Ticker

6/recent/ticker-posts

Saukowar Allah Zuwa Saman Duniya A Karshen Dare

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum mallam kwanaki na ji wani malami yana  bayani akan saukan Allah saman farko a karshen dare ko wani rana don amsa rokon bayinsa, amma sai mutumin ya karyata hadisin, yana mai cewa wai kowace kasa lokutan su daban wasu sai gari ya waye agun su tukunna mu daren mu yake rabawa, to ta yaya za ace Allah na sauka sulusi na karshe, kodai yana sauka a kowace kasa ne, in ji shi, haka ya yi wasa da hankulan mutane har kusan zan ce ni ma na kusa fadawa, Allah Ya kiyaye.

Ina neman ko mallam zai yi sharhi akan wannan zance, koda Allah zai sa zuciyata ta samu nutsuwa. Allah ya saka da Alkhairi.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum salam, Matsalar da mutumin ya samu shi ne ya kwantanta Allah da bayinsa ne, shi yasa ya kasa fahimtar hadisin.

Duk wanda ya yarda cewa Allah ba ya kama da komai, kuma babu abin da ya yi kama da shi, wannan zai sa ya fahimci SIffofin Allah da kyau, ya kuma yi imani da su ko da kuwa sun zarta tunaninsa.

Har a tsakanin bayi ana samun fifiko a sIffofi  da saurin zartar da lamura, saurin Aljani ba daidai yake da saurin mutum ba, karfin Zaki ba ya daidai da karfin akuya, balle kuma tsakanin bayi da mahaliccinsu, wanda ba sa kamanceceniya  da shi ta kowacce fuska.

Hadisin saukowar Allah zuwa saman duniya, hadisi ne ingantacce, mutawatiri, sama da sahabbai ashirin (20) suka rawaito shi daga Manzon tsira, duka manyan kundayan hadisi guda tara (9), sun ambaci hadisin daga sahabi Abuhurairah.

Bisa abin da ya gabata ya wajaba kowanne Musulmi ya yarda cewa, Allah Yana saukowa a karshen kowanne dare saukowar da ta dace da mulkinsa da katafaren ikonsa,

Irin wadannan siffofin wadanda suke nuna girman Allah da rashin kamanceceniyarsa da bayi, suna da yawa a cikin hadisai, a ranar Alkiyama Allah zai sanya sammai guda bakwai a dan'yatsansa guda ɗaya.

Allah ne mafi sani.

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments