Ticker

6/recent/ticker-posts

Wanda Ya Tuba Daga Zina Saboda Hiv, Allah Zai Amshi Tubansa?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum malan, mutumen da yake mazinacine an masa wa'azi amma yaki ya daina...... Har sai da aka tabbatar masa da cewa cutar HIV ta kama shi sannan ya tuba... To Allah gafarta malan miye matsayin wannan tubar tasa?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikum assalam, In har ya tuba tuba ingantacce, Allah zai iya amsar tubansa. Annabi yana cewa: "Allah yana amsar tuban bawa mutukar bai zo gargarar mutuwa ba", kamar yadda Tirmizi ya rawaito kuma ya kyautata a hadisi mai lamba ta: (3537), a wani hadisin kuma yana cewa "Duk wanda ya tuba kafin rana ta fito daga yamma Allah zai amshi tubansa", kamar yadda Bukhari ya rawaito a sahihinsa a lamba ta: (6141).

Hadisan da suka gabata suna nuna cewa ana karbar tuban bawa ko da kuwa ya shiga rashin lafiyar da zai iya mutuwa a cikinta.

Kasancewar ya samu cutar HIV ya daina ba zai hana a amshi tubansa ba, tun da akwai wadanda suna da cutar amma suna yi, tun da cutar ba ta hana jindadin zinar kwata-kwata. Wanda ya bar zunubi saboda gajiyawa za'a rubuta masa alhakinsa cikakke, kamar yadda hadisi mai lamba (6672) a Bukhari ya yi nuni zuwa hakan.

Allah ne mafi sani

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/J1hm5Tw12uYBqfaiPwf28l

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments