Na
SAMIRA ABUBAKAR WALI
Gabatarwa
Wannan dai aikin
gida ne da ake bayarwa don auna fahimtarmu akan koyarwar da aka yi mana a cikin
aji, domin a auna fahimtar mu.
Aiki ne da aka baiwa kowa mai laccar ALH 406 Comtemporary Prose in Hausa.
Aikin ya nemi kowa
ya yi nazarin littafin da ake zube masa. A inda ni aka zaɓa mani littafin
MUMMUNAN ZATO.
To
zan yi nazari a hanyar gargajiya. A nazarin gargajiya ana amfani ne da dabaru
guda biyu wato:
1.
Gabatar
da littafi
2.
Jigonsa
3.
Salonsa
4.
Zubi
da tsari da kuma
5.
Bayanin
taurari
Gabatarda littafi
Littafin Mummunan Zato littafi ne da Halima Abdullahi K/Mashi (Mrs Sa’eed) ta wallafa kuma aka
buga shi a copyright ©K/Mashi an buga shi ne a salanu Bookshop. Littafin
mummunan zato ya na da shafi ɗari da sittin
(160).
Kuma babu wani
cikakken tarihi game da wadda ta wallafa wannan littafi sai dai ana iya cewa
mutumiyar Kano ce.
Haka kuma babu
wani cikakken bayani game da dalilin rubuta wannan littafi sai dai mafi yawa
littafan adabin kasuwar Kano ana rubuta su ne bisa ga sha’awa ko kuma neman kuɗi, don haka ana
iya hasashen cewa shi ma wannan littafi an rubuta shi ne bisa ga dalili na
sha’awa ko neman kuɗi.
Ƙunshiyar
littafin
Littafin mummunan
zato ya na ɗauke ne da labarin
miji da matarsa, shi ne Alhaji Sadik da Hajiya Jummai da Aisha a inda take
yawon zuwa wuraren boka, duk matar da ya aura ta na bibiya wuraren boka ta ne
bi sa boka yana kashe su mutan.
Jigo
Saƙon da marubuci ke
son isarwa shi ne jigo. Jigon wannan littafi bisa ga abin da ya bayyana a
cikinsa shi ne Boka ba ya iya kashewa sai in Allah ya so misali dubi abin da
aka yi wa amarya. Abin da ya soma ɗaga hankalin Jummai shi ne yau satin
amarya biyu kullum tare jiran ta ji Alhaji.
Salo
Salo shi ne
dabarun da aka bi wajen isar da saƙo, ko a ce salo
shi ne dabarun jawo hankali, waɗannan sun ƙunshi har da irin
su aron kalmomi, da sarrafa harshe, irin amfani da karin magana da su amfani da
jimsawa, kamance da sauransu.
Haka
salo ya ƙunshi amfani da zaɓen kalmomi da tsara jumloli yadda ya
kamata.
a.
Aron Kalmomi: Tsam ta miƙe neja ta bita da
kallo, ta shige (toilet) ta ɗauro alwala. (Mummunan Zato 107).
b.
Karin Magana: Karin magana
zance ne gajere mai faɗakarwa (Ɗanyaya, 2007).
Amfani da karin magana ana kallonsa a matsayin nuna gwanintar harshe.
c.
Jinsawa: Jinsawa shi ne ɗaukar halayyar
wani jinsi a liƙawa wani jinsi. Jinsawa ta kasu zuwa gida uku:
i.
Mutuntarwa
ii.
Dabbantarwa
iii.
Abuntarwa
d.
Kamance: Kamance shi ne
kwatanta wani abu da wani abu don mai sauraro ko karatu ya kalli wanda ake
kwatantawa kamar wanda aka kwatanta da shi.
Kamance ya kasu
gida uku ne:
i.
Daidaito
ii.
Fifiko
iii.
Kasawa
A wannan littafin
an samu kamance daidaito kamar haka:
“Ta ƙosa ta koma ɗaki don jinta take tamkar kan ƙaya”. (Mummunan Zato:
136).
Shi kuma kamancen
fifiko shi ne wanda ake nuna abin kwatantawa ya wuce abin kwatantawa da shi.
Ana amfani ne da kalmomi wajen yin sa irin su fi, zarce, wuce da sauransu.
Shi kuma kamancen
kasawa shi ne wani da ake samu abu bai kai kamar wannan abin ba, misali;
“Ta ce a’a tare can ni bazan iya jan mota ba”.
(Mummunan Zato: 90).
Zubi da Tsari
Zubi da tsari ya ƙunshi:
1.
Buɗewa da rufewa
2.
Dabarun
ƙulla
labari
3.
Tsarin
babuka
a. Buɗewa da Rufewa:
Wannan littafi an
buɗe shi da irin buɗewar da ake ya yi
a yanzu, wato a soma da bayanin abin da ke tsakar littafi ko abin da yake ƙarshe. A wannan
littafi an soma da cewa:
“Ya shigo gida cike da fara’a yana faɗin ina ummar yaron gidan nan ne?”
Rufewar wannan
littafi haka take kamar na ɗan uwansu ne adabin kasuwar kano, wato a kan tsaya ne
a wurin da dole sai ka nemi littafi na gaba don ganin abin da aka soma ba a
gaba ba. Misali,
“Domin ba ta ja da maganan bokayen nan guda biyu don
sune abin dogaronta, wa yanzu billa shin hakan ta kasance”?.
b. Dabarun Ƙulla Labari:
A gaskiya
marubuciyar ta yi ƙoƙari matuƙa wajen ƙulla labarin ta da
ta rubuta domin labarin ta ya na tafiya daidai wa daida, domin an san inda aka
nufa a cikin labarin da ta ke bayarwa.
c. Tsarin Babuka:
Tsarin babuka na
nufin yadda aka karkasa littafin. A wannan littafi an yi amfani ne da kalmomin
lissafi ne irin su ɗaya, biyu, uku,
wajen tsara babukan.
Taurari
Taurari a wannan
littafi ana iya kasa su gida biyu:
Manyan Taurari:
Manyan taurari
anan suna nufin waɗanda suka fi taka
rawa:
1.
Alhaji
Sadik Umar K.T: Shi ne tauraro na ɗaya a cikin wannan littafi domin shi ne
wanda yafi haskawa a cikin littafin kuma shi ne mai gidansu.
2.
Hajiya
Jummai: Hajiya Jummai ko tana cikin taurari da suka haskaka a cikin wannan
littafi.
3.
Aisha
– ita ma tauraruwa ce a cikin wannan littafi.
4.
Abdulrahman
– shi ma babban tauraro ne.
5.
Jafar
– shi ma babban tauraro ne.
6.
Munnir
– shi ma babban tauraro ne.
7.
Sulaiman – shi ma babban tauraro ne
8.
Ishak
– shi ma babban tauraro ne.
9.
Mustafa
Gumel
10. Boka na kan dutse
Ƙananan
Taurari
1.
Murja 11.
Hajiya Karima
2.
Jamilu 12.
Zainab
3.
Malam
Mamuda 13.
Suwaiba
4.
Rukayya 14.
Safiya (Sofy)
5.
Amina 15.
Suwaiba (Suby)
6.
Hafsat 16.
Mr. Joseph
7.
Malam
Dari 17.
Aunty Hasiya
8.
Fatima 18.
Rahina
9.
Nafisa 19.
Alhaji Najib
10. Sadiya 20.
Hajiya Ummi
Kammalawa
An ga yadda aka
soma gabatar da littafin ta hanyar bayyana sunan marubuciyar da kamfanin da ya
buga da kuma ƙunshiyar littafin da jigo da salo da zubi da tsarinsa
da kamancen da sauransu.
Manazarta
Atuwo,
A. A. (2017). Lacca Aji da ya Gabatar wa Ɗalibai ‘Yan Aji Huɗu ALH 406. Jami’ar
Usmanu Ɗanfodiyo, Sakkwato.
Bincike game da al’adun ko wace al’umma (wanda
kuwa Hausa ma na ɗaya daga cikin
al’ummu) abu ne mai matuƙar muhimmanci. Hakan ne zai sanya a killace ko
kundance ire-iren al’adun da suke suke barazanar ɓacewa. Kasancewar aure ɗaya daga cikin
mafiya muhimmanci daga cikin al’adun Bahaushe wanda kuma addini a ƙarfafa (Ibrahim,
1985), akwai buƙatar irin waɗannan bincike game da al’adun da ake
gudanarwa yayinsa (aure). A ɗaya ɓangaren kuma, za a iya kallon amfanin abinci a wani
matsayi makusancin amfanin rayuwa (Yabo, 2006). Kenan akwai buƙatar gudanar da
wani bincike wanda zai karanci irin sauye-sauye da aka samu game da ire-iren
abincin da ake samarwa yayin bukukuwan aure da kuma na haihuwa a ƙasar Hausa, sannan
ƙasar
Sakkwato a keɓance.
Lura da bayanan da
ke sama, ana sa ran wannan nazari ya waiwayi muhimmancin abinci musamman yayin
bukukuwa. Sannan aikin zai kawo ire-iren abincin da ake amfani da su yayin
bukukuwan Hausawa a da (bukin aure da na haihuwa). Baya ga haka, aikin zai dubi
yadda abin yake a yau. Wato irin sauye-sauyen da zamani ya zo da shi a wannan ɓangaren na abincin
bukukuwan Hausawa. Daga ƙarshe kuma ake sa ran aikin ya nazarci irin cigaba da
kuma koma baya da wannan canji ta fuskar abincin bukukuwan Hausawa zai iya
samarwa.
Daga ƙarshe, kamar yadda
aure ke da muhimmanci tare da gurbi na musamman (Abdullahi, 2008), sannan
abinci ya kasance a wani matakin dole ga rayuwar Bahaushe (Yabo, 2006), kenan
yana da matuƙar muhimmanci a gudanar da bincike kansu. Wato
musannam idan aka yi la’akari da tasirin sauye-sauye da cigaban zamani a kansu.
Wannan nazari zai kasance mai alfanu ga al’adar Hausawa a matsayin wani kundi
da ya killace ilimi dangane da abin da ya shafi abincin bukukuwan Hausawa.
Manazarta
Abba,
S. (2011). “Nason Al’adun Turawa a Bukin Aure a Ƙasar Sakkwato.
Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar
Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.
Abdullahi,
I. S. S. (2008). Jiya ba Yau ba: Waiwaye a Kan Al’adun Matakan Rayuwar Maguzawa
na Aure da Haihuwa da Mutuwa. Kundin digiri na uku wanda aka gabatar a Sashen
Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.
Abdullahi,
M. (1997). “Bukukuwan Musulunci a Garin Maidahini a Ƙaramar Hukumar
Mulki ta Bunza.” Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan
Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.
Abu,
M. (1985). Al’adun Aure da Canje-canjensu a Katsina. Kundin digiri na farko
wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo,
Sakkwato.
B/Kebbi,
M. A. (1997). “Yanayi da Tsarin Al’adun Aure a Birnin Kebbi.” Kundin digiri na
farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo,
Sakkwato.
Babajo,
S. A. (2001). “Yaji da Biko a Auren Bahaushe.” Kundin digiri na farko wanda aka
gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.
Bunza,
D. B. (2013). Zama Da Maɗaukin Kanwa Ke Sa
Farin Kai: Nason Baƙin Al’adu Cikin Al’adun Auren Hausawa. Muƙalar da aka
gabatar a taron ƙara wa juna sani na ƙasa a Sashen
Harusnan Nijeriya, Jami’ar Ummaru Musa ‘Yar’aduwa.
Faruk,
S. I. (2011). Tasirin Aikin Gwamnati A Kan Matan Auren Hausawa A Jihar Katsina.
Kundin digiri na biyu wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar
Bayero, Kano.
Funtuwa,
A. I. da Gusau, S. M. (2010). Al’adun da Ɗabi’un
Hausawa da Fulani.
Kaduna: El-Abbas Printers and Media Concept.
Gada,
N. M. (2014). Kutsen Baƙin Al’adu Cikin Hidimar Aure A Sakkwato. Kundin digiri
na biyu wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo,
Sakkwato.
Gobir, Y. A. (2012). Tasirin Iskoki ga Cutuka
da Magungunan Hausawa. Ph. D. theses submitted to the Department of Nigerian
Languages, Usmanu Danfodiyo Uniɓersity, Sokoto
Gusau,
G. U. (2012). Bukukuwan Hausawa.
Gusau: Ol-faith Prints
Gwarjo,
Y. T. da wasu (2005). Aure a Jihar Katsina. London: Oɗford Uniɓersity
Press.
Hassan, B. Y. (2013). Nason Baƙin Al’adu Kan Al’adun Aure Da Haihuwa Da Mutuwa Na
Hausawa. Muƙalar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani na ƙasa a Sashen Harusnan Nijeriya, Jami’ar Ummaru Musa
‘Yar’aduwa.
Ibrahim,
M. S. (1985). Auren Hausawa: Gargajiya Da Musulunci. Kundin digiri na biyu
wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.
Ibrahim,
S. M. (1981). Auren Hausawa. Zaria:
Ahmadu Bello Uniɓersity Press.
Ingawa,
Z. S. (2012). Tasirin Sauye Sauyen Zamni A Kan Rayuwar Matan Hausawa A Katsina
Daga 1960 Zuwa 2010. Kundin digiri na uku wanda aka gabatar a Sashen Harunan
Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.
Jungudo,
A. (2011). “Kwatance Tsakanin Auren Hausawa da na Fulani a Garin Gombe.” Kundin
digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu
Danfodiyo, Sakkwato.
Mohammad,
H. (2010). “Matsayin Ganye A Abincin Hausa A Ƙasar Bodinga.”
Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar
Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.
Muhammad, T. A. (1998). Aure Da Buki A Ƙasar Hausa. Kano: Ɗan Sarkin Kura Publishers Ltd.
Rambo,
I. (2007). Nazari Kan Wasu Keɓaɓɓun Al’adun Auren Hauswa Da Na Dakarkari. Kundin digiri
na biyu wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo,
Sakkwato.
S/Tudu,
H. Z. (1987). Tasirin
Zamani A Kan Al’adun Aure A Ƙasar Sakkwato. Kundin digiri na
farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo,
Sakkwato.
Sa’id,
B. da wasu, (editoci). Ƙamusun Hausa na
Jami’ar Bayero Kano. Zariya: Ahmadu
Bello Uniɓersity Press Limited.
Sa’id,
B. edita (2006). Ƙamusun
Hausa na Jami’ar Bayero. Zaia: Ahmadu Bello Uniɓersity Press.
Sani,
U. S. (1997). Zamani Riga Ne: Sababbin Al’adun A Lokacin Bukukuwan Auren
Hausawa A Garin Sakkwato. Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen
Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.
Umar,
K. F. (2004). Tasirin Al’adun Hausawa A Kan Na Dakarkari Daga 1800-2000. Kundin
digiri na biyu wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero,
Kano.
Umar,
K. F.
(2007). Tasirin Zamani Kan Ire-iren Auren Hauswa. Kundin digiri na farko wanda
aka gabatar a Jami’ar Maiduguri.
Usman,
A. (2013). “Al’adun Aure a Garin Kilgori.” Kundin digiri na farko wanda aka
gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.
Wasagu,
B. S. (2002). “Tasirin Al’adun Auren Hausawa a Kan na Dakarkarin Zuzu.” Kundin
digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu
Danfodiyo, Sakkwato.
Yabo,
B. A. (2006). “Kirarin Abincin Hausawa.” Kundin digiri na farko wanda aka
gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.
Yaro,
A. (1994). Jirwayen Al’adun Hausawa A Kan Fulanin Yola. Kundin digiri na biyu
wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.
Yauri,
B. M. (2011). “Tasirin Al’adun Auren Hausawa a Kan na Kambarin Kambuwa.” Kundin
digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu
Danfodiyo, Sakkwato.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.