𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalaamu
Alaikum Wa Rahmatul Laah. Na ji amsar Fatawa a kan matan da suke miƙa
hannuwansu da ƙafafunsu ga waɗansu
maza su yanke musu farce, to tambaya ta ita ce: Idan a gaban mijinta ne fa?
Watau kamar ta kira mai yankewa ya yanke mata amma mijinta yana kallo?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus
Salaam Wa Rahmatul Laahi Wa Barakaatuh.
A asali
zamansu a haka tare su uku ba laifi ba ne. Keɓancewa
a tsakanisu ce aka hana.
« لاَ يَخْلُوَنَّ رَجُلٌ بِامْرَأَةٍ إِلاَّ كَانَ ثَالِثَهُمَا الشَّيْطَانُ »
Wani namiji
bai taɓa keɓancewa da wata mace ba
face kuwa na-ukunsu ya zama sheɗan
ne. (Sahih Al-Jaami’: 2546).
Shafar jikinta
da mai yakan ƙumbar zai yi ce matsala ko da kuwa da izinin mijinta ne, domin
kusantar zina ce wanda kuma haram ne, kamar yadda Ubangijinmu Ta’aala ya ce:
وَلَا تَقۡرَبُوا۟
ٱلزِّنَىٰۤۖ
Kuma kar ku
kusanci zina. (Surah Al-Israa’i: 32).
Sai dai ko in
akwai larura, kamar likita da zai karɓi
haihuwa ko kuma wacce zai yi wa aiki, a inda mijinta ko wani muharraminta ba
zai iya.
A nan kuwa
babu irin wannan larurar.
Domin ko da
ita ba za ta iya yanke ƙumbunanta ita da kanta ba, ai wata matar kamar abokiyar
zamanta ko ƙawarta ko ’yarta
ko ’yar’uwarta tana iya yi mata,
kamar yadda ta ke yi mata kitso, misali. Idan kuma hakan bai yiwu ba, sai
mijinta ko ɗanta, ko
dai wani muharraminta daga cikin maza ya yi mata. Amma ban da ma’aikacin
gidanta, kamar mai gadi ko direba ko mai wanki da sauran duk wanda shari’a ta
amince yana iya auren wannan matar in ba domin tana da miji ba.
Allaah ya ƙara
mana shiriya da fahimta a cikin addininmu.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh
Muhammad Abdullaah Assalafiy
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.