Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Cancanta (Kashi na 18)

Jin ƙarar tsaida motar ya sa ni dawowa daga duniya tunanin rayuwata da na faɗa Yaya Samir na ɗago na kallah ni ma ni yake kallo a daidai lokacin, kafin na maida kallona bakin titi dan duk tunanin da na faɗa na tabbatar rabin Kano ma ba muyi ba, a daji Yaya Samir ya tsaida motar, na sake kallonshi da yana yin tsoro, saboda rashin tsaron da ke ƙasar a ɓangaren Katsina abun ya fi tsanani, na fara magana ga Yaya Samir da tsoro ƙarara fuskata

"Yaya Samir na ga ka tsaya daga nan, ko babu mai ne?"

Kai ya girgiza min, "Ko ɗaya Sumayyah natsuwarki nake so ne, Dan Allah ki daina tunani ko baki faɗa min ba na san ki na yi ba zan iya ciro zuciyarki ba da nacirota na cire miki tunanin, dan Allah Sumayyah kiya haƙuri da abunda ya faru Samir na tare da ke ki yafema Abbah mu masa addu'a Allah ya sa ya gano gaskiya, abun nashi ba yamin daɗi ban da Ummi ma sai ya fi haka Sumayyah ina ji ne ina ma Abbah Abdullahi da Ummi Hauwa'u iyayena duk rayuwarku zan jureta hakama ina tayaku rayuwar, Sumayyah ina sanki ko ba dan halinki ba da Abbah Abdullahi, umminku ma kin cancanta a so ki aso zama dake a ƙarar da komai dan samun ki, ina ji dan ko baki dauko halin iyayenki duka ba kin dauki wani bare ma na san Sumayyah kin zarta su ma, dan Allah Sumayyah ki yarda dani, karki manta da rayuwata ki karɓi wani komai daɗewa Sumayyah, ni ne ke, ke ce ni”

Kallonshi na yi ina hawaye, tare da rasa me zance na yi ƙarfin hali na ce” Dan Allah Yaya Samir ka ja motar mu tafi haka ina tsoron wani abu ya samemu anan, ban san amsar da Zan ba ka ba ba abin da ke min daɗi, bare har na yi tunanin gano cancanta da kake gani kai da Halima kuna ta cemin NA CANCANTA, har yau banganeta ba, Dan Allah karku ƙarama zuciyata raɗaɗi ku barni haka, nafi yarda da maganar Abbah Hashim ne, ban da wata cancanta, inama rantsuwa da Allah mu talakawane abincin yau da gobe kullum muke nema, na yarda da Kai ne na biyoka nan na tsallake mutane mafi daraja a bayan iyayena amma ga makomata a nan haba Dan Allah me zance wai. . . . . "kuka kawai na fashe da shi to me Zan ce ne wai wata jin wani zafi nake daga zuciyata zuwa kirjina

Lallashina ya fara” Haba Sumayyah dan Allah ki bar kukan ka da kisa na yi na san komai Sumayya na san na yi laifi dan Allah kada kisa zuciyata ta ƙara ƙunci banajin daɗin abin da ya faru ina sanki Sumayyah, duk duniyar da Kika shiga zan tayaki shiga ne Sumayyah, ni ma fa Katsinan ba tamin daɗi bana jin zan sake komawa katsina Sumayya ni ma na barota saboda ban cika alƙawarin da na daukarma Abbah Abdullahi akanki ba”

Da kallon mamaki da goge hawaye nake kallonshi” Yaya Samir ni din fa na yafema, ni ma Mai laifi ce, amma karka tafi ka bar Ummi dan Allah ina zakaje Yaya Samir"

Murmushi na ga Yaya Samir ya yi kawai” Ai Sumayyah zamana ba shida anfani zanje ni ma na samu rayuwar da zan tsaya da ƙafafuna saina dawo na aureki dan Allah, banajin daɗi ni ma dama ina Shirin barin katsinan abokina ya kirani zan samu aikin da ya fi nanan, Allah Sumayya banaji zan iya zama a nan babu ke din, dan Allah ki bawa wancan haƙuri Sumayyah"

Daganan ya ja motar muka ci gaba da tafiya, shirun kurame ya ci gaba da ratsa tsakaninmu, na rasa gane duniyar tunanin da zan faɗa duniyar batamin daɗi abubuwan sun cunkushewa zuciyata, ƙarar taka burki ya sa na farka daga barcin da na yi a motar a lokacin na kallo agogon dake jikin motar 4:00pm dai dai ta window nake kallon mutanan da ke alwala suna shirye shiryen tafiya masallaci sai sannan na gano inda nake mun ƙaraso layin gidanmu muna gefen gidanmu daidai ƙofar gidan Alhaji Yassar Makama masallacin jikin gidansa ake ta shiga sainaga unguwar tana sauyawa a idona maganar Yaya Samir ta katseni

"Sumayyah mun ƙaraso fa muje na sauke miki kayan, ina sauri ne”

Kallonshi na yi ido cikin ido abin da banwai taɓa yi ba” Yaya Samir ba za ka shiga ka gaida su Umma ba”

Kai ya girgiza” Haba Sumayyah idan na shiga me kike tunanin zan ce musu, ba zan taɓa iya haɗa ido da Ummi Hauwa'u ba, bare Abbah Abdullahi”

Wani hawayen na ji yana ƙoƙarin fitomin na yi ƙoƙarin gogesu na buɗe murfin motar na fito da ciwan jikin dukan da Abbah Hashim yayi min sai yanzu jikina kemin tsami da na tashi, Yaya Samir kayana ya fiddomin ina gefe tsaye sai lokacin na lura da ƙaton jakarshi a gefen da ya ciro tawa, ya ja boot din ya rufe, aljihu ya sa ya fito da kuɗi ya mikomin na yi kamar ba Zan amsa ba ya haɗemin rai na amsa na yi godiya ya kalle ni

"Kiya haƙuri Sumayyah, kowa da yadda rayuwa ke zuwa masa, dama na yi niyyar maidoki gidan, amma naso da shirin na biyamiki kuɗin ko neco ce, tun da abokina ya kirani maganar aikin da na daɗe inasan samu a saboda ke da na haƙura da na Katsinan amma Abba ya kasa fahimta, ba zan iya haɗa ido dasu Ummi Hauwa'u ba, na san na tauyemiki kiya haƙuri yanzu banasan na yi biyu babu ne baki ba wannan babban aikin da nake saka rai na samu"

Daganan ban ɗago kaina ba saboda hawaye har na Fara jin ƙoƙarin tashin motar Yaya Samir na ɗago da sauri ta cikin glass na hango fuskarshi babu gitso hawaye ne fuskar Yaya Samir da ba zance yaga zubar su ba murmushi ne kawai ykemin da ya fi kuka ciwo ana wa hasashen ga ma zahiri na gani hawayen sun yi nasarar zubo masa, ƙurar motarshi kawai na gani ban yi aune ba gefen kayana na duƙa ba kuka nake ba, amma bana yana yi me kyau, Yaya Samir kam mutumin kirki ne sai yanzu ni ma nafi hangen dacewata da Yaya Samir din duk da AbdulHamid din amma banajin Zan iya barin Yaya Samir ɗin Kuma na yi minti a ƙallah biyu wajen na daure na tashi da jan jakata, Dan yanzu a fara tambayar lafiya mutane akwai tambaya mara anfani anawa tunanin saboda bana yana yi mekyau wani gabana ne ya yanke ya faɗi ƙofar gidanmu na gani da kwaɗo, haka nan na ji jikina na ba ni babu lafiya, na daɗe wajen tsaye

"Yaya Sumayyah"naji an anbata, hakan ya sa ni saurin waiwaya wa, Haris na gani a tsaye shi nake kallo shi ma haka, Haris abokin Ahmad ne kuma makwabtanmu ne na yi hanzarin ce wa

"Na'am Haris, inasu Mama sukaje ne na dawo na tarar gidan rufe?"

Haris ya dan dube ni ya kau dakai” wallahi Yaya Sumayyah ai su Mama sunfi sati da barin nan, Mai gidan ya koresu, ba su biyan haya, ya ce idan ba su tashi ba kafin gobe a lokacin, ya ce hukuma zai Kira musu, Ahmad dai ya ce min gida za su koma, sai lokacin ya ce min ke dama kin daɗe bakinan, wallahi su mamana ma ba su ji daɗi ba ki ƙaraso gidanmu mana ki huta, ya ce min kinje katsina”

Ban iya tsayawa cikakken amsawa Haris ba, na ce” A'a Haris na gode ni ma zan bisu ne”

Kai ya girgiza "Yaya Sumayyah yamma ta fara ki samu wani gidan ki kwana, tun da ba za ki shiga namu ba bari na Kira miki napep"

Kai na ɗaga kawai ya wuce to ni ina na nufa ke nan, Aunty Asma'u ba za ta karɓeni na kwana ɗaya ba ma zan iya zuwa ba, mama Atika ta faɗomin rai banjin zan iya, zuwa wajen ta inada tabbacin ta watsar da zumun ci saboda mama ke bin ta kullum cikin ƙorafin ayyukan gida ta keyi gidansu Halima ya faɗomin a rai na, da wannan tunanin na ji hawaye masu ɗumi sun sauka kan fuskata ƙarasowar su Haris a adaidaita sahun ya sani saurin gogewa na kalli Haris da ya fito da ga motar yana

"Yaya Sumayyah ga napep din ki faɗa masa ina za ki bari na shigarmiki da jakarki din"

Murmushi na yi kawai na matsawa Haris ya sa jakartawa ciki na shiga na ce wa mai napep "zoo road zani”

Haris ya sa hannu aljihu ya bawa mai napep kuɗi ina ce wa

"Haba Haris da ka barshi ni ma da kuɗi hannu na, wallahi”

Kai ya girgiza "Haba Yaya Sumayyah aike yayarmu ce ko ba Ahmad zan yi miki, dandai kin ƙi ne da kinzo gidanmu da safe sai ki wuce na san Umma na bata labari ba zataji daɗi, a gaishemin da Ahmad da su Mama har Abba ma?, ki ce wa Ahmad zanzo insha Allah"

Na yi murmushi na ce” Ah bawa Umma haƙuri za suji, insha Allah, Muna jiranka, Haris na gode”

Daganan napep ya ja Haris na ɗaga mana hannu Haris yaron kirki abokin Ahmad ne sosai ko da yaushe tare za ka gansu ina da tabbacin har kuka Haris zai yi na rashin Ahmad ko makaranta bencinsu daya da Ahmad kwana ke rabasu da Ahmad watarana ma tare suke kwana daƙin su Haris idan ana ruwa, ban da jarabawar rayuwa a lalacewar wannan gidan har a nemi cin mutuncinmu saboda kuɗi na haya daidai gwargwado Abba na ƙoƙarin biyansu, dalilin dawowarmu nan din da Abba kaɗai yake zaune shagon da wasu 'yan garinmu suka Kama haya a nan to zaman Mama a gwarzo babu daɗi a gidansu Abbah take zaune duk ƙorar da suka kwaso za su ce Mama ce ko duk barnar da aka yi a daƙin Hajiya mamarsu Abbah to mu ne, haka za mu ci duka ba damar magana, duka Khalil da Aisha mama ta haifa a nan din muma munfisan zama gida amma babu muhalli acan, amma ko ba komai gwaggo na ƙoƙarin mana abin da ya samu mahaifiyar Mama, Mama bisa ƙaddara take zaune da Abbah kaf 'yan uwanta ta fisu matsalar rayuwar gidan aure, gurin miji ne kawai bata samun matsala, da wannan tunanin muka ƙarasa zoo road da kwatance nama mai napep muka ƙarasa layin gidansu Halima ina ji Ina gani muka wuce ƙofar gidan Aunty Asma'u duk girman gidan a ce ka gaza jan naka a jiki dai dai da minti goma ba ka so ya yi a ciki wannan arziƙi bai rana ba na faɗa a Raina kofar gidan su Halima da na ga wani ɓangaren an fara buga siminti an cire langa langan muka tsaya na fito Mai napep fiddomin jaka ta ya yi gaba ba ni da zaɓin da kunyar da ke tare dani ganin ƙatuwar jaka hannuna ban san yana yin tunanin da iyayen Halima za suyi ba ganina da jakar ganin kowa yana ta kanshi komai ya canza masu kuɗin ma suna kukan tashin kayan masarufin ina ga mu talaka, duk da iyayan Halima ba su da matsala amma sainake jin nauyi da haka na ƙarasa tura kofar na shiga ciki da sallamata Faisal da Yaya Baffa da suke tsakar gidan suka amsamin, suna

"Mutanan Katsina, yanzu kuke tafe, hala tare kuke da Asma'u ko?, na ji Kabir ya ce ta je unguwa” Yaya Baffa ke faɗin haka

Yaya Hakim da Yaya Abdussalam, da suka fito daga dakinsu da alama fita za suyi suka kalle ni Yaya Abdussalam ya ce” wato kin ji ranki Halima na zazzabi ke nan shi ne daga saukarku kanki zarce gida Kika zo nan"

Murmushi na yi muka gaisa dasu Faisal ya anshi jakata ya Kai daƙi na bi bayanshi duk hankalina ya yi wajen Halima jin tana zazzabi amma jiya fa mun yi waya bata faɗa min ba

Faisal ya fito yana

"Kin ga bata ma daƙin bari na duba bayan gida ko ƙila ta shiga wanka ai taji sauƙi Mama batanan ta ce kada ta yi wankan sai ta yi zazzabi ya dawo ta cikamu da raki cikin dare”

Murmushi na yi na zauna saman kujera ina ci gaba da tunane tunane.

**** **** 

Masu Neman Wannan Littafi na Iya Tuntuɓar:
Marubuciya: Halimatussa'adiyya Ibrahim Khalil
Lambar Waya: 08124915604

Na Cancanta

Post a Comment

0 Comments