Bashir Aliyu Sallau, Ph. D.
Sashen
Koyar da Hausa
Jami’ar
Gwamnatin Tarayya Dutsin-ma,
Jihar Katsina,
Nijeriya
TSAKURE
Hausawa na cewa, “magana jari ce, yaro kawo kuɗi a gaya maka”. Wannan batu gaskiya ne domin kuwa dukkan wanda Allah Ya ba baiwar iya magana da kowane harshe na duniya zai sami masu sauraron su don ƙaruwa da ire-iren hikimomin da suke ƙunshe cikin waɗannan maganganu. Haka kuma, wasu ba su gajiya da sauraren sa ko da kuwa za su biya kuɗi don shiga wuraren da ake aiwatar da ire-iren waɗannan maganganu na hikima. Ba a bar al’ummar Hausawa baya ba wajen aiwatar da ire-iren waɗannan maganganu na hikima ba, don kuwa Allah Ya ba al’ummar Hausawa da harshen Hausa maganganun hikima masu tarin yawa waɗanda suke ƙunshe cikin karin-magana da baƙar magana da habaici da kacici-kacici da ƙarangiya da zaurence da sauransu da dama. Masana da manazarta da ɗalibai sun yi ƙoƙarin ta hanyar taskace su a bugaggun littattafai da kundaye a jami’o’i da kwalejojin zurfafa ilimi da sauransu. Wasu kuma sun gabatar da su a tarukan ƙara wa juna ilimi, wasu kuma an buga su a mujallu don al’umma ta sami abin karantawa don ƙarin ilimi ko don samun nishaɗi. Domin samun abin karantawa ne ya jawo hankalin Mande Muhammad Kurfi ya rubuta littafi mai suna “Magana Iyawa Ce”. A wannan littafi an kawo nau’o’i daban-daban na maganganun hikima na Hausawa ciki har da karin magana. Dangane da haka, maƙasudin wannan takarda shi ne, ta yi nazari wannan littafi don fito da ire-iren maganganun hikima da suke ƙunshe cikinsa, sannan a yi tsokaci kan wasu daga cikinsu.
1. 0
Gabatarwa
Marubuta adabin Hausa
irin su, Madauci, I. da wasu (1972) da Skinner. N (1980) da Ɗangambo. A, (1984, 1990) da Yahaya, I. Y. (1981, 1988, 1989,
1995) da Gusau (1995) da Skinner. N, (1980) da Umar, M. B. (1984) da Ɗanhausa, A. M. (2012) sun gabatar da muhimman ayyuka waɗanda suka shafi
maganganun hikima na Hausawa a kan karin magana da baƙar magana da azancin magana da habaici da ƙarangiya da kacici-kacici da adon magana da take da
kirari da sara da sauransu.
A wannan zamani an sami
wasu marubuta irin su Mande Muhammad Kurfi RN, CNO, wanda aka fi sani da suna
Ali Kano, ya wallafa littafi a kan ire-iren maganganun hikima da al’ummar
Hausawa suke amfani da su a bakunansu a yau da kullum. Ya raɗa wa littafin suna Magana Iyawa ce. Tun kafin a yi nisa
wannan suna da aka ba wannan littafi ya dace da ƙumshiyar gundarin jawaban da suke cikin littafin.
2. 0 Taƙaitaccen
Tarihin Mawallafin Wannan Littafi:
Domin samun cikakken
bayani kan tarihin wannan mawallafi, ana iya duba bangon littafin na baya, amma
duk da haka, a taƙaice, an haifi Mande Muhammad Kurfi,
a garin Kurfi, Ƙaramar Hukumar Kurfi ta Jihar
Katsina, a ranar 22 ga watan Afrilu, 1959. Ya yi karatun Firamare a nan Kurfi, na
Sakandare a Katsina. Sannan kuma ya yi karatun kiwon lafiya. Ya yi aikin
koyarwa a Firamare, kuma ya yi aiki a asibitoci da dama a Jihar Katsina. Ta
fuskar rubuce-rubuce, ya rubuta litttattafai masu yawan gaske. Bayan wannan
littafin akwai wasu da ya rubuta waɗanda suka haɗa da Ƙamusun
Ingilishi da Hausa, sai kuma In Ɓera da
Sata, Daddawa ma na da Wari.
3. 0 Zubin Wannan Littafi
Bayan shafi takwas (ɗiii) na
gabatarwa, wannan littafi yana da yawan shafuka 179 waɗanda aka wakilta da
alamun ƙirga na Romanci. Duk da kasancewar
ba a raba littafin zuwa babi-babi ba, amma an shirya shi bisa bin tsarin abjadi,
wato daga A zuwa Z. Sakamakon bin wannan tsari, an yi amfani da maganganun
hikima waɗanda suka haɗa da karin magana da azancin magana da adon magana da baƙar magana da sauransu a wuri ɗaya, inda suka riƙa yi wa juna shigar giza-gizai, ta hanyar bin baƙin da ya fara fitowa a wannan magana. Haka kuma, baƙaƙe masu laƙwasa Ɗɓɗ da Ɗɗɗ da Ɗƙɗ an kawo magangunun hikima da aka fara da waɗannan baƙaƙe tare da takwarorinsu Ɗbɗ da Ɗdɗ da Ɗƙɗ kamar haka;
BAƘI |
MAGANAR
HIKIMA TA FARKO DA TA ƘARSHE |
ADADI |
A |
A bakin tsoho goro kan tsufa, sai aka ƙare da, A zuba Shinkafa ruwa a ga tashin kwafsa, shafi
na 9-29. |
546
|
B/Ɓ |
Ba a azawa kaza sirdi, aka ƙare
da, Buzuzu da ya bugi bango ya ce kai duniyar ma ta ƙure, shafi na 29-44. |
417 |
C |
Caca asara ce ga wanda ya santa, sai aka ƙare da Cuta gaba aka yi ko baya, shafi na 44-46. |
48 |
D/Ɗ |
Da a’a da a’a majiyaci yake cika cikinsa, sai aka ƙare da Ɗuwawu
ne mu dole a zauna da mu, shafi na 46-65. |
487 |
F |
Faɗa mai tada taro, sai aka ƙare da, Fuskar da aka zaga ba ta fi ƙarfin mari ba, shafi na 65-66. |
51 |
G |
Ga abin kwaɗo babu ƙuli, sai
aka ƙare da, Gyara lafiyar wani kai ka ɓata
taka, shafi na 66-74. |
293 |
H |
“Haba ina mazan su ke” Ɗan
Daudu ya shiga layin mata, sai aka ