Ticker

6/recent/ticker-posts

Manuni Ko Ishara

Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.

About Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa

265. Duba ishara tana a dokar haɗe zance,

 Yanzu za mu zayyano su mu tantance,

 Yadda ake haɗe su, ka gan su rubuce,

In magana ta zo da nuni na kwatance,

  Da ishara irin na nuni ga gwadawa.

 

266.  Kalmomin da ke fita nan ga zubinsu,

 Wani loton akan ji tamkar biyu ne su,

 A haƙiƙan guda-guda suke tsarinsu,

 Domin haka in ka zo rubutun zana su,

  Tare ake zubinsu don ba a rabawa.

 

267. Ba su yawa a Hausa su kalmomin nan,

 Sai mu riƙe mu hardace ai shi ke nan,

 Mui nazarin zubinsu, dokarsu tana nan,

 Sa wannan gami da wancan biyu ke nan,

  Duk nuni sukai ga zancen Hausawa.

 

268. Da waɗannan  idan abubban da yawa ne,

 A rubutunsu in ka ware su kure ne,

 Doka ce ka san da komai tsari ne,

 Sai ka haɗe su duk gaba ɗai tsari ne,

  Da ‘waɗancan’ idan ana son nunawa.

 

269.  Cana Basakkwace ya ce wanga da wagga,

 Kalmar ‘wanga’ an musanya ta da ‘wagga’,

 Can Sakkwato nig gano ana bin tsaringa,

 Ko ma ya abin ya zo dai bari yanga,

Hadda ‘waɗanga’ in yawa yaka nunawa.

 

270. In aka zo fagen rubutu a haɗe su,

 Ba a sa ‘waɗan gadon ba a raba su,

 Mun samu bakwai ka duba ka riƙe su,

 Kalmomi manuniya mun gane su,

  Ba a rabe su don ka zan mai ganewa.

 

271. Zan lura da yadda du mun ka saka su,

 Sai ka haɗe su, inda duk aka tar da su,

 Ba a ware ba, ba mu ƙaunar a raba su,

 In kuwa kar raba su to ka ɓata su,

Sai nahawun ya shirɓace ba ya fitowa.

Post a Comment

0 Comments