Ticker

6/recent/ticker-posts

Fitsari A Cikin Ɗaki

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum. Ba na son shiga makewayi (toilet) na cikin ɗakina da dare, don haka sai na ajiye wani ɗan bokiti wanda ni da yara muke yin fitsari a ciki. Shi ne nake son jin ko musulunci ya amince da hakan?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Babu laifi ga hakan matuƙar dai fitsarin ba zai fantsalu ya ɓata jiki ko tufafi ko wuraren zama ba. Domin Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya faɗa game da waɗansu mutum biyu da suke kwance a cikin ƙabrukansu cewa

إنَّهُمَا لَيُعَذَّبَانِ وَ مَا يُعَذَّبَانِ فِي كَبِيرٍ، أَمَّا أَحَدُهُمَا فَكَانَ لَا يَسْتَنْزِهُ مِنَ الْبَوْلِ، وَ أَمَّا الْآخَرُ فَكَانَ يَمْشِي بِالنَّمِيمَةِ

 Lallai ne azaba ake yi musu. Amma ba ana yi musu azaba a kan wani babban abu ba ne. Ɗayansu dai ba ya tsarkaka ne daga fitsari. Ɗayan kuma yawo yake yi da gulma a tsakanin jamaa. (Sahih Al-Jaami: 2440).

Sannan kuma ya tabbata a cikin hadisin Umaimah Bint Ruqayyah cewa: Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) yana da wani kwano kamar akushi da yake yin fitsari a cikinsa a cikin dare

كَانَ لِلنَّبِىِّ -صلى الله عليه وسلم- قَدَحٌ مِنْ عَيْدَانٍ تَحْتَ سَرِيرِهِ يَبُولُ فِيهِ بِاللَّيْلِ.

Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) yana da wani kwano na katako da yake yin fitsari a cikinsa, yana ajiye shi a ƙarƙashin gado. (Sahih Abi-Daawud: 19, Sahih An-Nasaaiy: 32).

Wannan fitsarin ne wata mace mai suna Barakah ta zo ta shanye shi watarana. Da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya nema bai gani ba kuma aka sanar da shi cewa, ai Barakah ta shanye shi sai ya ce:

لَقَدِ احْتَظَرَتْ مِنَ النَّارِ بِحِظَارٍ

Lallai ta tsare kanta daga Wuta da babbar kariya. (Al-Mu’ujam na Ibn Al-Muqri’: 138, masu tahqeeq na littafin sun ce riwayar sahihiya ce).

Allaahu Akbar!

Wal Laahu A’lam.

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Ga masu tambaya sai su turo ta WhatsApp number: 08021117734

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments