Matsalar Sakai A Karni Na Ashirin Da Daya

    Takardar ƙara wa juna sani da aka gabatar a ajin ALH 400: Seminars, a Sashen Nazarin Harsuna Da Aladu, Jamiar Tarayya Gusau, Nijeriya, (2022/2023 Academic Session).

    Federal University Gusau (FUG) Nigeria

    Matsalar Sakai A Karni Na Ashirin Da Daya

    NA

    Suna: Sani Tijjani
    Imel: sanitijjani8890@gmail.com
    Lambar waya: 09030478889

    Tsakure

    Manufar wannan bincike itace nazarin kwakwkwafi domin gano matsalar dake ƙunshe cikin sanaar sakai a ƙarni na ashirin da ɗaya. An yi amfani fa dabarun sanya ido da nazarta kundayen rubuce-rubuce domin tattara bayanai, an dora aikin kan fahimtar Hausawa ta “iya ruwa fidda kai” sakamakon binciken ya gano cewa, matsalar dake a kwai a kan masu sana’ar sakai tun ƙarnin daya wuce na can baya na tauye mudu ta na nan har yanzu bata wuce ba, sai dai binciken ya gano jirwayen tauye mudu da kuma waɗansu dabaru na tauye mudu kari bisa ga nada.

    1.1 Gabatarwa

    Sakai wato kasuwancin hatsi na saye da siyarwa sana’ace daɗaɗɗiya wacce ta ginu tun lokacin annabawa ana saye da sayarwa, saye da sayarwa san’ace mai dogon tarihi,

    Kuma tun lokacin akwai waɗansu matsaloli dake akwai a wajen masu gudanar da wannan san’ar na tauye mudu da kuma na ha’inci da rashin cika alƙawari ammafa a wajen wasu to wannan matsalar har yanzu tana nan tana cigana da wanzuwa. Binciken zai ganomana matsalolin da ke akwai a can da da kuma ƙarin matsalolin da anka samu kari ga na da da kuma waɗansu hanyoyi da za’a bi domin magance matsalar.

    1.1 Dabarun gudanar da bincike

    Wannan bincike ne da keda tsurar bayanai (qualitative form of research). An yi amfani da lura (observation) a matsayin babbar hanyar tattara bayanai tun daga tushe na farko (primary source), zuwa Babbar hanyar tattara bayanai ta biyu (Secondry Source), da akayi amfani da ita ita bibiyar rubuce -rubuce ce musamman kundaye.

    Bayan haka an yi mafani da irin (interview) a matsayin hanyar tabbatar da ingancin bayanai an samu bayanai game da wadansu halaye na masu gudanar da san’ar sakai, wadanda suka shafi tauye mudu da damfara a cikin sana’ar da kuma wasu hanyoyin da ake bi domin ayi wa mutum damfarar, an samu Karin bayanai daga masu gudanar da sana’ar

    1.2 Ma’anar sakai

    Sakai na nufin saye da sayarwa na dangin hatsi, idan an kace dangin hatsi ana nufin duk wani abu dake da alaka na awo da sikeli ko na ma’aunin awo (ajiya) masu wannan san’ar duk ana kiransu musa sana’ar sakai, amma a wajen wasu Kalmar sakai ta takaita ne kawai ga masu sana’ar

     Dawa

     Gero

     Masara

     Shinkafa

     Maiwa

    Da dai duk wasu nau’in kayan buƙata na rayuwa waɗada aka sarrawa a matsayin abinci amma ban da kayan cikin kwali da masu kama dasu,

    wannan itace tshohuwar ma’anar sakai yanzu sakai na nufin duk wani abu da za’a saye a sayar dangin hatsi da ma wanda anka sarrafa a injin saboda zuwan zamani anka sanya shi cikin kwali ko kuma gwangwani an ka yi roll dinsa cikin leda to, wadansu ma daga cikin wadannan suna shiga cikin nau’in sakia kamar garin rogo da sauransu.

    2.1 Bunƙasa sanaar sakai a karni na ashirin da daya

    Sakai ya bunkasa ne a karni na ashirin da daya sakamakon samun yawan bakin al’umma da suke kara shigowa a kasar Hausa, haduwa da bakin al’ummane ya sa kasuwancin sakai ya sauya ta hanyar samun cigaba da kuma koma baya a wadansu bangarori.

    Wadannan matsalolin guda biyu zamu dubesu kuma mu tatatauna a akai duba da zamaninmu.

    2.2 Cigaban da aka samu a sana’ar sakai a ayau

    Ansamu cigaba ta fannoni daban-daban waɗaa suka hada da p. o. S wato Kalmar p.o.s tana nufin (“point of sell”) wadda ake gudanarwa ta mashin mai aiki da ƙwaƙwalwa,

    hanyace ta tura kudi nan take (money transfer) da kuma (mobile transfer) domin yin sayeda da sayarwa a gun masu sana’ar sakai, wannan cigabane mai girman gaske wanda ya haifar da saukin saye da sayarwa tsakanin al’umma, kuma yana bayar da kariya ga kilace dukiya ga rashin salwanta na zubewa ƙudi ko kuma sacewa a hannun ɓarayi,

    sannan kuma hakan ya samar da sirri na ba a iya gano nawa ne mutum ke da su hakan ya taimaka wajen bayar da kariya da tsaro.

    3.0 Rashin cigaban da aka samu

    An samu rashin cigaba ta danfara da zalunci da suka shigo ta waɗannan hanyoyin ada babu wata hanya da za’a cuci mutum wajen sayen kayansa in har ba kwacewa ankayi gun mai sana’ar ba sai dai in danfara ta hanyar bani kayanka inje can in kawo maka kudinka,

    Kuma waɗannan hanyoyin da wuya a damfari mutum ta hanyar amafani dasu saboda kowa yasansu . duba da wannan zamani da muke ciki sai anka shigo da danfara ta hanyoyin sadarwa wato (transfer) za’a tura ma mutum kudi na bugi wanda a hanzu akafi sani da (fake alert) mutum zai ga shigowar ƙudin amma idan ya duba asusunsa na banki ba zaiga komaiba wannan shi ake kira da fake alert,

    ana damfarar mutane da yawa ta wannan hanyar shi kuma mai kayan ya bayarda kayansa ba lallene ya gane cewa transfer din karya ce ankayi mashi ba, masu sana’ar sakai da dama sun rushe ko ince sun kare a wannan hanya ta transfer din bugi wannan rashin cigabane a wannan hauji.

    3.1 Matsalar yan sakai

    Sakai sunan sana’ar ne masu su kuma masu yin sana’ar sune ake kirada yan sakai, idan akace yen sakai ana nufin jam’in masu sana’ar sune yen sakai dan kasuwa guda da yake sana’ar shi kuma ana kiransa da "dan sakai" babbar matsalarsu shi ne tauye mudu wajen kai mai kaya in ka kawo masu su saye suna amfani da mudunsu su yi ma wani awo wanda su ka kema laƙabi da cewa (wawan birni) shi wannan wani nauin awo ne da sukeyi wanda yin wannan awon kan iyasa kayanka daga tiya goma su dawo tiya takwas ko tara .

    I dan kai kuma zasu auna maka da tiyarsu yar karama ta yadda zaka iya siyen tiya biyar amma idan kaje gida ka auna kaga ta dawo tiya hudu wannan kuma dadaddar matsala ce tun zamanin da can baya ana fama da wannan matssalr kuma har yanzu ba’a magance ta ba.

    3.2 Magance algussu a san’ar sakai

    A wajen masu yin sana’ar sakai yanada kyau masu gudanar da ita su san cewa haramunne tauye mudu wajen saye sannan kuma haramunne tauye mudu wajen sayarwa, sannna kuma duk rashin tsare gaskiya shi ne yak e kawo masu bala’o’a a cikin sana’arsu , sais hi kuma bangaren mai saye ya sanya ido sosai wajen sayen domin kada ayi mai mugun awo in yaga an yi mai mugun awon da shi idan yaje saye bah aka ake mai ba to yanada damar da zaice shi bai yarda da awonda akayi mai ba a bari ya auna da kansa.

    3.3 Tasirin zama a cikin sana’ar

    A da can baya sai an yi amfani da raƙumma ko jakuna ko amalanke yayin ɗuko kaya amma yanzu a wannin zamani da muke ciki tasirin zamani yana taka rawa wajen sana’ar ta hanyar sauƙaƙa saukin fatauci,

    ya zamana ana amfani da

    • Motoci

    • Masuna

    • Jiragen sama

    da kuma jiragen ƙasa

    Kai harma da jiragen ruwa na zamani

    Hakan ya kawo canji sosai a harkar sakai wajen sufuri yanzu za’ayi saurin kawowa dan kasuwa kayansa daga inda yasiya har zuwa inda yake ba ma wannan kadaiba wannan haryan tana kara taimakawa wajen shigo da kaya da yawa da kuma sauri fiye da dabbobi, tafiyar da dabba zatayi cikin kwana goma jirgi zai iya yenta cikin awa biyu.

    Cigaba ta fuskar tsaro

    Ansamu cigaba ta fuskar tsaro ya yin yin fatauci wanda a can da ana tafiya bisan dabbobi wajen dauko kaya ko sayarda su, a hanya za’a iya haduwa da barayin hanya ko na daji suyi awon gaba da dukiya ko kuma su kasha mai dukiyar amma zuwan zamani da ake amfani da jiragen sama an samu kariya daga barazanar barayi domin gujewa salwantar rai da ma ta dukiya.

    Haka zalika ansamu cigaba a wajen lafiya domin a can baya kafin mutum ya kai wajen fataucin zai sha rana da zafi da kuma san yi ga kuma dukan ruwan sama kasancewar saman yawanci saman rakummai ne ko wata dabba ake tafiya akai kasancewar zuwan zamani ansamu cigaba sosai ta wannan bangaren mutun ba ruwansa da zafin rana ko dukan ruwan sama.

    4.0 Sakamakon bincike

    lamarin sakai lamarine da mun kaga yadda al’umma ke aiwatar dashi a da da kuma yadda ake ai water dashi a yanzu munga irin cigaban da zamani yakawo da kuma nakasun hakan.

    Sakamakon bincike bai tsaya iya nan ba ya nuna muna sana’ar sakai sana’ace wadda take saurin kawo kudi da kuma saukin gudanarwa musammman a irin wannan zamani da muke ciki.

    Amma kuma idan mutum baiyi taka tsantsaba takan iya jefashi a halaka, haka kuma sana’ace wadda take tafiya dai dai da zamani sana’ace wadda takeda wayewa a cikinta kwarai da gaske kasancewar tana daya daga cikin manya manyan kasuwanci na duniya baki daya, hakan ya sa binciken ya tafi sosai wajen ganin an samo sakamakon bincike domin duk biciken da baida sakamako to bai zamo cikakke ko kamamalallen bincike ba

    5.0 Kammalawa

    sakamakon wannnan bimnciken ya ci karo da has ashen dabinciken yayi tun farko Hasashen daanka gina bias ganin an magance matsalar tauye mudu a harkar sakai. Akwai bukatar gudanar da binciken da zai tabbatar da dalililn da yassa wadansu mutane cigba da tauye mudu a harkarsu ta sakai. A gefe guda a kwai bukatar malamai su sa ido sosai sannan kuma su cigaba da fadakarwa kan matsalar da take cikin tauye ma’auni, sannan su fadi irin tanadin da Allah (s.a.w) yayi ma duk wanda yake irin wannan na azaba.

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.