Na Cancanta (Kashi na 37 - 42)

    Na Cancanta (Kashi na 37)

    Gefen Mama nake zaune ina matsar ƙwalla gami da tunani mabanbanta da na ɗade da nasabarwa kaina dasu tun lokacin da Mama ta fara rashin lafiya mai zafin gaske kuma yau sati guda ke nan dole na sallamar da zuwa islamiyya bokon ma karatun bana ganewa tunanina na wajen Mama dafa awarar da komai ninake yi, A baya muna ganin farkon zazzaɓin nata da tasha paracetamol ya wadatar hakan ya sa ko su Gwaggo ba mu faɗa wa ba har saida mukaga paracetamol ɗin ya ƙare babu sauƙi Ahmad ya je ya sanar mata, maganar Gwaggo ta katse min tunanin nawa

    "Yanzu haka za ki zauna, ciwo fiye da sati ba a asibiti ba wani magani babu abinci ta kamaimai da za ki ci haba Hauwa'u, shi ne dalilin ƙin faɗa min ɗin ke nan?"

    Cikin muryar ciwo na ji Mama na cewa "A'a Gwaggo ba Sumayyah ta baki labari nasha magani ba sauƙin ne dai ya kasa samuwa” Mama ta ƙara sa maganar tanajan nishi

    Gwaggo da yana yin damuwa tare da fusata ta ce” Dama ina za ki ji sauƙin da wani paracetamol tuni ciwo a jikinki yaci ya cinyeki daga ke har yarannaki gakunan a fukace a wahale, aini yanzu duk na gano gaskiya mijinnaki ne baya ƙaunarki shi ya akai bai koma haka ba iye?"

    Hawaye nake jin na zubomin daga soma jin kalmomin Gwaggo, lallai ita ma ta kai ƙarshe wajen zafafa

    "Gwaggo wallahi yanasona shi ma baki ga yadda ya koma ma ba laifin na wajen ƴan uwansa” Mama ce mai faɗin hakan cikin wahala hawaye nabin fuskarta

    "Rufemin baki wallahi kona taso na make bakin naki, da bakisan ciwan kanki ba ki kwana da yunwa ki tashi da ita wanne ciwone ba zai yi nasarar kamaki ba da na yi zaton abun na mutuncine, yanzu ina muke da arziƙin kaiki asibiti a wannan yana yin dubunnai nawa za a cajemu shi garemu ko wani muka bawa ajiya”

    Sai yanzu na sa baki tare da cewa” Gwaggo Abbah ya tafi samo kuɗin ai”

    Gwaggo cikin tsawa ta kalle ni tare da wurgamin harara

    "Ubanki zai basa kuɗinko, ya gama yawan ciranin nashi bai samo komai ba iyayensa ƴan uwansa sun koresa wa kike tunanin zai basa, Ni dai ta kama naje mu sami rance a zo akaita asibitin, taji sauƙi kuma a rabata da ubannaku mara zuciyar neman na kanshi na gaji daganin ɗiyata cikin wannan tashin hankalin na yau daban na gobe da ban"Gwaggo na gama faɗar haka ta miƙe ta fice fuu kamar iska ko waigomu bata yi ba

    Kuka na kife kaina a jinyoyina ina yi muryar Mama ta dakatar da shi tana cewa” Kin gani ko faɗan Gwaggo na yi gudu ya sa na ce karku faɗa mata gashinan kun faɗa ai kunji daɗi”

    Hawaye na goge na kalli Mama” To Mama ya zamuyi ai gwara su sani ɗin duk abin da zai faru ya fi zuwa da sauƙi” bata ba ni amsa ba hakan ya sa na ɗauki mafici na ci gaba da yi mata fifitar da ita nake yi Gwaggo ta ce na bari ta isa

    Sallamar Rumaisah na ji tare da kukan A'isha da ta ɗauke ta ta fita da ita tun ɗazu dama da kukan aka fita da ita gashinan an dawo dashi, kuma Mama ko Nono bata iya bata kwana biyu sai dai mu dinga ɗinkiramata ruwa gashi bata isa a fara bata ko koko ba ita ma duk ta rame dama ba wani ƙoshi a tare da ita, katse tunanin na yi jin Muryar Rumaisah

    "Yaya wallahi taƙiyin shiru na rasa ya zan mata tana barcin fa ta farka ta ci-gaba da kukan, Gwaggon ta zo kuwa?"

    Cikin yana yin fuskar damuwa na ce” Eh ta zo, ƙara ɗebo ruwa mu bata ɗin ko za ta yi shiru"

    Miƙomin ita ta yi ta fita, na soma jijjigata ko za ta yi shiru amma kukan take tsandarawa, Rumaisa cikin saurinta ta dawo da ruwa a hannunta a ƙaramin kofi ta miƙomin tana cewa

    "Kin gani ko ba za ta yi shiru ba yarinyar nan"

    Bance komai ba na amshi ruwan na soma bata tana sha sau ɗaya sau biyu ta zubo da shi ta ci gaba da tsanyara kuka da nake jinsa har raina na rasa dame zan ji

    "Kawo ta na fita da ita tsakar gida na lallasheta karta damu Mama, amma wallahi yunwa take ji” Rumaisa ta yi maganar da miƙo hannu ta amsheta ta fice

    Mama na kalla idanta biyu amma ba damar magana ita tasan irin ciwon da ke damunta

    Muryar Rumaisah na jiyo daga wajen, a lokacin A'isha ta rage kukan da take yi "Wai har yanzu Abbah bai dawo ba ma ashe”

    Na ce mata” Eh"yarda za ta iya juyowa, dan ko Abbah ya jima da fita, tun kafin a tafi kiran Gwaggo, ya ce zai je ya samo rancen kuɗi akaita asibiti amma shiru ba mu jima da maganarsa ba muka jiyo sallamar Abbah ɗakin ya shigo ya zauna kusa da Mama ya sai kuma na hango hawaye nabin fuskarsa

    "Hauwa'u kiya haƙuri idan ciwo ya samu marashi sai haƙuri, da anyi shawara dani kan ciwan gwara ni ya kamani, bakiga yawon da na yi ba bansamu bashin ba shi kansa Musa da na yi tsammani sai ba ni bashi da shi na san wasu ɗin da na tambaya akwai amma duba da ba ni da abin biyan na san babu mai bani” sai kuma ya sake rushewa da kuka kamar ƙaramin yaro, ni ma kukan ne na ji ya zomin haka na fara yi tsakanin Abbah babu mai iya rarrashin wani cikinmu

    ****************

    "Ya jikin Mama ɗin?"

    Juraid ya tambayeni da yake tsaye jikin ƙofar gidanmu da ba dan naso ba na iya tsayawar a wannan yana yin da nake ciki, sai dai banasan ya ga kamar na masa wulaƙanci dan tun da Mama ta fara ciwo bana fitowa wajensa sai ko mun haɗu wajen awarata, Yanzuma na kammala soyar ne ta dole ya tsayar dani ba dan naso ba dan hankalina yana gida na duba halin da Mama ke ciki

    Murmushin ƙarfin hali na yi na ce” Jiki Alhamdulillah"

    "Amma ya kamata akaita asibiti fa tun da ga yana yinki ya nuna babu wani sauƙi, Ni zan kaita asibiti ɗin"

    Saurin girgizamasa kai na yi jin ƙarshen zancensa "A'a gobe ma insha Allah za a kaita asibiti Gwaggo ta ce ɗazu zataje ta dawo a kaita amma na san yanzu ta bari sai safenne”

    Kallona Juraid yake yi har na gama maganar ya cire idonsa akaina” Kawai ki bari na kaita ta yiyu ba su samu kuɗin da za su kaita ba, Abbah kuma na san bashida halin hakan da tuni yayi”

    Girgiza kai na yi na ce” A'a mungode, zuwa da safen za a kaita, bari na shiga ciki”

    Sallama muka yi na shigo ciki ina saƙe saƙe a raina bana so Juraid yasan komai game da rayuwarmu sai dai kuma abun ya kasa yiyuwa da hakan gaba ɗaya baya min daɗi wani lokacin saidai na sani Juraid mai tsananin sona ne da san abunda nakeso da muradin shi ma ya ka sance da shi a tun kafin soyayyah ta shiga tsakaninmu yake ƙoƙarin hakan bare kuma yanzu dan ajiyan ma da a ranar Malika ta bashi labari leda ya ciko ya kawo na dubiyar Mama Abbah ya gaji da faɗan hidimar sa gareni harya haƙura dan Juraid baya cikin marasa kirkin samari duk da ba ni ke da zuciyarsa ba amma ina kyautata masa zato, Ina shiga kukan A'isha ya fara yi min sallama sai kuma hayaniyar su Aunty Jamila ƙannen Mama da Aunty Maryam yayarta da tun magriba suka zo shiga na yi ɗakin Mama na fara yi na yi sallama na sake gaishesu, Ina ƙoƙarin zama kusa da Mama da ko ido bata buɗewa Aunty Maryam ta miƙomin A'isha da take kukan har zuwa yanzu

    "Amsarta dan Allah ki yi waje da ita ta zo ta isa mutane da kuka haba muji da abin da ya damemu na ciwan ƴar uwarmu, haka nan kawai ta saki jiki sai haihuwa take kamar akuya ai gashinan ni baƙin cikin kalar rayuwar da Hauwa'u take ciki nake kwana na tashi da shi baƙin cikin auren Hauwa'u ban da da zuriyya saina ce ina ma ba'ayi ba”

    Amsarta na yi na fara ƙoƙarin barin ɗakin dan tun da Aunty Maryam ta fara maganar na san sauran ma ƙannen Mama sun samu hanya, wanda maganar ba ita bace mafita ba, amma a yaƙininsu ita ɗin ce mafitar da ina tofa wani abu za su ce rashin kunya zan yi musu kuma ina kallon kaina idan Rumaisa ko Khadijah ce a wannan halin ta yiyu na yi abin da ya fi nasu, Har nafara taka ƙafafa da zummar barin ɗakin na ji muryar Aunty Jamila

    "Mu wallahi idan Gwaggo bata dawo ba tafiya zamuyi tasa ta ɗin da zamuyi ma mu ba halin kaita asibiti ba, gashi mijinnata ma waye yaga ɗuriyarshi, shi da zaman ya kama tun da a gidansa ciwan ya kamata ai”

    Aunty Asiya ta yi hanzarin ƙarfe zancen da cewa” Ciwon yunwa da na baƙin ciki ba, aini wallahi yanzu mutumin nan ya ficemin a raina dubi fa wulaƙancin da iyayenshi da ƴan uwansa ke shukawa ai dole shi ma mu ga laifinsa mu kuma ji haushinsa”

    Da wannan firar tasu na fice a ɗaƙin raina na suya yarda yanzu dukkan laifin Abbah ake ɗaurawa, dame zaiji na kasa ganewa, ina ji inama ba mu dawo gidaba, yarda kowa ya juya mana baya wanda duk laifin da ya faro na ɓangarensu Abbah, ɗakinmu na shiga da A'isha da na samesu sunata kuka gaba ɗayansu kasa zama na yi na nufo waje dan ni ma kukan nake ji na ƙoƙarin zuwarmin kuka dole ne muyi shi duba da yarda lamuran kullum ke cakuɗe mana, da yunwar cikin kama ta isheka ko babu ciwan Mama da na san yunwar ma ta isa mutum kukan danma muna da juriyarta wanda hakan ya jawo mana samun sauƙi dan da ba mu juriya nata tuni zancen sauran kyakkyawar rayuwa garemu ya sha banban, Ƙofar ɗaki na zauna na durƙushe tsawan lokaci kukan A'isha na sake ta damin da nawa hankalin na rasa ina zan dosa wazai ji kukana ya sharemin da gaggawa sai na tuna da ubangiji waman yatawakkal Alal lah fa huwa hasbuh hakan ya sani jin sauƙin wani damuwar dake bijirowa gareni matsananciya, sai dai kuma kukan nawa ya kasa tsagaita wa ina hango rayuwarmu idan babu Mama ya za ta fara hango waɗanda ke kukan maraici nake yi a yanzu da rayuwar ta iyayen ga yadda zumun ci ya yi tsallen baɗaken aiwatarwa inaga zumuntar da za a kirata a bayan rai ta ganin idon ta tuƙe sai mai ƙarfin imani da sanin meye zumun cin a musulunce mai kuma ƙoƙarin bin kuma abin da ya sani ɗin. . . . . . . . . . .

    Na Cancanta (Kashi na 38)

    Dafanin da na ji anyi ya sani ƙara riƙe A'isha na miƙe tsaye da rawar jiki

    "Sumayyaah!"Jin Muryar Aunty na yi kamar daga sama hakan ya sa na rungumeta da A'isha na fashe da kuka ina cewa

    "Aunty ki taimaka mana akai Mama asibiti kar ta mutu cikin wannan mawuyacin halin"

    Bayana ta shiga bubbugawa

    "Ya isa haka kukan Sumayyah share hawayenki insha Allah zan yi iya ƙoƙarin ganin Hauwa'u ta samu lafiya, zan taimaka muku"

    Jin hakan ya sani sakin Aunty, A'isha dake kwanyara kuka ta amsa daga hannuna ta shiga jijjigata kafin ta ce

    "Kaini ɗakin Mamartaku"

    ****

    Aunty tana ganin Mama kwance ta ƙara sa wajenta ta rushe da kuka

    "Hauwa'u sannu Allah ya baki lafiya na san na yi laifi a karo na biyu na kasa ci gaba da nemanki sai da ɗanki ya zo da kukansa yake sanarmin"

    Da na fahimci Ahmad ne ya faɗa mata fitar da ya yi ɗazu ashe gidan Aunty ya je

    Aunty Maryam cikin kukan da Aunty na farawa ta fara ita ma, ta ce

    "Kin ga dai yadda jikin Hauwa'u tashi guda ya canza Rumaisah, Gwaggo ta fita nemo kuɗi har yanzu bata ɓullo ba shi ma mijinnata babu shi babu labarinsa”

    Aunty ta girgiza tare da tsagaitawa da kukan da take yi "ku fiddota asata a mota mu tafi asibiti, ai zama bai kamamu ba, da kun sanarmin ba wanda zaije yasha wahalar nemo wasu kuɗi ai”

    Aunty Asiya ta fara miƙewa da ƙoƙarin ƙomawa wajen Mama domin tayarda ita Aunty Jamila ma matsawar ta yi sukayi kama kama suka fidda ta daga ɗakin dan ko ciwon sati gudan yaƙara sabgar da ita

    Aunty ta dube ni

    "Yawwa haɗo mata kayanta ki kawomin mota dan wannan jikin nata ba sallamar da za mu samu washe gari”

    Kai na mayar ƙasa na fara sosa ƙyeya, dankuwa dai rabanmu da wanki saina ce ban san ranar ba babu sabulu ba omo sai zamusa muke jiƙawa a ruwa mu barbada omo mu wanke

    "Kina ji ana magana kin yi tsaye kina sosa ƙeya uwar taki kikewa hakan ke nan?"Muryar Aunty Maryam na ji ta katse tunanina

    Kaina na ɗago na kalli Aunty da A'isha ke kafaɗarta tana jijjiga ta ta yi shiru abunta kamar ba ita ce ke kukan da ta ɗagawa kowa hankali ba

    "Wallahi Aunty babu wankakku ko ɗaya”

    Aunty Maryam ta kalle ni taja tsaki” Dama na san za a rina, kowacce taɓarɓarewa da lalacewa sun tattara a kan Hauwa'u, ba'asamu abinci bama, inaga wanki”

    Aunty ta katse Aunty Maryam da cewa” mu je kawai Yaya Maryam na samo mata cikin nawa idan zan taho asibitin Abban Jabir na san mu yake jira, ga A'isha karta ci gaba da kukan"ta ƙara sa maganar tana ci gaba da jijjiga A'isha ɗin

    Aunty Maryam bata sake cewa komai ba suka fito ni ma na biyo bayansu, ban yi gigin binsu inda motar take ba dan na san Aunty Maryam na ganin na bi bayansu faɗa zansha wajenta ƙila ma ya fi na farko dan gaba ɗaya laifin Abbah yana ƙoƙarin komawa kanmu, ina tsaye ƙofar gida har motar ta tashi ina share hawaye da yiwa Mama addu'ar samun sauƙi, rufo ƙofar gidan na yi da tsoro ya fara ziyartarmin lokacin domin mu kaɗaine Abbah da Ahmad har lokacin babu wanda ya waiwayo gidan ɗakinmu na shiga na zauna na zuba tagumi da hannu biyu ƙannena nake kallo ɗaya bayan ɗaya yarda suke kwance a cure sun takura kansu da alama ba barcin daɗi suke ba ba ma da alama ba azahirin gaskiya ma hakan ne ka kwana da yunwa ka tashi da ita, ga yarda zumun cin yanzu yake tafiya musamman kalar namu da shi ne musababbin ƙara lalacewar rayuwar tamu izuwa wannan halin, tausayinsu nake ji fiye da tausayin kaina, Bugun ƙofar da na ji ana yi ya sani miƙewa na fito da tsammanin kodai Ahmad ko Abbah cikin biyu akwai ɗaya dayake kwankwasowa ko kuma dukkansu ne a tare

    "Wanene?" na yi maganar ina ƙara sawa kusa da ƙofar

    "Nine” jin Muryar Ahmad ya sani buɗe wa na matsa gefe ya shigo kallonsa na yi shi ma ni yake kallo

    "Ya jikin Mama?, ko ankaita asibiti?"

    Kai na gyaɗa na ce” Eh mana Aunty ta zo ta kaita yanzu ba su daɗe da tafiya ba, ashe kaine kaje ka faɗa wa Aunty ɗin ma?

    Ya ɗaga kai ba tare da ya ce komai ba ya wuce ni ma ƙofar na rufe na biyo bayanshi na ci gaba da magana

    "Wallahi Ahmad Aunty na da kirki tama tafi da A'isha”

    Ahmad ya ce” Sosaimah Yaya, ganin da na yi Gwaggo bata da alamun dawowa, Abbah ma shiru shi ya sa naje na faɗa wa Aunty na san za ta taimaka mana”

    Na ce” Sosaimah har suka tafi ba wanda ya dawo daga Abbah har ita Gwaggon da take ta ke fuffuka”

    Ahmad ya ce "kin san halin dai Gwaggo gaba ɗaya ta canza, inasu Rumaisah ba dai sun yi barci ba su ci abinci ba?"

    Murmushi na yi na ce” kaima dai Ahmad da wani zance abin da ya zamar mana jiki kwana da yunwar"

    Haka muka ci gaba da firarmu a tsakar gida har Abbah ya dawo muka ɗan yi ƴar fira duk dai a kan rashin lafiyar Mama da taimakon da Aunty ta yi mana da saida Abbah ya dawo gida ya san da ankai Mama asibiti shi dama bai samo komai ba, mun jima a zaune kafin muka tashi muka nufi makwancinmu

    Ƙasa barci na yi na dai kwanta amma ji nake daren yana yi min tsayi, tunanika ya dabaibaye ni da tsoro musamman na rashin sanin halin da Mama take ciki ga rashin lambar Aunty bare na kirata na ji halin da Mama ke ciki zan iya cewa barci ɓarawo ne ya ɗaukeni amma ba dan na yi shirin barcin ba

    Kukan Khalil da asubar fari ya tashemu daga barcin da muke yi lallashinsa muke yi dukkanmu amma ina shi gurin Mama zaije, Abbah ne ya shigo ɗakinmu ya zazzarewa Khalil ɗin ido sannan ya yi shiru ya ce mu tashi muyi sallah ya kaimu gurin Mama ɗin, gari na wayewa Abbah ya bawa Ahmad ya siyo mana koko mu kasha sannan muka sake wanke ƙafafu kowacce ta daka gawayi ta wanke baki sannan muka fito gidan Aunty muka nufa danshi Abbah bai je asibitinba ajiyan tun da dare ya dawo yaga ya yi babu kuma mai rakashi, da wannan dukukun muka fito gida dan kuwa bakwai saura bata ma ƙara sa ba

    A rufe muka tarar da ƙofar gate ɗin Ahmad dukkanmu muka kalla

    "Ahmad ya gidan a rufe?" Abbah ne ya yi tambayar

    Ahmad ya ce” Ai Abbah saimun ƙwanƙwasa tun da safiya ce”

    Rumaisa ce ta fara ƙwanƙwasa ƙofar ni ma na taya ta, mun jima a tsayen kamar wasu korarru su Khalil zaune sukayi ƙofar gidan ni kaina na gaji dan barcin bawai ya ishe ni ba ne, Sautin tafiyar da mukaji ya sa mu dakatawa da buga gidan saida akazo gaf da ƙofar gate ɗin mukaji tsayawar tafiyar muka jiyo ana cewa wanene daga bakin gate ɗin

    "Wanene?"Da muryar namiji kuma ba muryar babban mutum bace da alamu cikin ƴaƴan Aunty ne ko Jabir ko Muhammad da na sansu a hoto

    Abba ya sassauta murya

    "Nine Abdulllahi mijin Hauwa'u"

    Buɗe mana gate ɗin aka yi muka shiga sai bayan mun shiga gidan na ga wanda ya buɗe mana gate ɗin Jabir ne da na sanshi a hoto kuma bai wuce kamar Ahmad ba a tsaye saidai Ahmad zai iya ɗan girmarsa ko babu yawa

    Ahmad ya kalla Jabir ɗin da murmushinsa” Allah ban yi tsammanin ku ba ne ba, ku shigo ciki”

    Bayansa muka bi zuwa hanyar falon muna ƙoƙarin shiga Abbah ya ce

    "Bama sai kun shiga duka ba, iya kwatancen asibitin ai za ta yi mana”

    Jabir dake ƙoƙarin saka ƙafarshi cikin falon na ga ya dawo da baya da murmushi fuskarsa” Abbah ka shigo mana Daddy ma yana falon ai, kuma Aunty ma bata shirya tafiya asibitin ba, na san kuma ba za ta bari ku tafi ku kaɗai kuma Ummi Hauwa'un taji sauƙi”

    Haka Jabir ya lallaɓa Abbah ya yarda ya shiga cikin falon shiru muka samu falon, babu kowa

    Jabir ya kallemu"ku zazzauna mana na kira Aunty ko Daddy, Daddy ma yanzu ya koma ciki”

     

    Saida Jabir ya tabbatar mun zauna ya gaishe da Abbah sannan ni sai su Rumaisa da suka gaidashi, sannan ya miƙe ya bar wajen da ido na bi Jabir sosai ya kwantamin raina nake jinsa kamar jinin jikina kamar Ahmad, yana yin tarbiyyarshi ta ƙara burgeni da shi da ko mu ɗin ba za mu nuna masa ba jinjina wa iyayensa su Aunty nake da suka bashi tarbiyya duk da kuɗin da suke da shi haka kuma sukayi ƙoƙarin aiwatar kuma da abubuwa masu kyau idan suna tare da su duk da banga Muhammad ba amma ina kyautata masa zato murmushi nake yi har ya ɓace a falon

    Ahmad dake kusa dani ya taɓoni hakan ya sani dawowa dai dai na aje tunanina” Yaya Sumayyah Jabir ne fa akwai hankali kin ganshi nan kuma Aunty ta ce nama girme masa da shekara ɗaya amma kin gani dai, kuɗi shi baisa ya sangarce ba”

    Murmushi na yi kawai” Sosaima na gani Ahmad banga Muhammad ba?"

    Tsaki Ahmad yayi” shagwaɓaɓɓe ke nan ai ita Aunty lallai shi ne auta shi ya sa yake yin shagwaɓarshi san ranshi a gidannan danma Daddy na masa tsawa” Ahmad da yake ɗan gida haka ya ci gaba da ba mu labari jin sallama falon ya samu tsayawa da firarmu gaba ɗaya kallonmu ya koma falon Abbahnsu Jabir ne ya ƙara so fuskarsa da murmushi amsa masa sallamar mukayi inda Abbah yake ya nufa ya bashi hannu suka gaisa, sannan ya nemi waje kusa da Abbah ya zauna gaishesa mukayi cikin sakin fuska ya amsa mana, sannan suka gaisa da Abbah

    "Wato kai jiya ba ka biyomu asibiti ba sai yau ka bugo sammako kaji labarin matarka ta fara samuwa ko?, za ka nuna mana matarka ce?"Daddynsu Jabir ya yi maganar da murmushinsa

    "Ko ɗaya ba haka ba ne na fita tun yamma ajiyan na samu na samu rance ko taimako na kaita asibiti amma haka aka dinga wulli dani kamar inji ban samo komai ba, sanda na dawo kun tafi ga dare ya yi ga yara su ɗaya a gida shi ya sa na zauna tare dasu"cewar Abbah

    Daddynsu Jabir ya yi murmushi "To Allah dai ya yassare wannan matsalar rayuwar babu mai kuɗi babu talaka yau ta isa kowa”

    "Toh Amin dai amma ganina matsalar yau da gobe sai talaka” Abbah ya yi maganar na bisa da kallo yadda ya saki jiki da Daddynsu Jabir ɗin kamar dama cen akwai sanayya a tsakaninsu duk da alamu sun nuna hirace kawai data kama suyi maganar Daddynsu Jabir ta katse min tunani

    "Uhmmmm Allah dai ya ƙara rufa mana asiri, aida Jabir ya faɗa min ka toge ƙofar falo"

    Abbah ya ce” Eh mana kwatancen asibitin ai za ku yi mana ba ma son ƙara muku wata wahalar tamu"

    Daddy ya yi murmushi” Bar maganar nan haka kada Rumaisah ta jika dan kuwa saiku ɓata indai taji kace mata wahalar Hauwa'u, wahalar data damu iya Hauwa'u ce, domin dai ban taɓa jin ko a labarai aminta irin tasu ba sai dai makamanciyarta kullum dai zancenta Hauwa'u dai sai dai haɗuwa ta yi wuya tsakaninsu, sanda kuke ɗan zuwa gida kafin ku dawo, mu kuma yawancin lokutan muna Abuja ka sancewar munfi zama acan sai karatun yara yanzu daya riƙemu, tun jiya Rumaisah ta siyowa A'isha madarar yara wai a haukanta ma ita A'isha ta zo ke nan bata komawa wajen Hauwa'u"

    Murmushi Abbah ya ɗan yi kaɗan ya ce” Ita ma Hauwa'u gareta haka ne har sunan Rumaisah aka sanyawa ƴarta ta uku ka ganta nan Rumaisah"ya ƙara sa maganar yana nuna masa Rumaisah

    Daddy ya ce” Masha Allah, Allah ya ƙara aminta tsakaninsu"

    Duka muka amsa da” Amin"Daddynsu Jabir ya miƙe yana cewa” Bari na kira Rumaisah ɗin na baro tana bawa A'isha madara

    10:00am

    Aunty ta riƙemu saida muka karya muka yi wanka sannan muka fara shirin tafiya asibitin dan Aunty ta ce tun da dasu Aunty Maryam ba sai mun je da sassafe ba, kuma cewa take Mama taji sauƙi sai dai hankalina gaba ɗaya yana wajen Mama ɗin magana kawai nake yi amma ba dan hankalina yana kwance ba, A ɓangaren Abbah ma hakanne da Daddynsu Jabir suketa fira duk da na san hankalin Abbah shi ma baya jikinsa ko abincin kaɗan ya ci, Su Khalil kuwa suna ganin A'isha hankalinsu ya kwanta ko damuwa ba su yi ba, Daddynsu Jabir ne ya kaimu asibitin harda Aunty da su Jabir ka sancewar weekend ne babu makaranta. . . . . . .

    Na Cancanta (Kashi na 39)

    Asibiti mai kyau aka kai Mama da alamun ma na kuɗine, haka Daddynsu Jabir ya yi parking muka fito kai tsaye ɗakin da aka kwantar da Mama muka nufa tun a bakin ƙofar muke jiyo tashin maganganun su Gwaggo da Aunty Maryam handling ɗin ƙofar Jabir ya murɗa, Gaba ɗaya muka tura kanmu cikin ɗakin da sallama bakinmu

    Mama idona ya fara tozali da ita, kwance take a gadon da robar jini a hannunta yana tafiya idanunta rufe yake da hakan ya sake tabbatarmin jikin Mama babu zancen sauƙi sai dai na wajen ubangiji

    Ƙarasa shiga cikin ɗakin mukayi da su Gwaggo muka tarar dasu kan kujerun Roba guda biyu kusa da gadon da ɗaya Gwaggo ce ke kai ɗayar kuma Aunty Maryam, tsugunne mukayi gaba ɗayanmu muna gaishe su da tambayar ya mai jiki

    Su Abbah ma haka suka yi, Miƙewa mukayi muka ƙara sa gefen gadon da Mama ke kai muna mata sannu duk da ba amsawa za ta iya yi ba ba, Abbah dake tsaye bayanmu muka dawo ƙasa kan tabarma muka zauna shi kuma ya ƙara sa gefen gadon yana jerawa Mama Sannu

    Gwaggo da tun shigowarmu na ga yadda ranta yake a haɗe na ji cikin ɗaga murya tana cewa

    "Hauwa'u bata buƙatar sannunka Abdulllahi ganinka ma bata buƙatar yi saboda bata farko ta ganka ba, ka tafi yawon da ba zai amfaneka ba saboda ba kaine ka haifarmin ita ba idan ta mutu wata matar za ka canza, shi ya sa ka rainawa mutane hankali gaka gaka za ka je ka dawo ka samo kuɗi babu kai babu alamunka”

    Daddynsu Jabir ya juya inda Gwaggo take da har da yakai bakin ƙofa yana shirin fita

    "Haba Gwaggo baikamata ki faɗi hakan ba gashi gaban yara, kuma asibiti koma mene ya kamata ayi haƙuri ayi masa uziri, tun da gashi ya zo yanzu"

    Gwaggo cikin yana yin ɓacin rai ta sassauta murya ta ce” A'a Zaidu ai banso ayi masa wannan uzirin ba, ta kwana matarshi ta fara tarar da hantsi bai zo dubata ba dama na san ko ba daɗe ko ba jima ungulu gidan ta take komawa ya bi zugar da ƴan uwanshi a kullum sukeyi masa akanta saboda ta fara tara ƴaƴa, shi ya sa bai damu da ciwonta ba”

    Daddynsu Jabir da na tabbatar shi ne Zaidu ɗin goshi ya dafe” Kash Gwaggo ya kamata ki yi shiru ko ba dan yara ba dan ita Hauwa'u ɗin ki duba fa a yana yin da take ciki mana Gwaggo, yanzu ma wajen likitan zan koma, kuma Abbahn Ahmad bakwai ba ta yi ba ya zo gidana yamin bayani kuɗi yake nema bai samu ba tun da ya fita da yadawo dare ya yi ga yara babu damar yabarsu ya taho neman asibitin da aka kai matarshi ko ya fara tafiya neman gidana dan na san bai sani ba, ki masa uziri, ya kamata ki tausaya masa magidanci kamarsa yana fama da abincin da za suci, ba shida wani mataimaki sai Allah sai wanda yaga Allah ya yi koyi da annabin tsira(SAW)"

    Jin kalaman Abbah Zaid ya sa Gwaggo kuma fashewa da kuka” Na gode Zaidu duk da ban haifi matarka ba bare kuma kai da haƙuranka talatin na ganka da yaranka sai na ce a jiya ma na sanka, amma ka tunasar dani abin da namanta, inaso na ƙara wa zuciyar surikina wani mikin da yake cin ransa”

    Sai kuma ta juyo ga Abbah ɗin tana cewa” Abdullahi ka yafemin dan Allah gaba ɗaya damuwar Hauwa'u mantar dani komai take yi tana cikin jarrabawa Hauwa'u ina tausayinta da yaranta, da babu Rumaisah tayiyu wani labarin ake bana Hauwa'u ba yau na yarda komai daga Allah ne amma akwai sababi, Allah ya kawo muku canji na alkhairi waɗanda suka zalinceku Allah ya yi gaggawar saka muku waɗanda suka muku alkhairi Allah ya yi gaggawar biyansu da alkhairi linkin waɗanda suka yi muku"

    Gaba ɗaya jikinmu sanyi ya yi Abbah ya goge hawayen dake bin fuskarsa duk juriyar Abbah yau gaza ta yadai daure ya ce” Amin Gwaggo"

    Abbah Zaid ne ya fasa murza handling na ƙofar ya dawo cikin ɗakin

    "Abdullahi taho muje wajen Doctor ɗin, ka ga da ba'ayi maganar nan ba na manta ban ce ka taho ba” Daganan suka fice tare da Abbah

    Aunty da take tsaye tana goge hawayenta, Aunty Maryam ta miƙe gami da kallonta cikin sanyin murya tace

    "Ga kujera Rumaisah kizo ki zauna mana”

    Aunty ta girgiza kai "A'a Yaya Maryam nan ma ya yi ina zama A'isha farkawa za ta yi”

    Aunty Maryam ta ce” ƙyaleta inta farka sai ki bawa Sumayyah ko takwararki su lallasheta, Ni gida nakeson zuwa tun da kunzo dama jiranku ya tsaidani”

    Aunty ta ce” Eh haka ne ya kamata ki je gidan aga halin da ya ke ciki” ta ƙara sa maganar tana dawowa inda Aunty Maryam ta tashi ɗin

    *********

    Aunty Maryam na fita a ɗakin su Abbah su ka shigo tare da likita ledar jinin da ya sanya mata ya kalla da take daidai rabi

    "Allah ya bata lafiya, matsalar da na faɗa muku ita ce dai ba wani damuwa bayan ita” Likitan da suka shigo taran na ji yana ambatar hakan yana danna inda jinin ke ƙara gudu

    Su Abbah suka haɗa baki gurin cewa "Amin"

    "Yara gaba ɗaya sun ruɗe sunga Mamarsu haka kwance” Abbah Zaid ya ɗaura da faɗar hakan

    Likitan ya yi murmushi yana kallanmu "Karku damu insha Allah mamarku za ta samu lafiya da wuri”

    Muka ɗaga kai alamun gamsuwa duk da ni nawa ƙasan zuciyar yana tantama dan na ɗauki babban ciwo ne kaɗai kesa ayima mutum ƙarin jini kuma mutum yakai tsawan lokaci yana sharar barci, na dai fi tsammanin yunwa ta yiwa Mama kamun kazar kuku, Saidai yadda likitan ya ce Insha Allah hakan ya sa na ajje wancen tunanin na sallama komai ga ubangiji Mai kunfayakun yana cewa ka sance sai ya ka sance komai da ikonsa yake samun gurɓin ka santuwa, Ah saboda shi ne gaba ɗaya wasu tunaninka ba su samun gurbin zama a zuciyata bare su gurɓatar da tunanina na yarda komai ya yi farko zai yi ƙarshe kuma duk abunda ya yi tsanani ya yi tsanani ƙarshe sauƙi zai haifar na har abada amma saida izinin ubangiji ɗin in yaso sai rayuwar ta ƙare a haka amma akwai gidan madauwami da idan ka yarda da ƙaddarar Allah gareka sai yama musanye koba gidan duniya ba toh a gidan Aljannah

    Muryar Abbah Zaid ta katse min tunanin da nake Aunty ya kallah

    "Ba yanzu za ki je gida ba ne zan wuce ne tun da an gama komai”

    Aunty da take bawa A'isha madara tace” A'a zani mana ka jiramu madarar A'isha ma ai ya ƙare saina haɗo wata”

    Abbah Zaid ya riƙe baki da ya dubi Abbah"Abdullahi kaji dai Rumaisah kukayi wasa za ta muku magaji da ɗiyarku fah"

    Abba Zaid Aunty ta hararesa ta wasa tare da cewa” Nidai banasan irin wannan abun fa haɗa rigima yayima yawa”

    Abba Zaid ya hararareta shi ma” Faɗar gaskiyar ce haɗa rigima, shike nan na yi shiru gaki ga masu ƴar nan"

    "Ai ɗiyartace tun da yarinyar Hauwa'u ce saisu ma fini iko da ita tun da ɗiya macece” Abbah ne maiyin maganar da sai yanzu ya saka baki a zancen

    Gwaggo kuwa ci gaba ta yi da fifita Mama ko uhmm bata ce ba dan da alama ta barwah yara firarsu ne sai dai murmushi da yake ɗauke da fuskarta da ya yi nasarar ɓoye tsintsar damuwar da lamarin ciwan dake damun Mama

    Abbah Zaid inda muke zaune dasu Jabir ya kallo tare da cewa” Kunga Jabir ku taso mu fara fita tafiyin hanzari kuma kunsan za ki yi girki ?"

    Aunty ita ma miƙewar ta yi "A'a nifa na shirya, da Sumayyah zan tafi ta tayani aikin girkin ma”

    Gwaggo maida dubanta ta yi ga Rumaisah"Anya kuwa hidimar nan bata yawa Rumaisah kin ga fa su Asiya duk anjima kaɗan za su zo kuma kowacce za ta zo da abincinta ga Sha'aban na san zai baiwa ƙannensa su ƙara wani a kan na gida ai. . . . "

    Da sauri Abbah Zaid ya tsaida Gwaggo maganar da take ƙoƙarin ci gaba dayi” A'a Gwaggo babu wata hidima ai Rumaisah komai ta yiwa Hauwa'u ina jin bata faɗi ba ai abotar makaranta wani lokacin sai ta ma ɗara wani zumun cin na jini musamman yadda abun ke taɓarɓarewa ki mana fatan Allah ya karɓi ayyukanmu"

    Aunty ta yi murmushi ita ma ta cewa Gwaggo"Toh Gwaggo idan banma Hauwa'u ba ma waye zai mata bata da shi mijinta babu kuma babu sai rufin asiri da za a ce kawai, tare muke komai daga Primary har junior, muna ma waɗanda alaƙarmu bata kai haka bama, shi arziƙi kyawunka da shi ka morawa wasu ai, shi ne zai sake yalwata”

    Itadai Gwaggo rasa bakin magana ta yi sai zuba sanya albarka take wa su Aunty Ni kaina Aunty da rayuwarta ta gama burgeni hakan ya ƙara min san Aunty yadda ya kamata a raina Aunty na ansarwa Aisha na rungumeta muka fito muna gaba nida su Jabir muna fira su Aunty na bayanmu dan mun rigasu fitowa da Jabir rabin firar tawa nake yi dan shikam Muhammad saboda Abbah Zaid ya jera damu a yanda na fahimta ke nan dan muna tafiya yana hangen Aunty a haka muka ƙara sa parking space na asibitin inda Abbah Zaid ya yi parking motarshi muka ƙara sa muka tsaya jikin motar, kafin su Auntyn suka ƙara so suka buɗe motar muka shiga gidan baya a motarm firar muka ɗaura da Jabir ɗin duk da ni a ɓangarena firar batamin wani daɗi yarda tunanin ciwon Mama ya addabi zuciyata. . . . . . . . . . .

    Na Cancanta (Kashi na 40)

    "Sumayyah har yanzu baki ƙarasa blending ɗin ba”

    Muryar Aunty da na jiyo ta dakatar dani daga blending kayan miyan da nake yi a electric blander da duk lokacin ta nuna min yadda zan yi aiki da ita juyawa na yi na kalleta mai take soyawa lokacin tana gaban Cooker Gas Mai zaune jikin lokar kitchen ban iya gane mai nawa ba ne saboda ba ma anfani da shi kuma ba kalar na gidan Abbah Hashim ba ne ba ajiye tunanin na yi na ce

    "Eh Aunty amma nakusa gamawa”

    "Ok ki yi a hankali fa idan ya soyo man sai a fara saka wanda kikayi blending ɗin, shi ya sa nafisan akaimin markaɗe ya fi saurin aiki toh kina jina dƙ mutumin naki Jabir kansa ke ciwo"

    Murmushi na yi na ce "Eh Aunty tun a mota ya faɗamin da gaske yake”

    "Hmmm baki san Jabir da ƙin aike ba Sumayyah, danshi harma yafisan na barmasa ya yi girki, shi kuma Muhammad shiririta garesa ne” Cewar Aunty ta ƙarasa maganar tana ɗaukar robar kayan miyan da na zuba wanda na gama markaɗawar masu yawa, Kayan miyan suna da yawa ba laifi duk tsadar da sukeyi ita Aunty bata gani ba acewarta ai Mama inta farko irin wannan abincin take son ci mai miya mita, shi ya sa har kifi mai yawa Aunty tasa Abbah Zaid ya siyo dan kafin mu gama aikinsa Aunty ta nuna min yadda zan yi blending ɗin na fara

    "Kamar kukan A'isha na ji” tayi zancen tana ci gaba da juya kayan miyan da tagama zubawa

    Kunne na kasa cikin falon da ni ma kamar kukan na ji kallonta ta dawo gareni ta ce

    "Kin ji ko kema?"

    Na daga kai "Eh Aunty wallahi kamar kukanta”

    Aunty ta dube ni” Kin ga cire mana kokwanton jeki dubota, ƙila Muhammad ya bar falon ma a jiye blending ɗin maza ki wanke hannu"

    Umarnin Aunty na bi na Tara hannuna cikin fanfon wanke wanken kitchen na sa omo na wanke cikin sauri na bar kitchen ɗin

    Ban same ta tana wani kukan a zo a gani ba dan idanta rufe take kukan alamun tashi take yi, hakan ya sa na ɗauke ta na fara jijjigata dandanan ta koma barci ganin Muhammad baya falon ya sa ɗauki towel ɗin ta na rufe ta da shi na koma kitchen ɗin

    Sallama na yi Aunty ta amsamin ta dubemu nida Aisha ɗin

    "Kukan take ko?"

    Kaina ɗagama Aunty daganan na ce” Eh Aunty za dai ta fara tana ƙoƙarin tashi barci ne, kin gama ta koma”

    Aunty ta gyaɗa kai” Wato shi Muhammad ya fice ya barmin yarinya a haka yakeson ƙanwar zai dawo ya sameni ne”

    Dariya na yi kaɗan jin zancen Aunty dan yadda na san Aunty da Muhammad bata bugunsa ko faɗa Jabir ya ce batasan a yima Muhammad ta ce mai babban suna ba’a masa faɗa bare zagi, duk da dama ban da ƙin jin kaɗan na yarinta baya komai saidai da ɗan gatane

    "Kina dariya ke nan Allah kuwa, dan Abbansa na hana ni make yaron nan wani lokaci, juyo na sa miki ita baya, kema na lura wahala kike so ki baiwa baiwar Allah"

    Ni dai shiru na yiwa Aunty jin zancenta dan Jabir yana faɗa min za mu fito asibiti cewa Muhammad na kuskurewa sai Aunty ta ce Abbah Zaid ne kaza kaza alhalin ita ce, Miiƙa mata A'isha na juya baya ta sakamin ita na ɗaure zanin

    Cabbage da Gurji da Karas da sauransu Aunty ta ba ni yankansu na zauna brander a kan kujera a ƙofar baya ta kitchen na fara yankawa ganin banajin daɗin aikin saboda goyo saidai ina miƙewa na sauke A'isha Aunty za ta ce a'a ba za a kwantar da ita a barta ita ɗaya ba wani gata nake gani Aunty na nunawa A'isha dan ko Mama albarkarshi, Wani girma na uwa na baiwa Aunty a zuciya irin yadda take kulawa da lafiyar Mama a yanzu ita da mijinta danko Aunty batayi hakaba ko waccen maganar ni banga aibun Aunty ba duk da a kan mahaifinane dan a tunanina a zuciya da ɗan uwan nasu aganii za su iya ɗawainiyarsa su masa abin da suke yaudararsa ya rabu da Mama za suyi masa ɗin, sai nake ji ta cire min wani daga cikin ciwan na idanuna duk da ban shekaru ban taso da saninta ba amma ta fiye min Aunty Mubaraka, Aunty Maimuna da sauran su musamman Aunty Asma'u ma da har zuwa yanzu abunda tayi min ya kasa barin tunanina nakan ji ciwo mai tsanani a raina na tarin girman laifinta da zuciyata take gani

    "Ɗauko carpet ki zauna ƙasa mana Sumayyah za ki fi jin daɗi ga lokaci yana tafiya ma” Maganar Aunty ya katse min tunanina

    Juyawa na yi na kalli daga inda maganarta hangota na yi ta leƙo da kanta inda nake ɗin, cire hannuna na yi a cabbage tare da wuƙar ina ƙoƙarin miƙewa na ce "Toh Aunty"

    Cikin kitchen ɗin na dawo ina ƙoƙarin wuceta ta ce

    "Yawwa Sumayyah idab baki ga ko ɗaya a falo ba, ki duba ɗakin Jabir ko na Muhammad koma nawa”

    "Toh Aunty" Ina zuwa falon na tarar carpet sallaya ɗin na ɗauko na dawo na zauna na zauna na ci gaba da aikin wajen 1:30pm na rana muka gama komai dan aikin Gas ba dai sauƙi ba, Muna kammalawa Aunty ta dube ni

    "Yawwa ki je ki watsa ruwa sai ki yi alwala akwai zafi ki kwantar da Aishar a gado ki mata addu'a kafin ki shiga wankan"

    Nace "Toh Aunty"

    Badan na so ba dan mun yi wanka da safe gidan Aunty ɗin kuma yanzu ba a cikin rana mukayi aikin ba haka na fito na shiga bed room ɗin Aunty dake ƙasa da a nan da safen ma mu kayi komai A'isha na kwantar na mata addu'a da Aunty ta ce na yi Sannan na tura banɗakin na shiga Aunty tana da tsafta sosai a ɗari ɗari na yi wankan da alwala ma kuma sake wanke bayin yadda na samesa na fito ina jin wani daɗi jikina ga ƙamshin sabulu mai tsada da nake yi dan Aunty sabon soso da sabulu kalar wanda take wanka da shi da na ganshi a bayin da safe shi ta aje mana da yanzu ma inda muka barshi a bayin na tarar da shi

    "Alhamdulillah"na furta a hankali dan kuwa mai wanka da omo ko sabulun wanki ya yi da ƙaton sabulu haka mai ƙamshi da ban san sunanshi ba Aunty ta cire kwalin ta kawo mana

    Mai vaselline dake saman madubi na ɗauka na fara shafawa kaɗan ƙaɗan saboda zafi ina cikin shafawar na ji ƙwanƙwasa ƙofar Handling ɗin ƙofar naje na murɗa na buɗe yadda na yi tsammani Aunty na gani matsa mata na yi ta shigo ciki kallona Auntyn tayi

    "Ba dai kayan jikinki za ki mayar ba?"Kayana dake saman drower ta jikin gado riga da ɗankwali da zanin ke ɗaure jikina nakai dubana kai, Sannan na kalli Aunty na ce

    "Eh Aunty ai banzo da wasu ba”

    Auntyn ta girgiza kai” Oh Sumayyah to ba ga nawa ba sai kisa, tun da ai sun ɓaci wannan ɗin kin yi wanka da zanin ya yi laima bare ma akwai na Intisar sabo da na yi mata ta zo hutu ban sani ba ta gudu gidansu ni kuma na ce nafasa bata kayan bari na ɗauko miki kisa ɗaya daga ciki” ta ƙarasa zancen tana ƙoƙarin buɗe Sib ɗin ta

    Material mai kyau Aunty ta fiddomin a Sib ɗin ta ajemin gefen gado

    "Yawwah gashinan ki saka ita Intisar kin ga tama kanta ai”

    Murmushi na yi sannan na ce” Na gode Aunty"

    "Yawwah ba ki yi sallah ba ko?"

    Kai na ɗagawa Aunty na ce” Eh na yi alwala

     Daddynsu Jabir yana jira zamuyi Jam'i sun sha barci sun makara zuwa masallaci yi maza ki saka kayan"

    Tayi maganar ta na maida kanta cikin Sib ɗin kaya ta fiddo ta yi hanyar fita

    "Yawwah ki fa zura kayan kawai in za ki saka powder ki bari ayi sallar"

    "Toh Aunty"

    Tura ƙofar ta yi ta fita ni kuma na ɗauki kayan rigar na ware ina warewa na ga pant a jiki jin daɗi na yi sosai dan dama ya yi laima na jikin nawa brezia na saka na zura material ɗin da ya yi min cif kamar an gwada danni aka yi shi gashi mai kauri ne sosai ko ba underskirt za ka sakashi, nawa under skirt ɗin da yasha jiki ya koɗe Black color ne da aka ce kalar dauɗa sai dai a zahirin gaskiya baƙar kala tafi kowacce kala saurin yin datti da bayyana shi ina sawa na ɗaura ɗankwali na sa hijabi na fito a falo na samesu har sun tada sallah na koma baya naja sahu sai ga Aunty ta zo ta jera dani mun yi

    Da muka iddar Addu'a mabanbanta Abbah Zaid yake kwararowa kamar ba sallar farilla mukayi ba aka ma Mama addu'a mukayi Azkar muka shafa addu'a

    "Daddy Ina yini?, Aunty Ina yini?"Jabir da Muhammad na jiyo sun faɗa cikin haɗa baki

    "Lafiya ƙalau"naji Muryar Abbah Zaid ya faɗa ita ma Aunty da murmushi ta amsa da "Lafiya ƙalau"

    Yadda su Jabir sukayi ni ma na yi na gaida Aunty da Abbah Zaid cikin kulawa suka amsamin

    Su Jabir dake ƙoƙarin tashi Abbah Zaid ya daka musu tsawa "Ina zakuje?, wuce ku zauna ita yayartaku ba ku gaidata ke nan?"

    Kai suka girgiza sannan suka gaishe ni suka miƙe

    Abbah Zaid inda muke da Aunty ya juyo ya kalli Aunty

    "Kin bawa Sumayyah wasu kayan tasa ko?"

    Ta ɗaga kai” Eh Daddyn Jabir na bata na Inteesar"

    "Ok ya yi ki zubo abinci muci sai ku tafi asibitin su Muhammad su wuce islamiyya”

    Aunty ta ɗan ɓata fuska” Mu tafi dai zakace ka san banasan driving wallahi”

    Miƙewa Abbah Zaid ya yi ya ce” Toh ki zauna sai dare ni dai zan koma tun da ba za ki yi tuƙin ba, kuma zan kaiwa Maman Inteesar motar"

    Miƙewa ita ma Aunty ta yi ta ce” Ina ba zai yiyu ba zan iya ma”

    Abbah Zaid dariya ya ɗan yi ya koma kujera ya zauna ya ce

    "Toh na ji karkimin bori zubo mana abincin muci”

    Hararar wasa Aunty ta ma Abbah Zaid ta ce” Ni ce ma zan yi borin ko?"

