Takardar da aka Gabatar a Taron Ranar Hausa na Ƙungiyar Raya Al’adun Hausawa, A Babban Ɗakin Taro, Sashen Nazarin Harshen Hausa, Kwalejin Ilimi Ta Isa Kaita, Dutsin-Ma,ta Jihar Katsina, A Ranar 22 Ga Watan Agusta, 2019
BUKIN SHAN KABEWA A ƘASAR HAUSA: MADUBI NE NA КYALLARO
RAYUWAR HAUSAWA TA GARGAJIYA
Daga
Abdulrahaman Ado PhDP
Sashen Harsunan
Nijeriya,
Jami'ar Umaru Musa
Yar'adua, Katsina-Nijeriya
e-mails: ado.abdulrahaman@umyu.edu.ng
ado_fashi63@yahoo.com
Phone Nos: (+234) 08066177053 (MTN)
08077610084 (GLO)
07089706117 (AIRTEL/ZAIN)
Tsakure
Kowace al’umma ta duniya tana gudanar da
bukukuwanta na wasu al’amuranta da kan samu na fari ciki. Hausawa ma, a
matsayinsu na al’umma ta ‘yan Afirka, ba a bar su a baya ba, a wajen gudanar da
bukukuwansu na gargajiya da na zamani, domin nuna farin cikin samuwar wani abu
na murna. Kasancewar al’umma cikin murna da farin ciki, abu ne wanda ke kawo
mata ci-gaba da bunƙasa
da kuma samun walwalar gudanar da dukkan rayuwarta a cikin farin ciki. A cikin
wannan takarda, an kawo bayanai a kan Bikin Shan Kabewa, wanda ake yin shi don
murnar zagayowar kakar samuwar abinci iri-iri. Wannan biki ne da ‘yan bori ke
shirya shi, amma ya kasance yana taɓa
ruhin kowa a cikin al’ummar Hausawa. Muhimmancinsa a al’ummar Hausawa yana da
yawa, amma ɗaya daga cikinsu shi ne
samuwar mizani na madubi mai ƙyallaro rayuwar Hausawa ta gargajiya gaba ɗayanta. A cikinsa ake ƙyallaro harshen Hausawa
wanda akan furta wasu kalmomi da lafuzzan da suka keɓantu da bikin. Haka kuma, bikin yana ƙyallaro al’adun Hausawa
da suka danganci addininsu na gargajiya da ire-iren abincinsu da suturarsu da magungunansu
da makamantansu. Kazalika, akwai ƙyallro adabin Hausawa da bikin ke yi, ta fuskar
ire-iren raye-rayensu da waƙe-waƙensu da kirarinsu da takensu da kayan kiɗansu da makamantansu da yawa. Bayan nan kuma, a cikin
takardar, an yi bayani na hanyoyi uku da aka bi don gudanar da wannan bincike,
wato karantawa daga rubutattun bayanai da hira da mutane ta hanyar tambayarsu
da kuma ganin da ido, na yadda ake yin bori. An gabatar da takardar bisa
manufar fito da muhimmancin bukukuwan Hausawa na gargajiya a ƙasar Hausa, musamman a
bikin shan-kabewa. An zaɓi a ɗora wannan bincike a bisa “Ra’in Ƙyallaro Al’adu”
(Cultural Reflection Theory), wanda wani Bature mai suna John Locke (1632-1704) ya assasa. Shi
ra’i ne mai zama a matsayin madubi, wanda ake yin amfani da shi domin hango
abubuwan da ke faruwa a cikin al’umma. Sakamakon binciken ya nuna cewa, Bikin
Shan Kabewa, bikin ne da ke kawo bunƙasar rayuwar ‘yan bori da ma dukkan Hausawa ta fanin
harshe da adabi da al’adu.
Muhimman Kalmomin
Bincike:
1.Biki
2. Shan Kabewa
3. Gargajiya
4.
Madubi
5.Ƙyallarowa
1.0 Gabatarawa
Biki wani taro ne da
ake yi na shagali da manufar nuna farin cikin samuwar wani abu da ake murnar
samuwarsa, a cikin al’umma (Jami'ar Bayero, 2006:46; Abraham, 1978:99; Ado, 2015:2).
Hausawa suna da nau’o’in bukukuwa daban-daban. Wasu bukukuwan na gargajiya ne,
wasu kuwa na zamani ne. Kazalika, wasu suna da dangantaka da addini, wasu kuwa
na nishaɗi ne kawai. Akwai kuma waɗanda ake gudanar da su a yau da kullum, saboda samuwar
abubuwan fari ciki, a kai-a kai. Amma kuma, wasu akan gudanar da su sau ɗaya a shekara, ya yin da abubuwan shekara-shekara na
farin ciki suka samu (Galadanci, 2011:81; Funtua, 2010:63; Alhassan, 1988:74).
Shi kuwa Bikin Shan
Kabewa, biki ne da ake gudanarwa sau ɗaya a
shekara. Biki ne na gargajiya wanda ‘Yan bori, ma’abota addinin gargajiya, wanda
ke yi wa iskoki bauta da sauran hidimomi, ke yin sa (Galadanci, 2011:81). ‘Yan
bori su ne suke yin bori. Bori kuwa tsohuwa al’ada ce ta nau’in addinin
gargajiya wadda ake bin wata hanya da ake bautar iskoki ko aljanu da
lallashinsu domin a sami biyan wata buƙata (Sallau, 2013:25; Abubakar, 2012:6). ‘Yan bori, a
kodayaushe, suna bin tadar bori, ta yadda za su bi dokokin da aka shimfiɗa masu, na yi wa iskoki hidima (Bunza, 2006:83). ‘Yan
borin da ke gudanar da Bikin Shan Kabewa rukuni ne na Hausawan da ba su cikin
waɗanda ke bautar Kan-Gida da Dodanni (Ado, 2005:6).
Shi kuwa addini, wata
hanya ce ta bautar mahalicci ko wani abu da ake jin tsoronsa domin gudun kada
ya lahanta mutum, ko kuma domin a samu biyan wasu buƙatu daga wajensa. Ita aƙida ce ta kowane ɗan’Adam da ke sosa zuciya. kuma shi ne ke sarrafa al’ummar
da ɗan’Adam ke zaune a cikinta (Yakasai,
2012:141).
Shi kuwa addinin
gargajiya, shi ne tsohon addinin da Hausawa ke riƙe da shi, tun kaka da kakanni, wanda ba saukakke ne
daga Allah ba. Irinsa ne kamar su bori da tsafi, wanda al’umma ke samun wani
abin da suke tsoro, yake biya masu buƙatu, su yi ta bautarsa, kamar dodo ko aljani da
makamanyansu (Sule, 1974:26; Abubakar, 2012:8).
Ƙasar Hausa ita ce wadda take cikin Afirka ta Yamma, a
cikin farfajiyar da ke a tsakanin hamadar Sahara. Idan aka duba daga kudu, ta
iyaka da dazuzzukan da suka nusa suka nufi gaɓar
tekun Atlantika. Ita ce wadda wasu masana ke kira da sunan ƙasar Sudan ta Yamma, wadda daga yamma take
a tsakanin Tafkin Cadi da guiwar Kogin Kwara. A yau, ƙasar Hausa tana cikin farfajiyar Arewa a
cikin Nijeriya. Mutanen da ke zaune a cikin wannan farfajiya, akasarinsu
Hausawa ne da Fulani (Alhassan, 1988:3; Gusau, 2010:1).
Hausawa mutane ne masu
tsananin riƙon
al’adunsu na gargajiya. Tun a jiya, har zuwa yau, suna riƙe da al’adunsu da ya danganci addininsu na
gargajiya, ba ma kamar irr-iren abubuwan da suka danganci camfi da bokanci da
tsibbu, wanda akan yi ɗa’a ga iskoki da yi masu abubuwan da suke
buƙata. Tun daga zamanin
dauri har zuwa yau, akan gudanar da wasu bukukuwan da suka danganci bauta ga
iskoki, irin su Bikin Shan Kabewa da Bori da sauran wasu tadodin da suka
danganci wannan bauta (Alhassan, 1988:6).
Manufar gabatar da wannan
takarda shi ne a yi bita da yin waiwaye akan al’adun Hausawa na gargajiya domin
a sake bijiro da muhimmancinsu a idon duniya. An kawo nazari a kan Bikin Shan
Kabewa a matsayin samfuri wanda daga gare shi ake iya hango waɗannan muhimman lamurra da suka shafi rayuwar Hausawa.
2.0 Hanyoyin Gudanar da Bincike.
Wannan bincike
ne irin na tarihi. Irin wannan bincike shi ne wanda mai bincike ke bin diddigin
wasu abubuwan da aka yi, waɗanda suka wuce, amma ana
nazarinsu, ta hanyar bayyanan yadda suke a zamanin dauri, sannan a yi amfani da
bayanan da aka samu a kansu domin gyara abubuwan da ke faruwa a yau (Ado,
2018:39; Akuezuilo, 1993:7). Kazalika, irin wannan bincike na son a ziyarci
wuraren tarihi n inda abubuwan dauri suka gudana domin gani da ido na hotuna ko
wasu gine-gine da makamantansu (Bello, 2010:5).
Bikin Shan Kabewa, biki ne na zamanin dauri, wanda ake
samun ɓurɓushin yadda yake a yau, a
cikin al’adun bori da kuma gudanar da wasu abubuwan bautar al’ajanu na
maguzanci da Hausawa kan aikata a yau. Don tabbatar da an binciko yadda bikin
yake, da yadda ake gudanar da shi, da kuma tasirinsa ga al’ummar Hausawa, an bi
waɗannan hanyoyi guda uku na bincike, kamar haka:
Da farko, an yi amfani da rubutattun bayanai a kan
yadda wannan biki yake da yadda ake gudanar da shi a ƙasar Hausa. Rubutattun bayanan sun haɗa da bugaggun litattafai da kundayen bincike da
takardun da aka gabatar a tarukan ƙara
wa juna sani da kuma mujallu da aka buga ƙasidu a cikinsu.
Hanya ta biyu, ita ce wadda mai bincike ya gani da
ido, tare da ganawa da wasu waɗanda suke da dangantaka da
wannan biki, irin su ‘yan bori da bokaye. Waɗannan
rukunin mutane ne da ke da alhakin gudanar da bukukuwan da suke da ɓurɓushin wannan biki da ake
bincike a kai.
Daga ƙarshe,
hanya ta uku da aka bi ita ce ta tsara wasu tambayoyi na bincike a cikin
takarda, wadda aka ba wasu mutane, malamai da ɗalibai,
waɗanda suke da ilimi a kan wannan biki. Amsohin da suka
bayar ne aka yi amfani da su a wannan bincike.
3.0
Ra’in Bincike
An zaɓi a ɗora
wannan bincike bisa “Ra’in Madubin Ƙyallaro
Al’adu” (Cultural Reflection Theory). Wannan ra’i ne wanda ake iya yin amfani
da harshe ko al’’ada ko adabi a matsayin wani madubin da za a iya hango
ire-iren abubuwan da ke faruwa a cikin al’umma (Ado, 2017:84; Ado, 2018:7). Bincike
ya tabbatar da cewa, wannan ra’i ne da ya samo asali daga Makarantar Zahiranci
ta Biritaniya (British School of Cultural Reflection) (Gusau, 2015:5; Ado,
2018:7). Wani masani mai suna John Locke (1632-1704) ne ya assasa shi, a bisa aƙidar cewa dukkan ilimin da mutum yake da shi, wani
madubi ne shi mai hango rayuwar duniya ta haƙiƙa
(Rogers, 2017:1-10). Daga baya, wasu Turawan, masana rayuwar al’umma, irin su
Hegel da Lenin, suka ƙara
bunƙasa ra’in. Kazalika, a shekara 2007, wasu masana irin
su Jaeroen Jansz da Rynel G. Martins suka ɗora
ra’in a kan nazarce-nazarcen da suka danganci kafofin yaɗa labarai da kuma addini.
A yau, ana
amfani da wannan ra’i a kan nazarce-nazarcen da suka danganci harsuna da adabi
da al’adu da duk wasu nazarce nazarcen da ya danganci baibayi da kimiyyara
zamanatakewar al’úmmomin duniya (Ado, 2018:8).
A nazarce-nazarcen da wasu masana al’adun Hausawa suka
gudanar, an sami wasu waɗanda suka yi amfani da wannan
ra’i, irin su El-Azzazi (2015) da Ado (2018) da Mukhtar (2013). Sun yi amfani
da shi ta hanyar yin amfani da al’ada domin ƙyallaro rayuwar Hausawa, a ƙasar waje da hango rayuwar Hausawa a cikin bukukuwansa
da mkamantansu.
A wannan bincike, an yi amafani da ra’in domin bincike
ne wanda ya danganci ƙyallaro
rayuwar al’ummar Hausawa a cikin Bikin Shan Kabewa. Abin nufi, an yi amfani da
bikin a matsayin wani hoto ko fitila mai hasko rayuwar Hausawa ta gargajiya.
4.0
Bikin Shan Kabewa A Taƙaice
Shi wannan biki,na shekara-shekara, wanda akan gudanar
da shi a farkon ɓullowar kaka na kowace shekara. Sarkin Bori da
Sarauniyar Bori, waɗanda aka naɗa su saboda sun fi kowa kayan
bori, su ne ke zaunawa su shawarta gudanar da bikin. Sukan faɗa wa Sarkin Gari domin a nemi izinin masu ƙasa. Bayan an sami izini, sai a gayyaci sauran
sarakunan bori na karkarar da aka shirya gudanar da bikin, domin a tsara shiri.
Idan shiri ya kammala, sai a aika da goron gayyata ga duk sarakunan bori na ƙasar baki ɗaya. Wannan ce za ta ba su
damar su gayyaci sauran jama’a.
Kafin ranar biki ta zo, Sarkin Bori da Sarauniyar Bori
sukan gudanar da tanade-tanaden kayan biki da suka haɗa
da masaukin baƙi da abincin baƙi da babbar kabewar da za a girka a ranar biki da
itacen girki da kuma babbatar tukunyar da za a yi girki a cikinta. Haka kuma za
a tanadi kayan haɗin da za a haɗa da kabewar biki a dafa, irin
su yakuwa da yalo da gauta da albasa da kanwa da ‘ya’yan kanya da ‘ya’yan
goriba da gwandar daji da makamantansu.
Idan ranar bikin ta rage da kwana uku zuwa biyu, baƙi za su fara turarowa daga ƙauyuka da birane. Baƙi maza kan tafi wajen Sarkin Bori a ba shi masauki.
Sukuwa mata, sukan tafi wajen Sarauniyar Bori.
Da marecen jajibirin biki ake fara wasa. Masu kiɗan garaya sukan goce da kiɗa.
Akan kaɗa taken bori iri-iri, kama daga sarkin rafi, ko sarkin
baka, ko Malam-Alhaji,magiro, ko na-kada, ko ‘yar fillo, ko kuturu, ko gajere
(kyambo), ko gajimare, ko kure da makamantansu da yawa. ‘Yan bori za su yi ta
shiga fage suna taka rawar irin iskar da aka kaɗa
masu. An dinga yi, har sai gari ya waye, a dai dai lokacin da “hantsi ya dubu
ludayi,” kusan lokacin “ban ruwan dawaki,” wanda lokaci ne wanda rana ta fara ɗagawa. Akan ba kowa abincin kari, ya karya kumallo, a
huta.
A dai dai wannan lokaci, Sarauniyar Bori da muƙarrabanta kan fito su hasa wutar girki a cikin wani
babban murhu. Akan ɗora tukunyar girki bisan murhun, a sanya mata ruwa,
bayan rushi ya yi ringis! Sarauniya kan sheda wa sarki cewa tukunya ta tafasa.
Sarkin Bori kan kai ƙatuwar kabewar da ya tanan da ƙarƙashin
wata itaciya da ke a tsakiyar filin wasa na ƙofar fada ko kuma a gefen wani dogon turmi da ake
tanada. Sarki zai hau itaciyar ko turmin domin a fara harkar bori. Yana hawa,
sai makaɗan garaya su goce da kiɗan
“Sarkin Rafi.” Wannan kiɗa ke tsima sarki. Daga nan,
sai ya yi tsalle ya faɗo kan kabewar da mazaunansa.
Kabewar kan fashe, ta yi rugu-rugu. Sarauniya da maƙarrabanta za su goce da guɗa,
sannan su kwashe rududdugaggar kabewar, su rubɗa
ta cikin tukunyar girki. Bayan wani lokaci, sai a kawo kayan haɗi na kayan marmarin da aka tanada, a haɗa a cikin tukunyar, a yi ta hasa wuta. Yayin da kayan
cikin tukunya ke ci gaba da dahuwa, su kuma sauran ‘yan bori za a ci gaba da kaɗa masu takensu, har gari ya waye.
A washe garin “Fashin Kabewa,” akan tsayar da kiɗa. Sai kuma mata su shiga tasu hidimar. Za su kawo
akusa, sanan a sanya wata babbar ƙoshiya,
a rinƙa ɗebo girkin nan, na kabewa, ana
zubawa, ana ba manyan baƙi,
irin su sarakuna da tsofaffi da mata. Bayan an gama, sai Sarkin Bori ya bayar
da izinin yin rububi. Yakan ce: “A yi rububi!” Sai kowanne ɗan bori ya runtumo, ya afko wa tukunyar girki domin ya
samu ya sha “Faten Bori.” Wannan hark ace ta jaruntaka. Duk ɗan borin da ya sha faten borin nan, zai sami waraka
daga cututtukan da masifun da ka iya tasowa a wannan shekara. Kazalika, shan
kabewar yana zama a matsayin buɗa baki na samun izinin cin
kayan gona na wannan shekar. Su kuma ‘yan kallo, waɗanda
ba ‘yan bori ba, akan ba su nono, su tha a matsayin tsari (magani).
Bayan an gama shan kabewa, Sarkin Bori kan yi jawabin
ban kwana ga jama’a. Zai ayyana dokoki da sauran camfe-camfen da ‘yan bori za
su kula da su, domin kiyayewa ga iskokin da suke bauta. Bayan ya gama, za a ci
gaba da wasa, ana kuma girka sababbin shiga addinin. A hankali, kowa zai tafi
garinsu, sai kuma wata shekarar (Galadanci, 2011:81; Ado, 2005:6; Ado, 2015:7;
Abdullahi; 2018:3)
5.0
Abubuwan da Bikin Shan Kabewa Ke Ƙyallarowa
Bikin shan kabewa, a matsayinsa na biki, ya kasace
yana yin nuni da wasu abubuwan na rayuwa da kan faru a cikin al’ummar Hausawa
(Ado, 2015). Kamar yadda aka yi bayani a baya, bikin na ƙyallaro rayuwar Hausawa, kamar haka:
5.1
Ƙyallarowar Harshen Magana na Hausawa
Harshe na daya
daga cikin abubuwan da bikin shan kabewa ke ƙyallarowa da adanawa (Yakasai, 2014:14). Bincike ya
tabbatar da cewa, harshe na a matsayin ɗaya
daga cikin abubuwa masu muhimmanci da ake amfani da shi domin kare salwantar
al’ada (Yakasai, 2012:37). Don haka, a wannan biki, akwai sunayen wasu abubuwa
waɗanda akan ambata a matsayin sarrafa harshe. Misalan
irin su, sun haɗa da kalmomin da ake amfani da su masu alaƙa da wannan biki, kamar su “bori” da “girka” da “shigar
iska” ko “gamo” ko “doki” da “fitar iska” da “faɗuwar
bori” da “zanen sarkin bori” da “rawar wanzamai” da “rawar guragu da “dokin
nakada” makamantansu (Bilkisu, 2019; Bunza, 2005:5; Madauci,1982:79).
Haka kuma, akwai sunayen iskokin da ake yi wa kirari,
a lokacin gudanar da wannan biki, waɗanda suka haɗa da: “Mutanen Ɗoye” “Farfaru” da “Babbaƙu” da “Magiro” da “Uwar-gona” da “Mai-nakada” da “Kure”
da “Doguwa”da “Malam-Alhaji” da “Bature” da “Kuturu” da “Barahaza” da “Sarkin-Baka”
da “Sarkin-Rafi” da da “Babule” damakamantansu ( Sallau, 2013:26; Bilkisu, 2019;
Zurmi, 2014:40; Jinju, 2001:34).
Haka kuma,
akwai sunaye wuraren zaman al’janu, irin su manyan biranansu, kamar “Ƙwanƙwanbilo”
da “Jangarai” da “Dutsen Dala.” Akwai kuma, sunayen itatuwa da ake ambato na
mazaunan al’janu, irin su “Kuka” da “Tsamiya” da “Tumfafiya” da “Gamji” da
makamantansu (Bilkisu, 2019; Bunza, 2004:5; Sule, 1974:25; Ado, 2005:6).
Baya ga nan, akwai kalmomi da lafuzzan da suka
danganci abubuwan da ake gudanarwa a wajen bikin, irin su: “Sarkin Bori”” da
“Sarauniyar Bori” da “ ‘Yan Bori” da “Rububin Shan Kabewa” da “Girkar Sabon-Shiga”
da “Kabewar Bikin Shan Kabewa” da “Kayan Haɗin
Kabewar Bikin Shan Kabewa da makamantansu (Ado, 2005:8)
5.2
Ƙyallarowar Adabin Hausawa.
A kodayaushe, al’amarin da ya danganci shagalin biki,
to, dole ne a sami sha’nin raye-raye da kiɗe-kiɗe da waƙe-waƙe da kirare-kirare da makamantansu (Alhassan, 1988:74;
Umar, 1987:15). To, shi ma a Bikin Shan Kabewa, akwai al’amurran da ake
gudanarwa da ya shafi adabin Hausawa, kamar haka:
5.2.1 Kayan Kiɗan Bikin Shan Kabewa
Bincike ya tabbatar da
cewa, a wajen Bikin Shan Kabewa, makaɗan
bori sukan goce da yin kiɗan bori, ana hawa bori iri-iri domin nishaɗantarwa da gudanar da harkar bauta a wannan biki.
Akasarin kayan kiɗan da ake ake amfani da su, a wajen harkar
da ta danganci bori, sun haɗa da
garaya da gurmi da ƙwarya
da goge da molo da kalangu (Galadanci, 2011:81; Ado, 2005:7; Bunza,2005:7;
Madauch,1982:78). Akan kaɗa waɗannan
kayan kiɗa domin a kirawo aljanu, su taho, domin a
hau borinsu, don girka su a kan wani da ake son a girka (Bilkisu, 2019:17).
5.2.2 Waƙoƙi da Kirare-Kiraren
Bikin Shan Kabewa
Masana da manazarta
al’adun Hausawa sun tabbatar da cewa, duk abin da ya danganci bauta ta
gargajiya, akan yi wa abubuwan bautar waƙa ko kirari (Isah, 1988:9). To, a wajen gudanar da
Bikin Shan Kabewa, masu gudanar da bikin kan yi wa abubuwan bautarsu waƙe-waƙe da kirare-kirare, kamar haka:
Da
farko, masu bautar “kure”, sukan yi masa kirari da cewa:
Kuren bakin rafi,
Ka sha jini, ka ci
kurwa,
Mai tauna
garazum-garazum,,
Durungu daguyau,
Mai haɗiya da sauran kwana,
Gazau borin arna.
(Ado, 2014:44; Zurmi, 2014;39)
Ire-iren waɗannan
kirare-kirare da waƙoƙi ne akan yi wa abubuwan da ake bauta, a
lokacin da ake gudanar da wasannin Bikin Shan Kabewa. Wasu daga cikinsu sun haɗa da uwar gona da duna da gajimare da ɗan Galadima da gajere da makamantansu da yawa (Isah,
1988:9; Sallau, 2013:24; Kano, 2002:7).
5.2.3 Ƙyallaro Halayyar Wasan Kwaikwayo
Wasan Kwaikwayo wani wasa ne wanda ake
gudanar da shi a cikin al’ummar Hausawa wanda akan yi ta hanya kwaikwayar wasu
halaye na mutane, wanda ake shirya shi ta hanyar “sake-kama,” a yi shiga irin
ta mutanen da ake kwaikwayar (Ahmed, 2007:4-5, Ado, 2019:3). A wajen gudanar da
Bikin Shan Kabewa, akwai halayyar da ake nunawa, irin ta wasan kwaikwayo.
Bincike ya tabbatar da cewa, a lokacin da ’yan bori suka hau
bori, na wasu aljanu da ake yi wa hidima, sukan kwaikwayi halayyar wannan
al’ajani, ta siffar yadda mutane ke aiwatar da wannan halayya (Yakasai,2014:14;
Bilkisu, 2019:11). Alal misali, duk ɗan borin da ya hau “Kuturu,” za a same
shi yana kwaikwayar halayyar kuturu. Haka ma, wanda ya hau ‘yar Fillo, to, zai
nuna halayyar ta Bafillatana, ta hanyar kwaikwayar halayyarta. Idan Bature ko
Balarabe da makamantansu, aka hau, to, halayyrsu za a nuna (Bunza, 2006:6).
Wannan duk al’amari ne da ya danganci wasan kwaikwayo.
5.3 Ƙyallarowar Al’adun Hausawa
Masana da manazarta sun
tabbatar da cewa, bikin da ake gudanarwa a cikin al’umma, yana taimakawa a
wajen fito da hoto na zahirin ire-iren abubuwa na rayuwar wannan al’umma da ke
gudanar da shi (Funtua, 2010:63). Don haka shi ma Bikin Shan Kabewa ba a bar
shi a baya ba, a wajen fito da hoton al’adun da Hausawa ke gudanarwa a cikin
al’ummarsu, kamar haka:
5.3.1 Ƙyallaro Ala’adar Tufafin Hausawa
Tufafi jam’i ne na
tufa. Ita kuwa tufa abu ne da ake sanyawa a jiki domin a rufe tsirarci, irin su
riga da wando da makamantansu (Jami’ar Bayero, 2006:440). Hausawa suna da
tufafi iri-iri na gargajiya, kamar su walki da shabka da rawani da ‘yar shara
da alkyabba da zane da hula da ɗan
kwali da rawani da makamantansu da yawa (Funtua, 2010:23). To, shi Bikin Shan
Kabewa, abu ne wanda akan ƙyallaro
tufafin Hausawa na gargajiya da na zamani. Alal misali, a wajen gudanar da bori
na ire-iren aljanun da ake hawa, dole akan sanya suturar da ta dace da wannann
aljani. Misali, akan sa baƙin saƙi da baƙar hula da baƙin wando, idan aka hau aljanin Sarkin Rafi. Idan
Bature aka hau, sai an sanya kwat da nakatayil da hula malfa. Idan kuwa Malam
Alhaji aka hau, akan sanya babbar riga da hula da rawani da carbi. Idan ‘Ya
Fillo aka hau, sai an sanya kayan Fulani da makamantansu (Madauci, 1982:81).
5.3.2 Ƙyallaro Al’adar Abincin Hausawa
Abinci shi ne duk wani
abu na cimaka da ake ci domin a yi maganin yunwa (Jami’ar Bayero, 2006:1)
Hausawa suna da abinci iri-iri, kama daga na gargajiya har ya zuwa na zamani
(Abubakar, 2012:103).Wasu daga cikin abincin gargajiya na Hausawa sun haɗa da tuwo da dambu da ɗanwake
da fate da waina da makamantansu. Akan yi su ta hanyar haɗa abubuwan ci, irin su albasa da tumatur da tattasai
gyaɗa da kabewa wasu ganyaye, irin su alayyahu
da kuka da makamantansu (Funtua, 2010:44). To, shi ma a wajen bikin Shan
Kabewa, ana ƙyallaro
abincin Hausawa na gargajiya, a lokacin da ake yin haɗin yin “faten kabewar biki.” Baya ga kabewa, akan haɗa da albasa da yalo da gauta da gwandar dawa da
‘ya’yan goriba da ganyaye irin su yakuwa da alayyahu da makamantansu (
Galadanci, 2011:81; Ado, 2005:7; Ado, 2015:7)
5.3.3 Ƙyallaro Al’adar Zumunci
Zumunci shi ne kyakyawar
dangantaka ta kusanci ko dangantaka jini ko auratayya ko abota (Jami’ar Bayero,
2006:496). Hausawa suna da al’adar nuna zumunci da mu’amala ga junansu, kamar
su iyaye da dangi da abokai, ba ma kamar abin da ya danganci ziyarar juna a
lokacin samuwar wasu abubuwa irin su haihuwa ko aure ko lokacin sallah da
makamantansu (Alhassan, 1988:7). Wannan halayya ta zumunci ana ƙyallaro ta a lokacin Bikin Shan Kabewa.
Alal misali, idan aka shirya gudanar da bikin, akan gayyaci duk wani ɗan bori na birane da ƙauyuka da maroƙa da mawaƙa da makaɗan
garaya da goge da gurmi da makamantansu. Kusan duk wanda ya amshi goron
gayyata, yakan halarci bikin (Ado, 2015:6; Ado, 2005:6).
5.3.4 Ƙyallaron Al’adar Karamta Baƙo
Bincike ya tabbatar da
cewa, Hausawa mutane ne masu taimakon juna. Don kusan a wajensa ne ake ganin
halayya ta kirki da ta girma da girmamawa ga mutanen gida da kuma baƙi da sauran jama’a (Amfani, 2012:6). To,
shi ma Bikin Shan Kabewa, ya kasance kamar wani dandali na ƙyallaro ire-iren halayen Hausawa na nuna
halin girma da kirki ga baƙi.
Bincike ya tabbatar da cewa, tun kafin ranar da aka sanya ta gudanar Bikin Shan
Kabewa, waɗanda suka shirya bikin kan tanadi masaukai,
waɗanda suke saukar da sarakunan bori na ƙauyuka da ’yan
bori da sauran baƙi. Baya ga wuraren kwana, sukan ba su
abinci da abin sha, safe da rana da dare, tun daga lokacin da suka zo, har
lokacin da za su tafi (Ado, 2005:6). Wannan halayya ce ta kirkin Bahaushe ake ƙyallarowa a
Bikin Shan Kabewa.
5.3.5 Ƙyallaro Al’adar Bayar da Magungunan Gargajiya
Masana
da manazarta sun bayyana ma’anar magani a matsayin duk wata dabara ko hanya da
ake bi domin kawar da cuta ko rashin lafiya daga jikin ɗan Adam ( Bunza, 2003:68; Ibrahim, 2012:51;Ado,
2017:39). A bisa al’adar Hausawa, kowane mutum yana tsoron cuta, don ita ce ke
raunata lafiyar mai lafiya (Bunza, 2003:64). A bisa al’adar Hausawa, sun yarda
da cewa duk wata cuta tana da magani. A don haka, a duk inda Bahaushe ya ji
zancen magani na wata cutar da ta same shi, ko domin kariyar kada ta same shi,
yakan garzaya ya amsa, ya yi amfani da shi. To, Bikin Shan Kabewa yana
taimakawa wajen ƙyallaro
rayuwar Hausawa ta fannin bayar da magungunan gargajiya, domin maganin
cututtukan da ke cikin al’umma. Bincike ya tabbatar da cewa, ‘yan bori sun
yarda cewa iskoki ne ke kawo cuta, wanda ta hanayar bori ne ake warkar da cutar
(Danmaigoro, 2010:99). Don haka ne, a wajen bikin, kowa ke ƙoƙarin shan kabewar da aka girka, domin maganin
cututtukan shekara. Saboda muhimmancin kariya da kabewar ke bayarwa, kowa kan
shiga rububin shan ta. Wanda ba ɗan
bori ba, akan ba su nono, don maganin cututtukan (Ado, 2005:10).
5.3.6 Ƙyallaro Tsarin Sarautar Hausawa
A bisa tsarin rayuwar
Hausawa, akwai tsari da suke da shi na shugabanci. Tsari ne na hawa-hawa, wanda
sarki shi ne a can ƙololuwar
zance (Alhassan, 1988:66). Sarki shi ne shugaban da yake yi wa al’ummarsa
jagorancinci a duk wata halayyar zamantakewarsu ta yau da kullum (Sallau,
2010:7). To, shi ma a sha’anin Bikin Shan Kabewa, akan yi ƙoƙarin ƙyallaro
wannan al’ada, domin ana gudanar da bikin bisa tsari na shugabanci. Akwai
Sarkin Bori da Sarauniyar Bori, waɗanda
ke kasancewa a matsayin manya masu shirya wannan biki. Duk wasu hidimomin bikin
su ne ke jagorantarsa, kamar yadda sarkin gari ke jagorantar ragamar sha’anin
jama’arsa (Jinju, 2001:35; Ado, 2015:6; Ado, 2005:7).
5.3.7 Ƙyallaro Ayyukan Mata a Zamantakewar Hausawa
A zahirin zamantakewar
Hausawa, kowanne mutum yana da rawar da yake takawa, kuma kowa yana da aikin da
yake aikatawa domin ci gaban al’ummar. An fi sanin maza da yin ayyuka na
jarunta da kokowar neman abincin da za a ci a cikin gida. Ita kuma mace, takan
gyara abin da mazaje suka kawo, ta sarrafa su domin su zama abinci da kuma
rarraba shi ga mutanen cikin gida domin su ci (Rimmer, 2002:40-41) Wannan
halayya ta rabe-raben ayyuka, a cikin al’ummar Hausawa, abu ne wanda ake ƙyallaro da shi, a yayin da ake gudanar da
Bikin Shan Kabewa. Maza su ne ke da alhakin samar da kabewar da ake yin biki da
ita. Su kuwa mata, su ne ke dafa kabewar, tare da rarraba fatenta ga mutane
(Galadanci, 2011:81; Ado, 2005:9).
5.3.8 Ƙyallaro Jaruntakar Hausawa
Jaruntaka na nufin nuna
halayyar ƙwazo
da bajinta (Nata’ala, 2010:195). Bincike ya tabbatar da cewa, Hausawa mutane ne
jarumai, waɗanda kuma suke ƙaunar jarumi mai nuna halayyara ƙwazo da juriya (Amfani, 2012:6, Alhassan,
1988:28). Bikin Shan Kabewa na ƙyallaro
wannan halayya ta jaruntakar Hausawa. Ana iya ganin haka a lokacin da tawagar
Sarauniyar Bori suka gama dahuwar kabewar biki, takan sanya wata babbar ƙoshiya ta zuba wa manyan baƙi, irin su sarakuna, da tsofaffi da mata,
faten kabewar bikin. Bayan nan, Sarkin Bori yakan bayar da izinin yin rububi.
Wannan al’amari ne da ya danganci nuna jaruntaka. Kowa zai yi ƙoƙarin sai ya kai ga babbar tukunyar da aka dafa kabewar
domin ya ɗebo faten ya sha, don ya samu buɗe bakin cin amfanin gonar shekara da kuma maganin
cututtukan shekara (Ado, 2005:9; Galadanci, 2011:81; Danmaigoro, 2010:98)
6.0 Sakamakon Bincike
A bisa binciken da aka
gabatar, an gano cewa, bukukuwan Hausawa na gargajiya, irin su Bikin Shan
Kabewa na ‘yan bori, suna da wani alfanu na ɓoye,
baya ga na sarari, da ake gudar da su a kai. Alfanu na sarari da ya sa ake
gudanar da Bikin Shan Kabewa shi ne, domin a tabbatar da bauta da ake yi wa
iskokai, waɗanda a bisa dokokinsu na camfe-camfe ake
rayuwa. Dokokin kuwa sun haɗa da
cewa, ana yin sa domin a sami “buɗe baki”
na “azumin” ƙin
cin abincin sabuwar shekara, sai an yi bikin, an sha kabewar biki. Haka kuma,
ana gudanar da shi, domin a sha kabewar biki, domin kariya daga cututtukan
sabuwar shekara da neman warkar daga cututtukan da ake da su da ma waɗanda za su zo nan gaba.
A ɗaya ɓangaren
kuma, alfanu na ɓoye da ake samu daga gudanar da bikin shi
ne na yadda yake hasko wa jama’a duk ilahirin rayuwar Hausawa a cikinsa. Kamar
yadda aka gani a cikin bayanan da suka gabata, yana hasko rayuwar Hausawa da
fannin abinci da sutura da shugabanci da zumunci da halayyar kirki da
magungunan gargajiya da jaruntaka da makamantansu da yawa.
7.0 Shawarwari
A bisa yadda aka
gudanar da wannan bincike, kuma a bisa sakamakon da aka samu, ake bayar da waɗannan shawarwari.
Da farko, ana bayar da shawara ga ‘yan bori da
su sake farfaɗo da Bikin Shan Kabewa saboda muhimmancinsa
ga al’ummar Hausawa. Haka kuma, hukumomin ƙasar Hausa da ma masu hannu da shuni, su rinƙa bayar da tallafi da ƙarfin guiwa ga ‘yan bori da ma duk wasau
masu shirya bukukuwan gargajiya na Hausa, domin kada su ɓace. Idan har aka bari suka ɓace, to salwantar al’adun Hausawa za ta ɓace. Wannan babbar ill ace.
Daga ƙarshe, ana shawartar malamai da ɗalibai domin a shiga gudanar da bincike a kan
bukukuwan Hausawa na gargajiya a yau, domin a samu abin kwatanci da na da.
Wannan zai taikama wajen adanasu domin amfanin jama’a.
8.0 Kammalawa
Wannan
bincike ne da aka gabatar a kan al’adar Hausawa wadda ta ta’allaƙa a harkar da ta danganci addinin gargajiya
ta bautar iskoki. An gudanar da binciken bisa manufar sake bitar bikin domin a
zaƙulo muhimmancinsa a
wajen zama wani madubi mai ƙyallaro
zamanatakewar Hausawa ta fannin harshe da adabi da al’ada. A cikin binciken an
kawo hanayoyin da aka bi aka gudanar da binciken. Haka kuma, an kawo bayanai na
ra’in da aka ɗora binciken a kansa. Bayan nan, an kawo
fannoni guda auku na rayuwar Hausa waɗanda
wannan biki ya hasko. Akwai rayuwar Hausawa dangane da harshensa. Saikuma
rayurasa a cikin adabinsa. Daga ƙarshe aka kawo bayanai na al’adun Hausawa.
Manazarta
Abraham,
R. C. (1978). Dictionary of the Hausa Language. Hodder and Stoughton.
Abubakar,
A. I. (2012a). Dangantakar Bori da Ruƙiyya a Ƙasar Hausa. Gidan Dabino Publishers.
Abubakar,
A. I. (2012b). Ire-Iren Abincin Hausawa na Gargajiya. In Al’ada Madubin Rayuwa.
Gidan Dabino Publishers.
Ado,
A. (2005). Bukukuwan Gargajiya A Ƙasar Hausa Madubi Ne Na Ƙyallaro Rayuwar Hausawa Ta Asali [Unpublished seminar
paper]. Department of Nigerian Languages, Usmanu Danfodiyo University.
Ado,
A. (2014). Sana’ar Gardancin Hausawa: Asalinta Da Yadda take Da Yadda Ake Yin
Ta A Ƙasar
Hausa. Maktabatul Adab.
Ado,
A. (2015a). Bikin Ranar Juma'a Na Hausawa A Masar A Yau: Yadda Yake Da Yadda
Ake Yin Sa A Birnin Alƙahira
[Conference presentation]. International Conference on Hausa Studies, Kaduna
State University, Nigeria.
Ado,
A. (2015b). Bunƙasar
Amfani Da Kabewa Wajen Hausawa Jiya Da Yau [Seminar presentation]. Department
of Nigerian Languages, Umaru Musa Yar’adua University, Katsina, Nigeria.
Ado,
A. (2017a). Nazarin Magungunan Gargajiya Na Gardawan Macizai: Yadda Suke Da
Yadda Ake Bayar Da Su Da Amfaninsu Ga Hausawa. Studies in Hausa Traditional
Medicine, 7. Centre for Research in Nigerian Languages, Translation and
Folklore.
Ado,
A. (2017b). Ra’o’in Bincike Kan Al’adun Hausawa. Kanki Classical Media
Enterprises.
Ado,
A. (2018a). Bincike na Kimiyya a Hausa: Yadda Yake da Yadda ake Gudanar da Shi.
Government Printing Press.
Ado,
A. (2018b). Reflection of Hausa People’s Traditional Life in Modern Folklore: A
Case Study of Cultural Day Marriage Ceremony [Conference presentation]. 4th
Annual Congress and 13th NFS Conference on Folklore and Folklife in Nigeria,
Bayero University, Kano, Nigeria.
Ado,
A. (2019). Kwaikwayon Al’adun Larabawa A Cikin Bukukuwan Aure Na Hausawa:
Nazari A Kan Bikin Daren Larabawa A Garin Katsina [Conference presentation].
International Conference on Language and Culture, Kaduna State University,
Nigeria.
Ahmed,
U. B. (2007). Nau’o’in Wasannin Kwaikwayon Hausa. Ahmadu Bello University
Press.
Akuizuilo,
E. O. (1993). Research Methodology and Statistics (New ed.). Christon Printing
and Publishing Company.
Alhassan,
H., et al. (1988). Zaman Hausawa (2nd ed.). Islamic Publication Bureau.
Amfani,
A. H. (2012). Hausa Da Hausawa: Jiya Da Yau Da Gobe. In Champion of Hausa Cikin
Hausa: A Festschrift in Honour of Dalhatu Muhammad. Ahmadu Bello University
Press.
Bello,
A. S. (2010). Dabarun Gudanar da Bincike a Hausa. Effective Media Services.
Bilkisu,
M. (2019). The Social Role of Bori Dramatic Performance: A Case Study of
Batagarawa Town In Katsina State [Unpublished bachelor's thesis]. Umaru Musa
Yar’adua University.
Bunza,
A. M. (2003). Hausa Medicine: Its Relevance and Development in Hausa Studies.
Ibrash Islamic Publications Centre Ltd.
Bunza,
A. M. (2004). Magana da Iskoki ta Bakin Dokinsu [Conference presentation]. 6th
National Conference on Hausa Language, Literature and Culture, Bayero
University, Kano, Nigeria.
Bunza,
A. M. (2005). Boruƙiyya:
Tazarar Bori da Ruƙiyya
a Idon Manazarta [Seminar presentation]. Centre for Research in Nigerian
Languages and Folklore, Bayero University, Kano, Nigeria.
Bunza,
A. M. (2006). Gadon Feɗe Al’ada. Tiwal Nigeria Ltd.
Danmaigoro,
A. (2010). Magungunan Gargajiya na Hausawa da Fulani. In Al’adu da Dabi’un
Hausawa da Fulani. El-Abbas Printers and Media Concepts.
El-Azzazi,
A. M. H. (2015). Maduban Ƙyallaro
Hausawa A Ƙasar
Waje: Nazari Kan Hanyoyin Gane Hausawa A Cikin Ƙasar Masar A Yau. In Language and Identity in Africa
in Light of the Current Variables (Vol. 2). Cairo University.
Funtua,
A. I. (2010a). Abincin Hausawa Da Fulani Na Gargajiya. In Al’adu da Dabi’un
Hausawa da Fulani. El-Abbas Printers and Media Concepts.
Funtua,
A. I. (2010b). Bukukuwa. In Al’adu da Dabi’un Hausawa da Fulani. El-Abbas
Printers and Media Concepts.
Galadanci,
M. K. M., et al. (2011). Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandare (Book 2). Longman Nigeria
Plc.
Gusau,
S. M. (2010). Al’adun Hausawa A Taƙaice. In Al’adu da Dabi’un Hausawa da Fulani. El-Abbas Printers and
Media Concepts.
Gusau,
S. M. (2015). Mazhabobin Ra’i da Tarke a Adabi da Al’adu na Hausawa. Century
Research and Publishing Limited.
Ibrahim,
B. (2012). Magungunan Gargajiya Na Ƙasar Hausa. In Al’ada Madubin Rayuwa. Gidan Dabino
Publishers.
Isah,
T. A. (1988). Irin Rawar Da Addinin Gargajiyar Hausawa Ya Taka Ga Ƙarfafawa Da Kuma Raunana Imaninsu Game Da
Addinin Musulunci [Seminar presentation]. Department of Nigerian Languages,
Bayero University, Kano, Nigeria.
Jami'ar
Bayero. (2006). Ƙamusun
Hausa Na Jami'ar Bayero. Centre for the Study of Nigerian Languages, Bayero
University, Kano.
Jinju,
M. H. (2001). Islam in Africa: Historico-Philosophical Perspective. Ahmadu
Bello University Press.
Kano,
A. A. W. (2002). Kano Ta Dabo Cigari. Northern Nigerian Publishing Company Ltd.
Madauci,
I., et al. (1982). Hausa Customs. Northern Nigerian Publishing Company.
Mukhtar,
I. (2013). Duba ga Al’adun Hausawa Cikin Tafiya Mai Nisa: Daga Ina Zuwa Ina? In
The Deterioration of Hausa Culture. Ahmadu Bello University Press.
Nata’ala,
A. M. (2010). Zaruntaka. In Al’adu da Dabi’un Hausawa da Fulani. El-Abbas
Printers and Media Concepts.
Rimmer,
E. M., et al. (2002). Zaman Mutum Da Sana’arsa. Northern Nigerian Publishing
Company.
Rogers,
G. A. J. (2017). John Locke: English Philosopher. In Encyclopædia Britannica.
Sallau,
B. A. (2010). Wanzanci da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. M. A. Najiu
Professional Printers.
Sallau,
B. A. (2013). Wanzanci da Sauye-Sauyen Zamani. Ahmadu Bello University Press.
Sule,
A. Y. M. (1974). Bori a Ƙasar
Hausa. In Makon Hausa na 1973-1974. Department of Nigerian Languages, Bayero
University, Kano.
Umar,
M. B. (1987). Dangantakar Adabin Baka Da Al'adun Gargajiya. Triumph Publishing
Company.
Yakasai,
S. A. (2012). Jagoran Ilimin Walwalar Harshe. Garkuwa Media Services.
Yakasai,
S. A. (2014). Language and Cultural Preservation: Hausa in the Face of
Technological Advancement. Gidan Dabino Publishers.
Zurmi,
Y. S. (2014). Matakan Nazarin Hausa Don Ƙananan Makarantun Sakandare. Kanki Multimedia
Enterprises.

0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.