Ticker

6/recent/ticker-posts

Farin cikin Musulmin Duniya, Mai martaba na Abubakar, Ci fansa Alhaji Maccido (Wakar Makada Sa'idu Faru)

Farin cikin Musulmin Duniya, Mai martaba na Abubakar, Ci fansa Alhaji Maccido (Wakar Makada Sa'idu Faru)

Jagora:

Majalisad' ɗunkin duniya

Majalisad' ɗunkin duniya

Tayi ododi ga manoma

A riƙa aiki ag gaskiya

A aje abinci ag  gaskiya,

A tarda gero,

A tarda dawa,

A saida gujjiya,

A saida kaɗa,

A aje gero so nai mukai, 

Babban abun Nanjeriya,

Kan dawo in yash sha nono,

Ko Bature kab bashi

bashi girgizawa amsa yakai,

Ko da yash sha..


Jagora /Y/Amshi :

Sai kaji ya ɗwad'wa Ingilishi,

Kai nai ya hwashe da yat tamni tcakin dawo,

Asha hura ayi wasa,

D/Tumba shan hura ba lahani ba ne,


Jagora /Y/Amshi :

Asha hura ayi wasa,

D/Tumba shan hura ba lahani ba ne,

Farin cikin Musulmin Duniya,

Mai martaba na Abubakar, 

Ci fansa Alhaji Macciɗo

Ɗiyan Waƙa ne daga cikin Waƙar Makaɗa Sa'idu Faru ta Marigayi Mai Alfarma Sarkin Kudun Sakkwato /Sarkin Musulmi Muhammadu Bello Macciɗo Abubakar III mai gindi "Farin cikin Musulmin Duniya, Mai martaba na Abubakar, Ci fansa Alhaji Macciɗo". Allah ya kyauta makwanci, amin.

Daga Taskar:
Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

Post a Comment

0 Comments