    "Bafa borin komai nake nufi ba Malama”

    Kwafa Mama ta yi ta wuce tana kirana na zo na taya ta fiddo abincin a dining Area muka shirya su Jabir suka fito muka ci gaba ɗayanmu, muka ƙara sa shiryawa zuwa asibiti a babbar kula ba laifi Aunty ta zuba abincin asibiti ta zuba miya a ƙarama food flask cabbage da sauran a wata ƙatuwar roba sai farantai da ruwa na manyan ledoji masu sanyi, Jabir ya tatayani fitarwa muna sawa a boot ɗin motar Aunty mai kyau sosai, Aunty ta tsaya Kitchen lokacin haɗawa A'isha madara

    Abbah Zaid ya buɗe mana gate muka fito tare da su Jabir za ta ajesu a makarantar Islamiyya

    Sosai rayuwar gidan Aunty take ƙara burgeni musamman yanzu a ɗan yinin da na yi ina sake fahimtar kyawun rayuwar gidan komai cikin sanin rayuwa sukeyi da ƙoƙarin shimfiɗa tarbiyyar gidan a tafarkin tsira, ba suda wulaƙanta kowanne ɗan adam dan da suna yi duk yadda suke da Mama ba za ta so ƙara zama da ita a yadda rayuwarmu take a yanzu ba da sai ta mana wulaƙanci fiye da na Aunty Asma'u a matsayinta na karatu kaɗai ya haɗata da Mamarmu bayan wannan ba zance ga wani abu ba mijin Aunty bai san Abbah ba dan a yadda Jabir yake ba ni labari Abbah iyayensa a porthacourt suke zaune shi ma kasuwancin iyayensa da yake yi a gida ya maidoshi Gwarzo, Amma suka karramamu da mutuntamu karamci da Abbah Imran ba zai iya ba bare kuma Abbah Hashim kuma zumun cinmu ya gama lalacewa tsakaninmu dasu ban kuma san yaushe ne zai dawo yarda yake ba, sai dai roƙona Allah ya ganar dasu kawai da mu kanmu ɗin. . . . . . .

    Na Cancanta (Kashi na 41)

    3:02pm shi ne ya yi daidai da ƙara sa parking ɗin mu a parking space na asibitin cire kaina na yi daga kallon agogon cikin motar na miƙa hannuna na taɓa handling ɗin motar na buɗe zancen Aunty ya katseni tana miƙo hannu

    "Kawo Aishar ki sauka saina miƙo miki ita” ba tare da na yi musu ba na miƙa wa Aunty, Aisha, Ni Kuma na fito daga wajen ina fitowa Aunty ta fito da A'isha a kafaɗarta rufe murfin ƙofar ɓangaren da na fito na yi Aunty ma na ɓangaren da ta fito ta yi ta sawa motar key

    "Yawwa Sumayyah dawo tanan na goya miki ita mu ƙara sa Boot mu ɗauki abincin"Abin da ta faɗa ɗin na aiwatar ba tare da na yi musu ba, kuma ba tare da na ji komai ba bare yazamarma zuciyata ƙorafi dan ko Mama ɗin haka take mana ɗin ma indai munanan mune masu goya A'isha da ɗaukar ta ni ma raino yabi jinin jikina zan iya cewa

    Ƙofar boot ɗin Aunty ta buɗe muka ciro kayan sannan ta rufe Boot ɗin muka ɗauka muka ƙara sa zuwa ɗakin da Mama take kwance

    A brander ta kusa da ɗakin muka tarar da su Gwaggo su Rumaisa sai su Aunty Jamila sun shimfiɗa tabarma sun yi zazzaune ga kulolin abinci gefen su gaisawa mukayi dasu

    Gwaggo ta dubemu ni da Aunty da muke ƙoƙarin aje kulolin namu abincin gefen Gwaggo

    "Har da wata hidimar haka Rumaisah?, Ai da kin bari ma su Jamila duk sunzo mana da shi yanzu muka gama ci” Cewar Gwaggo

    Aunty ta ɗago fuskarta ta ce” A'a Gwaggo ai ba wata hidima abincine kuma ba yawa ma sosai, na su Jamila ai dabanne nawa ma dabanne, zuwa anjima sai aci wannan"

    Gwaggo ta riƙe baki” A'a Rumaisah akwai fa hidima tun jiya da aka kawo Hauwa'u kuke ta faman yi, yanzu kuma ga ɗawainiyar abinci kuma haka mai yawa”

    Aunty ta girgiza kai ta ce

    "Allah Gwaggo ba wata hidima a nan ban ganta ba, duk abin da zan yiwa Hauwa'u ai ban faɗi ba, Domin na san da Hauwa'u ce mai ƙarfin fiye da wannan za ta yi min kuma ba tare data gaji ba, kin tuna dai yadda muke tare dai Gwaggo in ban yi mata ba gani nake wazai mata kuma ina jinma kamar ubangiji ba zai yafe min ba indai ina da shi ban yiwa Hauwa'u ba”

    Gwaggo ta girgiza kai” A'a Rumaisah kidaina faɗar hakan ai mune dolen Hauwa'u mu ya dace muyi mata idan ba muyi ba Allah ya iya kamamu da laifi ma”

    Aunty ta yi murmushi ai ni ma dolenta ce Gwaggo"

    Gwaggo ta jinjina kai ta ce” Allah ya barku tare ya ƙara danƙon zumun ci, Allah ya biya ki abin da kikayi”

    Aunty ta yi murmushi ta ce” Amin Yawwa Gwaggo haka ya kamata ki ce kawai, yanzu dai ya jikin nata ta farka ko?"

    Gwaggo ta ɗaga kai” Eh ta farko ba daɗewa an kirama likita mijinta yana ciki Likitan ma yanata faɗa da ya zo ya samemu a ciki gaba ɗayanmu shi ne kika gan mu wajennan yanzu ma ya ce ko sun fito bame sake shiga sai can anjima”

    Aunty da take ƙoƙarin zama kusa da Gwaggo ta ce” Alhamdulillah, Allah ya ƙara mata lafiya dama ba'asan ana damun mara lafiya da hayaniya ai Gwaggo ɗazun ma ina jin abin da ya sa basuyi magana ba saboda anyimata alluran barci, barcinnata ya yi nauyi amma yanzu zaryar ma sai an rage ta ai tun da private asibiti ne "

    Gwaggo ta jinjina kai gami da kallon Aunty ta ce "Eh haka shi ma duk ya yi bayani likitan, amma ya za ki zauna kuma?ai ya kamata ki shiga kema dake fa aka yi komai jiyan "

    Aunty cikin ladabi ta ce” A'a Gwaggo tun da Abdulllahi na ciki kuma shi ne mijinta ba sai naje ba da dai Daddynsu Jabir ya zo ne sai ya shiga jiyan ma duk shi ne ya yi abubuwan da ya kamata a ce anyi ɗin ba ni ba”

    Gwaggo ta ce "Haka ne amma da kin shiga ɗin kiga yana yin jikin nata kun yi ɗawainiya da ita da ƙarfinku da kuɗin ku daga jiya zuwa yau ɗin nan kuma abunda kuke buƙata yasamu, Allah dai ya saka muku da alkhairi ya ƙara zaman lafiya ke da mijinnaki, dan a tunanina a baya gatansu ya ƙare daga abin da ya faru tsakaninsu da waɗancen mutanan yanzu saina ƙara miƙa wa Ubangiji lamuranmu na sake yaƙinin gatan kowa Allah ne”

    Ina jin Gwaggo na maganar waɗancen mutane na fahimci ƴan uwan mahaifinmu take nufi da a zahirin gaskiya ma zancensu ma banasan ji wata tsana mai girman gaske nake ji tana tasomin da zarar na tuna su da me laifin da marasa laifin duk na musu kuɗin goro, maganar Aunty ta maidoni cikin tunanin da na faɗa

    "A'a Gwaggo ai wannan dan Allah kawai mukayi waɗanda ma ba ka sani ba kana yi musu idan ta kama ba tare da ka tsaya jiran komai ba daga garesu ko da godiyar su ma bare wannan kuma, su kuma Allah ya ganar dasu in za su gane”

    Ni da nake tsaye ƙiƙam ban iya cewa Amin ba da sauran na ji suna ambata dan na san da wuya dai wanda ya yi nisa ya gane gaskiya dan wasu ko mutuwa bata zamar musu wa'azi bare halin rayuwar da wani ya tsinci kansa a dalilin abunda ya yi ya damesu

    "Oh Soja za ki ta fi ke nan? Hajiya Sumayyah"Muryar Aunty Asiya da na ji ta fidda ni tunanin da nake na ɗago na kalleta na yi murmushi

    Gwaggo ta kalli Aunty Asiya ta ce” Wanne irin soja kuma Asiya”

    Aunty Asiya ta kalle ni ta maida kanta ga Gwaggo"Eh mana Gwaggo tun fa da suka zo take tsaye a nan kamar soja ko body guard shi ya sa kikaji na tambayeta”

    Aunty Maryam ta kalle ni” To ai goyon A'isha ne bayanta ina jin za ta tashi ne tana zama”

    Aunty Jamila ta ce” Ai fah za ta iya tashi yarinya abu ba abu ba ko girma batayi amma sai rigimar tsiya, ƙyaleta ki zauna abinki in ta yi kuka a kaiwa uwarta”

    "A kaiwa wacce uwar tata nufinki kin san dai Hauwa'u bata ɗaukar ta yanzu ina ma tagama dawowa hayyacinta saidai a baki ita”

    Aunty Maryam ta yi maganar tana hararar Aunty Jamila

    Ina ƙoƙarin zama kusa da Gwaggo ba tare da na ce komai ba dan haka nan na ji inasan tsaiwar dan A'isha ta yi barci tuni

    Aunty na ji ta ce” A'a fah ai ni ce uwartata, sai nake ji ina ma Hauwa'u ta barmin ita wallahi Aunty Maryam"

    Aunty Maryam ta yi murmushi” Anya kuwa ai dama ta yayeta ne yanzu kuwa ai ba zai yiyu ba”

    Fitowar su Abbah daga ɗakin shi da likita ya katse firar da akeyi likitan ne ya wuce yabar Abbah hankalin su Gwaggo ya dawo kan Abbah suka haɗa baki gurin cewa

    "Ya jikin Hauwa'u ɗin"

    Abbah da yana yin damuwa kaɗan ya ce "Alhamdulillah amma an sake jona mata jinin ma yanzu allurar barcin ma an sake mata, sunce suna buƙatar ta riƙa samun barci”

    Sake haɗa baki suka yi da cewa” Toh Allah ya ƙara sauƙi”

    Abbah ya kalli Aunty"Yaushe kuka dawo?"

    Aunty ta ce” Yanzu babu daɗewa, amma daga wannan ai ina jin an gama saka jinin, inda buƙata za su sake ɗibar jinin nata duba iya adadinsa kafin su ƙara tun da ansa uku ke nan"

    Abbah ya girgiza kai ya ce "Wallahi ban sani ba, baiyi min bayani ba”

    Aunty ta ɗaga kai” Eh dama ba tambaya ba ne na ji suna ma Daddynsu Jabir bayani ne jiyan, Allah ya bata lafiya”

    Abbah ya ce "Amin Allah ya saka muku da alkhairi”

    Duka muka amsa da Amin, Gwaggo ce ta kalli Abbah

    "Yawwa bari a zubo maka abincin gama na Rumaisah na san da zafinshi”

    Aunty Asiya ta kalli Gwaggo"wai dama baici abincin ba Gwaggo?"

    Gwaggo ta ce” Eh mana kin manta, zai ci Hauwa'u ta tashi ya tafi kiran likita”

     

    Aunty Asiya ta ɗaga kai sannan ta kalle ni” Sumayyah zuba wa Abbahnku abinci mana”

    Miƙewa na yi jiki a sanyaye kamar ƙwai ya fashemin haka na fara zubawa Abbah abinci, tun da na ji ana sake ƙara wa Mama jini ga wata allurar barcin jikina ya sake sanyi ina jin kamar muna gaf da zama marayu duk da bawai a nan take ba ita mutuwa saita ɗauki mai lafiya tabar wanda yake buƙatar mutuwarma idan kwana ya ƙare dole ne ba makawa ka tafi, Hakan na ci gaba da tunanina har na gama zubawa Abbah abinci na ƙara sa inda yake ina ƙoƙarin miƙa masa na ji muryar Gwaggo

    "Bari Sumayyah Ahmad ya ɗauko kujera a ciki ya sa masa acan wajen" Juyowa na yi ina kallan inda Gwaggo ke nunawa da hannu gefen inda muke ne kaɗan, Dawowa na yi na rufe abincin da wani plat ɗin sannan na koma na zauna inda nake, Ahmad ne ya miƙe ya ɗauko kujerar ya sawa Abbah ya dawo ya ɗauki plate ɗin ya kai ma sa

    Kamar jira Aunty Asiya take ya bar gurin ta fara magana

    "Allah Gwaggo dan kince abar tuna bayane kika ji na yi shiru ni ma amma ba abin da ke damun Yaya Hauwa'u sai yunwa wallahi haba ni na rasa abin da ke damun wancen mutumin"

    Aunty Jamila ta amshe zancen"Kema dai kin faɗa Asiya abun na cikin tuwo a kwarya kamar wanda aka yiwa asiri haba rayuwar dai gaba ɗaya sai a hankali”

    Aunty Maryam harara ta auna musu"Zaku fara halin naku ko?, gaban ƴaƴanshi su yi muku fitsara kuce basuda kunya”

    Aunty Jamila ta ɓata fuska "Wanne halin namu kuma mufa gaskiya ce sai mun faɗa indai mun ganta, Dangin ubansu za su yiwa rashin kunya idan ma ita ce, wa ma ya sa ni ko saboda ƙiyayyar da suke yiwa Yaya Hauwa'u suka asirceshi, ya zauna ba a tsiya ba arziƙi ba”

    Gwaggo ta kalli Aunty Jamila ta harareta” Yi ta yi Jamila tun da ba kyajin magana sai ki yi ke kaɗai ko idan ƙannanki su Zainab masu biye miki sunzo ku yi zancenku tare, mu dai ta lafiyarta muke yi”

    Aunty sai yanzu tasa baki” Ni Gwaggo ma maganar asirin da tayine bata yi min daɗi ba, inma shi sukayi ai ɗan su ne kuma komai ya samu bawa rubuce yake wani sila kawai yake zama dan Allah Jamila ki iya bakinki dai”

    Aunty Jamila ta ɗaga kai "Haka ne Yaya Rumaisah"

    Gwaggo ta harareta "Watoh Maryamu kin rainata kina ganin ta kullum ko?"

    Aunty bata bawa Gwaggo amsa ba saima tashin da tayi” Bari naje dubo wani yaro ɗan makwabciyata an kawoshi nan"

    Aunty Asiya ta harareta” Wa toh ba za ki ce na zo muje tare ba?"

    Aunty Jamila ta ce” Yanzu fa zance kin cika ƙorafi wallahi”

    Gwaggo ta kallesu"In madai abin da ya fi ɗan makwabciyane kun yi gulmarku ku gama”

    "Haba Gwaggo maimakon ki yimasa addu'a amma kina neman ma ƙaryata wa” suka haɗa baki gurin bawa Gwaggo amsa da haka

    Aunty Maryam ta yi dariya kaɗan"Ai Gwaggo ta hardace halinku ne”

    Dariya suka ƙunshe suka bar wajen kallon bayansu Gwaggo ta yi ta ce "Allah dai ya shirya yarannan kawai”

    Su Aunty suka amsa da "Amin"

     A raina ni ma da "Amin"ɗin na amsa ina murmushi na bisu da kallo, suna burgeni Aunty Jamila da Aunty Asiya bakinsu kusan a haɗe yake ka sancewarsu sakwanni da halinsu ya zo ɗaya kuma gidajensu babu nisa da na juna

    Maganar Aunty ta katse min dogon tunanin da nake shirin faɗawa” Kin haɗawa Abbanku da ruwa ne?"

    Kai na girgiza” A'a Aunty ai kamar mun manta ruwan ma a mota” na ƙarasa maganar ina juyar da kaina inda muka aje kayan

    Aunty ta ce” Kwarai kuwa kayan ne sun yi mana yawa, Ahmad tashi ka buɗe Boot ka ɗauko za ka iya?"

    Ahmad ya ɗaga kai” Eh Aunty"

    Aunty ta yi murmushi” Au na fa manta karambaninka kaida Jabir"

    Ahmad amsar key ɗin ya yi ya bar wajen, Aunty ta shiga ba da labarin ƙinjin da Ahmad ke mata lokacin yana zuwa gidan nata Gwaggo na sake ƙara mata wani labarin na rashin jin Ahmad. . . . . . .

    Na Cancanta (Kashi na 42)

    Ina ɗago idona ya sauka kan Malika da take ta aikamin saƙon harara har ta ƙaraso inda muke zaune da sallama sannan ta gaishe dasu Gwaggo Aunty da batasan Malika ba na ji tana cewa Gwaggo

    "Gwaggo wace ce Malika ko ɗiyar Yaya Maryam ce?"

    Gwaggo ta girgiza kai” A'a wannan ƙawar Sumayya ce makwabtansu ne kuma, Amma ɗiyar Maryama ko Nasiba tafi su Sumayyah girman jiki bare Abida kamar Maryama jikinta yake da girmanta, kuma Abidah ta girmi Sumayyah da a ƙallah shekara uku ma ƙanwarta kuma Nasiba ma ta girmi Sumayyah, duk suna makaranta da tuni kin gansu sunzo"

    Aunty ta yi murmushi "Alhamdulillah ai karatun na da anfani indai da halin yi ɗin tun da zaman ma ba auran ba ne sai Allah ya kawo, Allah ya taimaka ya ba su sa'a ya kawo miji na gari”

    Gwaggo tace” Uhmm ke dai Rumaisah to Amin dai amma ƙoƙartawa kawai akeyi dai haka nan, gashi a haka har Abida ta kusa gamawa, sai bautar ƙasa ita kuma ƙanwarta Nusiba tana Shekara ta biyu ne da shiga ita ce ta ba Sumayya kusan shekara”

    Aunty ta ce "To ya za ayi Gwaggo haka za a ci gaba da ƙoƙartawa, Allah ya ƙara horewa ai ilmi makarine indai da shi ko ya yake za kiga banbanci da wanda baiyi ba a dai wannan zamanin da muke ciki bare su kuma ai za ki ƙara ganin rayuwarsu ta ƙara canzawa da abubuwa masu kyau insha Allah addu'ar ku dai ita ce makaminsu a ko ina”

    Ni ko da hankalina na ga hirarsu Aunty da Gwaggo da har nama manta da zuwan wata Malika ma dukan da na ji a cinyata ya sani maido da hankali na zuwa ga inda aka dokeni Malika ce da take zaune kusa dani da ban san ma ta kai ga zama ba

    Cikin haɗe fuska na juyo gaba ɗaya ina kallan Malika ita ma haɗe fuskar ta yi ta kuma ƙimin magana ni ce na katse shirunmu

    "Haba Malika me na yi miki?"Duk da na san laifin nawa amma inason sake jin ba'asi

    Hararata Malika ta yi "Bansa ni ba Sumayyah, tsabar wulaƙanci na zo gaishe da mamarku ki juyamin baya ma ni ce ma na zo ai tun da baki iya faɗa min ba”

    Ganin na yi laifi inji Hausawa sunce gaishe da mai gaisheka ko ba zai amsaba hakan ya sa na sassauta da murya na ce” Haba mana ƙawata shi ne to na dukan hankalina yana wajen maganar su Aunty ne fa, kuma wallahi da wuri muka taho asibitin ne, waye ya miki bayanin asibitin"

    "Uhmm kin gama daɗin bakinki ba buƙata kisan waye ya faɗa min ai bari na tashi saiki fi sauraron labarin da kyau"Malika ta yi maganar tana miƙewa, ni ma miƙewar na yi ganin ta fara tafiya ya sa ni ma na bi bayanta

    "Toh sai kizo ki gaishe da Mama tun da kinƙi yarda ki haƙura”

    Kallona ta yi "Rakani to wajen Mama ɗin"

    Murmushi na yi” dan Allah kiya haƙuri Malika ita Mama ba a fara ganin ta ba ma kin san private Hospital sunce batasan hayaniya ne”

    Daƙyar na lallashi Malika ta dawo ta zauna, Aunty ta dube ni

    "Ya na ga ɗazu ta tashi?"

    Na yi murmushi na kalli Malika sannan na ce” Ai da ta yi fushi ne Aunty"Murmushi Aunty ta yi ba tare da ta ce komai ba suka ci gaba da fira da Aunty Maryam

    Har Yamma sosai Malika takai a asibitin sannan ta ce za ta tafi za ta yi suyar dankali, dama ta jira ko za a bari a ga Mama amma har lokacin ba su ba riba, sallama ta yiwa su Gwaggo sannan na biyota na ɗan rakata hanya muna tafe muna ɗan fira

    "Juraid kuwa ya san Mama bata da lafiya?"Malika ta jefomin tambayar a lokacin muna ƙoƙarin rabuwa

    Kaina girgiza mata Sannan na ce” A'a gaskiya ban faɗa masa ba”

    "To wai maiyasa ne?, kin san ba zaiji daɗi ba idan baki faɗa masa da wuri ba”

    Cikin sassauta murya na ce "zan fa faɗamasa amma kin san me Malika banasan wannan hidimar tashi tana yin yawa gashi Abbah ma bayaso duk ya kawo saiya yi min faɗa

    Malika ta ɗan taɓe baki” Haka nan za ki daure ki faɗa masa, ai hidima ta zama wajibi indai kanasan mutum shi ma duk ciki soyayya ne ko mai ƙantarta musamman ma ke kuma ai kin cancanta ayi miki saima a samu lada”

    "Haka ne dan Allah toh kifaɗamasa idan kin koma gida na san zaizo ai wajen dankalinki”

    Ɗan rausayar dakai tayi” Eh ƙila suzo, idan madai ba su zoba Yaya Nasir zan faɗa masa, kin ga dasu Zainab sunzo tare”

    "Ai Gwaggo ta ce sunzo da rana kafin muzo saidai ƙila Uncle Jabir ya zo da wata cikinsu"

    "Toh shike nan sai kun taho zance” cewar Malika

    Kai na ɗaga mata "Toh shike nan mun gode sosai a gaidamin Na'im"

    Murmushi Malika tayi” wato iya Na'im ko?Yawwa Sumayyah ban gane wannan Aunty taku ba na ji Gwaggo ta ce mata Rumaisah sister ɗin waye?"

