Ticker

6/recent/ticker-posts

Nau'ukan Kunu Da Yadda Ake Sarrafa Su (Kunun Koko, Kunun Zogale, Kunun Alkama, Kunun Acca, Kunun Gyada)

Gabatarwa

A babi na goma sha biyar (15) an kawo bayanai kan kunun gargajiya da nau’o’insa. Akwai nau’o’in kunu da dama da ba su sauya ba har ya zuwa yau; sakamakon ‘yan bambance-bambancen da ake samu ba su taka kara sun karya ba. Misali, kunun gero da ake kira kunun tsaki, yana nan yadda aka san shi a gargajiyance. Sai dai a yau ana iya sanya masa wasu nau’ukan kayan ƙamshi da babu su a gargajiyance. A wannan babi, za a iya lura da cewa, ba a kawo wasu daga cikin nau’o’in kunun da ake samu yau a ƙasar Hausa ba. An yi haka ne domin guje wa maimaicin nau’o’in kunun da aka tattauna a ƙarƙashin babi na goma sha biyar.

Kunun Kamu (Kunun Koko)

i. Barkono (tonka) 

ii. Citta  

iii. Gero 

 iv. Kanunfari

v. Kimba   

vi. Madara 

vii. Ruwa  

viii. Suga

Yayin samar da kunun kamu (kunun koko), akan surfe gero a bushe a wanke (wani lokaci ma akan haɗa geron da masara kaɗan). Za a jiƙa wannan gero kuma a bar shi har sai ya kwana, sannan sai a kai markaɗe bayan an sanya masa kayan yaji nau’in barkono da citta da kanamfari da sauransu. Bayan an dawo da shi daga markaɗe, za a ƙara masa ruwa, sannan a yi amfani da matata a tace shi sarai, sannan sai a ajiye shi domin ya kwanta.

Bayan ya kwanta, za a samu abin da ake kira kamu; fari mai laushi. Da wannan kamu ne ake dama kunu. Hanyar da ake bi domin dama shi daidai yake da wanda aka yi bayani a sama.

 Kunun Zogale

i. Gero

ii. Kayan yaji

iii. Ruwa

iv. Zogale

Wannan kunun yana kama da sauran kunu da aka yi bayanin su sama. Bambancin shi ne, yayin tafasa ruwan kunun, ana sanya zogale a tafasa su tare. Sannan ana iya sanya zogalen cikin gero yayin da za a kai niƙan gumba, wato dai a niƙo su tare. Wannan nau’i na kunu na kasancewa ɗauke da ƙamshi da kuma ɗanɗanon zogale. Masana na ba da shawarar amfani da shi domin taimakon da zogale ke yi ga lafiyar ɗan Adam.

Kunun Alkama

i. Alkama  

ii. Aya  

iii. Citta

iv. Kanamfari  

v. Madara 

vi. Masoro

vii. Nono  

viii. Ruwa  

ix. Suga 

x. Zuma

Da farko, za a surfe alkama a wanke ta sannan a shanya. Kafin a kai niƙa, za a ɗebi wani adadi na alkamar a jiye gefe guda (amma ajiyewar ba dole ba ne). A ɓangare ɗaya kuma, za a ɗauko aya a wanke a shanya. Bayan duka sun bushe, sai a haɗa alkamar da ayar sannan a kai niƙa. Bayan an dawo da su daga niƙa, za a tankaɗe, sannan a ƙwaɓa garin da ruwan sanyi. Daga nan za a tafasa ruwa sai a sanya cikin wannan gumba. Za a iya sanya masa lemon tsami da suga da madara.

Idan har an ajiye ragowar alkama kafin a kai niƙa, to za a sanya ruwa cikin tukunya daidai gwargwado sai a sanya tsakin tankaɗen da aka yi. Za a yi ta gaurayawa bisa wuta har sai ya haɗe ya yi kauri. Bayan an sauƙe sai a sanya ragowar alkama da aka adana ciki sannan a mayar da su cikin tukunya a yi ta juyawa. Akan zuba shi cikin kunun bayan an dama.

Kunun Zaki

i. Dankali  

ii. Gero   

iii. Kayan ƙamshi

iv. Kwakwa 

 v. Lemon tsami 

vi. Ruwa   

vii. Suga

Kunun zaƙi na kama da kunun koko ta fuskar yadda ake sarrafa su, sai dai sun ɗan bambanta. Yayin samar da kunun zaƙi, ba a ajiye tataccen markaɗe domin ya zama kamu. A maimakon haka, da zarar an tace, sai a ɗebi wani adadi a matsayin gasara a ajiye gefe guda. Sauran kuwa za a zuba musu ruwan zafi kamar dai yadda ake kunun koko. Yanayinsa zai kasance da ruwa-ruwa amma ba kamar na kunun koko ba. Yayin da aka zuba wannan gasara a ciki (wadda ita ma tana da yawa), sai ya dawo ruwa-ruwa sosai.

Kunun Acca

i. Acca

ii. Ruwa

iii. Suga

iv. Tsamiya

Shi ma kunun acca na kama da sauran nau’o’in kunu da aka yi bayani a sama. Bambancin kawai shi ne, bayan an dawo da niƙan accar an tankaɗe, to ana ƙwaɓa garin ne da ruwan tsamiya. Da ma dai ita acca ba a surfe ta. Ana wanke ta ne kawai a shanya kafin a kai niƙa.

Kunun Gyaɗa

i. Gyaɗ

ii. Kayan ƙamshi 

iii. Lemon tsami

iv. Madara 

v. Ruwa  

vi. Shinkafa  

vii. Suga

Da farko, akan gyara gyaɗa sannan a jiƙa ta. A gefe guda kuma, za a wanke shinkafa kaɗan (amma za a yi la’akari da adadin gyaɗar da yawan kunun da ake son yi) ita ma sai a jiƙa ta. Bayan sun jiƙa, za a haɗa su a kai markaɗe. Za a sanya kayan ƙamshi kafin a kai niƙa. Da zarar an dawo da shi daga markaɗen, sai a yi amfani da matata domin tacewa. Bayan an tace, sai batun damawa da ruwan zafi. Ba dole ne a tanadi gasara ba a wannan nau’i na kunu. Idan an kammala dama kunun, ana iya sanya masa lemon tsami da madara. Suga kuwa da ma, “farilla ne tusar mai bacci.”

Kammalawa

Duk da cewa Bahaushe na da salon maganar da ya gina labari da shi da ke faɗin: “Kunu abincin mutane uku ne; da tsoho da yaro da marar lafiya,” a nan za mu ce wannan labarin ƙanzon kurege ne. Dalili kuwa shi ne, kunu nau’i ne na abin sha da ake ta’ammuli da shi sosai a ƙasar Hausa. Za a tabbatar da haka ko ta la’akari da nau’o’in kunu daban-daban da aka tattauna a sama, waɗanda kuma duka akan same su a ƙasar Hausa. 

Citation (Manazartar Littafin):  Sani, A-U. & Umar, H.A. (2022). Cimakar Hausawa. Kano: WT Press. ISBN: 978-978-984-562-9.

Get a copy:
To obtain a copy of this book, kindly send a WhatsApp message to:
+2348133529736

You can also write an email to:

Post a Comment

0 Comments