Ticker

6/recent/ticker-posts

Limancin Bebe Da Kurma

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum Warahmatallahi Wabarkatahu. Malam menene hukuncin limancin BEBE (wanda baya

iya magana) DA KURMA (wanda bayaji amma yana iya magana)

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu

Limancin bebe wanda baya iya magana baya iya karanta Fatiha baya iya yin kabbarar Haramah bai ingantaba ya zama limami domin yafi mamun (masu binshi sallar) tawaya. Yazo acikin littafan fiqhu na mazhabobi guda huɗu game da sharuɗan limanci: akwai nafarkonsu shi ne karatu tayinda anaso liman ya zama mai kyautata qira'ane sallah bata inganta sai da wannan.

sannan limancin kurma wanda bayaji shi ansamu saɓani wasu malaman sunce yana inganta kurma yayi limancin sallah suna cewa hukuncin shi kamar hukuncin limancin makahone sunce ji da gani basu kebanta da wani Sharaɗi daga sharuɗan sallah ba (wato ba inda aka shardanta sai liman yana gani ko yana ji limancinshi zai inganta) Mazhabar malikiyyah suna ganin limantar da wanda ba kurma ba shi ne yafi kuma sunce makruhine (abin kyama ne) asa kurma wanda bayaji limami ratibi (na kullum-kullum) Hidabi acikin mawahibul jaleel yana cewa: Kai dalibin ilmi kasani shi kurma bai kamata asashi zama limami na kullum kullum ba saboda zai iya yin rafkanuwa (sahawu) ayi mai tasbihi baiji ba hakan kuma zai iya zama sanadiyyar ɓacin sallar kuma wannan ita ce magana mafi rinjaye

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/K7RkQRMf2b57l3UENoJ1Or

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments