Ticker

6/recent/ticker-posts

Wazirin Kwangilar Lardin Arewa

Wazirin Kwangilar Lardin Arewa

A cikin shekarar 1905 ne aka haife shi a wani gari da Mahaifinsa ya ƙirƙira da ake kira Tattije dake cikin Ƙaramar Hukumar Mulkin Zaki mai hedikwata a Katagum ta Jihar Bauchi. Sunan Mahaifinsa Malam Adamu Ɗanjuma wanda tsatso ne daga zuriyar Arɗo Muniru na Shuni , wato Ɗan Majalisar  masu zaɓen Mai Alfarma Sarkin Musulmi tun zamanin mulkin Amirul Muminina Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi da ya yi mulki daga shekarar 1817 zuwa shekarar 1837. Malam Adamu Ɗanjuma ya bar gida Shuni ta Ƙaramar Hukumar Mulkin Dange /Shuni a Jihar Sakkwato ta yau sanadiyar rikicin siyasar sarauta ta cikin gida. Ya miƙa ya zuwa Ƙasar Katagum ta Jihar Bauchi ta yanzu, ya ƙirƙiri wannan gari mai suna Tattije, anan kuma ya haifi 'yaya/ɗiya 7, Maza 3, Mata 4 ciki kuwa har da wannan Bawan Allah da muke magana akai. Yanzu daga cikin zuriyar Malam Adamu Ɗanjuma ɗin ne ke Sarautar wannan Ƙauye na Tattije.

Bawan Allah da muke magana akai, ɗan Malam Adamu Ɗanjuma ya fara karatun Allo tun ya na ɗan ƙaraminsa a nan Tattije da Azare tare da sana'ar goro bayan ya ɗan tasa. Ya shiga neman ilimin Addinin Musulunci bayan ya sauke Al'kur'ani mai tsarki, fagen da ya ɗauke shi zuwa Maiduguri da Yola da Jalingo da Damaturu da Kano. Ya dawo da zama Sakkwato inda ya ci gaba da sha'anin kasuwancin siye da siyar da Gyad'a da Fata, a daidai wannan lokacin ne kuma suka ƙulla aminci shi da Marigayi Mai Alfarma Sarkin Musulmi Abubakar III, Allah ya jaddada masa rahama, amin.

Ya baro Sakkwato zuwa Gusau a cikin 1940s inda ya sayi gidansa dake tsakanin Tsohuwar Kasuwa da Tsohuwar Tasha ( inda aka yi Shatale - talen  Bello Bara'u /Bello Bara'u Round about, bakin Gidan Man Total) akan kuɗi Sule Goma Sha Shida/16 Shillings. Ya ci gaba da sabgar kasuwancin Auduga da Gyad'a kafin daga baya ya shiga sha'anin kwangila inda ya fara sabgar da siyen Jakuna /Jakkai fiye da 100 da ya yi amfani dasu wajen ɗauko yashi da dutsi da sauran kayayyakin aiki kafin daga baya ya fara amfani da Amalanke/Kura ya zuwa Mota Kitika. Shi da Marigayi Sarkin Fawan Gusau Alhaji Ibrahim aka baiwa kwangilar ginin Tsohuwar Kasuwar Gusau, aikin da suka kammala a cikin shekarar 1958. Ya na cikin manyan 'yan kwangilar da suka yi aikin gina Kwalejin Sarkin Musulmi Abubakar dake Sakkwato /Sultan Abubakar College, Sakkwato. Shi ne ya yi kwangilar shimfid'a titin ɓurji na farko da ya tashi daga garin Kwatarkwashi zuwa Mada. Ya na daga cikin 'yan kwangilar da suka yi aikin ginin Tsohon Gidan Yarin Gusau dake Unguwar Tudun Wada, Gusau ya kuma samu shiga cikin masu ciyar da ' Yan Gidan Yari tun kafin a fara yin irin wannan aiki ta hanyar buga Tanda/Tender. Ya ɓullo da shirin Karatun Al'kur'ani da Sadaka a gidansa, dalilin da yasa ma ake kiran gidan nasa da "Gidan Almajirai". Firimiyan Tsohuwar Jihar Arewa, Sir Ahmadu Bello, GCON, KBE, Sardaunan Sakkwato ya ba shi muƙamin "Wazirin Kwangilar Lardin Arewa". 

Allah SWT ya karɓi rayuwarsa ranar 21/07/1994. Ya bar zuriya mai dama ciki kuwa har da 'yaya /ɗiya 18, 7 Maza, 11 Mata. Allah ya jiƙan Marigayi Alhaji Adamu Ɗankwagila Gusau shi da sauran magabatanmu, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin. 

Daga Taskar:
Malam Ibrahim Muhammad Birnin Magaji
Ɗanmadamin Birnin Magaji
Imel: birninbagaji4040@gmail.com
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815 

Post a Comment

0 Comments