Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Akwai Masu Bautar Annabi (Sallallahu Alaihi Wasallam)?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Ko akwai masu bautar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ne a cikin musulmi? Don wani kirista ne na ji yana zargin musulmi da hakan. Kuma har yake nuna fifikon Annabi Isaa (Alaihis Salaatu Was Salaam) a kan Annabinmu (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) saboda wai shi ya tashi daga matattu! Don Allaah ina son a yi min ƙarin bayani a kan wannan da hujjoji in zai yiwu?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

[1] A wurin dukkan mutane masu hankali Allaah ne kaɗai abin bauta, domin shi ne kaɗai Mahalicci Mai Azurtawa mai iko a kan dukkan komai. Shi da kansa ya yi shaidar haka, kamar inda yake cewa

شَهِدَ ٱللَّهُ أَنَّهُۥ لَاۤ إِلَـٰهَ إِلَّا هُوَ وَٱلۡمَلَـٰۤىِٕكَةُ وَأُو۟لُوا۟ ٱلۡعِلۡمِ قَاۤىِٕمَۢا بِٱلۡقِسۡطِۚ لَاۤ إِلَـٰهَ إِلَّا هُوَ ٱلۡعَزِیزُ ٱلۡحَكِیمُ

Allaah ya shaida cewa: Lallai babu wani abin bautawa da gaskiya sai dai shi, haka ma Mala’iku da ma’abuta ilimi (duk sun shaida): Yana tsaye da adalci, babu wani abin bautawa da gaskiya sai dai shi Mabuwayi Mai Hikima. (Surah Al-Imraan: 18).

Sannan kuma wannan shi ne saƙon da Allaah ya aiko dukkan Annabawansa da Manzanninsa da shi ga alummominsu, kamar yadda ya ce

 وَلَقَدۡ بَعَثۡنَا فِی كُلِّ أُمَّةࣲ رَّسُولًا أَنِ ٱعۡبُدُوا۟ ٱللَّهَ وَٱجۡتَنِبُوا۟ ٱلطَّـٰغُوتَۖ فَمِنۡهُم مَّنۡ هَدَى ٱللَّهُ وَمِنۡهُم مَّنۡ حَقَّتۡ عَلَیۡهِ ٱلضَّلَـٰلَةُۚ فَسِیرُوا۟ فِی ٱلۡأَرۡضِ فَٱنظُرُوا۟ كَیۡفَ كَانَ عَـٰقِبَةُ ٱلۡمُكَذِّبِینَ

Kuma haƙiƙa! Mun aika da Manzo a cikin kowace alumma yana cewa: Ku bauta wa Allaah, kuma ku nisanci bautar ɗagutu. (Surah An-Nahl: 36).

Ɗagutu shi ne: Duk wanda ake bauta masa ba Allaah ba, kuma ya amince da hakan.

Har su kansu Yahudawa da Kiristoci ma dokar da aka ba su kenan, kodayake ba su yarda sun bi ta ba

ٱتَّخَذُوۤا۟ أَحۡبَارَهُمۡ وَرُهۡبَـٰنَهُمۡ أَرۡبَابࣰا مِّن دُونِ ٱللَّهِ وَٱلۡمَسِیحَ ٱبۡنَ مَرۡیَمَ وَمَاۤ أُمِرُوۤا۟ إِلَّا لِیَعۡبُدُوۤا۟ إِلَـٰهࣰا وَ ٰ⁠حِدࣰاۖ لَّاۤ إِلَـٰهَ إِلَّا هُوَۚ سُبۡحَـٰنَهُۥ عَمَّا یُشۡرِكُونَ

Sun riƙe malaman cikinsu da masu bauta a cikinsu a matsayin abubuwan bauta ba Allaah ba, haka ma Al-Maseeh Ɗan Maryam, alhali ba a umurce su da komai ba sai dai kaɗai su bauta wa abin bautawa guda ɗaya: Babu wani abin bautawa da gaskiya sai dai shi. Ya tsarkaka daga duk abin da suke yin tarayya da shi. (Surah At-Taubah: 31).

[2] Don haka, Allaah shi kaɗai ne musulmi suke bauta wa, ba su haɗa shi da komai ko da kowa a cikin Ayyukansa da Nau’o’in bautarsa da Sunayensa da Siffofinsa, ko da kuwa makusanta ga Allaah ne kamar Mala’iku ko Manzanni da Annabawa ko manyan waliyyai da shehunai, ballantana sauran halittu kamar aljanu ko rana da wata da taurari da dabbobi da tsuntsaye da bishiyoyi da duwatsu da sauransu. Allaah Ta’aala ya ce

 ۞ وَٱعۡبُدُوا۟ ٱللَّهَ وَلَا تُشۡرِكُوا۟ بِهِۦ شَیۡـࣰٔاۖ

Kuma ku bauta wa Allaah, kada kuma ku haɗa komai da shi. (Surah An-Nisaa’i: 36).

Sannan kuma Al-Imaam Al-Bukhaariy (#3435) ya riwaito hadisi daga Sahabi Ubaadah Bn Saamit (Radiyal Laahu Anhu), daga Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce

« مَنْ شَهِدَ أَنْ لاَ إِلَهَ إِلاَّ اللَّهُ وَحْدَهُ لاَ شَرِيكَ لَهُ ، وَأَنَّ مُحَمَّدًا عَبْدُهُ وَرَسُولُهُ ، وَأَنَّ عِيسَى عَبْدُ اللَّهِ وَرَسُولُهُ وَكَلِمَتُهُ ، أَلْقَاهَا إِلَى مَرْيَمَ ، وَرُوحٌ مِنْهُ ، وَالْجَنَّةُ حَقٌّ وَالنَّارُ حَقٌّ ، أَدْخَلَهُ اللَّهُ الْجَنَّةَ عَلَى مَا كَانَ مِنَ الْعَمَلِ »

Duk wanda ya shaida cewa: Babu abin bautawa da gaskiya sai Allaah, shi kaɗai babu abokin tarayya gare shi; kuma cewa: Annabi Muhammad (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) Bawansa ne kuma Manzonsa ne; kuma cewa: Annabi Isaa (Alaihis Sallam) Bawan Allaah ne kuma Manzonsa ne kuma Kalmarsa ce da ya jefa ta ga Maryamu kuma wani Ruhi daga gare shi; kuma cewa: Aljannah gaskiya ce; kuma Wuta ma gaskiya ce: Allaah zai shigar da shi Gidan Aljannah a bisa abin da ya kasance a kansa na aiki.

[3] Shiyasa a wurin musulmi Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ba abin bauta ba ne, amma dai shi ake bi domin ya koya wa sauran al’umma yadda ake yin bautar Allaah. Dubi umurnin da Allaah Ta’aala ya ba shi

 قُلۡ إِنَّمَاۤ أَنَا۠ بَشَرࣱ مِّثۡلُكُمۡ یُوحَىٰۤ إِلَیَّ أَنَّمَاۤ إِلَـٰهُكُمۡ إِلَـٰهࣱ وَ ٰ⁠حِدࣱۖ فَمَن كَانَ یَرۡجُوا۟ لِقَاۤءَ رَبِّهِۦ فَلۡیَعۡمَلۡ عَمَلࣰا صَـٰلِحࣰا وَلَا یُشۡرِكۡ بِعِبَادَةِ رَبِّهِۦۤ أَحَدَۢا

Ka ce: Kaɗai ni fa mutum ne kawai kamar ku: Ana yi mini wahayi cewa: Kaɗai abin bautarku abin bauta guda ɗaya ne kawai. (Surah Fussilat: 6; Surah Al-Kahf: 110).

[4] Me yiwuwa a wani lokaci a samu wani ko waɗansu da ba su gama fahimtar sahihin addinin musulunci ba su aikata wani abin da ya sha bamban da koyarwar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) a cikin hakan, waɗannan ba a kiran aikinsu da cewa shi ne koyarwar musulunci.

Kamar yadda aka samu wani daga cikin Sahabbai ya ce wa Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam): In Allaah ya so kai ma kuma ka so, sai ya ce

أَجَعَلْتَنِي مَعَ اللهِ عَدْلاً ؟! لَا ، بَلْ مَا شَاءَ اللهُ وَحْدَهُ

Ka mayar da ni daidai da Allaah ne?! A’a. Kai dai in Allaah ya so shi kaɗai kawai. (As-Saheehah: 139).

Wanda bai yarda a gaya masa irin wannan maganar ce ba zai yarda a mayar da shi abin bauta tare da Allaah ko ban da Allaah?!

[5] Shi ma kansa Annabi Isaa (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ba Allaah ba ne, kamar yadda Ayoyi da Hadisai suka yi bayani. Kamar wannan

یَـٰۤأَهۡلَ ٱلۡكِتَـٰبِ لَا تَغۡلُوا۟ فِی دِینِكُمۡ وَلَا تَقُولُوا۟ عَلَى ٱللَّهِ إِلَّا ٱلۡحَقَّۚ إِنَّمَا ٱلۡمَسِیحُ عِیسَى ٱبۡنُ مَرۡیَمَ رَسُولُ ٱللَّهِ وَكَلِمَتُهُۥۤ أَلۡقَىٰهَاۤ إِلَىٰ مَرۡیَمَ وَرُوحࣱ مِّنۡهُۖ فَـَٔامِنُوا۟ بِٱللَّهِ وَرُسُلِهِۦۖ وَلَا تَقُولُوا۟ ثَلَـٰثَةٌۚ ٱنتَهُوا۟ خَیۡرࣰا لَّكُمۡۚ إِنَّمَا ٱللَّهُ إِلَـٰهࣱ وَ ٰ⁠حِدࣱۖ سُبۡحَـٰنَهُۥۤ أَن یَكُونَ لَهُۥ وَلَدࣱۘ لَّهُۥ مَا فِی ٱلسَّمَـٰوَ ٰ⁠تِ وَمَا فِی ٱلۡأَرۡضِۗ وَكَفَىٰ بِٱللَّهِ وَكِیلࣰا ۝ لَّن یَسۡتَنكِفَ ٱلۡمَسِیحُ أَن یَكُونَ عَبۡدࣰا لِّلَّهِ وَلَا ٱلۡمَلَـٰۤىِٕكَةُ ٱلۡمُقَرَّبُونَۚ وَمَن یَسۡتَنكِفۡ عَنۡ عِبَادَتِهِۦ وَیَسۡتَكۡبِرۡ فَسَیَحۡشُرُهُمۡ إِلَیۡهِ جَمِیعࣰا

Ya ku mutanen littafi! Kar ku zaƙe a cikin addininku, kuma kar ku faɗi komai dangane da Allaah sai dai gaskiya kaɗai! Shi Al-Masihu Isa Ɗan Maryam Manzon Allaah ne kaɗai, kuma Kalmarsa ce da ya jefa ta ga Maryam, kuma Ruhi daga gare shi. Sai ku yi imani da Allaah da Manzonsa, kuma kar ku ce: Uku! Ku hanu! Shi ya fi alheri gare ku! Shi Allaah abin bautawa guda ne kaɗai. Ya tsarkaka da ya kasance yana da ɗa! Na sa ne duk abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa, kuma Allaah ya isa a matsayin Madogari. Al-Masihu ba zai taɓa ƙyamar ya zama bawa ga Allaah ba, haka ma Malaiku Makusanta! Kuma duk wanda ya ƙyamaci yin bauta gare shi kuma ya yi girman kai, to duk zai tattara su a gabansa gaba-ɗaya. (Surah An-Nisaa’i: 171-172).

