Idan ba gidan mijinki ba, ta ina za a bar ki da kaza sukutum a ɗaki, da guda kuma a kitchen? A gida kina yin hanyar kitchen za a biyo ki.
Lokacin da nake yaro, na yi zaton duk wani mai ƙaton ciki yana da kuɗi.🤦♂️
Lokacin da nake yaro, na yi zaton ko'ina mutum ya je da dare wata bin sa yake yi. Sai da na ƙara wayo na gane cewa ashe kowane lungu suna da watansu.🤔🌙
Na je gidan abokina, matarsa ta ce ga shi kuwa ba ta gama abinci ba. Na ce: "Mu da muka jira kuɗin NPOWER ma ballantana girki..." Na nemi wuri na zauna.🥳🥳
Sometimes, we men want to stay with one woman, but when we see another woman without a man, it hurts us.😍🥳
Duniya ta lalace! Yanzu maganin ɓera ma ana yin jabu.😨 Duk wanda zai sayi magani ɓera, to ya buɗe ya ɗanɗana tukuna. Mai kyau ɗin yana da gishiri-gishiri.
Idan ba ka da kuɗi, ko 'yar danginku ka ce kana so sai dai ka ji ana cewa: "Shi zuciya, ita zuciya, ai zamansu ba zai yiwu ba!"😢🙄
Kana nan kana kallon ƙanuwarka a matsayin marar wayo. Wani kuma yana can ya kasa bacci saboda ita. 🤭🤭
Ta kai ziyara gidan su saurayinta. Tana zaune a falo ta jiyo muryar ƙannensa a kitchen suna magana ƙasa-ƙasa: "Kin ga goshinta?" 🤭🤭
To chop woman money, you have to be either fake pastor or native doctor or you dey cure infection.🤪
Cin kuɗin mata abu ne mai sauƙi. Kawai ka fara sayar da maganin mallakar miji.🕺
Ana cikin yanayi a ƙasar nan. An gama sallar isha'i liman ya ce "assalamu alaikum." Ladan ya ce "wa'alaikumussalam."😅😅
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.