Ticker

6/recent/ticker-posts

Falalar Karanta Suratul Kahfi A Ranar Jumma'a

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Yaushene Lokacin Karanta Suratul Kahafi Ranar Juma'a, Menene Falalar Karanta Ta Ranar Juma'ar?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

الحمد لله.

An ruwaito falalar karanta Suratul kahafi ranar juma'a ko daren juma'ar hadisai ingantattu, daka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam daka ciki akwai.

1- Daka Abu Sa'idul Khudry Allah yaqara yarda dashi, Yace: (Wanda Ya karanta Suratul Kahafi Adaren juma'a Allah Zai haska Masa Haske tsakaninsa da Ɗakin Ka'aba) Darumi (3407), Albani ya Ingantashi acikin Sahihul Jami'i ( 6471).

2-Wanda Ya karanta Suratul Kahafi Ranar Juma'a, Allah zai Haska Masa Haske Tsakanin juma'ar Zuwa wata Juma'ar.

Hakim ya ruwaito shi (3/399) Da Baihaqy ( 3/249) Ibnu Hajar acikin Takarijin "Azkaar" Yace: Hadisine Kyakkyawa, Yace; Shine Hadisin Da yafi Qarfin cikin Abunda Aka ruwaito akan karanta Suratul kahafi ranar juma'a. Duba Faizhul Qadeer (6/198) Albani Ya ingantashi acikin Sahihul Jami'i ( 6470).

3- Daka Abdullahi dan Umar Allah yaqara yarda dasu yace:, Manzan Allah Sallalahu Alaihi wasallam yace: ( Wanda ya karanta Suratul Kahafi ranar juma'a, za a sanya Masa haske A qar-qashin Qafarsa har sama dazai dunga haska Masa ranar Alqiyama, Za a gafarta Masa tsakanin Juma'ar Zuwa wata Juma'ar). Munziri yace: Abubakar Bin Mardawaihi ya ruwaito shi, da Isnadin da Babu laifi dashi, acikin Tafsirinsa, Duba Attargeebu Wattarheebu ( 1/298).

Ana Karanta Suratul kahafi acikin daren juma'a ko a yinin juma'a, daren juma'a yana farawane daka faduwar ranar Alhamis, Ranar juma'a ko Wuninta yana qarewa da faduwar ranar juma'ar, .

Abisa Wannan lokacin karanta Suratul kahafi ranar juma'a yana farawa daka faduwar ranar Alhamis, izuwa faduwar ranar juma'a.

Manawi Yace: Ibnu hajar yace: haka ya faru acikin wasu ruwayoyi "Ranar juma'a" a wasu kuma "daren juma'a" faizhul qadeer (6/199).

Manawi Yace: Abin sone Mutum ya karanta ta ranar Juma'a ko daren Juma'a kamar yanda Imamu Shafi'i ya Nassanta. Faizhul Qadeer (6/198).

Ba'a ruwaito hadisai ingantattu ba akan karanta Suratul Ãli Imran ba, ranar juma'a, duk wani hadisi da aka ruwaito akan haka, mai raunine sosai, koma Na qaryane.

Daka Ibnu Abbas Allah yaqara yarda dasu yace: Annabi Sallallahu Alaihi wasallam yace: ( Wanda ya karanta surar da'a cikinta aka Ambaci Ãli imrana, Mala'iku zasuyi ta yi Masa salati har Rana ta fadi). Dabarani ya Ruwaitoshi acikin "Mu'ujamul Ausad" (6/191). da Kabeer (11/48).

Hadisin Mai raunine Sosai, Haitami yace; dabarani ya ruwaitoshi acikin "Mu'ujamul kabeer" acikinsa Akwai Dalha Bin zaid, Mai raunine Sosai. Duba Mu'ujamul zawa'id (2/168).

Ibnu Hajar yace: Dalha mai raunine sosai, Imamu Ahmad da Abu dauda Sun dangantashi cewa yana Qir-qirar hadisan Qarya yana jinginawa Annabi Sallallahu Alaihi wasallam. Duba Faizhul Qadeer (6/199).

Albani yace; Hadisin Qaryane, duba hadisi Mai lamba ta ( 5759) acikin "Za'iful jami'i "

Daka ciki Akwai Abunda haitami ya ruwaito, Wanda ya karanta (Suratul Baqara da Ãli Imrana a daren Juma'a yana da ladan da yawansa yakai tun daka Qasan Bakwai zuwa Saman Bakwai)!.

Manawi Yace: Rarraunane Sosai, duba Faizhul Qadeer (6/199).

WALLAHU A'ALAMU.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/GUq2GCCzlcdL6nknqLYYox

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments