Ticker

6/recent/ticker-posts

Tasirin Rubutun Larabci

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

708. Larabci yana da h ga rubutunsa,

 Shi ne ya wakilci h haruffanmu na Hausa,

 Kwai ha babba ga ƙarami kuma na bin sa,

Ha babba  muke da sautin na Hausa,

Ba mu da mai ruwa daɗai mu Hausawa.

 

709. Ba mu faɗin “Khadija” balle mu rubuta,

 In ka lura mai ruwa an ka rubuta,

 Ita ko Hausa babu shi ga haruffanta,

 Sai dai h ka lura in za ka karanta,

Lura da kyau “Hadiza” za mu rubutawa.

710. “Alkhairi” a bar wa Larabci wannan,

 Shi ma dai ruwa sun ka yi wannan,

 Ai tsarin rubuta Larabci ne nan,

 Ita ko Hausa ba a samun ta da wannan,

“Alheri” da Hausa shi za ku rubutawa.

 

711. Al’ummah a ɗebe h don ƙari ce,

 Kar ka saka ta ka ga ai Larabci ce,

 In aka sa ta ma’ana ta lalace,

 An saɓa ma ƙa’ida an dabirce,

  Al’umma wajen rubutu aka sawa.

 

712. Ba mu da “p” da “q” da “x” don a kiyaye,

 Turanci ya zo da su Hausa ta jaye,

 Ba ta da hurrumi da su sai a kiyaye,

 In aka sa su to ka san an yi tawaye,

Ba mu da “v” ga Hausa don ƙara kulawa.

Post a Comment

0 Comments