Biyayya Ga Miji Tana Gaba Da Biyayaya Ga Iyaye

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Assalamu alaikum Mallam ina cikin wani tashin hankali, iyayena ne suka samo min aiki, mijina yace ba zan yi ba, nayi nayi ya ki ya yarda, su kuma sun ce sai nayi, mahaifina yace idan mijin nawa ya ki yarda na yi tahowa ta na amshi posting letter na, in mijin ya gaji ya biyoni. Dan Allah mallam meye abin da ya kamata nayi? na rasa yadda zanyi. Magana ta gaskiya mijina bai rageni da komai ba, babu abin da baya min kawai dai aiki yace ba yanzu ba. Yanzu ni dai bana son na saɓa ma iyayena kuma bana so na ki bin umurnin mijina ya zanyi dan Allah ?

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Wa alaikum assalam. Ki yi kokari wajan gamsar da iyayanki, da hakurkurtar da su, Idan ba su yarda ba, ki yi biyayya ga mijinki saboda ya fi mahaifinki girman hakki a kanki.

    Allah ya yi Umarni da biyayya ga iyaye a ayoyi masu tarin yawa a cikin Al'qur'ani da hadisai, saidai a wajan Mace miji yana gaba da Uba, Annabi Sallallahu alaihi Wasallam yana cewa: "Inda zan umarci wani ya yi sujjada ga wani, to da na umarci mace ta yi sujjada ga mijinta".

    Tun da mijinki yana biya miki dukkan bukatunki, barin aikin ya zama wajibi, saboda aikin Gwamnati ga mace yana halatta ne in akwai bukata kuma ya aminta daga cakuɗawa da maza.

    Tafiya wajan aiki ba tare da iznin mijinki ba saɓon Allah ne da keta alfarmar Shari'a, Allah ya umarci Mace da ta zauna a gidanta a aya ta (33) a suratul Ahzaab

    وَقَرْنَ فِي بُيُوتِكُنَّ وَلَا تَبَرَّجْنَ تَبَرُّجَ الْجَاهِلِيَّةِ الْأُولَىٰ ۖ وَأَقِمْنَ الصَّلَاةَ وَآتِينَ الزَّكَاةَ وَأَطِعْنَ اللَّهَ وَرَسُولَهُ ۚ إِنَّمَا يُرِيدُ اللَّهُ لِيُذْهِبَ عَنْكُمُ الرِّجْسَ أَهْلَ الْبَيْتِ وَيُطَهِّرَكُمْ تَطْهِيرًا

    Kuma ku tabbata a cikin gidãjenku, kuma kada ku yi fitar gãye-gãye irin fitar gãye-gãye ta jãhiliyyar farko. Kuma ku tsaĩda sallah, kuma ku bãyar da zakka, ku yi ɗã,ã ga Allah da ManzonSa. Allah na nufin Ya tafiyar da ƙazamta kawai daga gare ku, yã mutãnen Babban Gida! Kuma Ya tsarkake ku, tsarkakewa.

    Allah ne mafi sani

    Dr. Jamilu Yusuf Zarewa

    Zauren Fatawowi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.