    Murmushi na yi” Oh wai ba kisan Aunty Rumaisah ba ƙawar Mama ce baki ji Rumaisah da sunanta ba?, zan iya ce miki ta mafi ƙawarta ma, duk itafa ta yi komai na asibitin nan"

    Jinjina Malika ta yi "Masha Allah ban ɗauka da ƙawa irin wannan a yanzu ba Allah na yi zaton sister ɗin Mama ce ta jini ko wannan zaman asibitinma da ta yi batayi komai ba ai ta yi ƙoƙari matuƙa, amma ba mu taɓa zuwa gidan ta da keba ko?"

    Ɗaga mata kai na yi na ce” Eh mana mu kanmu ba mu jima da saninta ba, mu muna kano ita kuma sunfi zaman Abuja karatun yaranta ya zaunar dasu gida yanzu, kuma ko bakin Mama banma san sunan Aunty ba kin san Mama batasan shiga cikin ƙawayenta yanzu sai taga kamar za a nuna mata ko in kula tun da ita bata da shi yanzuma Ahmad ya sake haɗa mu aikinnan da ya fara toh a gidanta ne”

    "Allah sarki amma na ga tana da kirki sosai namaga A'isha hannunta, Mama fa nada gaskiya Sumayyah yanzu ɗan uwanka ma sai kanadashi kake nashi shi ya sa nesa nesa ko Ummanmu haka take”

    Kai na ɗaga alamun gamsuwa da zancen Malika Sannan na ce "Haka ne Malika ni ma daga kan Aunty na ƙara tabbatar ba duka masu kuɗi suke haka ba wasu talakawa suka fi ƙaunama tun da Mama fa jiya aka kawota asibiti A'isha ke hannunta, kin ga bari dai sai mun haɗu gida sai muyi labarin sosai kar magriba tayi”

    Malika sama ta kalla sannan ta kalle ni

    "Haka ne kuwa kin ga har rana ta gama rufewa ma”

    Harta fara tafiya ta juyo"Yawwah ki gaida min Mama idanta tashi”

    Kai na ɗaga mata ita kuma ta juya ta ci gaba da tafiya

    Bayanta na bi da kallo Malika akwai kirki sosai ita ma tana cikin mutane masu muhimmanci a rayuwata da wannan tunanin naja ƙafafuna na koma cikin asubitin inda muke

    ***********************************

     Ƙarfe takwas da mintina Mama ta tashi likita ya ba mu damar shiga mu dubata

    Kallon Mama nake cike da tausayi haka ita ma idanta na kanmu har muka ƙara so gefen gadonta muna jera mata sannu

    Gwaggo zama ta yi gefen gadon "Sannu Hauwa'u Allah ya ƙara kiyaye gaba kawo muku mafita ta Alkhairi, yanzu meke miki ciwo?"Gwaggo ta ƙara sa maganar tana goge hawaye

    Mama cikin muryar ciwo ta ce” Gwaggo ta yardani na gaji da kwanciyar"

    Gwaggo da Aunty da suka fi kusa da ita suka tayar da Mama, sai sannan Khalil ya ƙara sa inda Mama take Aunty ta ɗaurasa kan gadon

    Mama da ta fara waige waige ta maida dubenta ga Gwaggo

    "Mama ya banga A'isha ba?ko ta mutu ne?"

    Gwaggo ta girgiza kai ta yi murmushi kaɗan"A'isha na wajen Rumaisah tun jiya madara ma ta siya mata ana bata yanzu ta yi barci, Hauwa'u Rumaisa ta gama zama ƙawar arziƙi ba wajenki kaɗai ba har wajenmu ma ba dan ita ba da ƙila zancen wasu akeyi yau ba naki ba ita ta tsaya kan komai itada mijinta”

    Mama kai ta ɗago ta maida dubenta ga Aunty, da tun da Gwaggo ta fara magana idan Aunty ya koma kallan ƙasa kasa magana Mama ta yi ita ma

    Gwaggo ta ci gaba da cewa” Tun da na zo na ga jikinki na fita nemo kuɗi ni ma yarda mijinki ya fita nemo wa haka muka dinga cigitawa babu ba’a samu komai ba kafin mu dawo gidan kuma Ahmad ya kira Rumaisah sai ji mukayi ankaiki asibiti ba ma na gwamnati ba na kuɗi, da da ƙawaye kamar Rumaisah na tabbatar da babu wanda rashin shaƙiƙin ɗan uwan da dan babu shi ko yana da shi ya ƙiyi ko bashi da shi damuwar hakan za ta dameka tun da aka kawoki nan ɗin daga jiya zuwa yau ita da mijinta ke hidima da. . . . "

    "Habah!Gwaggo kin san bata gama jin sauƙi ba kuma ba komai cikinta dan Allah ki kyale maganar nan haka” Aunty Maryam ce ta yi hanzarin katse Gwaggo da cewa hakan

    Gwaggo ta goge hawayenta ta kalli Aunty Maryam tare da harararta” Na ƙi na yi shiru abin da ba mu da halin yi muka samu mutane masu arziƙin da suka fiyewa Hauwa'u dangin mijinta da ta tara ƴaƴa ɗaya ɗaya har shidda da su dan na yi zancen shi ne abun laifina kome?"

    Aunty Jamila jin Gwaggo ba za ta bar maganar ba ya sa sauri matsawa gadon da Maman take a hankali na ji tana cewa” Sannu Yaya Hauwa'u, me kike son ci yanzu?"

    Mama ta girgiza kai a hankali ta furta "Babu komai”

    Aunty Mama ta ɗago ta kalla” A'a ba zai yiyu ba likita ya ce lallai kici abinci sannan kisha magani, Sumayyah bare ayabar can ki miƙo mata”

    Da saurina na ƙara sa inda ledar ayabar take ajiye da Uncle Sha'aban na ji Gwaggo ta ce shi ne ya kawo ɗazu buɗe ledar na yi na ciro ayabar na ɓare na miƙa wa Mama tas ta cinyeta

    Aunty ta dube ni” Ƙaro mata wata tun da ta cinye "

    Ƙara ɗauka na yi na ɓare na miƙa mata na koma na tsaya inda nake

    Gwaggo ta dubi Rumaisah "Wai ina kujerar da muka fita da ita ɗazu, miƙowa Auntynku takwararki ta zauna mana”

    Aunty na kalla da sai yanzu na fahimci ashe tsaye take Aunty Asiya take zaune a kujera tana baiwa Adil Mama

    Aunty Maryam ta yi murmushi kaɗan"Ai Gwagg da Sumayyah ki kace kawai ita ce ƴar wajen Rumaisah bata yi da takwararta ɗin"

    Gwaggo ta yi murmushi ita ma” Haka ne kuwa Maryama ina lura da ita gashi ma Rumaisah ma ita ce ta ɗebo Hauwa'u sosai ita wannan Sumayyah ai tafi kwaso dangin ubannata marasa kirki”

    Aunty Jamila ta kalle ni sannan ta ce” Sosai kuwa Gwaggo kina kallonta kin ga ƙanwar ubanta Asma'u Khalil ko Asma'u Halil take nema na manta kin san ƴar ajinmu ce”

    Ita dai Rumaisah kujerar ta janyowa Aunty inda take Aunty ta zauna sannan ta fara magana

    "Toh nidai Gwaggo duk bahaka ba ne kawai dai saboda Sumayyah ce babba shi yas sa”

    Aunty Maryam ta kalli Gwaggo"To kin ji dai Gwaggo ko, zancenmu na bayyana”

    Murmushi Aunty ta yi jin su Aunty Maryam tsokana suke ji gurin Gwaggo Aunty ta maida kanta” Kin ga shiru magani ɗaya ya yi wuya”

    Gwaggo ta mai da kanta kallan window"Wallahi kuwa ko ɓurɓushin Abdullahi kin ga ban hangaba ko aɗan bata Yoghurt ɗin can kafin ya dawo?"

    Aunty ta ɗaga kai "Eh haka ne da an bari sai zatasha maganin tun da ɗaya ne amma Rumaisah ɗauko abata rabi, Kar su Auntynku su ci gaba da yi min tsiyar komai nafi kiran Sumayyah"Ta ƙara sa maganar tana murmushi

    Su Aunty Maryam murmushi suka yi haɗin bakin cewa” Ai gaskiya muka gani ne”

    Aunty bata sake cewa komai ba sai murmushin da ta sake yi

    Rumaisah da bata ce komai ba cikin sanyinta ta fara tafiya aiwatar da saƙon Aunty inda Yoghurt ɗin yake ta ƙara sa ta ciro Rufaidah Yoghurt da shi ma yana cikin ledar da Uncle Sha'aban ya kawo, miƙa wa Gwaggo haɗe da cokalin jikin Yoghurt ɗin, Gwaggo ta maido mata da cokalin "Ungo ki ɗaurayeshi”

    Aunty Maryam ce ta kalli Rumaisa ɗin "Ɗauki wancen ruwan kisa a ciki kular can sai ki ɗaurayeshi”

    Yadda Aunty Maryam ta ce haka Rumaisah ta yi nidai da ido nake bin Rumaisah duk abin da take yi Rumaisah tana da natsuwa sosai komai nata cikin sanyi da taushi take yi dan halin Mama kaf Rumaisah tafi kowa cikinmu kwashewa ban da kamanninta da Mama ɗin kuma da take yi. . . . . . . . . . . 

    **** **** 

    Masu Neman Wannan Littafi na Iya Tuntuɓar:
    Marubuciya: Halimatussa'adiyya Ibrahim Khalil
    Lambar Waya: 08124915604
    Na Cancanta

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.