𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum. Malam don
ALLAH, me Malamai suka ce a kan Transliteration na Al-Qur’an?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul
Laah.
Abin da na sani dai shi ne
(i) Sahihiyar hanyar koyon
Alqur’ani ba shi ne ɗalibi
ya zauna a gaban malami ya biya masa, shi kuma ya ɗauka baki da baki ba?
(ii) Maimakon a tsaya koyo da
koyar da Alqur’anin ta transliteration da haruffan boko din, domin wai a
taimaka wa wanda ba ya gane haruffa larabci, ba gara ya zauna a koya masa da
larabcin kawai ba?
(iii) Haruffan Larabci kamar
harafin: (خ) da (ص) da (ض) da (ط) da (ظ) da (ع) da (غ) da (ق) da makamantansu ba su
da waɗanda suka yi
daidai da su a cikin haruffan boko. Idan aka je transliteration dole sai an yi
bayani yadda ake furta su a larabci, a yi ƙoƙarin haɗa
su waɗansu alamu ko
haruffan boko domin su zama kusa da yadda ake furta su a larabci. To idan kuwa
har mutum zai tsaya ya koyi duk wannan, me ya sa ba zai tsaya a koya masa na
asalin ba kawai?
(iv) A mafi rinjayen fahimtata,
mutane ne suka ƙare rayukansu wurin koyon boko zalla har sai da suka girmama
suka tasamma tsufa, ba tare da sun iya karatun larabci ba. Kuma shiga
makarantun Islamiyyah a matsayinsu ya zama musu da nauyi ko abin kunya. Shi ne
suka zaɓi bin wannan
hanyar. To amma kuma wannan mafita ce?
(v) Sannan tsakani da Allaah! A
cikin transliteration ta yaya za a nuna ma irin wannan dattijo ko tsohon har
kuma ya iya gane waɗansu
muhimman ƙa’idojin tajweed, irin su
idghaam da iqlaab da ikhfaa’
da hukunce-hukuncen muduud da rarrabuwansu da sauransu? A tsawon lokacin da za
a ɗauka ana masa
bayaninsu ba gara a koya masa da larabcin ba kawai?!
(vi) Da Allaah Maɗaukakin Sarkin ya ce:
وَلَقَدْ يَسَّرْنَا الْقُرْءَانَ لِلذِّكْرِ
wannan bai zama kamar zugawa ko ƙara ƙaimi
ne ga wanda bai iya karatun da larabci ya je ya koya ba?
(vii) Kuma idan har baturiya za
ta muslunta a halin tana da shekaru hamsin, kuma ta hardace Alqur’ani a wannan
shekaru, me ya hana bahaushe ko bayerabe ko banufe ko babarbare koyo da iya
karatun da larabci, ko da kuwa yana da shekaru sittin ko saba’in ne a rayuwa?!
(viii) Yanzu bai zama abin kunya
mai girma ga musulmi ɗan
shekaru talatin ko arba’in ko ƙasa ko sama da haka, a ce ya iya karatun
dukkan littaffai da jaridu da wasiƙun turanci, har ma yana iya cin gyaran
duk wani kuskuren nahawu da aka yi a ciki, amma wai bai iya karatun Littafin
Allaah da larabci ba?!
(ix) Kuma mu da Allaah ya ce mana
وَمَا خَلَقْتُ الْجِنَّ وَالْإنْسَ إلَّا لِيَعْبُدُونِ
zai yiwu mu gama tsawon rayuwarmu
a duniyar nan muna cin abincin Allaah, muna shan ruwan Allaah, muna shaƙar
iskar Allaah amma kuma mu yarda mu mutu ba mu iya karatun littafinsa yadda yake
so ba?!
(x) Yanzu a shekarunsa na wanda
yake shirin gangarawa Lahira yana jin idan aka kira wani mutum a filin taron
Alqiyamah kamar yadda Alqur’ani ya faɗa,
aka ce masa
قْرَأْ
كِتَابَكَ
(Karanta Littafinka) yana jin da
turanci ne zai ga rubutun? Kuma yana jin hujjar cewa bai iya larabci ba a ranar
za ta kuɓutar da
shi? Wannan kaɗai
bai isa zama mai ƙara iza musulmi zuwa ga koyon karatun Alqur’ani da Larabci ba?!
Allaah ya ƙara mana ƙoƙari
da ƙarin
himma.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh Muhammad Abdullaah
Assalafiy
Ga masu tambaya sai su turo ta
WhatsApp number: 08021117734
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.