Ticker

6/recent/ticker-posts

Mijina Ya Sake Ni, Sai Ya Mai Da Ni, Ni Kuma Bana Son Na Koma Gidansa.

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalaamu Alaikum Malam Khamis. Mijina ya sakeni saki ɗaya, ina da ciki wata 6 a jikina, sai daga baya kafin na haihu sai yace ya dawo dani, ni Kuma naki komawa tunda Daman hakuri nakeyi dashi yazo ya sakeni batare da nace yasakeni ba, Kuma Malam har cikin Raina banason sake komawa gidansa sabida gaba ɗaya yafita a raina, Babu sonsa azuciyana, meye matsayina donshi yanacewa ni matarsace nikuma inacewa ba matarsa bace, don yana ikirarin zaiga ubanda zai dauramin aure, ataimakamin da amsa, bissalam🙏🙏

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam Warahmatullah Wabarkatuhu

To 'yar'uwa tabbas miji yana da damar da zai yiwa matarsa kome mutukar tana cikin idda. Duk Mutumin da ya saki matarsa. Matukar dai Iddarsa bata Cika Akanta ba. Sai kuma Yace ya Maidata. To ba Makawa ta Maidu. Ko tana so ko bata so. kuma iyayen matar ko ita kanta ba su da damar da za su ja masa birki Sabida Faɗin Allah da Yake Cewa

وَبُعُوْلَتُهُنَّ اَحَقُّ بِرَدِّهِنَّ فِىْ ذٰلِكَ اِنْ اَرَادُوْۤا اِصْلَاحًاۗ

Kuma mazan aurensu su ne mafiya haƙƙi ga mayar da su a cikin wancan, idan sun yi nufin Maslaha. (Surah: Al-Baqara, Ayat: 228)

Amma mutukar bai yi mata kome ba har ta kammala idda to ba shi da dama akan ta, amma zai iya shiga cikin manema.

Yadda ake Yiwa Irin Waɗannan Mazajen Waɗanda Basa Son Zaman Lafiya. Domin Suna Maida Mace ne dan Su Azabtar da Ita. Ba don Su cigaba da zama don Maslaha ba, Sabida Sun San Allah ya ba su wannan Damar.

Idan har Akwai Cutarwa da Wulakanci da Sauransu. Wanda Wannan Halayen Nasa ne ma yasa Kika ji ya Fita a Ranki. Har ta kai da son sa baya Zuciyarki. Kuma baki da Ra'ayin Komawa Gidansa. To babu laifi ki nemi khul'i daga gareshi. Wato ki bashi sadaqin da zai isheshi ya auri wata matar, (Amma wannan agaban alqali ake warwarewa) a ɓata auren a Kasheshi yazama ke da mijinki babu wani ƙulli tsakaninku, dan haka baze yiwuba a gyara Auren ko ya maida ki ba sai in ya sake biya sabon Sadaki an sake ƙulla Sabon Aure, domin shi khul'i ba Saki bane, Asali Faskhune shi.

Allah Yace

اَلطَّلَاقُ مَرَّتٰنِۖ فَاِمْسَاكٌ بِۢمَعْرُوْفٍ اَوْ تَسْرِيْحٌ بِۢاِحْسَانٍۗ وَلَا يَحِلُّ لَـکُمْ اَنْ تَأْخُذُوْا مِمَّاۤ اٰتَيْتُمُوْهُنَّ شَيْـــًٔا اِلَّاۤ اَنْ يَّخَافَاۤ اَ لَّا يُقِيْمَا حُدُوْدَ اللّٰهِۗ فَاِنْ خِفْتُمْ اَ لَّا يُقِيْمَا حُدُوْدَ اللّٰهِۙ فَلَا جُنَاحَ عَلَيْهِمَا فِيْمَا افْتَدَتْ بِهٖۗ تِلْكَ حُدُوْدُ اللّٰهِ فَلَا تَعْتَدُوْهَاۚوَمَنْ يَّتَعَدَّ حُدُوْدَ اللّٰهِ فَاُولٰۤٮِٕكَ هُمُ الظّٰلِمُوْنَ

Saki sau biyu yake, sai a riƙa da alhri, ko kuwa a sallama bisa kyautatãwa. Kuma ba ya halatta a gare ku (maza) ku karɓe wani abu daga abin da kuka bã su, fãce fa idan su (ma'auran) na tsõron bã zã su tsayar da iyãkõkin Allah ba, Idan kun (danginsu) ji tsõron bã zã su tsayar da iyãkõkin Allah ba, to, bãbu laifi a kansu a cikin abin da ta yi fansa da shi. Waɗancan iyãkõkin Allah ne sabõda haka kada ku ktare su. Kuma wanda ya ƙẽtare iyãkõkin Allah, to waɗannan su ne azzãlumai. (Surah: Al-Baqara, Ayat: 229)

Mallamai ma'abota ilimi sunyi bayanin ya halasta ga mace idan tana fuskantar zalunci da cutarwa daga mijinta babu laifi ta nemi saki daga gareshi, wasu suna ganin wajibi ne ma ya sake ta in dai ta nemi sakin, sannan bayan ya sake ta kuma aladabtar da shi, Idan kuma ya ki sakin ta to zata iya yin khul'i ta fanshi kanta daga wajan mijinta ta hanyar ba shi sadakin da ya ba ta lokacin auranta kamar yadda matar Thabit Bn Kais bn Shammas ta yiwa mijinta a hadisin da ya tabbata a manyan Kundayan musulunci.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp. com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www. facebook. com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments