A yankin Tsohuwar Jihar Sakkwato musamman Jihohin Sakkwato da Kabi da Zamfara na yanzu a kan kira mai suna Ibrahim da laƙabin "Maigandi /Mai Gandi" domin tunawa da Malam Ibrahim ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello ɗan Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodio tagammadahullah birahamatihi da ya fara Sarautar Garin Gandi dake cikin Ƙaramar Hukumar Mulkin Raɓah ta Jihar Sakkwato ta yau, bayan masu jihadin jaddada addinin musulunci na Daular Usmaniya sun samar da garin na Gandi a matsayin Ribaɗi. Bayan an kai Malam Ibrahim ɗan Sarkin Musulmi Muhammadu Bello a wannan gari ne dalilin da ya sa aka mayar dashi "Mai Gandi" wato wanda ke da Garin Gandi a matsayinsa na Sarkin Garin kuma wannan shi ne dalilin ya zuwa yau a wannan yanki da aka ambata a sama ke kiran mai suna Ibrahim da wannan laƙabi na "Mai Gandi".
Bayan Marigayi Ɗangaladiman Shinkafi, Malam Ibrahim ya
zamo Dagacin Shinkafi da laƙabin Magaji a shekarar 1950, Makaɗa Alhaji (Dr.) Ibrahim Buhari Abdulƙadir
Mai Dangwale Narambaɗa
Tubali ya yi masa Waƙoƙin da suka shahara cikin su kuwa har da wata mai amshi
"Ibrahimu Na Guraguri, Mai Shinkahi Bajinin Zagi mu dai Allah ya bam muna
kayaa".
Ya haɗa
shi da wani ɗan uwansa
/aminin sa ne da ake kira Jibril/Jibrin dake
riƙe
da wata sarauta da ake kira "Guraguri" anan Shinkafi a cikin wannan
Waƙar
inda yake cewa "Ibrahimu Na Guraguri". Sannu a hankali sai wannan haɗin sunan ya zamo laƙabin
gama-gari ga kusan dukan wani mai suna Ibrahim musamman a yankin Zamfara.
Ma'ana daga nan ne sai aka samar da laƙabin "Na Guraguri" ga mai suna
Ibrahim. Magajin Shinkafi Ibrahim ya yi Sarautar Shinkafi daga shekarar 1950
zuwa wafatin shi a shekarar 1990.
Zuriyar Malam Muhamman Ballo ne, jagoran wasu Fulani da suka
fito daga Ƙasar
Gwandu ta Jihar Kebbi ta yau, suka samar da Ƙasar Shinkafi, farko da hedikwata a garin
Badarawa a shekarar 1835 da laƙabin Sarautar Magaji.
Magaji Malam Muhamman Ballo wanda shi ne Sarkin su na farko
ya shekara goma ya na sarauta, kenan daga shekarar 1835 zuwa 1845 lokacin da
Allah ya masa wafati. Bayan wafatin sa Sarakunan da suka biyo bayansa sun ci
gaba da sarauta a Badarawa har ya zuwa mulkin Magaji Ahmadu Lamiɗo wanda ya yi Sarauta daga
1930s zuwa rasuwarsa a shekarar 1950.
A lokacin mulkin sa ne ya dawo da hedikwatar Kasar a
garin Shinkafi daga Badarawa ta hanyar
kasa sati kashi biyu na zamansa
tsakanin Badarawa da Shinkafi,
daga baya ya baro Badarawa zuwa Shinkafin.
A halin yanzu Fadar Masarautar wacce ta samu ɗaukaka daga Ƙasar
Dagaci zuwa Sarki mai daraja ta biyu a Jihar Zamfara da laƙabin
Sarkin Gabas ( ana kyautata wannan laƙabi na Sarkin Gabas baya rasa nasaba da
tushen waɗan da suka ƙirƙiri
Kasar ta hannun Malam Muhamman Ballo, Magaji Mai Badarawa /Magajin Badarawa na
farko da ya jagoranto su daga Gwandu, domin laƙabin Sarautar ko Hakimcin Gwandu
/Gundumar Gwandu/Uban Ƙasar Gwandu dake sarauta a garin na Gwandu, a Masarautar
Gwandu mai hedikwata a Birnin Kebbi, Babban Birnin Jihar Kebbi shi ne
"Sarkin Gabas na Gwandu") na nan a Garin Shinkafi.
Allah ya jiƙan magabatanmu da rahama, ya sa mu wanye lafiya, mu cika da kyau da imani, amin.
Lambar Waya: 08149388452, 08027484815
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.