Tasirin Zamani a Kan Abincin Bukukuwan Hausawa

    KUNDIN BINCIKEN KAMMALA KARATUN DIGIRI NA FARKO (B.A HAUSA) A SASHEN NAZARIN HARSUNAN NIJERIYA, JAMI’AR USMANU ƊANFODIYO, SAKKWATO, OKTOBA, 2017

    Tasirin Zamani a Kan Abincin Bukukuwan Hausawa 

    SAMIRA ABUBAKAR WALI

    ƘUMSHIYA

    Taken Bincike                                                                                   

    Tabbatarwa                                                                                       

    Sadaukarwa                                                                                      

    Godiya                                                                                             

    Ƙumshiya                                                                                             

    BABI NA ƊAYA

    GABATARWA

    1.0   Shimfiɗa

    1.1 Bitar Ayyukan da Suka Gabata

    1.2 Hujjar Ci Gaba da Bincike

    1.3 Farfajiyar Bincike

    1.4 Hanyoyin Gudanar Da Bincike

    1.5 Muhimmancin Bincike

    1.6 Kammalawa

    BABI NA BIYU

    ABINCI DA BUKUKUWAN HAUSAWA

    2.0 Shimfiɗa

    2.1 Ma’anar Abinci

    2.2 Rabe-raben Abinci

    2.2.1Abincin Yau-da-kullum

    2.2.2 Abincin Ƙwalama/Maƙulashe

    2.2.3 Abincin Bukukuwa

    2.3 Ma’anar Buki

    2.4 Ire-iren Bukukuwan Hausawa

    2.4.1 Bukukuwan Gargajiya

    2.4.2 Bukukuwan Zamani

    2.5 Bukin Aure

    2.6 Bukin Haihuwa

    2.7 Naɗewa

    BABI NA UKU

    ABINCIN BUKUKUWAN HAUSAWA NA ZAMANI A BIRNIN SAKWKATO

    3.0 Shimfiɗa

    3.1 Abincin Bukin Aure Na Zamani A Birnin Sakkwato

    3.2 Ababen Sha na Zamani a Bukin Aure a Birnin Sakwkato

    3.3 Abincin Bukin Haihuwa na Zamani a Birnin Sakwkato

    3.4 Ababen Sha na Zamani a Bukin Haihuwa a Birnin Sakwkato

    3.5 Tasirin Abincin Zamani ga Abincin Hausawa na Gargajiya

    3.6 Naɗewa

    BABI NA HUƊU

    SAKAMAKON BINCIKE DA KAMMALAWA

    4.0 Shimfiɗa

    4.1 Sakamakon Bincike

    4.2 Kammalawa

    4.3 Shawarwari

    Manazarta

    BABI NA ƊAYA

    ƘUDIRIN BINCIKE

    1.0  Gabatarwa

    Kamar yadda duniya ba a wuri ɗaya take tsaye ba, ta kasance tana zagayawa, haka ma al’amuran duniya suke samun canje-canje. Wannan irin canji da ake samu ya shafi kusan dukkanin ɓangarorin rayuwar al’ummun duniya. Wato kamar ɓangaren harshe da zamantakewa da gine-gine da tafiye-tafiye da sutura da abinci da sauran abubuwan da suka shafi adabi da al’ada (S/Tudu, 1987; Umar, 2007; Abba, 2011) Hausawa ma ba su kasance daban ba wurin fiskantar waɗannan canje-canje. Al’adun Hausawa a yau kwata-kwata sun bambanta da yadda suke idan za a tuna baya kaɗan. Daga cikin irin ɓangaren da aka samu canji ga al’adar Bahaushe har da ire-iren abincin buki da kuma na suna. Saboda haka, maƙasudin wannan aiki shi ne binciko yadda yanayin wannan sauyi yake. Wato nazartar irin abincin da ake amfani da su yayin bukukuwan aure da na Haihuwa a garin Sakkwato.

    An raba aikin zuwa babi-babi har guda huɗu. Babi na farko sharar fage ne ga aikin, inda ya ƙunshi abubuwan da suka shafi bitar ayyukan da suka gaba ta hujjar ci gaba da bincike da hanyoyin gudanar da bincike. Babi na biyu kuwa yana dauke da bayani game da abinci da kuma bukukuwan Hausawa, musamman bikin aure da na haihuwa. Babi na uku kuwa shi ne gundarin aiki. Ya kawo ire-iren abubuwan ci na zamani da ake samu a wuraren biki da kuma suna a ƙasar Sakkwato. Babi na huɗu kuwa yana ɗauke da kammalawa da kuma sakamakon bincike.

    1.1 Bitar Ayyukan Da Suka Gabata

              Kafin fara bincike na ilimi, yana da kyau mai bincike ya yi bitar ayyukan da suka gabata waɗanda ke da dangantaka da aikin da ya ya ƙudurta. Muhimmancin yin hakan shi ne kaucewa maimaita aikin da aka rigaya aka gudanar. Sannan hakan zai ba wa manazarci ƙarin haske game da aikin binciken da ya/ta sanya a gaba. Wannan bitar ayyukan da suka gabata zai dubi kundayen digiri da uku da na biyu da kuma na farko. Sannan zai dubi littattafai da kuma muƙalu da aka gabatar a tarurrukan ƙara wa juna sani. Ga yadda abin yake a ƙasa:

    Abdullahi, (2008) ya rubuta kundin digiri na uku a Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato mai taiken: “Jiya ba Yau ba: Waiwaye a Kan Al’adun Matakan Rayuwar Maguzawa na Aure da Haihuwa da Mutuwa.” Wannan kundi yana ɗauke da bincike mai zurfi game da matakan rayuwar maguzawa na aure. Wannan ya haɗa har da irin shagulgula da ake yi yayin aure da kuma irin zamantakewar auren kansa. Sannan aikin yana ɗauke da bayani mai zurfi game da abin da ya shafi haihuwar Maguzawa. Maguzawa dai al’umma ce da ba su da wani harshe bayan Hausa. Saboda haka, a duk lokacin da ake bayani game da Hausawa ba tare da an ambaci Maguzawa ba, to kamar an yi tuya ne an amce da albasa.

    Haƙiƙa aiki nasa yana da dangantaka matuƙa da wannan bincike, musamman da yake dukkaninsu sun taɓo magana game da aure da kuma haihuwa. Sai dai aikin nasa bai kawo bayani game da ire-iren abincin zamana na bukukuwan aure da haihuwa na Hausawa ba, musamman a garin Sakkwato a yau. Wannan aiki kuwa zai mayar da hankali ne kan abincin bukukuwan aure da haihuwa na zamani a Sakkwato.

    Rambo, (2007) ya rubuta kundin digiri na biyu a Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato mai taken: “Nazari Kan Wasu Keɓaɓɓun Al’adun Auren Hauswa Da Na Dakarkari.” Wannan kundi ya kawo faffaɗan bayani game da wasu al’adun aure na al’ummar Hausawa da kuma Dakarkari. Waɗannan al’adu kuwa sun haɗa da ɗaurin aure, da kai amarya da hidimar biki da makamantansu. Kundin dasa yana da dangantaka da wannan aikin bincike kasancewar dukkaninsu sun kawo batu kan aure. Sai dai aikin nasa ba zai dakatar da wannan bincike ba. Dalili kuwa shi ne, shi Rambo ya karkata ne kan wasu keɓaɓɓun al’adun auren Hausawa da na Dakarkari. Amma bai kawo batu kan abincin zamani na bukukuwan aure da haihuwa na Hausawa ba a yau. Saboda haka, aikin nasa ba zai dakatar da wannan bincike ba.

    Gada, (2014) ta rubuta kundin digiri na biyu mai taken: “Kutsen Baƙin Al’adu Cikin Hidimar Aure A Sakkwato.” A cikin wannan kundi nata ta kawo ma’anar aure da kuma yadda ake yin sa a garin Sakkwato. Ta kasa al’adun aure gida biyu, wato wanda Bahaushe ke yi bayan zuwan Musulunci da kuma al’adun da suka samu sakamakon kutsen zamani. Al’adun aure na asali sun haɗa da biɗa/nema da zance da jinkira da kai lehe/lefe da gayyata da kimtsa amarya da wankin amarya da ɗaurin aure da ɗaukar amarya da wankin ango da zaman bakwai da sayen baki da sayen hura da kitso da gyara ɗaki ko jere da makamantansu. Amma tasirin zamani ya sanya an samu ƙari da kuma sauyi a cikin lamarin aure. Irin al’adun aure na zamani sun haɗa da hidimar tabbatar da so da zance da na-gani-ina-so da sa lalle da wankan amarya da ƙunshi da walima da ranar ƙauyawa da daren Larabawa da da daren Indiya da sauransu.

    A gaba kuwa, Gada ta kawo illolin wannan kutse na baƙin al’adu a hidimar aure a Sakkwato da kuma nasarorin waɗannan al’adu, wato amfaninsu. Haƙiƙa aikin nata na da dangantaka da wannan bincike, domin kuwa kowannensu ya taɓo magana game da aure da kuma sauyin zaman. Bayan haka sun yi tarayya wurin farfajiyar bincike (Sakkwato). Saidai kuma sun bambanta, domin kuwa Gada ta yi magana ne a kan kutsen baƙin al’adu cikin hidimar aure a Sakkwato. Ma’ana ta dubi tasirin baƙin al’adu kan tsarin aure a Sakkwato bai ɗaya. Wannan aikin kuwa zai keɓanta ne kan nazarin abincin zamani na bukukuwan aure da haihuwa na Hausawa a garin Sakkwato.

              Nuhu da Maude, (1990) sun rubuta kundin digiri na farko mai taken: “Ɗabi’un Cin Abincin Bahaushe Ƙwalama da Kwaɗayi.” A cikin wannan kundi sun kawo ire-iren abinci na ƙwalama da kwaɗayi. Sun haɗa da abincin ƙwalama na maza yara da na maza manya da na mata yara da kuma na mata manya. A babi na uku, sun nuna cewa, wuraren da ake yin ƙwalama da kwaɗayi sun haɗa da gidan suna da kuma gidan buki. Wato wasu daga cikin irin abincin da ake ci a gidan buki.

              Haƙiƙa wannan aikin na Nuhu da Maude na da alaƙa da wannan bincike. Domin kuwa dukkaninsu sun shafi abincin suna da kuma na buki. Sai dai su sun kalli abincin ƙwalama ne bai ɗaya. Wannan aiki kuma ya taƙaita ne ga nazarin abincin Hausawa na bukin suna da kuma haihuwa a yau. Saboda haka, aikin nasu ba zai dakatar da wannan bincike ba.

    Babajo, (2001) ya rubuta kundin digiri na farko a Sashen Harsunan Nijeriya, ta Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato. Wannan kundi na da taken: “Yaji da Biko a Auaren Bahaushe.” A babi na biyu na aikin ya kawo ma’anar aure sannan kuma ya yi tsokaci game da auren maguzanci da kuma aure cikin addinin Musulunci. A babi na uku kuma na wannan aiki, an kawo ma’anar yaji da dalilan da ke kawo yaji da kuma illoli da amfanin yaji. A babi na huɗu kuwa, an yi bayanin ma’anar biko da yadda ake biko da muhimmancin biko.

              Wannan aikin na Babajo yana da dangantaka da wannan bincike, domin dukkaninsu sun karkata kan lamuran da suka shafi aure. Saidai aikin na Babajo bai taɓo ire-iren abincin Hausawa na aure ko na haihuwa ba, musamman a birnin Sakkwato. Saboda haka, aikin nasa ba zai dakatar da wannan bincike ba.

              Yabo, (2006) ya rubuta kundin digiri na farko mai suna: “Kirarin Abincin Hausawa.” A babi na huɗu na wannan aiki, ya kawo bayani game da abincin Hausawa da kuma rabe-raben abincin Hausawa. Daga cikin rabe-raben abincin Hausawan akwai: na marmari da na yau da kullum da kuma na buki. A babi na biyar kuwa, ya kawo iri kirarin da ake yi wa abinci kala-kala, daga ciki har da abincin buki.

              Haƙiƙa aikin nasa yana da dangantaka da wannan bincike, musamman la’akari da dukkaninsu sun taɓo magana dangane da abincin buki. Amma duk da haka, aikin na Yabo ba zai dakatar da wannan bincike ba, domin shi bai yi keɓaɓɓen nazari game da abincin bukukuwan aure da na haihuwa na Hausawa ba a yau. Wannan aiki kuwa zai mayar da hankali ne kan abincin bukukuwan aure da haihuwa na zamani a Sakkwato.

    Abba, (2011) ya rubuta kundin digiri na farko mai taken: “Nason Al’adun Turawa a Bukin Aure a Ƙasar Sakkwato.” A babi na biyu na wannan aiki, ya dubi garin Sakkwato ta fuskar addini da harshe da kuma al’adu. Sannan a ƙarƙashin al’adun ya dubi bukukuwan Sakkwatawa. Daga cikin waɗannan bukukuwa kuwa har da bukin aure da na haihuwa. A babi na huɗu kuwa, ya tattauna abubuwan da suka shafi canje-canjen bukin aure a Sakwkato. Daga ciki ya yi bayanin aure kafin jihadi da aure bayan jihadi da kuma aure bayan zuwan Turawan mulkin mallaka. Bayan nan ne kuma ya kawo ire-iren al’adun aure da suka samu bayan zuwan Turawa. Al’adun sun haɗa da kalanda da sitika da launching da fiknik da reception da makamantansu.

              Haƙiƙa wannan aikin na Abba yana da dangantaka da wannan bincike da aka sanya a gaba. Domin kuwa sun yi tarayya ta ɓangaren farfajiyar bincike (Sakkwato) da kuma kasancewar dukkaninsu sun karkata kan bukukuwan Hausawa ne. Amma aikin na Abba ba zai dakatar da wannan bincike ba. Dalili kuwa shi ne, Abba ya kalli nason al’adun Turawa ne a bukin aure a ƙasar Hausa. Wannan aiki kuwa zai mayar da hankali ne kan abincin bukukuwan aure da haihuwa na zamani a Sakkwato.

              Yauri, (2011) ya rubuta kundin digiri na ɗaya mai taken: “Tasirin Al’adun Auren Hausawa a Kan na Kambarin Kambuwa.” Wannan kundi nasa ya kawo ma’anar aure da yanayin neman aure da lokacin neman aure da yadda ake ɗaukar amarya da kuma shirye-shiryen da ake gudanarwa a gidan ango, duka a babi na uku. A babi na huɗu kuwa, an kawo ɓangarorin da al’adun auren Hauswa suka yi tsiri kan al’adun auren Kambari. Wannan tasiri akan same shi a ɓangaren sanya lokacin aure da na neman auren kansa da na ɗaukar amarya da kuma jeren ɗaki da makamantansu.

              Kundin na Yauri yana da alaƙa da wannan aikin bincike aksancewar dukkaninsu sun taɓo magana a kan al’adun auren Hausawa. Sai dai Yauri ya fi mayar da hankali ne kan tasirin da al’adun auren Hauswa suka yi a kan na Kambari. Saboda haka, bai kawo bayani game da ir-iren abincin bukin aure ko bukin sunan Hausawa ba. Wannan aiki kuwa zai yi bincike ne game da abincin bukukuwan aure da haihuwa na zamani a Sakkwato.

              Jungudo, (2011) ya rubuta kundin digiri na farko mai taken: “Kwatance Tsakanin Auren Hausawa da na Fulani a Garin Bombe.” A babi na biyu na aikin nasa, ya kawo ma’anar aure da rabe-raben aure da kuma muhimmancinsa. A babi na uku kuwa, ya kawo bayanai da suka haɗa da al’adun auren Hausawa da kuma na Fulani. Sannan sai ya kawo tasirin al’adun auren Hausawa a kan na Fulani, da kuma irin bambance-bambance da dangantakar da ake samu a tsakanin auren na Hausawa da kuma Fulani. Daga cikin tasirin al’adun Hausa a kan na Fulani waɗanda Junguɗo ya kawo akwai lokacin tarwar amarya da kuma kwanan zaune.

              Aikin na Jungudo yana da kamance da wannan bincike kasancewar dukkaninsu suna ɗauke da bayanai game da al’adun auren Hausawa. Sai dai shi ya fi mayar da hankali ne kan tasirin al’adun auren Hausawa a kan na Fulani, musamman a garin Gombe. A ɗaya ɓangaren kuma, wannan bincike zai mayar da hankali ne kan abincin bukukuwan aure da haihuwa na zamani a Sakkwato.

              Usman, (2013) ya rubuta kundin digiri na farko mai taken: “Al’adun Aure a Garin Kilgori.” A babi na biyu na wannan kundi, an kawo ma’anar al’ada da kuma ma’anar aure sannan da ire-iren aure a garin Kilgoi. Ire-iren auren na Kalgori sun haɗa da auren soyayya da auren tilastawa/dole da auren bare da auren gado/gata da auren yi wa kai da sauransu. A babi na uku kuwa, an kawo matakan aure a garin Kilgori waɗanda suka haɗa da na gani ina so da shigowar iyaye da kayan neman aure da toshi da kayan sa lalle da kayan sa ruwa da sa ranar aure da sauransu. Sannan babi na huɗu ya kawo fasalin bukin aure a garin Kalgori wanda ya haɗa da sa amarya lalle da ɗaurin aure da yinin buki da jere da kuma kai amarya.

              Aikin na Usman yana da dangantaka da wannan bincike, kasancewar dukkaninsu suna magana game da abin da ya shafi auren Hausawa. Sai dai aikin nasa ya taƙaita ne kan irin al’adu da hidindimun aure a Kilgore. Bai yi magana game da abincin Hausawa na aure ko haihuwa ba. Saboda haka, aikin nasa ba zai dakatar da wannan bincike ba. Domin shi wannan bincike zai mayar da hankali ne kan abincin bukukuwan aure da haihuwa na zamani a Sakkwato.

    Littattafai

    Ibrahim, (1981) ya rubuta littafi mai suna: Auren Hausawa. Wannan littafi ya yi cikakken bayani game da al’adun da suke baibaye da al’adar auren Bahaushe. Waɗannan al’adu sun haɗa da zance da toshi da lefe/kayan aure da ɗaurin aure da bikin aure da makamantansu. Saboda haka, littafin nasa yana da dangantaka da wannan aikin. Sai dai kuma littafin nasa ba zai tsayar da wannan bincike ba, domin bai kawo cikakken bayani ba game da abincin bukukuwan aure da haihuwa na zamani a birnin Sakkwato.

              Muhammad, (1998) ya rubuta littafi mai taken: Aure Da Buki A Ƙasar Hausa. Wannan littafi nasa ya kawo yalwataccen bayani kan aure a ƙasar Hausawa. Wannan ya haɗa da irin hidimar bikin aure da shagulgulan da ake gudanarwa yayin wannan biki. Saboda haka, aikin nasa yana da dangantaka da wannan bincike. Sai dai aikin nasa ba zai dakatar da wannan bincike ba kasancewar Muhammad bai kawo bayani cikakke ba game abincin bukukuwan aure da haihuwa na hausawa a yau, musamman a garin Sakkwato. Shi wannan bincike zai mayar da hankali ne kan abincin bukukuwan aure da haihuwa na zamani a Sakkwato.

    Gwarjo, da wasu (2005) sun rubuta littafi mai suna: Aure a Jahar Katsina. Wannan littafi ya ƙunshi bayanai da dama game da aure, musamman aure a Katsina. Littafin ya kawo ma’anar aure da kuma irin al’adun da suke cikin aure. Saboda haka littafin yana da dangantaka da wannan aikin kasancewa sun yi tarayya game da maganar aure. Sai dai kuma littafin nasu bai yi cikakken bayani na musamman ba game da abincin zamani na bukukuwan aure da haihuwa a birnin Sakkwato. Shi wannan bincike zai mayar da hankali ne kan abincin bukukuwan aure da haihuwa na zamani a Sakkwato.

             

    Maƙalu

    Bunza, (2013) ya gabatar da muƙala a Taron Ƙara wa Juna Sani na ƙasa da aka gabatar a Jami’ar Ummaru Musa ‘yar’adu, mai taken: “Zama Da Maɗaukin Kanwa Ke Sa Farin Kai: Nason Baƙin Al’adu Cikin Al’adun Auren Hausawa.” Wannan takarda ta Bunza ta mayar da hankali ne zuwa ga yadda aka samu baƙin al’adu a cikin lamurran auren Bahaushe a yau. Hakan kuwa ya samo asali ne daga irin cuɗanyar Hausawan da wasu al’ummu da kuma sauran abubuwan da zamani ya kawo kamar kallace-kallacen tibi da sauransu. Dangantakar takardar Bunza da wannan kundi shi ne kasancewar dukkaninsu sun taɓa batu a kan hidimar aure. Sai dai shi ya karkata ne kan irin nason wasu al’adu da ake samu a cikin hidimar auren Hausawa. A ɗaya ɓangaren kuma, shi wannan bincike zai mayar da hankali ne kan abincin bukukuwan aure da haihuwa na zamani a Sakkwato.

              Hassan, (2013) ya gabatar da takarda a taron ƙara wa juna sani da aka gabatar a Jami’ar Ummaru Musa ‘Yar’aduwa mai taken: “Nason Baƙin Al’adu Kan Al’adun Aure Da Haihuwa Da Mutuwa Na Hausawa.” Wannan takarda ta kalli yadda aka samu shigowar wasu baƙin al’adu cikin hidindimun Bahaushe da suka shafi haihuwa da aure da kuma mutuwa. Irin waɗannan baƙin al’adu da suka shafi aure sun haɗa da fati da ma wasu tarurruka na daban. Asalin irin waɗannan tarurruka kuwa al’adan Turawa ne da Indiyawa.

    Takardar ta Hassan na da alaƙa da wannan kundi kasancewar dukkaninsu sun taɓo batun hidimar aure da kuma haihuwa. Sai dai kuma suna da bambanci, domin shi Hassan ya dubi al’adu uku ne, wato aure da haihuwa da kuma mutuwa. Saboda haka bai kawo cikakken bayani ba game da abincin Hausawa na zamani na bukukuwan aure da haihuwa a garin Sakkwato. Shi kuwa wannan bincike zai mayar da hankali ne kan abincin bukukuwan aure da haihuwa na zamani a Sakkwato.

    1.2 Hujjar ci Gaba da Bincike

    Masana da manazarta da dama sun yi rubuce-rubuce daban-daban game da bukukuwan Hausawa. Waɗannan bukukuwa sun haɗa da na aure da haihuwa da makamantansu. Wasu daga cikin irin waɗannan rubuce-rubucen sun haɗa da: Abu, 1985; Sani, 1997; Abdullahi, 1997; B/Kebbi, 1997; Wasagu, 2002; Hassan, 2013. Bayan wannan kuma, akwai rubuce-rubuce da aka yi game da abinci, sun haɗa da: Maude, 1990 da Yabo, 2006 da makamantansu.

    Sai dai abin lura shi ne, duk cikin waɗannan rubuce-rubucen masana da manazarta (game da bukukuwa da kuma cin abinci), ba a samu aiki guda ɗaya wanda ya yi magana game da abincin abincin bukukuwan aure da haihuwa na zaman a garin Sakkwato ba. Saboda haka ne wannan aiki ya samu hujja da ƙarfin guiwar gudanuwa, domin fito da iri-iren abincin bukukuwan Hausawa na aure da haihuwa a birnin Sakkwato waɗanda zamani ya zo da su.

    1.3 Farfajiyar Bincike

            Wannan bincike zai taƙaita ne kawai kan nazarin abincin bukukuwan Hausawa na aure da haihuwa a garin Sakkwato a yau. Wannan na nuni da cewa, muhallin wannan bincike shi ne birnin Sakkwato. Haka ma, farfajiyar binciken shi ne abincin bukukuwan Hausawa na aure da haihuwa a yau. Saboda haka, dukkanin bayanai da wannan bincike zai zaƙule, zai nemo su ne ta la’akari tare da bincike game da ire-iren abincin da ake amfani da su a zamanin yau, yayin bukukuwan Hausawa na aure da kuma haihuwa. Bayan kammaluwan wannan aiki, za a iya amfani da sakamakon binciken wajen kwatanta shi da abubuwan da ke faruwa ga sauran sassan yankin ƙasar Hausa.

    1.4 Hanyoyin Gudanar da Bincike

              Za a yi amfani da wasu hanyoyi ko dabaru domin gudanar da wannan bincike. Hanyoyi sun haɗa da ziyartar ɗakunan karatu domin samun bayanai daga littattafai da kundayen digiri na uku da na biyu da ma na farko, har ma da takardun da aka gabatar a tarukan ƙara wa juna sani. Bayan haka, aikin zai yi amfani da kafar intanet domin samo bayanai masu alaƙa da wannan bincike. Wato musamman bayanan da suka shafi abincin Hausawa a yau da kuma bukukuwan Hausawa na aure da haihuwa. Daga ƙarshe kuma aikin zai yi hira da masana da kuma ma’aurata waɗanda suka tsallako irin waɗannan bukukuwa. Duk dai waɗannan domin binciko abincin bukukuwan aure da haihuwa na zamani na Hausawa.

    1.5 Muhimmancin Bincike

              Idan aka yi la’akari da canje-canjen da zamani ke kawowa ga fannonin rayuwar Bahaushe a yau, lallai sha’anin abincin Hausawa na da buƙatar da a gudanar da bincike a kansa. Musamman ta abincin Hausawa na bukukuwan aure da haihuwa a yau. Kasancewar su kansu al’adun auren da na haihuwa zamani ya yi tasiri a kansu. Ma’ana an samu sauye-sauyen yadda ake gudanar da su ta fuskoki da dama. Wannan bincike zai ba da haske game da wurin da aka baro da kuma inda ake a yau, da ma inda aka dosa.

              A taƙaice kenan, wannan bincike zai kasance mai amfani ta fuskoki da dama. Da farko zai kasance mai amfani ga al’umma baki ɗaya yayin da ya binciko irin abincin bukuwan aure da haihuwa na Hausawa a yau. Baya ga haka, aikin zai kasance mai amfani ga malumman al’ada da na adabin. Domin ya leƙo musu wani abin da za su faɗaɗa bayaninsa yayin da suke koyar da ɗalibansu a fagen ilimi daban-daban. Har ila yai, aikin zai kasance mai amfani ga ɗaliban ilimi, wato a matsayinsa na wani abin karatu. Daga ƙarshe kuma, wannan aiki zai iya zama shimfiɗa wanda daga kansa ne za a ɗora wasu bincike a nan gaba.

    1.6 Kammalawa

    Wannan babin an buɗe shi ne da gabatarwa. Ƙarƙashin gabatarwar an bayyana maƙasudin wannan bincike da kuma dalilan da suka sanya ake ganin dacewar gudanar da wannan bincike. Sannan an kawo hasashen sakamakon wannan bincike tare da amfanin binciken. Bayan haka kuma an gangaro bayani kan bitar ayyukan da suka gabata. A nan ne aka yi bitar ayyuka waɗanda suke da dangantaka da wannan aiki. Daga nan kuma sai aka kawo hujjar ci gaba da bincike. Sannan babin ya kawo muhimmancin bincike da kuma hanyoyin gudanar da bincike. Baya ga haka babin ya fayyace iyakacin binciken inda ya yi bayanin cewa, aikin zai taƙaita ne a garin Sakkwato. 

    BABI NA BIYU

    ABINCI DA BUKUKUWAN HAUSAWA

    2.0 Shimfiɗa

              Wannan babin zai dubi abinci, musamman na Hausawa. Wanan ya haɗa tun daga kan ma’anar abinci da kuma ire-iren abinci. Sannan ababin zai dubi bukuwan Hausawa, tun daga kan ma’anar bukukuwa da kuma ire-ire. Baya ga haka, babin zai yi tsokaci game da bukukuwan aure da kuma na haihuwa a ƙasar Hausa.

    2.1 Ma’anar Abinci

              Abinci dai na nufin duk wani abin da ɗan Adam zai sanya a ciki domin ya magance masa yunwa. Sa’id (2006) ya bayyana ma’anar abinci da cewa:

    Duk abin da ake ci don maganin yunwa (Sa’id edita, 2006:1).

              Yabo, (2006) ya bayyana cewa, amfanin abinci kusan daidai yake da amfanin rayuwa. Dalili kuwa shi ne, da zaran aka ce ɗan Adam ya rasa abinci na wani tsawon lokaci, to haƙiƙa ba zai iya rayuwa ba.

    2.2 Rabe-raben Abinci

              Hausawa suna da abinci iri-iri. Hakan na da nasaba da irin yalwar ƙasa da kuma albarkar noma da Allah sanya wa ƙasar Hausa (Mohammad, 2010).

    2.2.1 Abincin Yau-da-kullum

            Abincin yau-da-kullum shi ne irin wanda ake ci kowace rana domin ci gaba da rayuwa. Wato ana cin wannan abinci ne domin magance yunwa ba domin wani dalili na daban ba, kamar ƙwalama ko magance kwaɗayi ko buki da makamantansu. Yawanci akan ci abinci ne sau uku, wato:

    i.                   Abincin Safe: Wani lokaci akan kira shi da karya kumallo. Wannan shi ne irin abincin da ake ci da safe.

    ii.                 Abincin Rana: Irin wanan abinci shi ne wanda ake ci da rana.

    iii.              Abincin Dare: Wasu sukan kira wannan abinci da ‘kalaci’. Shi ne irin wanda ake ci da dare.

    Ire-iren abincin da Hausawa suke ci yau da kullum sun haɗa da:

    Jadawali na 1: Misalan Abincin Yau-da-kullum

     

    Nau’in Tuwo

    Nau’in Miya

    Nau’in Abinci Mai Ruwa-ruwa

    Nau’in Dafuwa ta Daban

    1.      

    Ɓula

    Miyar alayyahu

    Fura

    Fate

    2.      

    Tuwon masara

    Miyar zogala

    Kunun gero

    Waina

    3.      

    Tuwon dawa

    Miyar sure

    Kunun tsamiya

    Taliya

    4.      

    Tuwon shinkafa

    Miyar guro

    Kudun shinkafa

    Ƙosai

    5.      

    Tuwon maiwa

    Miyar kabewa

    Kunun alkama

    Rogo

    6.      

    Tuwon alkama

    Miyar shuwaka

    Kunun koko

     

    Madogara: (Yabo, 2006)

    2.2.2 Abincin Ƙwalama/Maƙulashe

              Abincin ƙwalama ko maƙulashe shi ne irin abincin da ake cin sa ba don yunwa ba. Akan ci ne kawai domin a mai da miyau (kwaɗayi). Irin wannan abinci na ƙwalama za a iya kallonsa ta ɓangarori guda biyu:

    1.     Kulagana: Wannan shi ne irin abincin ƙwalama wanda ake dafawa a cikin gida. Wato akan dafa wani abinci ɗan kaɗan, wanda ba a saba ci ko da yaushe a gida ba, sai a ci shi a marmarce domin mai da ƙwaɗayi.

    2.     Abincin ƙwalamar sayarwa: Yawanci a garuruwan Hausawa akan samu masu talla suna sai da abincin ƙwalama a bisa tituna da wurare na musamman, kamar bakin kasuwa ko bakin tasha da sauransu.

    Misalan abincin ƙwalama/maƙulashe sun haɗa da:

    a.      Alewa

    b.     Ƙaya da sukari

    c.      Fanke

    d.     Ɗanbuɗus

    e.      Ganda da makamantansu.

    2.2.3 Abincin Bukukuwa

              Abincin bukukuwa su ne irin abincin da ake samarwa yayin bukukuwa. Irin waɗannan abinci ba a faye ganin su ba sai lokutan bukukuwan Hausawa. Daga cikin irin bukukuwan Hausawa da ake yin girke-girke akwai:

    1.     Bukin Aure: Yayin bikin aure akan samar da abinci daban-daban domin baƙi ‘yan uwa da maƙwabta.

    2.     Bukin Suna: Ranar sanya wa jariri suna, maƙwabta da ‘yan uwa na nesa da na kusa sukan taru domin taya murna. A irin wannan rana, akan dafa abinci iri daban-daban.

    3.     Bukin Cika-Ciki: Wannan biki ne da ya samu bayan zuwan Musulunci ƙasar Hausa. Akan yi shi ne bayan sallar layya, wato babbar salla. Shi ma akan dafa abinci yayin wannan buki.

    Waɗannan kaɗan kenan daga cikin misalan bukukuwan Hausawa waɗanda ake dafa abinci dominsu. Yabo, (2006) ya kawo misalan wasu daga cikin irin abincin da ake dafawa yayin bukukuwan Hausawa kamar haka:

    1.     Cincin

    2.     Alkaki

    3.     Dibila

    4.     Kunun zaƙi

    5.     Kwango da makamantansu.

    2.3 Ma’anar Buki

              Mutum ɗaya ba ya yin biki. Buki ya ƙunshi taron mutane da ke haɗuwa domin nuna farinciki game da wani abu, kamar zagayowar shekara ko girbe amfanin gona ko aure, ko haihuwa da makamantansu. Gusau (2012) ya bayyana ma’anar buki kamar haka:

    Buki wani taro ne na mutane da suke shiryawa, su gudanr don nuna farin cikinsu a kan wata baiwa da Allah ya yi ma wani daga cikinsu ko ya yi wa wasu.

    (Gusau, 2012: 26)

    Wannan ma’ana ta Gusau tana nuna cewa, biki na faruwa ne a sanadiyar farin cikin wata baiwa da ɗan Adam ya samu, ko kuma wasu mutane suka samu. Saboda haka, taron jama’a don nuna alhini ko baƙin ciki, kamar lokacin mutuwa da makamantansu, ba zai kasance buki ba. Gusau ya yi ƙarin bayani game da buki da cewa:

    Buki ana yin sa don a nuna irin farin cikin da ake da shi ga wani abin farin ciki da ya faru, ko don tunawa da wani abu muhimmi ko don zagayowar wata rana. Biki ko bukukuwa suna daga cikin fitattun al’adun Hausawa waɗanda suka sami asali tun daga kaka da kakanni.

    (Gusau, 2012: 26)

              Wannan bayani na Gusau na nuna cewa, kowane biki yana ɗauke da sigar nuna farin ciki da annashuwa. Sannan, biki daɗaɗɗen al’amari ne wanda aka gada tun iyaye da kakanni. Za a iya hasashen cewa, an fara samun bukukuwa a ƙasar Hausa tun lokacin da Bahaushe ya fara gayyatar ‘yan uwansa domin taya shi murnar wani abin da ya same shi. Bayyana farkon faruwar irin wannan lamari kuwa abu ne mai buƙatar zurfafa bincike matuƙa.

    2.4 Ire-iren Bukukuwan Hausawa

              Za a iya raba bukukuwan Hausawa ta fuskoki daban-daban. Misali, za a iya raba bukukuwan ta fuskar lokacin da ake gudanar da su, kamar ƙarshen shekara ko mako-mako da makamantansu. Za kuma a iya kallon bukukuwan Hausawa ta fuskar rukunin jama’ar da ke bukukuwan suka shafa, kamar bukin masu sana’a (wanda ya shafi sana’o’i) ko bukukuwan sarauta (wanda ya fi shafar faɗa) da makamantansu. A cikin wannan aikin, za a kalli rabe-raben bukukuwan Hausawa ta fuskar kasancewarsu ko dai na gargajiya ko kuma na zamani.

    2.4.1 Bukukuwan Gargajiya

              Irin waɗannan bukukuwa su ne bukukuwan da Bahaushe ya gada iyaye da kakanni. Wato tun tasowar Bahaushe ya tarar da irin waɗannan bukukuwa. Ko da yake, akan samu sauyi daga ta fuskar yadda ake aiwatar da bukukuwan a dalilin tasirin zamani. Irin waɗannan bukukuwan gargajiya sun haɗa da:

    1.    Bikin Buɗar Daji: Irin wannan buki ana gudanar da shi ne shekara-shekara. Wannan ne ma ya a ake kiran sa da bukin cikar shekara a wasu wurare a ƙasar Hausa. Wannan biki yawanci yakan haɗa bokaye da ‘yan bori da mafarauta da makamantansu. Waɗannan rukunnen jama’a sukan haɗu su tattauna yadda fasalin bikin zai kasance. Gusau (2012) ya bayyana cewa, mafi yawanci akan yi amfani da siyaki a lokacin bukin buɗin daji. Akan kashe wannan dabba sannan a feɗe cikinta, inda za a tarar da nau’o’in hatsi daban-daban. Sun haɗa da gero da dawa da maiwa da makamantansu. Daga nan ne jagororin za su tantance irin amfanin gonan da zai yi kyau a shekara mai zuwa. Saboda haka, kowane manomi zai yi ƙoƙarin shuka wannan amfanin gona. Yayin bikin, akan gudanar da kaɗe-kaɗe da bushe-bushe da sauran shagulgula daban-daban.

    2.    Bikin Kaciya: A da, ba a yi wa yaro guda kaciya. A maimakon haka, akan tara yara ne sa’o’in juna sannan a musu kaciya lokaci guda. Sarkin aska shi ke jagorancin kaciyar yaran. Za a gina rami a cikin zaure ko shigewa sannan a tanadi toka wanda ake amfani da ita wajen tsai da jini. A wancan lokaci, Hausawa sun mayar da irin wannan hidima ta kaciya a matsayin biki. Amma a yanzu, tuni Hausawa sun watsar da irin wannan al’ada ta kaciyar yara lokaci guda.

    3.    Bukukuwan Naɗin Sarauta: Yayin naɗin sarauta a ƙasar Hausa. Mutane kan taru daga wurare daban-daban. Wannan taro yakan haɗa da sarakuna da wakilai daga garuruwa na kusa da na nesa, tare kuma da talakawan gari. Akan yi shagulgula da dama, kamar kaɗe-kaɗe da raye-raye da bushe-bushe. Har yanzu akwai irin waɗannan bukukuwa a ƙasar Hausa. Sai dai tasirinsu ya ragu idan aka kwatanta su da yadda abin yake a da.

    4.    Bukin Hawan Salla: Shigowar Musulunci ƙasar Hausa ya zo da salloli waɗanda suka haɗa da na kowace rana (guda biyar) da kuma sallar Juma’a, da wasu sallolin na lokaci zuwa lokaci kamar babbar salla da ƙaramar salla da kuma sallar jana’iza da na roƙon ruwa da makamantansu. Yayin babbar salla da ƙaramar salla, akan gudanar da bukukuwan Hawan Salla a ƙasar Hausa. A yayin irin waɗannan bukukuwa, sarki da jama’arsa za su ciyo ado sannan a yi wa dawaki ado. Haka za a zaga gari ana karɓar gaisuwa daga talakawa. Daga ƙarshe kuma za a koma fada inda za a ci gaba da kaɗe-kaɗe da bushe-bushen murnar salla.

    5.    Bukin Masu Sana’o’i: Irin waɗannan su ne bukukuwan da masu sana’o’i daban-daban suke aiwatarwa. Sun haɗa da:

    i.                   Bukin Manoma

    ii.                 Bukin Rundawa

    iii.              Bukin Buɗe Kasuwa

    iv.               Bukin Maƙera

    v.                 Bukin Wanzamai

    vi.               Bukin Masunta

    vii.            Bukin Maharba da makamantansu.

    Waɗannan wasu kenan daga cikin bukukuwan Hausawa na gargajiya. Akwai saura da dama waɗanda suka haɗa da bukin buɗar kai, da bukin shan kabewa da bukin ba da sandar muli da makamantansu.

    2.4.2 Bukukuwan Zamani

              Idan aka ce bukukuwan zamani, ana nufin nau’in bukukuwa wanda a sama Bahaushe ya same su. Wato ba irin waɗanda ya taso tun hasali ya tarar da ana aiwatar da su a ƙasar Hausa ba. Irin waɗannan bukukuwan Hausawa na zamani sun haɗa da:

    1.    Fatin Aure: Wannan biki ne da ya samu bayan cuɗanyar Hausawa da baƙin al’ummu musamman Turawa. Irin wannan biki akan yi shi ne bayan aure. Maza da mata sukan haɗu, sannan akan yi girke-girke tare da tanadar kayan shaye-shaye waɗanda ba na meye ba na maye ba, (duk da cewa akwai fatin da ake amfani da kayar maye). Sannan za a kawo mai kwamfuta ɗauke da waƙoƙin zamani daban-daban, wanda ake kira ‘dije’ (DJ). Haka za a ci a sha sannan a yi ta rawa maza da mata. Haƙiƙa irin wannan sabon salo ne wanda ya ci karo da sananniyar al’adar Hausawa ta biki.

    2.    Bikin Zagayowar Ranar Haihuwa: Wannan ma wani biki ne wanda ya shafi mutum guda. Akan yi irin wannan biki yayin da wani ko wata ya/ta ƙara shekara, wato ranar haihuwarta/sa ya zagayo. A nan abokai (wani lokaci har da iyaye) za su haɗa ƙwarya-ƙwaryar biki domin murnan wannan rana. Akan yi girke-girke sannan yawanci akan kawo ‘dije’ domin wannan hidima. Bikin zagayowar ranar haihuwa ma baƙuwar al’ada ce wadda ta samu bayan cuɗanyar Hausawa da Turawa. A harshen Ingilishi ana kiran irin wannan biki da Birth Day Party.

    3.    Bikin Kammala Makaranta: Turawa sun zo da karatun boko ƙasar Hausa. Ya zuwa yau, wannan karatu ya riga ya zama hanyar rayuwa ga mutane da dama. Domin karatun na boko shi ne ci da sha na ɗunbin jama’a. Wato kamar dai yadda karatun ne ke ba da damar a samu aikin gwamnati domin ɗaukar albashi. Ɗaliban da suka kammala wani mataki na karatun boko, kamar sakandare ko jami’a ko kwaleji, sukan shirya buki domin murnan wannan nasara. Yayin irin waɗannan bukukuwan kammala wani matakin karatun boko, akan yi dafe-safe da soye-soye, sannan a ɗauko ‘dije.’ Haƙiƙa irin wannan buki ma baƙo ne ga Bahaushe. Ya samu ne bayan cuɗanyar Bahaushe da baƙin al’ummu.

    4.    Bukukuwan Tallan Haja: Zamani ya zo da wani sabon salon tallata haja da ake gabatarwa ta sigar biki. Kamfanunnuka su ne suka fi amfani da wannan salo. Kaffununnuka irin na MTN da Indomie da Glo da makamantansu, duka sukan yi amfani da irin wannan bukukuwa domin yin talla. Yadda ake yi kuwa shi ne, za a zo da kayan amsa kuwa na zamani manya-manya masu kai sautuka nesa. Sannan za a zo da kwamfuta da ke ɗauke da waƙoƙi iri-iri. Akan samu kasuwa, ko wurin cunkuson jama’a sai a sanya waɗannan kaɗe-kaɗe. Akwai ‘ya’yan kamfanin maza da mata da za su yi ta tiƙar rawa. Hakan zai janyo hankulan jama’a, a taru wurin. Daga nan za a ci gaba da wasanni iri-iri, kamar gasar rawa, da gasar ƙwanji da makamantansu. Waɗanda suka yi nasara a gasannin akan ba su kyaututtuka. Kamfanin kuwa za su riƙa tallan hajarsu cikin hikima a yayin wannan biki.

    2.5 Bukin Aure

              Bahaushe ya ɗauki aure a matsayin al’ada mai matuƙar ƙarfi da muhimmanci. Zuwan addinin Musulunci kuwa ya ƙara ƙarfafa wannan al’ada ta aure. Bahaushe ya yi amanna cewa, cikar kimar mutum shi ne ya yi aure. Sannan mai kuɗi ko shugaba ba shi da cikar daraja har sai ranar da ya yi aure (Gada, 2014). Masana da manazarta da dama sun bayar da ma’anar aure a rubuce-rubucensu daban-daban. Daka cikin waɗannan amnazarta akwai Funtuwa da Gusau, inda suka ba da ma’anar aure tare da sharhi a kansa kamar haka:

    Aure yarjejeniya ce tsakanin mace da namiji bisa ƙa’idoji na al’ada. Kafin zuwan Musulunci, riƙon aure yana hannun mace ne, domin a tsarin gargajiya mutum yana da ‘yancin ya auri mata ko nawa yake so. Kuma yawan mata shi ke nuna arzikin mutum. Mace idan ya auro ta ita za ta zo da ƙyauren ɗakinta, ta yaɓe ɗakinta ta shafe shi, ta daddaɓe shi. kafin zuwan Musulunci mace ta fi namiji aiki, ita ke sharar gona da shuka da noma, da huɗa da girmbi da sussuka da kai mafanin gona gida. Ita za ta ci da kanta da mijinta, da ‘ya’yanta. (Funtuwa da Gusau, 2010)

    Baya ga wannan, Abdullahi, (2003) a cikin Usman, (2014) ya ba da ma’anar aure da cewa, aure hanya ce ta rayuwa mai ɗorewa tsakanin mace da namiji wadda aka gina ta a kan wasu shimfiɗaɗɗun ƙa’idoji da al’umma ta tanada waɗanda kan haifar da nishaɗi tsakanin ma’auratan da taimakon juna da samar wa ‘ya’yansu asali da kyakkyawan reno.

    Duk da cewa akan yi auren dole a wasu lokuta, al’adar Bahaushe ba ta yarda da auren dole ba. Saboda haka kafin a ɗaura aure tsakanin mace da namiji, dolene a samu amincewa a tsakaninsu (Saulawa a cikin Gada, 2014). A taƙaice za a iya cewa, aure na nufin ƙulla wata alaƙa ta musamman tsakanin namiji da mace bisa wasu dokoki keɓantattu waɗanda suka haɗa da bayar da sadaki da waliye da amincewar ma’aurata. Gusau (2012) ya bayyana ma’anar aure da cewa:

    A wajen Hausawa, aure wata alaƙa ce halattacciya, wadda ta halatta zaman tare tsakanin ma’aurata guda biyu, wato miji da mata. Ana yin sa ne, saboda abin da aka haifa ya sami asali, da mutunci da kiyayewar al’umma.

    (Gusau, 2012: 18)

    Babajo, (2001) ya ruwaito Alhasan (1982) yana cewa:

    Aure alaƙa ce ta haliccin zaman tare tsakanin namiji da mace. Ana yin sa ne saboda abin da aka haifa ya sami asali da mutunci da ɗaukaka da kiwon iyaye.”

    (Babajo, 2001: 12).

              Kasancewar aure abu mai muhimmanci ga al’ummar Hausawa, akan gudanar da bukukuwa domin shagali da nuna farin cikin aure. Yayin bikin aure, akan yi dafe-dafe da toye-toye daban-daban. Sannan maƙwabta da ‘yan uwa na kusa da na nesa sukan halacci wannan biki.

              Bukin aure ya samu sauye-sauye bayan zuwan Musulunci. Kafin jihadi, abu na farko da ake gudanarwa a lamarin aure shi ne toshi. Wato kyauta da saurayi yakan ba wa budurwa. Saurayi zai ta bibiyar yarinya har dai ya kai ga yi mata magana. Bayan sun shirya tsakaninsu, daga baya sai iyaye su shiganar, har a kai ga batun aure.

              Bayan zuwan Musulunci kuwa, musamman bayan jihadi jaddada addinin Musulunci, yawanci akan bi koyarwar addini ne a harkokin aure a ƙasar Hausa. Wanann ya haɗa da neman izinin iyayen yarinya kafin kafin saurayi ya yi mata magana. Sannan bayan zuwan Musuluncin, Hausawa, musamman waɗanda suka riƙi Musulunci sukan tabbatar da bin ƙa’idojin aure waɗanda suka shafi sadaki da alwali da makamantansu (Abba, 2011).

              Bayan Hausawa sun samu cuɗanya da Turawa, sai aka samu sauye-sauye da dama a cikin al’adunsu (Hausawa) na aure. Wannan ya haɗa da sigar neman aure, da hidimomin aure da kuma irin bukukuwan da ake shiryawa yayin bikin aure (tarurruka). Irin waɗannan bukukuwan aure bayan zuwan Turawa sun haɗa da; ranar iyaye (mothers’ day), da ranar Larabawa (Arabian day) da ranar Indiyawa (Indian day) da makamantansu (Gada, 2014).

    2.6 Bukin Haihuwa

              Haihuwa abu ne na farin ciki da ake yin biki dominsa. Kusan burin kowaɗanne ma’aurata shi ne su ga ƙwansu. Auren da ya jima ba tare da an haihu ba, na jawo cece-kuce a tsakanin al’umma. Wani lokaci har abin ya kai ga zunɗe da nuna har ma da habaici da ba’a. gusau, (2012) ya bayyana bikin haihuwa da cewa:

    Al’adun bikin haihuwa ko zanen suna al’adu ne, da Hausawa ke gudanarwa a lokacin a mace ta haihu, har zuwa ranar da aka eaɗa wa abin da aka haifa suna.

    (Gusau, 2012: 36)

    Mayan mace ta haihu, akwai al’adu daban-daban da ake aiwatarwa, har dai ta kai ga ranar sanya wa jariri suna. Irin waɗannan al’adun bayan haihuwa sun haɗa da; luguɗe, da guɗa da shan magani da karɓar biƙi da wankan biƙi da da barkar haihuwa, da makamantansu. A ranar suna ne ake yin asalin bikin haihuwa. Tun safe akan raba goro a masallaci, sannan a sanar da sunan da aka raɗa wa jariri, tare da yin addu’ar Allah ya raya.

    A cikin gida kuwa, mata za su fara girke-girke iri-iri. Maƙwabta da ‘yan uwa na kusa da na nesa za su riƙa tuɗaɗowa zuwa gidan domin wunin suna. A nan za a ci a sha. Yara mata kuwa za su kama raye-raye da waƙe-waƙen wasanninsu na yara.

    2.7 Naɗewa

              A wannan babi, an kawo ma’anar abinci tare da ire-iren abincin Hausawa. Baya ga haka, babin ya kawo bayanai game da bukukuwan Hausawa tare da ire-irensu. Daga ƙarshe kuma babin ya yi tsokaci game da bukin aure da kuma na haihuwa a ƙasar Hausa.

     

     

     

     

     

     

     

     

     

     

     

     

    BABI NA UKU

    ABINCIN BUKUKUWAN HAUSAWA NA ZAMANI A BIRNIN SAKWKATO

    3.0 Shimfiɗa

            Akwai abincin zamani iri-iri da ake amfani da su a birnin Sakkwato yayin bukukuwan aure da kuma na suna. Sai dai wani abin lura shi ne, da yawa daga cikin abincin da ake amfani da su a tarukan bukukuwan aure, akan kuma yi amfani da su a tarurrukan bukukuwan suna. Amma duk da haka, a wasu lokuta akan samu ‘yan bambance-bambance a nau’ukan abincin bukukuwan aure da na suna. Wannan abin haka yake a ɓangaren abubuwan sha na zamani da suka shafi bukukuwan aure da na suna a birnin Sakkwato. Wannan babi na uku zai kawo jerin ire-iren abubuwan ci da na sha na zamani da ake samu yayin bukukuwan aure da na haihuwa a birnin Sakkwato. Sannan babin zai kawo bayanin yadda ake samar da kowanne a taƙaice.

    3.1 Abincin Bukin Aure Na Zamani A Birnin Sakkwato

    Kamar yadda bayani ya gabata a ƙarƙashin gabatarwar wannan babi, ire-iren abinci da dama da ake samu a gidanjen bikin aure akan same su a na bikin suna. Amma duk da haka, akan samu ‘yan bambance-bambance. Wannan sashen ya tattaro irin abincin da aka fi samu a tarurrukan bukukuwan aure. Za a tattauna su ƙarƙashin waɗannan kasha-kashe:

    a.      Dibila/dibilon

    b.     Alkaki

    c.      Nakiya

    d.     Tawaita/tayota

    e.      Liyafa

    f.       Kek

    g.     Jolof ɗin taliya

    h.     Jolof ɗin shinkafa

    i.       Shadaka

    3.1.1 Dibila/dibilon

              Wannan na ɗaya daga cikin abubuwan ci na bukukuwan aure. Akan yi shi ne a matsayin abin marmari, ba abin ci a ƙoshi ba. A ƙasa an bayyana yadda ake samar da shi:

    Kayan Haɗin Dibila

           i.            Filawa/fulawa

         ii.            Sukari

      iii.            Man gyaɗa

       iv.            Yis

    3.1.2 Alkaki

              Wannan ma ɗaya ne daga cikin ire-iren ababan ci a gidajen bukukuwan aure. A ƙasa an bayyana yadda ake samar da alkaki:

    Kayan Haɗin Alkaki

           i.            Alkama

         ii.            Sikari

      iii.            Man gyaɗa

       iv.            Nono mai tsami

    Yadda Ake Alkaki

              Akan kai alkama a ɓarza a injin niƙa, a samar da ƙullinta. Daga nan za a cuɗanya ƙullin alkamar da nono mai tsami a killace wuri ɗaya har zuwa da safe. Yayin da gari ya waye, akan nemi turmi a lillisa wannan kwanannanen ƙulli domin ya gauraya sosai. Bayan an kammala kuma sai a aza man gyaɗa bisa wuta. Daga nan za a riƙa mulmula wannan gwaurayayyen ɓarzajjen alkama ɗaiɗai girman da ake buƙata, sannan a riƙa jefawa cikin tafasasshen mai. Bayan ya soyo daidai gwargwado sai a tsame. Daga nan kuma za a riƙa tsomawa cikin sukari wadda shi ma aka tafasa ya zama ruwa-ruwa. Yayain da aka yi haka, alkaki ya samu Kenan.

              Sai dai wani abun lura shi ne, akan yi alkaki ne a lokutan bukin aure ba domin a ci a ƙoshi ba. Akan yi ne kawai a matsayin abin cin marmari na kusa da baka. Wanann ne ma ya sanya, mafi yawa a leda ake ƙuƙƙullawa, a riƙa ba wa baƙin da suka samu halartar hidimar auren.

    3.1.3 Nakiya

              Nakiya ma ta kasance ɗaya daga cikin kayayyakin ci da ake samu a gidajen bukukuwan aure a birnin Sakkwato. Wannan aiki ya bibiyi yadda ake samar da nakiya, tare da tsara bayanin kamar haka:

    Ababan Haɗin Nakiya

           i.            Dawa/gero/maiwa

         ii.            Sukari

      iii.            Tsamiya/lemon tsami

       iv.            Citta

         v.            Barkono

    Yadda Ake Nakiya

            Akan je a surfa irin hatsin da za a yi amfani da shi, wato ko dai gero ko dawa ko maiwa. Naga nan kuma za a niƙo shi a injin niƙa. Naga nan za a sanya garin a tukunya a aza bisa wuta. Za a riƙa juya garin sannu a hankali har sai an tabbatar ya soyu yadda ya kamata.

              A ɗaya ɓangaren kuma, za a ɗauko sanya tukunya sannan a aza bisa wuta. Za kuma a sanya tsamiya ko lemon tsami a ciki. Haka za a riƙa motsa shi har sai ya fara yauƙi, wanda hakan ne ke nuna ya yi daidai. Daga nan za a haɗa wannan sukari da garin da aka soya sannan ya gauraya sosai. Da zarar an yi haka, to nakiya ta samu. Ita ma nakiya ba abin ci a ƙoshi ba ce. Akan yi ne a matsayin abin marmari yayin tarurrukan bikin aure.

    1.3.4 Tawaita/tayota

              Wannan ma nau’i ne na abinci da ake yi a gidajen bikin aure a birnin Sakkwato. A ƙasa an kawo bayanin yadda ake samar da wannan abinci kamar haka:

    Kayan Haɗin Tawaita

           i.            Filawa

         ii.            Sukari

      iii.            Gishiri

       iv.            Man gyaɗa

    Yadda Ake Tawaita

              Da fari akan kwaɓa filawa ruwa-ruwa. A ciki za a sanya sukari. Sannan sai a sanya gishiri amma ɗan kaɗan, domin ya samar da waɗi ɗanɗano na musamman. A ɗaya ɓangaren kuma, za a aza mangyaɗa bisa wuta. Da zarar komai ya daidaita, za a ɗauko masakin tawaita. Wannan masaki dai wani ɗan ƙarfe ne mara kauri, wanda kuma yake da ɗan tsawo kaɗan, daidai riƙewa. Akan samar da wannan ƙarfe ne musamman domin yin tawaita.

              Yadda ake aiwatarwa kuwa shi ne, akan sanya ƙarfen a cikin filawa. Hujin kororon da ke jikin ƙarfen zai ɗauko filawa ‘yar kaɗan. Daga nan sai a tsoma ƙarfen cikin mangyaɗa. Filawar da ƙarfen ya ɗauko za ta sauƙa cikin wannan mangyaɗa da ke tafasa. Haka za a ci gaba da yi har sai filawar ta ƙare. Da zarar an gama suyar, to kuwa tawaita ta samu. Ita ma abinci ne na marmari ba na ci a ƙoshi ba.

    1.3.5 Liyafa

            Wannan ma wani nau’in abinci ne da ake samarwa a gidan biki a wasu lokuta. Wannan bincike ya bibiyi yadda ake samar da shi, tare da tattara bayanan kamar yadda za su biyo a ƙasa:

    Kayan Haɗin Liyafa

           i.            Filawa

         ii.            Sukari

      iii.            Man gyaɗa

       iv.            Gishiri

         v.            Madara

       vi.            Bakin foda (barking fowder)

    vii.            Botta (butter)

    Yadda Ake Liyafa

              Akan kwaɓa filawa da sukari da bakin foda da botta, sannan a sanya gishiri kaɗan. A lokuta da dama akan sanya kwaɓaɓɓiyar filawar a baƙar leda domin ba ta adanawa mai kyau. Daga nan kuma za a sanya man gyaɗa bisa wuta. Sai a ɗauko kwaɓaɓɓiyar filawar a riƙa yin siraran yanka masu ɗan madaidaicin tsawo. Daga nan za a riƙa soyawa cikin wanann man gyaɗa. Da zarar an ƙare, to liyafa ta samu. Wannan nau’in abincin biki ma ba a ci a ƙoshi. A maimaikon haka, ya kasance abin marmari ne kawai.

    1.3.6 Kek

            Kek yana ɗaya daga cikin abincin da ake yawan yi a lokacin bukukuwa a garin Sakkwato. Ya kasance abinci mai farin jinni. A ƙasa an rattabo bayanin yadda ake samar da shi:

    Kayan Haɗin Kek

           i.            Filawa

         ii.            Man gyaɗa

      iii.            Sukari

       iv.            Gishiri

         v.            Bakin foda (barking fowder)

       vi.            Madarar ruwa

    vii.            Bulu ban (blue band)

    viii.            Ƙwai

    Yadda Ake Kek

            Akan fasa ƙwai (wanda yawansa ya danganta da yawan kek ɗin da ake da niyyar samarwa). Daga nan kuma za a sanya madara ta ruwa a ciki a gauraya. Sai kuma a zuba bulu ban da bakin foda da sukari, sannan a tarfa gishiri ɗan kaɗan. Bayan an gauraya sosai, sai a sanya filawa ciki a ci gaba da gaurayawa. A wasu lokuta akan sanya ruwa ɗan kaɗan. Amma an tabbatar da cewa, ruwan na iya ɓata shi, ko ya hana shi yin daɗi.

              Bayan an kammala wannan gaba ɗaya, sai a ɗauko gwangwanayen kek. Mafiya yawan lokuta akan shafa musu mai kafin a zuba kwaɓin da aka yi ciki. Bayan a zuzzuba kuma, sai a sanya su kan garwashi, ko kuma injin kek. Da zarar sun gasu, to kek ya samu.

    1.3.7 Jolof Ɗin Taliya

              Wannan na ɗaya daga cikin ire-iren abincin zamani da ake ci a ƙoshi yayin bukuwan aure da ma na suna a birnin Sakkwato. Wannan aiki ya kawo bayanin yadda ake samar da jalof na taliya kamar haka:

     

    Kayan Haɗin Jolof Na Taliya

           i.            Taliya

         ii.            Mai (na gyaɗa ko manja)

      iii.            Kayan miya (albasa da tumatur da attaruhu da makamantansu)

       iv.            Kayan ƙamshi (onga da magi da ajino moto da makamantansu)

    Yadda Ake Jolof Na Taliya

            Akan yi jajjagen kayan miya, ko kuma a markaɗa. Sai a sanya a tukunya a soya da mai. Daga nan za a zuba ruwa da kuma kayan ƙamshi danginsu onga da gishiri da magi da makamantansu. Yayin da ruwan ya tafasa, sai a kawo taliya a zuba. Za a bar shi ya nuna. Da zarar ya dahu, jalof ɗin taliya ya kammala.

    1.3.8 Jolof ɗin shinkafa

              Jolof na shinkafa ma ɗaya ne daga cikin abincin da ake ci a ƙoshi a gidajen bukukuwan aure da ma na suna. A ƙasa an kawo bayanin yadda ake jolof ɗin shinkafa:

    Kayan Haɗin Jolof Na Shinkafa

           i.            Shinkafa

         ii.            Mai (na gyaɗa ko manja)

      iii.            Kayan miya (albasa da tumatur da attaruhu da makamantansu)

       iv.            Kayan ƙamshi (onga da magi da ajino moto da makamantansu)

    Yadda Ake Jolof Na Shinkafa

    Akan yi jajjagen kayan miya, ko kuma a markaɗa. Sai a sanya a tukunya a soya da mai. Daga nan za a zuba ruwa da kuma kayan ƙamshi danginsu kori da onga da gishiri da magi da makamantansu. Yayin da ruwan ya tafasa, sai a kawo shinkafa a zuba. Za a bar shi ya nuna. Da zarar ya dahu, jalof ɗin shinkafa ya kammala.

    1.3.9 Shadaka

              Wannan ma nau’in abinci ne da ake samarwa a gidajen biki. Wannan bincike ya bi diddigin yadda ake samar da shi tare da tattaro bayanan kamar yadda yake a ƙasa:

    Kayan Haɗin Shadaka

           i.            Gyaɗa

         ii.            Dawa

      iii.            Sukari

       iv.            Kayan yaji

    Yadda Ake Shadaka

              Akan surfa dawa a niƙe ta, sannan a soya garin. Wato a sanya bisa wuta a riƙa juyawa, har sai ta yi yadda ake buƙata. A ɗaya ɓangaren kuma za a soya gyaɗa a murje ta. Daga nan za a gauraya gyaɗar da garin da aka soya tare da kayan yaji, sannan a mayar inji domin a niƙe su. Bayan an niƙa, sai a sanya sukari cikin garin sannan a sanya a turmi a yi ta faman dakawa. Bayan ya haɗu sosai, sai a riƙa curawa dunƙule-dunƙule. Da zarar an kammala, to shadaka ta samu.

    3.2 Ababen Sha na Zamani a Bukin Aure a Birnin Sakkwato

              Akwai abubuwan sha iri daban-daban da ake amfani da su yayin bukukuwan aure. Wannan ɓangare na aikin ya zayyano wasu daga ciki tare da bayaninsu kamar haka:

    3.2.1 Kunun Dankali/Kudaku

              Kunun dankali wani sabon salon kunu ne wadda ya samu a zamanance. Wato ba ya cikin tsarin ire-iren kunun Bahaushe na asali. A ƙasa an kawo bayanin yadda ake samar da kunun dankali:

    Kayan Haɗin Kunun Dankali

           i.            Dankali

         ii.            Dawa

      iii.            Kayan ƙamshi (citta da kanamfari da masoro da makamantansu)

       iv.            Sikari

     

    Yadda Ake Kunun Dankali

            Da farko za a surfa dawa a wanke ta tsaf, sannan a jiƙa domin ta yi laushi. Sai kuma a samu dankali a fere shi, a yi yanka ƙanana-ƙanana. Daga nan za a kai wannan dawa da kuma dankali markaɗe. Yayin zuwa markaɗen za a sanya kayan yaji a ciki domin samar da ƙamshi. Bayan an dawo da wannan markaɗe, za a aza bisa wuta a tafasa. Bayan ya tafasa kuma za a sauƙe a sanya sikari. Da zarar an kammala wannan, to kunun dankali ya samu.

    3.2.2 Jinja

              Jinja ma tana ɗaya daga cikin kayan sha na zamani da ake yawan samu yayin bukukuwan aure a garin Sakkwato. Wannan aiki ya tattaro bayanan yadda ake samar da jinja:

    Kayan Haɗin Jinja

           i.            Kayan yaji

         ii.            Lemon tsami

      iii.            Lemon zaƙi

       iv.            Sukari

         v.            Filebo

    Yadda Ake Jinja

              Da farko akan daka kayan yaji tsaf sannan a jiƙa da ruwa. Sai kuma a nemi abin tata a tace ruwa sarai. A kuma sanya ruwan lemon tsami da na zaƙi da filebo. Bayan wannan ya kammala, sai a sanya sukari a gauraya. Da zarar wannan ya samu, to kuwa an kammala jinja. Yawanci akan ƙuƙƙulla a ƙananan ledodi ko kuma a raba a cikin ƙananan kofuna.

    3.2.3 Zoɓo

              Zoɓo ma na ɗaya daga cikin ababan sha na zamani yayin bukukuwan aure a garin Sakkwato. A ƙasa an bayyana yadda ake samar da zoɓo:

    Kayan Haɗin Zoɓo

           i.            Ganyen Zoɓo

         ii.            Kayan yaji

      iii.            Sukari

       iv.            Filabo

    Yadda Ake Zoɓo

              Akan jiƙa ganyen zoɓo ya jiƙa sosai. Daga nan sai a nemi abin tata a tace shi tsaf. Sai kuma a kawo sukari da filabo a sanya, sannan a gaurayi shi sarai. Da razar an gama haka, to zoɓo ya samu. Shi ma akan ƙuƙƙulla shi a ledodi domin a raba wa baƙi, ko kuma a sanya a ƙananan kofuna idan nan take za a sha.

    3.3 Abincin Bukin Haihuwa na Zamani a Birnin Sakwkato

              Duk da cewa bukin suna da na aure sun yi tarayya kan wasu ire-iren abinci, wannan aiki ya tsaƙulo irin abincin da aka fi amfani da su yayin bukukuwan suna a birnin Sakkwato. Sun haɗa da:

    a.      Masa

    b.     Mit-fayit (meat-pie)

    c.      Fish-fayit (fish-pie)

    d.     Fof-fof/cincin

    e.      Alkubus

    f.       Fankasau

    3.3.1 Masa

              Masa iri-iri ce. A zamanance an fi yin masar shinkafa yayin tararrukan bukin suna. A ƙasa an kawo bayanin yadda ake masar shinkafa:

    Kayan Haɗin Masa

           i.            Shinkafa

         ii.            Man gyaɗa

      iii.            Yin (a wasu lokuta)

     

    Yadda Ake Masa

              Yayin samar da masar shinkafa, akan samu shinkafa a wanke. Daga nan za a dafa kaɗan daga ciki. Sauran kuma za a kai domin a markaɗa. Bayan an dawo da markaɗen, sai a gauraya da ragowar da aka dafa. A wannan gaɓa wani lokaci akan sanya yis, amma ba dole ba ne. Daga nan kuma sai a fara soyawa a kaskon masa. Akan ci irin wannan masa da miya a mafiya yawan lokuta. A ɗaiɗaikun lokuta kuwa, akan ci da sukari.

    3.3.2 Mit-fayit (meat-pie)

              Wannan wani nau’in abinci ne da ake yawan samu yayin tarukan bukukuwan haihuwa a birnin Sakkwato. A ƙasa an kawo bayanin yadda ake samar da shi:

    Kayan Haɗin Mit-fayit

           i.            Filawa

         ii.            Nama

      iii.            Man gyaɗa

       iv.            Kayan miya (attaruwa da albasa da tumatur da makamantansu)

         v.            Kayan ƙamshi

     

     

    Yadda Ake Mit-fayit

            Akan yayyanka nama daidai girman da ake buƙata, daga nan sai a sulala. A ɗaya ɓangaren kuma, za a yi jajjagen kayan miya a kuma soya su sama-sama. Daga nan za a gauraya naman da jajjagen kayan miyan sannan a ƙara kayan ƙamshi. Bayan wannan ya kammala sai a kwaɓa filawa. Daga nan kuma za a riƙa yanku curin fulawar tare da baza shi ya kasance mai ɗan faɗi. Sai a riƙa sanya wannan nama da jajjagen kayan biya a tsakiya, a riƙa naɗewa.

              A gefe ɗaya kuma, za a aza mangyaɗa bisa wuta. Bayan ya yi zafi, sai a ɗauko wannan fulawa da aka ƙunshe jajjagen kayan miya da kuma nama, a riƙa soyawa. Da zarar ya soyu, to an samu mif-fayit.

    3.3.3 Fish-fayit (fish-pie)

              Wannan ma abinci ne da ake samu a wuraren tararrukan bukukuwan suna. Hanyar da ake samar da shi daidai yake da na mit-fayit. Bambancin da yake tsakaninsu kawai shi ne, shi mit-fayit ana yin sa ne da nama. Shi kuwa fish-fayit da kifi ake yin sa.

    3.3.4 Fof-fof/cincin

              Wannan ma abincin Hausawa ne na zamani wanda ake samu a gidajen bukukuna suna a birnin Sakkwato. A ƙasa an kawo bayanin yadda ake samar da wannan abinci:

    Kayan Haɗin Fof-fof

           i.            Filawa

         ii.            Sukari

      iii.            Yis

       iv.            Mangyaɗa

    Yadda Ake Fof-fof

              Yayin samar da fof-fof, za a kwaɓa filawa sannan a sanya sukari da yis. Sai a yi dunƙule-dunƙule sannan a aje a rana domin ya kumbura. Bayan nan za a aza man gyaɗa a wuta. Bayan man ya yi zafi, sai a riƙa tsoma filawar a cikin wannan mangyaɗa. Da zarar ya soyu, to an samu fof-fof.

    3.3.5 Alkubus

              Wannan ma nau’in abinci ne da ake samu lokutan bukukuwan suna a birnin Sakkwato. A ƙasa an kawo bayanin yadda ake samar da alkubus:

    Kayan Haɗin Alkubus

           i.            Filawa

         ii.            Gishiri

      iii.            Magi

       iv.            Kayan miya

    Yadda Ake Alkubus

            Yayin samar da alkubus, akan kwaɓa filawa, a sanya gishiri da magiciki, a gauraya sosai. Daga nan za a nemi leda a ƙuƙƙula tamkar yadda ake ƙulla alala. Sai a sanya tukunya a dafa sarai. A ɗaya bangaren kuma, za a yi amfani da kayan miya a samar da ‘yar ƙwarya-ƙwaryar miyar jajjage. Daga nan za a riƙa cin wannan dafaffen alkubus da miyar jajjage.

    3.3.6 Fankasau

              Fankasau ma wani nau’in abinci ne da ake samu a gidajen bukukuwan suna. Wannan aiki ya bibiyi yadda ake samar da fankasau. Ga bayaninsa kamar haka:

    Kayan Haɗin Fankasau

           i.            Alkama

         ii.            Man gyaɗa

      iii.            Yis

    Yadda Ake Fankasau

              Akan kai alkama a niƙa ta, a tankaɗe sarai. Daga nan sai a ƙwaɓa garin a haɗa shi da yis. Bayan ya kammala sai a sanya shi a rana domin a tashi. Da zarar ya tashi sai a aza man gyɗa bisa wuta, a hau suya. Yayin da aka kammala soya alkubus, akan ci shi da miyar alayyaho ko dai miya makamanciyar wannan.

    3.4 Ababen Sha na Zamani a Bukin Haihuwa a Birnin Sakwkato

    Akwai abubuwan sha iri daban-daban da ake amfani da su yayin bukukuwan suna a garin Sakkwato. Wannan ɓangare na aikin ya zayyano wasu daga ciki tare da bayaninsu kamar haka:

    3.4.1 Kunun Shinkafa

              Kunun shinkafa ɗaya ne daga cikin ababan sha na zamani wanda ake samu a gidajen bukukuwan suna a birnin Sakkwato. A ƙasa an kawo bayanin yadda ake samar da wannan nau’i na kunu:

    Kayan Haɗin Kunun Shinkafa

           i.            Shinkafa

         ii.            Gyaɗa

      iii.            Balila

       iv.            Sukari

         v.            Lemon tsami

       vi.            Kayan ƙamshi

    Yadda Ake Kunun Shinkafa

            Akan jiƙa shinkafa domin ta yi laushi. Sannan sai a haɗa ta da gyaɗa a markaɗa. Daga nan za a tace ta tsaf. Daga nan za a sanya a tukunya a ɗora bisa wuta. Haka za a yi ta gaurayawa har sai ya yi kauri, sannan a sauƙe. A sanya lemon tsami da sukari. Da zarar an yi haka, to kunin shinkafa ya samu.

    3.4.2 Kunun Gyaɗa

              Kunun gyaɗa ma ɗaya ne daga cikin ababan sha na zamani da ake samu a gidajen bukukuwan suna a birnin Sakkwato. A ƙasa an kawo bayanin yadda ake samar da shi:

    Kayan Haɗin Kunun Gyaɗa

           i.            Gyaɗa

         ii.            Sukari

      iii.            Tsamiya/tsami

       iv.            Gero

    Yadda Ake Kunun Gyaɗa

              Akan soya gyaɗa sannan a murje ɓawon. Daga nan sai a kai ta a markwaɗo. Bayan an markaɗa, sai a tace. A ɗaya ɓangaren kuma, za a surfa gero a jiƙa. Daga nan kuma sai a markaɗa sannan a tace. Bayan haka, za a ɗora ruwan gyaɗan a tukunya a aza bisa wuta. Za a bar shi sai ya tafasa sannan a yi amfani da shi wajen dama markaɗaɗɗen geron da aka yi. Daga nan za a sanya tsamiya ko tsami da kuma sukari. Da zarar an yi haka, kunun gyaɗa ya samu.

    3.5 Tasirin Abincin Zamani ga Abincin Hausawa na Gargajiya

              Haƙiƙa abincin zamani ya yi tasiri matuƙa ga abincin gargajiya. Wannan tasiri ya shafi fannonin abincin gargajiya daban-daban. Sun haɗa da abincin yau da kullum, wanda Bahaushe ke ci sau uku a al’adance; wato safe da rana da kuma dare. Sannan ya haɗa da abincin makulashe/kwaɗayi/ƙwalama da kuma abincin bukukuwa. Wannan ne ya sanya, ire-iren abincin bukukuwan Hausawa na aure da suna a yau suka bambanta da na da. Za a iya hasashen dalilan da suka ƙarfafa wannan tasiri na abincin zamani a kan na gargajiya kamar haka:

    1.     Ire-iren abincin zamani sun samar da sauyi da sabuntawa ga nau’o’in abincin Bahaushe na gargajiya wanda ya daɗe da su, kuma ya gaji da su (suka gundure shi).

    2.     Abincin zamani sun zo da nau’ukan ɗanɗano da ƙamshi mafifici idan aka kwatanta su da nau’o’in abincin Bahaushe na gargajiya. Hakan na faruwa ne dalilin nau’ukan kayan ƙamshi daban-daban da kuma sauran kayan haɗin abinci wanda ake amfani da su yayin girka abincin zamani.

    3.     Ire-iren abincin zamani sun zo da wani sabon salo na musamman mai ƙayatarwa ta fuskar tsaftarsu da fasalin jikinsu.

    4.     Nau’ukan abincin zamani da dama sun zo da sauƙin dafawa. Ma’ana akan dafa abincin cikin ƙanƙanin lokaci ba tare da an sha dogon aiki ba.

    Haƙiƙa waɗannan dalilai da sun taka muhimmiyar rawa wajen kawo tasirin abincin zamani kan na gargajiya. A yanzu, ya tabbata cewa, hatta abincin Bahaushe na gargajiya (misali kunun koko da kunun tsamiya da tuwon dawa da makamantansu) akan bi hanyoyin zamani yayin dafa su. Wannan na faruwa ta hanyar sanya musu wasu kayan haɗi na zamani, wato dangin kayan ƙamshi da kuma kayan yaji. Saboda haka, za a iya cewa, abincin zamani ya yi matuƙar tasiri kan abincin Hausawa na gargajiya.

    3.6 Naɗewa

              Wannan babi ya kawo nau’o’in abubuwan sha da kuma na ci na zamani da ake amfani da su yayin bukukuwan aure da na suna a birnin Sakkwato. A babin an fahimci cewa, akwai nau’ukan ababan sha da na ci da ake samunsu a gidajen bukukuwan suna da kuma na aure bai ɗaya. Sai dai kuma akwai wasu da an fi samunsu ko dai a gidan sunan ko kuma aure. Daga ƙarshe kuma babin ya yi tsokaci game da tasirin abincin zamani a kan na gargajiya.

     

     

     

     

    BABI NA HUƊU

    SAKAMAKON BINCIKE DA KAMMALAWA

    4.0 Shimfiɗa

            Wannan babi na huɗu ha kasance kammalawa ga aikin. Babin yana ɗauke da sakamakon wannan bincike da kuma jawabin kammalawa. Daga ƙarshe kuma an kawo shawarwari daidai da abubuwan da binciken ya gano.

    4.1 Sakamakon Bincike

    Wannan bincike ya yi nazari ne kan abubuwan ci da na sha na zamani a birnin Sakkwato. Binciken ya fahimci abubuwa da dama kamar haka:

    1.     Zamani yana da matuƙar tasiri game da al’amuran Hausawa daban-daban. Daga cikinsu har da nau’ukan abincinsu na aure da kuma suna/haihuwa. Wannan tasiri ha haɗa da ɓacewar nau’ukan ababen ci da na sha na gargajiya, da kuma yin amfani da hanyoyin zamani domin samar da wasu daga cikin abinci da abin sha na gargajiyar.

    2.     Abubuwan ci da na sha da dama da ake amfani da su yayin tarukan bukukuwan aure da na haihuwa a birnin Sakkwato na zamani ne.

    3.     Bukukuwan aure da na haihuwa a birnin Sakkwato sun yi tarayya wurin wasu daga cikin abubuwan ci da na sha. Sai dai duk da haka, akwai wasu nau’ukan abinci da suka keɓanta ga bukukuwan aure yayin da wasu kuma suka keɓanta ga bukukuwan suna.

    4.2 Kammalawa

            Da ma Bahaushe ya ce: “Duniya juyi-juyi, kwaɗo ya faɗa a ruwan zafi!” Har kullum ana ci gaba da samun sauye-sauye da cance-canje a ɓangarorin rayuwa. Ciki har da sauye-sauye a nau’o’in abincin da ake amfani da su. A wannan gaɓa, ba magana ce ta tunanin yadda za a kare tasirin zamani a kan abincin gargajiya ba. Domin a abu ne mai yiwuwa ba. A maimakon haka, ya fi dacewa tunani ya karkata kan yadda za a kundace ire-iren abincin gargajiya domin su kasance a tarihi madauwami. A ɗaya ɓangaren kuma, zai kasance ilimi mai amfani yayin da aka yi bincike da Nazari game da dalilan tasirin abincin zamani kan na gargajiya da kuma yana-yanayen sauye-sauyen da ake samu ga abincin na gargajiya.

    4.3 Shawarwari

    1.     Bincike game da al’adun ko wace al’umma (wanda kuwa Hausa ma na ɗaya daga cikin al’ummu) abu ne mai matuƙar muhimmanci. Hakan ne zai sanya a killace ko kundance ire-iren al’adun da suke barazanar ɓacewa. Kasancewar aure ɗaya daga cikin mafiya muhimmanci daga cikin al’adun Bahaushe wanda kuma addini a ƙarfafa, akwai buƙatar irin waɗannan bincike game da al’adun da ake gudanarwa yayin aure da ma haihuwa.

    2.     A ɗaya ɓangaren kuma, za a iya kallon amfanin abinci a wani matsayi makusancin amfanin rayuwa. Kenan akwai buƙatar gudanar da wani bincike wanda zai karanci irin sauye-sauye da aka samu game da ire-iren abincin da ake samarwa yayin bukukuwan aure da kuma na haihuwa a ƙasar Hausa. Wannan zai sanya a samu tarihinsu a kundace, ko da su nau’o’in abincin sun ɓace.

    3.     Ya kamata a samu binciken da Nazari na ilimi game da dalilan tasirin abincin zamani a kan na gargajiya, da kuma yanaye-yanayen sauye-sauyen da ake samu ga abinci da abin shan gargajiya na Bahaushe.

    Manazarta

    Abba, S. (2011). “Nason Al’adun Turawa a Bukin Aure a Ƙasar Sakkwato. Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

    Abdullahi, I. S. S. (2008). Jiya ba Yau ba: Waiwaye a Kan Al’adun Matakan Rayuwar Maguzawa na Aure da Haihuwa da Mutuwa. Kundin digiri na uku wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

    Abdullahi, M. (1997). “Bukukuwan Musulunci a Garin Maidahini a Ƙaramar Hukumar Mulki ta Bunza.” Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

    Abu, M. (1985). Al’adun Aure da Canje-canjensu a Katsina. Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

    B/Kebbi, M. A. (1997). “Yanayi da Tsarin Al’adun Aure a Birnin Kebbi.” Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

    Babajo, S. A. (2001). “Yaji da Biko a Auren Bahaushe.” Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

    Bunza, D. B. (2013). Zama Da Maɗaukin Kanwa Ke Sa Farin Kai: Nason Baƙin Al’adu Cikin Al’adun Auren Hausawa. Muƙalar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani na ƙasa a Sashen Harusnan Nijeriya, Jami’ar Ummaru Musa ‘Yar’aduwa.

    Funtuwa, A. I. da Gusau, S. M. (2010). Al’adun da Ɗabi’un Hausawa da Fulani. Kaduna: El-Abbas Printers and Media Concept.

    Gada, N. M. (2014). Kutsen Baƙin Al’adu Cikin Hidimar Aure A Sakkwato. Kundin digiri na biyu wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

    Gwarjo, Y. T. da wasu (2005). Aure a Jihar Katsina. London: Oɗford Uniɓersity Press.

    Gusau, G. U. (2012). Bukukuwan Hausawa. Gusau: Ol-faith Prints

    Hassan, B. Y. (2013). Nason Baƙin Al’adu Kan Al’adun Aure Da Haihuwa Da Mutuwa Na Hausawa. Muƙalar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani na ƙasa a Sashen Harusnan Nijeriya, Jami’ar Ummaru Musa ‘Yar’aduwa.

    Hassan, B. Y. (2013). Nason Baƙin Al’adu Kan Al’adun Aure Da Haihuwa Da Mutuwa Na Hausawa. Muƙalar da aka gabatar a taron ƙara wa juna sani na ƙasa a Sashen Harusnan Nijeriya, Jami’ar Ummaru Musa ‘Yar’aduwa.

    Ibrahim, M. S. (1985). Auren Hausawa: Gargajiya Da Musulunci. Kundin digiri na biyu wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero, Kano.

    Ibrahim, S. M. (1981). Auren Hausawa. Zaria: Ahmadu Bello Uniɓersity Press.

    Jungudo, A. (2011). “Kwatance Tsakanin Auren Hausawa da na Fulani a Garin Gombe.” Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

    Mohammad, H. (2010). “Matsayin Ganye A Abincin Hausa A Ƙasar Bodinga.” Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

    Muhammad, T. A. (1998). Aure Da Buki A Ƙasar Hausa. Kano: Ɗan Sarkin Kura Publishers Ltd.

    Rambo, I. (2007). Nazari Kan Wasu Keɓaɓɓun Al’adun Auren Hauswa Da Na Dakarkari. Kundin digiri na biyu wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

    S/Tudu, H. Z. (1987). Tasirin Zamani A Kan Al’adun Aure A Ƙasar Sakkwato. Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

    Sani, U. S. (1997). Zamani Riga Ne: Sababbin Al’adun A Lokacin Bukukuwan Auren Hausawa A Garin Sakkwato. Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

    Sa’id, B. edita (2006). Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero. Zaia: Ahmadu Bello Uniɓersity Press.

    Umar, K. F. (2007). Tasirin Zamani Kan Ire-iren Auren Hauswa. Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Jami’ar Maiduguri.

    Usman, A. (2013). “Al’adun Aure a Garin Kilgori.” Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

    Usman, H. S. (2014). Bokanci A Finafinan Hausa Na Zamani Daga 1990-2012. Kundin digiri na biyu wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

    Wasagu, B. S. (2002). “Tasirin Al’adun Auren Hausawa a Kan na Dakarkarin Zuzu.” Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

    Yabo, B. A. (2006). “Kirarin Abincin Hausawa.” Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

    Yauri, B. M. (2011). “Tasirin Al’adun Auren Hausawa a Kan na Kambarin Kambuwa.” Kundin digiri na farko wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo, Sakkwato.

    www.amsoshi.com

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.