NA
ZALAIHAT SANI
KAGARA
DA
ZAHARADDEEN SALEH
Gabatarwa
Kowane marubucin ƙagaggen labari yana da manufar da yake son isarwa a cikin ƙagaggen labarin da ya rubuta haka ma Malama Zulaihat Sani tana daga cikin ire-iren waɗannan marubuta ƙagaggen labari wanda daga cikin littafin ta akwai wanda za a duba domin nazari ko sharhin muhimman abubuwan da ke cikin saƙonta.
Wannan littafi shi
ne “WANI GARI YAFI GABAN KUNU” shi wannan littafin an gina shi ne a kan sarauta
da kuma yaƙi, wannan shi ne babban jigon da aka gina wannan
littafin. Haka kuma an yi amfani da salo irin na da can wanda babu su a yanzu,
sannan suturu da ababen hawa dukkaninsu an yi amfani da irin na da ne.
Haƙiƙa marubuciyar
wannan littafin ta yi nasarar isar da saƙonta ta amfani da
salailai da fitar da taurari da bayyanar da tubalanta a fili da sauran abubuwa
dai mabanbanta dake cikin wannan littafin nata.
Yanzu kuma za mu
yi ƙoƙarin shiga
gundarin aikin don mu warware garin dake cikin tsakuwa don mu fahimci abin da
marubuciyar ta isar ga masu karatu.
Jigo
Wannan na nufin saƙo ko kuma manufa
ta marubuci da yake son isarwa ga al’umma, shi ake nufi da jigo. Saboda idan
muka zo sharhi a kan jigon littafin “WANI GARI YAFI GABAN KUNU” za mu iya nuna
babban jigon littafin an gina ne akan sarauta da kuma yaƙi, idan kuma muka
waiwayi ƙananan jigogi za mu tarar akwai wa’azi da faɗakarwa da
jimantarwa da kuma tarbiyantarwa. Alal misali idan muna son tsokaci akan nuna
babbar manufar littafin za mu tun daga farkon shafi aka fara ambatar masarauta
kuma har ƙarshen littafin haka ake ta magana. Haka kuma ake ta
faman gwabza yaƙe-yaƙe tsakanin wannan masarauta da kuma
wannan har izuwa ƙarshen shafin littafin.
Sannan idan muka
waiwaya ƙananan manufar wannan littafi za mu ga akwai shafukan
da wa’azi ne zalla a cikin su haka in muka ɗauki ita babbar masarautar an gina ta ne
bisa tafarkin shari’ar musulunci. Sannan in muka kalli yadda aka nuna
muhimmancin ilimi za mu ga shi ya bawa sarki Afgas damar aiwatar da bin dokokin
Allah (SWT). Sannan marubuciyar ta nuna rashin neman ilimi kan janyo sanadin
aikata munanan ayyukan da har za su kai mutum ga halaka in muka kalli rayuwar
Sagir da Nuzak yadda ta kasance. Baya ga waɗannan akwai manufofi da dama da
marubuciyar ta bayyana a rubutunta mun dai taƙaice aikin namu ne
saboda yanayi na lokaci.
Salo
Wannan na nufin
wasu hanyoyi da marubuta ko mawallafa ke bi wajen isar da saƙonsu na rubutunsu
shi ake ƙira da salo. Wasu na ganin salo da duk wani abu da zai
ƙarawa
rubutu armashi da jawo hankali da sarrafa Hausa wannan shi ne salo kamar yadda
suka gani.
Kamar yadda na
kalli abin da aka ce dangane da salo bayan na leƙa rubutun Malama
Zulaihat Sani kagara naga ta yi amfani da ire-iren salailai mabanbanta daga
cikinsu akwai:
1.
Siffantawa
2.
Kamantawa
3.
Karin
magana
4.
Tarihi
5.
Salsala
ko nasaba da sauransu.
Yanzu zamu duba ɗaya bayan ɗaya mu ga kaɗan daga cikin
ire-iren waɗannan abubuwa na
ire-iren salon da marubuciyar ta yi amfani da su kamar haka:
Siffantawa
Siffantawa na
nufin a zayyano hoton wani abu da ake magana akai kamar yadda yake. To wannan
marubuciya ta yi amfani da irin wannan salon don ta inganta rubutunta ga masu
karatu, misali, akwai shafuka da dama a cikin littafin nata da ta zayyana
iri-iri misali lokacin da Sarki Abdul’aziz ya dawo daga tafiyar da yayi an yi
ta zayyana ire-iren yadda aka tarɓe kamar…wani doki ya sha kwalliya, wata
yarinya ce ke kansa gaba ɗaya ba za ta zarce
shekaru takwas ba, ita kanta ta sha ado na ban sha’awa farin mayani aka rufe
kanta da…
Idan ana magana a
kan salon siffatawa a littafin da muke sharhi, za mu tarar salon siffantawa shi
mamaye rubutun kusan duk shafin da za ka duba ba za ka rasa salon ba.
Salon kirari
Wannan ma an same shi a shafi na
bakwai (7) misali, “lafiya toron giwa!
Lafiya zaki! Sauƙa lafiya bijimin duniya! Taka lafiya ɗan sa’ada…”
Salon kamance
Malama Zulaihat a
cikin rubutunta ta yi amfani da wannan salon na kamance misali, a shafi na 84
an ce “Sarki Ja’iz da tsohon Shamaki
Iliya kamar zasu sheƙa barzaƙu saboda baƙin ciki. Bukkar
sarki suka shige kowanne fuska kamar gobara”.
Haka kuma a shafi
na 213 an samu ire-iren wannan salon na kamance da sauran wasu shafukan.
Salon Karin Magana
Wannan salon shi ma marubuciyar ta yi
amfani da shi don ƙarawa rubutunta armashi a shafi na 92 an ce “waƙa a bakin mai ita
tafi daɗi”, haka kuma a
shafi na 94 da kuma 95 duk an yi amfani da ire-iren wannan salon.
Salon Tarihi
Wannan ma Malama Zulaihat ta yi amfani
da salon nan tun a farko shafuka rubutun yadda ta bada tarihin sarakunan da
suka ci zamani kafin sarki Abdul’aziz a ƙasar AFGAS.
Wannan salon da muka kawo ba su kaɗai ba ne aka yi
amfani da su a cikin littafin da muke sharhi, akwai salailai mabanbanta wanda
lokaci ne bai bamu damar leƙa su ba, amma in kere na yawo zabo
na yawo wata rana za a yi ciɓis.
Zubi da Tsari
A wannan fage na zubi da tsari na
littafi ana buƙatar irin abubuwa ne kamar haka:
i.
Buɗewa da rufewa
ii.
Dabarun
ƙulla
labari
iii.
Tsarin
babi ko kuma amfani da lambobi ko kuma adadin shafukan litttafin.
Yanzu bari mu
kalli fasalin zubi da tsarin littafin Malama Zulaihat mu ga yadda ta gudanar da
shi kamar haka:
-
Mabuɗin wannan littafi:
Ta buɗe ne da rubutu
kawai a zube yayin da take bada tarihi abubuwa waɗanda ta ce ba za su lissafu ba na
abin kuka da na tausayi.
-
Sai
ta rufe littafin da jan hankalin masu karatu da a haɗu a littafi na
biyu (2) don cikon labarin da mai karatu ya fara, kamar yadda ta nuna tare ma
littafan aka buga kuma sun fito ma tare.
-
Labarin
ya zo ne a zube ma’ana bai da wani tsari na babi, sai dai ya na da shafuka 216
ne kawai.
Taurari
Kalmar taurari
kalma ce ta jam’i wadda take nufin jarumi a tilo a jam’u kuma jarumai. Idan ana
magana ne a kan taurari a nazarin rubutun zube shi ne wanda sunansa ya mamaye
rubutun, duk inda aka faɗi aka tashi za a
same shi wannan shi ne tauraro.
A littafin da muke sharhi yanzu
tauraron wannan littafi shi ne Sarkin ƙasar Afgas wato
sarki Abdul’aziz kenan, saboda shi ne wanda ya mamaye dukkanin shafukan rubutun
da Malama Zulaihat ta yi. A taƙaice dai sarki Abdul’aziz shi ne
babban tauraro sai kuma irin su:
1.
Sarki
Ja’iz
2.
Jakadiya
3.
Waziri
4.
Gimbiya
Sumayya
5.
Yarima
6.
Umma
da sauransu
Manazarta
Z.
S. (2016). Wani Gari yafi Gaban Kunu, Maizar Pub. Zaria.
ALH
406 (2017). Lecture Note, UDU Sokoto
Acto
Ahmed Gidan-Dibino (2014). Shafin Goggle
Himma
Journal: Department of Nigerian Languages, UMYU, Katsina.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.