[6] Amma maganar cewa wai Annabi Isaa (Alaihis Salaam) ya mutu kuma wai ya tashi daga matattu kamar yadda Kiristoci suke faɗa, malamanmu masu bincike sun gano cewa: Akwai wurare a cikin Baibul da suka nuna saɓanin haka.

(i) (Yohanna 19: 33-34): Amma sa’adda suka zo wurin Yesu, suka gani kuma ya rigaya ya mutu, ba su karye ƙafafunsa ba. Amma wani a cikin yan yaƙi ya soke shi da mashi wurin haƙarƙari; nan da nan jini da ruwa suka fito.

Wannan ya nuna zuciyarsa tana cigaba da bugawa kuma tana harba jini zuwa ga sassan jikinsa kenan. Don haka wannan dalili ne a kan cewa bai mutu ba. (Ana iya duba bayanin haka a cikin: The Encyclopeadia Biblica, a ƙarƙashin bayanin: cross).

(ii) (Yohanna 20: 1; Luka 24: 2; Markus 16: 4): Ana nan bisa rana ta fari ga bakwai Maryamu Magdaliya ta zo ƙabarin da wuri, tun da sauran duhu, ta ga an ɗauki dutsen daga wurin ƙabarin.

Wannan ya nuna Yesu bai mutu ba kuma bai tashi daga matattu ba, shiyasa yake buƙatar sai an kawar da dutsen kafin jikinsa rayayye wanda bai mutu ba ya iya fitowa. Amma su waɗanda suka tashi daga matattu ba su buƙatar hakan, domin jikkunansu suna zama kamar na Malaiku ne. (Luka 20: 36).

(iii) (Yohanna 20: 14-15): Maryamu Magdaliya ta yi tsammanin Yesu kamar mai-noman ne.

Saboda me? Domin ya yi shiga irin na mai-noman. Meyasa? Don yana tsoron Yahudawa, kar su gan shi su kashe shi! Wannan dalili ne a kan cewa bai tashi daga matattu ba. Domin a ƙaida waɗanda suka tashi daga matattu ba za su sake mutuwa ba kuma. (Ibraniyawa 9: 27).

(iv) (Matta 12: 40): Mu’ujizar Yunana Annabi: Gama kamar yadda Yunana yana cikin cikin babban kifi na teku yini uku da kwana uku; haka kuma Ɗan Mutum za ya yini uku da kwana uku a cikin zuciyar ƙasa.

Kowa dai ya san a duk tsawon waɗannan kwanakin guda uku da Yunana ya zauna a cikin cikin kifi a raye ya ke, ba a mace ba. Don haka wannan alama (mu’ujiza) ta nuna shi ma Ɗan mutum (Yesu) a raye zai kasance a cikin ƙasar, ba a mace ba.

Idan kuma wani ya ce wai tsawon lokacin ne kawai ake magana a kai ba halin da suka kasance a kansa ba, to ai shi Yesu bai yi yini uku da kwana uku a cikin ƙasar ba: Yini ɗaya da kwana biyu kaɗai ya yi. (Daga Yammacin Jumma’a da aka gicciye shi zuwa Safiyar Lahadi da Maryamu Magdaliya ta je ƙabarin ba ta same shi a ciki ba).

[7] Wannan a cikin littafinsu kenan. Amma a cikin Alqur’ani ko kama shi ba su yi ba, kuma ko kusa da itatuwan gicciyewan ma ba a kai shi ba. Allaah Ta’aala ya ce:

 وَقَوۡلِهِمۡ إِنَّا قَتَلۡنَا ٱلۡمَسِیحَ عِیسَى ٱبۡنَ مَرۡیَمَ رَسُولَ ٱللَّهِ وَمَا قَتَلُوهُ وَمَا صَلَبُوهُ وَلَـٰكِن شُبِّهَ لَهُمۡۚ وَإِنَّ ٱلَّذِینَ ٱخۡتَلَفُوا۟ فِیهِ لَفِی شَكࣲّ مِّنۡهُۚ مَا لَهُم بِهِۦ مِنۡ عِلۡمٍ إِلَّا ٱتِّبَاعَ ٱلظَّنِّۚ وَمَا قَتَلُوهُ یَقِینَۢا ۝ بَل رَّفَعَهُ ٱللَّهُ إِلَیۡهِۚ وَكَانَ ٱللَّهُ عَزِیزًا حَكِیمࣰا ۝ وَإِن مِّنۡ أَهۡلِ ٱلۡكِتَـٰبِ إِلَّا لَیُؤۡمِنَنَّ بِهِۦ قَبۡلَ مَوۡتِهِۦۖ وَیَوۡمَ ٱلۡقِیَـٰمَةِ یَكُونُ عَلَیۡهِمۡ شَهِیدࣰا

Kuma da maganarsu cewa: Lallai ne mu! Mun kashe Al-Maseehu Isaa Ɗan Maryam Manzon Allaah ɗin! Alhali kuwa ba su kashe shi ba, kuma ba su gicciye shi ba, sai dai kawai an kamanta musu ne. Kuma waɗannan da suka yi saɓani a cikinsa suna cikin shakka ne a kansa. Ba su da wani ilimi sai dai kawai bin zato, amma dai a haƙiƙa ba su kashe shi ba. Kaɗai Allaah ya ɗauke shi zuwa gare shi, kuma Allaah ya kasance Mabuwayi ne Mai Hikima. Kuma babu wani daga cikin mutanen Littafi face yana yin Imani da shi kafin mutuwarsa, kuma a ranar Ƙiyama zai kasance mai shaida a kansu. (Surah An-Nisaai: 157-159).

Don haka musulmi ba su yarda da cewa an kashe Annabi Isaa Ɗan Maryam ba, amma dai Allaah Taaala ya ɗauke shi jiki da ran ne zuwa gare shi. Kuma sai nan gaba kaɗan zai sauko kafin tashin Ƙiyama domin ya tabbatar da gaskiyar alamura, kafin daga baya ya rasu kuma a tayar da shi da sauran halittu a Ranar Lahira. Al-Imaam Al-Bukhaariy (#2222, 2476, 3448, 3449) da waninsa daga cikin malaman Hadisi sun riwaito daga Sahabi Abu-Hurairah (Radiyal Laahu Anhu) ya ce: Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce

« وَالَّذِى نَفْسِى بِيَدِهِ ، لَيُوشِكَنَّ أَنْ يَنْزِلَ فِيكُمُ ابْنُ مَرْيَمَ حَكَمًا عَدْلاً ، فَيَكْسِرَ الصَّلِيبَ ، وَيَقْتُلَ الْخِنْزِيرَ ، وَيَضَعَ الْجِزْيَةَ ، وَيَفِيضَ الْمَالُ حَتَّى لاَ يَقْبَلَهُ أَحَدٌ ، حَتَّى تَكُونَ السَّجْدَةُ الْوَاحِدَةُ خَيْرًا مِنَ الدُّنْيَا وَمَا فِيهَا » . ثُمَّ يَقُولُ أَبُو هُرَيْرَةَ وَاقْرَءُوا إِنْ شِئْتُمْ :

Na rantse da Allaah wanda raina ke ga hannunsa! Tabbas Haƙiƙa! Ya yi kusa Ɗan Maryam ya sauko a cikinku, yana mai hukunci mai adalci. Sai ya karya gicciye (cross), kuma ya kashe alade, kuma ya ajiye karba jizya, kuma dukiya ta yawaita, har ya zama babu mai karɓarta. Har sujada guda ɗaya ta kasance mafi alheri fiye da duniya da duk abin da ke cikinta. Daga nan sai Abu-Hurairah ya ce, ku karanta (wannan ayar) in kun so: [Kuma babu wani daga cikin Ahlul-Kitaab face haƙiƙa yana yin imani da shi a gabanin mutuwarsa, kuma a ranar Al-Ƙiyama zai kasance mai shaida a kansu].

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments