Saniya Mai Shan Giya

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    As-Salaam Alaikum. Menene hukuncin bai wa shanu giya suna sha? Ko musulmi zai iya cin naman wannan saniyar?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

    [1] Tasirin zama Saniya Mai Shan Giya

    da arna kafirai ko fasiƙai kenan. Ban da shigar da giya da ƙwaya da sauran kayan maye a cikin matasa da matan aure da suka yi a cikin jama’armu, yanzu kuma abin har ya kai ga dabbobinmu?! Lallai bai halatta hukuma ta ƙyale ana yaɗa irin wannan ɓarnar a cikin al’ummarmu ta musulmi ba. Don haka lallai masu ikon faɗa-a-ji a cikinmu su yi magana har sai an ɗauki matakin horo mai tsanani a kan irin wannan ɓarnar ta dukiya, da ta’addanci a kan dabbobi da kuma zalunci ga waɗanda ake sayar musu da dabbobin ba tare da bayani ba. A lokuta da dama wa’azi kaɗai ba ya gyara mutane har sai an haɗa da ƙarfin shari’a. Kamar yadda Uthman Bn Affaan (Radiyal Laahu Anhu) ya faɗa ne cewa

    إنَّ اللَّهَ لَيَزَعُ بِالسُّلْطَانِ مَا لَا يَزَعُ بِالْقُرْآنِ

    Haƙiƙa Allaah yana karewa da mai sarauta irin abin da ba ya karewa da Alqur’ani. (Majmuu’ul Fataawa: 11/416).

    [2] Amma a kan ko za a ci wannan dabbar da aka ɗura mata giyar idan an yanka ta shari’a, ko ba za a ci ba? Amsar wannan zai fito ne a bayan an yi nazarin wannan al’amarin

    Shin ita giya najasa ce ko ba najasa ba ce? Malamai sun saɓa wa juna a kan wannan, bayan sun haɗu a kan cewa shan giyar haram ne.

    (i) Manyan malaman mazhabobin nan guda huɗu: Abu-Haneefah da Maalik da As-Shaafi’iy da Ahmad sun zaɓi cewa giya najasa ce. Wannan kuma shi ne zaɓin Shaikhul Islaam Ibn Taimiyah (Rahimahumul Laah).

    (ii) Waɗansu malaman kuma sun yarda cewa giya ba najasa ce kamar kashi ko fitsari ba. Daga cikin malaman da suke da wannan fahimtar akwai: Rabee’ah Bn Abdirrahman (Rabee’atur Ra’ay) malamin Al-Imaam Maalik, da Al-Laith Bn Sa’ad Al-Misriy, wanda As-Shaafi’iy da Ibn Bukair suka tabbatar da cewa ya fi ma Al-Imaam Maalik ilimi, da kuma Isma’eel Bn Yahya Al-Muzaniy ɗalibin Al-Imaam As-Shaafi’iy, da sauransu masu yawa daga cikin malaman Baghdad da Qairawaan (Rahmatul Laahi Alaihim), kamar yadda Al-Qurtubiy ya kawo a cikin Tafsirinsa: 6/88. (Tamaamul Minnah, shafi: 54-55).

    Daga cikin dalilinsu a kan hakan akwai ƙyalewar da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya yi aka riƙa kwararar da giyar a kan hanyoyin musulmi a lokacin da ayar haramcinta ta sauka. (Sahih Al-Bukhaariy: 2464, Sahih Muslim: 1980).

    Suka ce domin idan da giyar najasa ce, to da ta zama kamar fitsari kenan da aka haramta ƙazantar da hanyoyin musulmi da shi. (Sahih Muslim: 269).

    Haka kuma kafa hujja da kalmar ‘rijs’ (ƙazanta) da ta zo a cikin maganar Allaah Ta’aala cewa

    يَاأَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِنَّمَا الْخَمْرُ وَالْمَيْسِرُ وَالْأَنْصَابُ وَالْأَزْلَامُ رِجْسٌ مِنْ عَمَلِ الشَّيْطَانِ فَاجْتَنِبُوهُ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُون

    Ya ku waɗanda suka yi imani! Haƙiƙa giya da caca, da duwatsun yanka na gumaka, da kibiyoyin duba, duk ƙazanta ne daga aikin sheɗan. Sai ku nisance su, ko kwa samu cin nasara. (Surah At-Taubah: 90).

    Malaman sun nuna cewa: Wannan ƙazantar ta ma’ana ake nufi, ba ta haƙiƙa ba. Kamar dai maganar Allaah Ta’aala ne cewa

    إِنَّمَا الْمُشْرِكُونَ نَجَسٌ

    Lallai su mushirikai najasa ne. (Surah At-Taubah: 28).

    A nan ma najasa ta ma’ana ake nufi, ba ta haƙiƙa ba. Domin ba a taɓa ji ko ganin inda aka yi umurni da wanke wuraren da kafiran suka shafa da jikkunansu a zamanin farko ba.

    Kuma a ƙa’ida kodayake dukkan najasa haram ne, amma kuma ba kowane haramtaccen abu ne yake zama najasa ba. Domin kowa ya san matan da aka haramta su a cikin Surah An-Nisaa’: 23 duk ba najastattu ba ne.

    حُرِّمَتْ عَلَيْكُمْ أُمَّهَاتُكُمْ وَبَنَاتُكُمْ وَأَخَوَاتُكُمْ وَعَمَّاتُكُمْ وَخَالَاتُكُمْ وَبَنَاتُ الْأَخِ وَبَنَاتُ الْأُخْتِ وَأُمَّهَاتُكُمُ اللَّاتِي أَرْضَعْنَكُمْ وَأَخَوَاتُكُمْ مِنَ الرَّضَاعَةِ وَأُمَّهَاتُ نِسَائِكُمْ وَرَبَائِبُكُمُ اللَّاتِي فِي حُجُورِكُمْ مِنْ نِسَائِكُمُ اللَّاتِي دَخَلْتُمْ بِهِنَّ فَإِنْ لَمْ تَكُونُوا دَخَلْتُمْ بِهِنَّ فَلَا جُنَاحَ عَلَيْكُمْ وَحَلَائِلُ أَبْنَائِكُمُ الَّذِينَ مِنْ أَصْلَابِكُمْ وَأَنْ تَجْمَعُوا بَيْنَ الْأُخْتَيْنِ إِلَّا مَا قَدْ سَلَفَ ۗ إِنَّ اللَّهَ كَانَ غَفُورًا رَحِيمًا

    An haramta muku uwãyenku, da ´yã´yanku, da ´yan´uwanku mãtã, da goggonninku, da innoninku, da ´yã´yan ɗan´uwa, da ´ya´yan ´yar´uwa, da uwãyenku waɗanan da suka shãyar da ku mãma, da ´yan´uwanku mãtã na shan mãma, da uwãyen mãtanku, da agõlolinku waɗanda suke cikin ɗãkunanku daga mãtanku, waɗanda kuka yi duhũli da su, kuma idan ba ku yi duhũli da sũ ba, to, bãbu laifi a kanku, da mãtan ´yã´yanku waɗanda, suke daga tsatsonku, kuma kada ku haɗa tsakanin ´yan´uwa biyu mãtã, fãce abin da ya shige. Lalle ne, Allah Yã kasance Mai gãfara ne Mai jin ƙai. (Surah An-Nisaa’: 23)

    Haka ma zinare da alharini da aka haramta wa maza. (Ahmad da As-haabus Sunan suka riwaito shi daga hadisin Aliyu Bn Abi-Taalib).

    Ana iya duba waɗannan dalilan da makamantansu a cikin: Subulus Salaam: 1/52 na AS-San’aaniy da Ad-Daraarul Mudiyyah: 1/28 na As-Shawkaaniy da As-Sharhul Mumti’u: 1/428-432 na Al-Uthaimeen (Rahimahumul Laah) da sauransu.

    [3] Daga nan muna fahimtar cewa

    (i) Idan an yarda cewa giya ba najasa ba ce - a maganar da hujjarta ta fi ƙarfi - to batun matsalar cin naman saniyar da ake shayar da ita giyar ma bai taso ba. Dokar haramta shan giyar da ma a asali ya shafi mutane mukallafai ne kaɗai, ban da dabbobi. Sai dai ko idan ya tabbata cewa ana samun wata cutuwa kamar ta yin maye daga wanda ya ci naman wannan saniyar. Aukuwan hakan kuwa abu ne mawuyaci sosai.

    (ii) Idan kuma an yarda cewa giyar najasa ce - a maganar da manyan malaman mazhabobin nan shahararru guda huɗu suka zaɓa - to a nan ɗin ma ba za a yanke magana da haramcin cin naman saniyar da ake ba ta giyar ba kai-tsaye. Mafi girman abin da za a yi shi ne a yi ƙiyasinta a kan ‘Al-Jallaalah’, wato dabbar da mafi yawan abincinta najasa ne ko kuma wacce najasar ta yi tasiri a jikinta har ana iya ji ko ganin hakan daga gare ta.

    Abin da malamai suka ce a kan irin wannan dabbar mai cin najasa shi ne

    قَالَ الْخَطَّابِي اخْتَلَفَ النَّاسُ فِي أَكْلِ لُحُومِ الْجَلَّالَةِ وَأَلْبَانِهَا ، فَكَرِهَ ذَلِكَ أصْحَابُ الرَّأْيِ وَالشَّافِعِي وَأحْمَدُ بْنُ حَنْبَلِ ، وَقَالُوا لَا يُؤْكَلُ حَتَّى تُحْبَسُ أَيَّامًا وَتُعْلَفُ عَلْفًا غَيْرُهَا ، فَإِذَا طَابَ لَحْمُهَا فَلَا بَأْسَ بِأَكْلِهِ، وَقَدْ رُوِيَ فِي حَدِيثٍ أَنَّ الْبَقَرَ تُعْلَفُ أَرْبَعِينَ يَوْماً ثُمَّ يُؤْكَلُ لَحْمُهَا.

    Al-Khattaabiy ya ce: Malamai sun saɓa a kan cin naman Jallaalah da shan nononta. Malaman Hanafiyyah da As-Shaafi’iy da Ahmad sun karhanta shi. Sun ce ba za a ci shi ba har sai an bar ta na tsawon kwanaki, ana ciyar da ita wani abincin da ba wannan ɗin ba. Idan namanta ya gyaru, to babu laifi idan aka ci shi. Kuma an riwaito a cikin hadisi cewa ita saniya (jallaalah) ana ciyar da ita kyakkyawan abinci har na tsawon kwananki arba’in, sannan a yanka ta a ci. (Tuhfatul Ahwaziy: 5/447).

    Allaah ya shiryar da mu.

    WALLAHU A'ALAM

    Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

    Ga masu tambaya sai su turo ta WhatsApp number: 08021117734

    Ga Masu Buqatar Shiga Wannan Group Zaku iya bi ta Links ɗin mu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam 

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.