𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Salem Allah gafarta Mallam, kwanaki ina ta neman aiki ban
samu ba, sai nayi ta addu'a har nayi bakace cewa idan Allah ya bani aikin nan
nayi alkawarin zan yi sadakan naira dubu ashirin daga cikin albashina na farko
ga masu tsananin bukata. Sai kuma rannan da aka biya salary nayi hatsari da
motata kuma gyaranta zai ci kuɗi
da yawa, sannan kuma ga bukatan iyaye da Iyali.
Tambaya na anan shi ne
1. Zan iya jinkirta wannan sadakan da na yiwa Allah alkawari
zuwa wata Mai zuwa idan aka biya albashin?
2. zan iya bawa wani sadaqan cikin dangi na mubakata ko kuma
dole ne sai wasu awaje.
Wallahi banaso in butulci in karya alkawari da nayiwa Allah
SWT. Nagode
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.
Shi yin bakance halal ne a addinin Musulunci. Shi ne duk
wani alkawarin da mutum zai daukar wa kansa na yin wata ibada ta musamman bisa
sharadin cikar wata bukata tasa. Kuma idan har wannan bukatar tasa ta yiwu, to
fa wajibi ne akansa sai ya aikata abinda yayi wa Allah alkawarin akansa.
Allah Madaukakin Sarki yace
وَمَا
أَنفَقْتُم مِّن نَّفَقَةٍ أَوْ نَذَرْتُم مِّن نَّذْرٍ فَإِنَّ اللَّهَ يَعْلَمُهُ
وَمَا لِلظَّالِمِينَ مِنْ أَنصَارٍ
Kuma abin da kuka ciyar daga ciyarwa, ko kuka cika alwashi
daga wani bakance, to, lalle ne, Allah Yana sanin sa. Kuma azzalumai ba su da
wasu mataimaka. (Suratul Baqarah ayah ta 270).
Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya ce: "Wanda
yayi bakancen zai aikata wani aikin bin Allah, to lallai ya bishi. Wanda kuwa
yayi bakancen saɓa
wa Allah, to kar ya saɓeshi".
(Bukhariy da Muslim ne suka ruwaitoshi daga Nana A'ishah
r.a.).
Don haka tunda har Allah ya biya maka bukatarka, to wajibi
ne kai kuma ka nuna masa godiyarka ta hanyar aikata abinda kayi alkawari akanka
tunda kana da ikon yin hakan. Amma Qin cika alkawarin daga ɓangarenka zai iya zama
laifi ko kuma rashin ladabi ga Ubangiji (SWT).
Shawarar da zan baka anan ita ce idan har yin sadakar 20,000
ɗin nan ba zai janyo
afkuwar yunwa ko rashin abinci ga iyayenka da iyalanka ba, to kada ka
jinkirtashi. Amma idan yin hakan zai janyo tozartar da hakkokin mahaifa ko
iyalanka, to ka iya jinkirtawa zuwa wani watan mai zuwa in sha Allahu.
WALLAHU A'ALAM.
DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayaDaAnsa
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.