Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Wankan Janabah Ranar Juma'a

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum da fatan malam yana cikin koshin lafiya. idan mutum ya kasance yana mai janaba a ranar juma'a sai lokacin zuwa masallaci yayi, yaya zai yi? zaiyi wankan janaba ne kawai ya isar masa ko sai ya haɗa da na juma'a daga baya, kasancewarsa wajibi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikumus salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Malamai sun ce duk wanda janabah ta sameshi aranar juma'a alhali yana so yayi wankan Janabah ga kuma wankan juma'a agabansa, to zai haɗa yayi wanka guda ne bisa niyyar sauke wajibcin wankan janabah da kuma aikata sunnar wankan juma'a.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments