu yanzu abin wani ya
ɓ
ace”.
Da ta shigo gari cikin farin wata, sai kuwwa, da jifa, da duka, na tara in
tara.
[31]
. Don
ƙ
arin
bayani a kan camfi a dubi Abdullahi A. (1980) “Camfin
Ƙ
asar Hausa”, kundin BA.
[32]
. Don
ƙ
arin
bayani kan Tsafe-tsaf
e
n Hausawa a dubu Aliyu M. Bunza (1990) “Haya
ƙ
i Fi
d
da na Kogo, Nazarin Siddabaru da Sihirin
Hausawa”,kundin MA.
[33]
. Karin bayani kan bori a dubi Abubakar S.Y. (1997)
“Bori a Zariya”, Kundin MA.
[34]
. Don bayani kan kure a dubi Muhammdu S.I. (1982) Dangantakar
Addinin da Al’ada, Tasirin Mumlunci….. kundin, M.A.
[35]
. Ana yi wa iska
r
kirari da “kure borin arna”
mahaukaci ne tuburan. Haba! Wa ke rabon fa
ɗ
a da ta
ɓ
arya, in ba gyaran garaya ba? Wa ke girbi tun abincin bai
fitar da kai ba? To me ya girba? Mene ne sunan girbin? Hauka”.
[36]
. Wai babu iska daga cikin iskokin Bahaushe mai suna
irin sunan dabbobinsa “Kure” wato namijin kura ke nan.
[37]
. Yadda attahiyatu take ta
ƙ
arshe a salla, haka kura take ta
ƙ
arshe ga kawo fitina cikin gari. A wata fassara a ce,
ai kura ce, attahiyatu ga awaki, da ta gan su an kai
ƙ
arshe. Ga su nan dai.
[38]
. Ga tarihihin asalin Hausawa ga mu nan, da sunan
Bayajida, da Ayana, da Bawo, da Kusugu, da Daurama, kuma duk akwai su a ha
ƙ
i
ƙ
anin
ga
s
kiya a
ƙ
unshiyar
tatsuniya sai dai
ƙ
ir
ƙ
irarrun sunaye.
[39]
. Wannan tatsuniyar wani malaminmu wanda ya yi muna Headmaster
Bunza
Town
Primary School (1973/74) mai suna Abubakar Balarabe Bagudo ya yi muna ita muna
aji 5.
[40]
. Jakadiyar Sarki ce, ta ji kiran Sarki, ta rugo aguje,
tana tsakar fada,ta laluba kai, babu duk
a
, ta cire ma
ɗ
auri ta
ɗ
ora a kai, ta bar
ƙ
asa da kallon kunya (ga ta tsirara).
[41]
. Na samu wannan labari daga bakin Alhaji Muhammadu
Modibbo Gangara a Shagon Alhaji Muhammadu Tel
a
Gwadabawa wajejen shekarar
(1987/88), a garin Sakkwato, Tashar Illela. Na sake jaddada shi 2023 ga
Muhammadu Tela.
[42]
. Wannan labarin na same shi a Sakkwato gidan Sheikh
Sidi Attahiru Ibrahim ga wani
ɗ
alibi na manta da sunansa a
wajajen (1985).
[43]
. Ai du
k
kanin taken biyu na Na
ɓ
agarawa Bun
s
uru Bawa ne, mai la
ƙ
abi “Makau”. A ciki
n
takensa da maka
ɗ
a
Gambo ya fasa kuka cewa, an kashe masa jarumi, sai aka fasa
mutuwa
,
gawar ya ce:
Jagora: Na lahe na ban mace ba
,
: Don kar jama’ar banza su cutan
,
: Ka dinga hwa
ɗ
in Allar tsare gaba
,
:
Wanga rutcin dai mun wuce shi.
[44]
. To haka baligi yake, ko namijin aure cikin budare
[45]
.
Don
ƙ
arin
bayani a dubi, Aliyu M. Bunza (2003) Hausa
Medicine Its Relevance and Developoiment in Hausa Studies. Pg.9.
[46]
. Daga cikin maha
ɗ
ai akwai, maha
ɗ
in zuciyar kaza komai irin wula
ƙ
ancin da aka yi wa mace, ba ta barin gidan miji. Akwai maha
ɗ
in fitsarin karya, budurwa ta bi saura
y
i kamar yadda kare ke bin uban
gidansa. Akwai maha
ɗ
in jijiyar kan kifi gawo (bo
ɗ
ami), na kashe wa maza mazakuta. Akwai maha
ɗ
in farin sa
ƙ
a
zuma, na tsayar da harda, ga su nan dai.
[47]
. Yadda kura take da waibuwa duka haka wanda ya yi
walki, da fatanta yake da waibuwa. Da mutane, da dabbobin gida, kowa zai sha
jinin jikinsa in ya gan shi. Ba ya
ɗ
aga kai ya yi ido hu
ɗ
u da kowa, kai, wane mutum. In ji mutuwa.
[48]
. Lokacin ina aji biyu
na
firamare 1970, wanda ya
ɗ
auke fatar sunansa Garban Awwal,
ɗ
a yake ga, Audu Gaba na Unguwar Lokon Jugan Biri
,
Bunza, yana da yaya mai suna Awwal wanda maka
ɗ
a
Ɗ
antalata Maiduma ya yi wa wa
ƙ
ar:
Jagora: Bi da kayan fa
ɗ
a ba aja masu
,
: Mu gai
da wan Garba mai maganin kura
.
Yara : Bi da kayan hwa
ɗ
a wa ka ja ma su
,
: Gai da wan Garba mai maganin kura.
[49]
. Wata hira da Farfesa Ibrahim Sarkin Sudan Abdullahi
Kwantagora, na Sashen Koyar da Harsunan
Nijeriya,
Jami’ar Usmanu
Ɗ
afodiyo Sakkwato, wajajen
shekarar (2000).
[50]
. Katta’u shi ne magani mujarrabi, sha yanzu, magani
yanzu.
[51]
. Mafarautan da, har cikin rumbu suke ajiye nama kamar
hatsi.
[52]
. Miyagun dabbobi suna gane warin naman
ɗ
an
’
uwans
u
, da na mushens
u
.
[53]
. Naramba
ɗa
a cikin “wa
ƙ
ar ya ci maza” ya ce:
Jagora: Ku ce wa biri
,
Yara : Duk dabarar da ac cikin daji
,
: Giwa taka biya
.
Gindi : Ya ci maza ya kwan shina shire
,
: Gamda’aren Sarkin Tudu Alu.
[54]
. A makarantar tatsuniya, zaki ne
sarkin dabbobi. Naramba
ɗ
a ya tabbatar da haka a cikin “wa
ƙ
ar Al
ƙ
ali
Shirinai da kyawo”
Jagora: Ana tahiya da
giwa da zaki
,
Yara: Su biyu
ɗ
in ga su ad da daji
,
Gindi: Al
ƙ
ali shirinai da kyawo
.
: Shi yai zaune daidai-wa-daida.
[55]
. Hausawa na yi ma
s
a kirari da Dila Sarkin wayo. An
ce, da wutsiya
y
ake shan ruwa in
y
a je kogi, domin ba
y
a
yarda da kowa ba, hatta da kurwar
t
a. Shi ya sa
y
ake tafiya cikin inwa wai kar kurwa
r
ta ya bi
shi
.
[56]
. Babu dabbar da ta kai cira hauka, ita ce Garba
Ɗ
anwasa Gummi ke siffantawa da wani tauraronsa yana
cewa:Jagora : Namijin cirza ba a kallonka
,
: Kana kallo
.
Gindi : Ya sa ‘yan maza gudu ba da la
ɓ
ewa ba.
Ita kuwa damisa kirarin ta shi
ne, “ba a damisa biyu ga wuri” yanzu
ɗ
aya
na zama mussa ko mussai.
[57]
. An fi samun su cikin adabin Kabawa mazauna fadama da
harkokin kamun kifi. A dubi, Naisru,
A.
(2002) “Adabin Hausa a zamanin Mulkin Mallaka Nazarin Ayyukan Frank Edger”,
kundin MA, Jami’ar Sakkwato
[58]
. Maka
ɗ
a Garba Maitandu Shinkafi ya yi
wa
j
aki wa
ƙ
a
ta musamman
,
sai a dubi, Rabi’u
H
.
Shinkafi
(2012) “Garba Maitandu da Wa
ƙ
o
ƙ
insa”, kundin MA, Jami’ar Sakkwato. Ai Naramba
ɗ
a karyarsa mai suna Ramba
ɗ
a
ya fara yi wa wa
ƙ
a da kirari, sai a dubi, Aliyu M.
Bunza (2009) Naramba
ɗ
a
, shafi na 14-15. Ra
ƙ
umi ba Bahaushen dabba ba ne, amma duk da haka an s
a
mu
masu yi musu kirari na musamman a
ƙ
asar
Arg
u
ngu, da Gwandu, da Binji, don
ƙ
arin bayani a dubi, Nasiru Aminu (2012) Nazarin Kirarin
Madugan Ra
ƙ
umai na Illon Geza, cikin
Ɗ
un
ɗ
aye Journal of Hausa Studies,
Vol. 1, No. 4,
shafi 158-174.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.