Ticker

6/recent/ticker-posts

Namiji Zai Iya Yin Kunshi?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaykum Warahmatullahi, Da fatan malam yana lafiya, Malam ya halatta namiji ya yi kunshi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikum assalam, Ya halatta namiji ya yi kunshi a gemunsa da kansa, da launin da yake ba baki ba, kamar yadda Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam ya yi umarni a yiwa Abu-Khuhafa mahaifin sayyadi Abubakar R. A lokacin da ya musulunta ranar buɗe Makka a hadisin Ibnu Hibban mai lamba: 5472 Wanda Shuaibu Al'ar'na'u'd ya inganta.

Ya wajaba namiji ya nisanci duk wani kunshi da zai zama kamanceceniya da mata, saboda Allah ya la'anci namijin da yake kamanceceniya da mata kamar yadda ya tabbata a hadisin Tirmizi mai lamba ta: 2784.

Yana daga cikin ka'diojin da ya kamata a sani cewa: Kamanceceniya da mata yana iya banbanta daga wuri zuwa wuri, yana saɓawa daga al'ada zuwa wata.

Allah ne mafi sani

Amsawa:-Dr. Jamilu Zarewa.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat. whatsapp. com/DIcJIQrWyLP0oBOMSnDi5P

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www. facebook. com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments