Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Sallar Mai Yoyon Fitsari

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamualaikum, An yi min aiki a mara ta, aka samun robar Fitsari, yanzu an cire robar, amma in na yi Fitsari a toilet, Ina ganin danshin Fitsari a wandona, Yaya hukuncin alwalata da sallata ?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikum assalam,

Ka yi kokari wajan fitar da Fitsarin da tsanyewarsa daga mafitsararka gwargwadon iyawarka, duk lokacin da za ka yi Sallah ka yi alwala, bayan haka duk abin da ya fito ba matsala, ka karasa sallarka, kar ka yanke.

Allah Yana cewa a ayar karshe a Suratul Hajj

 ۚ هُوَ اجْتَبَاكُمْ وَمَا جَعَلَ عَلَيْكُمْ فِي الدِّينِ

"Kuma bai Sanya muku kunci a cikin addini ba"

Allah ne Mafi sani.

Amsawa ✍️

Dr. Jamilu Yusuf Zarewa.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏��👇

https://chat.whatsapp.com/BSA30hdZD7V3WSJF8WVwUj

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments