Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Mace Za Ta Iya Bayyana Karatu A Sallah

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Mene ne ingancin bayyana karatun sallah ga mu mata? Shin akwai banbancin tsakanin sallar mace da namiji?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

Malamai sun yi ijma’i a kan bayyana karatu a cikin dukkan raka’o’i biyu na sallar Asubah, da raka’o’i guda biyu na farkon sallar Maghriba, da raka’o’i guda biyu na farkon sallar Isha’i. Haka kuma da sirranta karatun a cikin dukkan raka’o’in sallar Azahar da La’asar da raka’ar karshe ta Maghrib da raka’o’i biyu na karshen Isha’i. (Aslus Sifah: 2/413)

Sannan kuma ya tabbata a cikin Hadisin Maalik Bn Al-Huwairith (Radiyal Laahu Anhu) cewa Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:

« ﻭَﺻَﻠُّﻮﺍ ﻛَﻤَﺎ ﺭَﺃَﻳْﺘُﻤُﻮﻧِﻰ ﺃُﺻَﻠِّﻰ »

Kuma ku yi sallah kamar yadda kuka ganni ina yin sallar. (Sahih Al-Bukhaariy: 631)

Wannan gamammiyar dokar ta haɗe maza da mata daga cikin musulmi, sai in an samu wurin da ya cire matan daga hakan.

Al-Imaam Al-Mujaddid Al-Albaaniy a ƙarshen littafinsa: Sifatu Salaatin Nabiy (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya bayyana cewa: Babu wani abin da ya zo a cikin Sunnah da yake hukunta cire mata a cikin siffar Sallar Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam). Har kuma ya kawo maganar da Ibn Abi-shaibah ya riwaito da ingantaccen isnadi daga Ibraahim An-Nakha’iy (Rahimahul Laah) ya ce:

ﺗَﻔْﻌَﻞُ ﺍﻟْﻤَﺮْﺃَﺓُ ﻓِﻲ ﺍﻟﺼَّﻠَﺎﺓُ ﻛَﻤَﺎ ﻳَﻔْﻌَﻞُ ﺍﻟﺮَّﺟُﻞُ

Mace a cikin sallah tana aikata irin abin da namiji yake aikatawa ne. (Aslus-Sifah: 3/1040)

Sannan kuma yana da kyau mu san cewa: Bayyana karatu ba yana nufin daga murya sai kowa da kowa a kusa da na nesa ya ji ba ne. Amma dai ɗagawa ne ta yadda mai sallah zai jiyar da kansa da wanda yake kusa da shi.

Kuma maganar cewa wai muryar mace al’aura ce ba daidai ba ce, domin dai maganar Allaah Ta’aala ta warware ta inda yake cewa:

يَا نِسَاءَ النَّبِيِّ لَسْتُنَّ كَأَحَدٍ مِنَ النِّسَاءِ ۚ إِنِ اتَّقَيْتُنَّ فَلَا تَخْضَعْنَ بِالْقَوْلِ فَيَطْمَعَ الَّذِي فِي قَلْبِهِ مَرَضٌ وَقُلْنَ قَوْلًا مَعْرُوفًا

Yã mãtan Annabĩ! Ba ku zama kamar kõwa ba daga mãtã, idan kun yi taƙawa, sabõda haka, kada ku sassautar da magana, har wanda ke da cũta a cikin zuciyarsa ya yi ɗammani, kuma ku faɗi magana ta alheri. (Surah Al-Ahzaab: 32)

Wace magana ce kuwa ta fi Alƙur’ani kyau da alheri?!

Allaah ya fahimtar da mu.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Asslafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu. . .

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp. com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www. facebook. com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments