𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu alaikum,Allah ya qarawa mallam Ameen, tambaya na anan shine shin Mallam zamu iya cin yankan arna? waɗanda ba musulmai ba?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
EH ya halatta mu ci yankan da Kirista ko Yahudawa suka
yanka. Amma da sharadi kamar haka
1. Ya zamto yankan ba su yi shi
domin wanin Allah ba. Saboda faɗin
Allah (swt)
حُرِّمَتْ عَلَيْكُمُ الْمَيْتَةُ وَالدَّمُ وَلَحْمُ الْخِنْزِيرِ
وَمَا أُهِلَّ لِغَيْرِ اللَّهِ بِهِ وَالْمُنْخَنِقَةُ وَالْمَوْقُوذَةُ وَالْمُتَرَدِّيَةُ
وَالنَّطِيحَةُ وَمَا أَكَلَ السَّبُعُ إِلَّا مَا ذَكَّيْتُمْ وَمَا ذُبِحَ عَلَى
النُّصُبِ وَأَنْ تَسْتَقْسِمُوا بِالْأَزْلَامِ ۚ ذَٰلِكُمْ فِسْقٌ ۗ الْيَوْمَ يَئِسَ
الَّذِينَ كَفَرُوا مِنْ دِينِكُمْ فَلَا تَخْشَوْهُمْ وَاخْشَوْنِ ۚ الْيَوْمَ أَكْمَلْتُ
لَكُمْ دِينَكُمْ وَأَتْمَمْتُ عَلَيْكُمْ نِعْمَتِي وَرَضِيتُ لَكُمُ الْإِسْلَامَ
دِينًا ۚ فَمَنِ اضْطُرَّ فِي مَخْمَصَةٍ غَيْرَ مُتَجَانِفٍ لِإِثْمٍ ۙ فَإِنَّ اللَّهَ
غَفُورٌ رَحِيمٌ
An haramta muku mũshe da jini da
naman alade da abin da aka ambaci sũnan wanin Allah a gare shi, da maƙararriya
da jefaffiya da mai gangarõwa
da sõkakkiya, da abin
da masu dagi suka ci, face abin da kuka yanka, da
abin da aka yanka a kan gunki (shĩ
ma an haramta). Kuma kada ku yi rabo da kibiyoyi na caca wannan fasiƙanci
ne. A yau waɗanda suka
kafirta sun yanke ƙauna daga addininku. Sabõda haka kada ku ji tsõronsu kuma ku ji tsõroNa. A yau Na
kammala muku
addininku, Kuma Na
cika ni´imaTa a kanku,
Kuma Na yarda da
Musulunci ya zama addini a gare ku. To, wanda aka sanya wa lalũra a cikin yunwa mai
tsanani, ba yana mai
karkata zuwa ga wani zunubi ba, to, lalle ne Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai. (suratul Ma'idah aya ta 3).
2. Ya zamto sunan Allah suka
ambata yayin da za su yanka dabbar.
Idan suka yanka da Sunan Jesus ko Holy spirit ko sunan wani pastor, to ba za a ci ba. Allah (swt) yana cewa
وَلَا تَأْكُلُوا مِمَّا لَمْ يُذْكَرِ اسْمُ اللَّهِ عَلَيْهِ
Kada ku ci daga abin da ba a
ambaci sũnan Allah ba a kansa. (suratul An'am ayah ta 121).
3. Ya kasance abin da suka yanka ɗin ba ya
daga cikin irin dabbobin da Allah ya haramta mana. Misali, alade ko kare ko
jaki ba zai halatta aci ba koda sun yanka shi tare da ambaton sunan Allah.
Amma bai halatta musulmi ya ci abin da 'yan addinin Buddah ko Hindu suka yanka ba. Ko da sun ambaci sunan Allah yayin da za su yanka dabbar.
WALLAHU A'ALAM.
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.