Ticker

6/recent/ticker-posts

Mijina Ya Sadu Dani Ina Cikin Iddah

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Miji ne ya saki matarsa saki ɗaya, amma sai ya ce ta zauna a gidansa ta yi iddah, to tana iddar kuma ya je mata kamar sau uku (ya Sadu da ita) sai daga baya ya ga ta yi jini uku saiya ce wai iddarta ta kare za ta iya tafiya gida. to ya ya wannan mu'amalar da ya yi da ita akwai aure ko ya lalace sai an sake sabon daurin aure?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Idan mutum ya saki matarsa, kuma wannan sakin ya kasance shi ne na farko ko na biyu to bata fita daga idda ba, idan ya so zai iya maido ta da furuci, misali ya ce na maidoki ko na ci gaba da rikonki. Koya maidata ta hanyar wani aiki da yake nufin mayarwa, kamar ya kusanceta da niyyar mayarwa to mayarwar ta yi.

Iddar macen datake haila shi ne: Al'ada uku (jini uku) idan ta samu tsarki daga wannan jini ukun ta yi wanka, to tagama iddarta.

Iddar macen da bata haila saboda yarinta kota daina hailar, wata uku ne za tayi.

Iddar mai ciki kuwa shi ne ta haife abin da ke cikinta, abin da ya gudana na jima'i bayan wannan aikin haramun ne.

Wajibine Wannan mijin ya tuba zuwaga Allah maɗaukakin sarki a kan afkawa jima'in dayayi tareda ke, bisa rashin kudurce komai na dawo dake ba, kuma ya zama wajibi Ku sake daura wani auren da Sharuɗɗansa na WALIYYI da SHEDU da SIGA da SADAƘI idan kowannenku ya na kwadayin hakan.

Ba ya halatta a gareshi ya sake kusantarki, harsai ansake daura muku aure sabo.

Saboda haka wannan kusantarki dayayi batareda ƙudurce yai maidake ta sigogin da malamai suka tattauna wanda suke nuna mutum yadawo da matarsa ba, haramunne yanzu agareshi ya sake yi miki duk wani abu daya halatta tsakanin miji da matarsa harsai an daura muku sabon Aure da sadaki da shaidu da waliyyi

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu. . .

MIJINA YA SADU DA NI INA CIKIN IDDA A GIDANSA

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu malam mijine ya saki matarsa sai ta zauna dan tayi iddah kafin tagama iddan kuma sai ya kwanta da ita kuma baice yamaida itaba, to malam ya matsayinta yake???

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikis Salaam Wa Rahmatullah wa Barakatuhu:-

Malamam Malikiyya Suka Ce ko Hannun ta ya Kama toh ya Maida ta Ma'ana yanzu tana a matsayin Matar sa. Bare kuma ya sadu da ita wato ya yi Jima'i da ita kin ga ai shikenan ta koma a matsayin Matar sa.

Amma dai Maganar Gaskiya sai an Binciki Niyyar sa tukuna?. Shin Yana Nufin Iskanci Ne ya sa ya sadu da ita, Ko kuma yana Nufin ya Maida ita a matsayin Matar sa?

Duk Abin da ya fadi, toh da shi za'a yi Amfani, Sabida Hadisin INNAMAL A'AMALU BINNIYYATI.

Sa'annan Ku ma Matan ai da naku, ai irin wannan duk Zumudin ki duk Sha'awar ki, yakamata ya yi ku yi shi Kai a waye, mene ne da naku? An San Cewa har gobe kina matsayin Matar sa ne, Kuma Shari'a ya yarda ki yi iddar ki a Cikin Gidan sa, toh Amma yakamata Idan kina idda a Cikin Gidan sa duk Lokacin da ya zo Miki da Cewa Zai Sadu da ke, Sai ki tambaye shi Malam a wani Matsayi kenan za ka Sadu Dani ko ka manta cewa ka Sake ni Ina Idda ne sai ki tsaya ki ji?

Ya Gaya Miki matsayin ki tukuna a yanzu kafin ki ba shi Kanki ya yi Jima'i da ke, Idan Ya ce Miki ya Dawo da ke ne yanzu kina a Matsayin Matar sa, kin ga Kin ji da Kunnen ki kina iya yin recording ki ajiye hujja domin kar ya gama ya ce ai shi bai Fadi hakan ba, idan Kun yi haka yanzu kin San matsayin Jima'in da zai Yi da ke.

Idan Kuma ya yi Shiru ya Ƙi ya ce Miki komai ya ƙi ya amsa ko ya yi niyyar cewa ya dawo da ke, ko Kuma ya ce shi kawai ki ba shi Kanki ba tare da ya Gaya Miki Cewar ya dawo da ke ko a'a ba, kawai ya ce ki ba shi kanki, toh sai Ki Ƙi ba shi kanki kar ki ta6ba yarda, Sai ki Ji ya ce ya dawo da ke, toh Yanzu kin dawo Matar sa sai ki ba shi Kanki ya yi abun da yake so, domin gudun abun da zai zo ya dawo, Saboda zai iya yin Jima'in da ke sannan ya dawo kuma ya ce ai Bai dawo da ke ba, ya ce Iskanci ya yi da ke, Kin ga an koma wani Ɓangaren kuma.

Saboda haka Shari'a ya Gama bayanin Komai, idan zakuyi Abu duk zumudin ki da kwaɗayin ki da Sha'awar ki yakamata kiyi tambaya, ki San matsayin ki tukuna kafin nan ki Mika Masa kanki ya yi abun da yake so, amma Kuna tare Jiya Bai ce ya ce dawo da ke ba, Dazun ma bai ce ya dawo da ke Kafin ya Sadu da ke ba, bai ce ya dawo da ke kawai ya zo yanzu ya ce ku yi Jima'i! ke Kuma ba ki tambaye shi a wani Matsayi ba kawai Kika ba shi Kanki, idan shi a Niyyar sa bai Yi Niyyar dawo da ke fah? Kuma ga shi ya yi Jima'i da ke ya za ki yi toh? akwai wadda hakan ya taɓa faruwa da ita sai da suka gama Jima'i ta ce toh yanzu Ina matsayin Matar ka ai shikenan Allah ya Kara haɗa kan mu! ya ce ina ai shi bawai ya dawo da ita ba ne, kin ga kenan Sha'awar ta da zumudin ta ya jawo mata wani abun.

Sabida Haka ki tambaye shi ya Gaya Miki duk abun da ya ce sai ayi Amfani da shi. Sannan ku kiyaye irin wannan ko Hannun ki ya taɓa kin dawo ballatana ace ya Sadu da ke. Toh amma me Niyyar sa? iskanci ya yi da ke ko me?

Allah Shine Masani.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance damu cikin wannan group domin Fadakarwa...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp. com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www. facebook. com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments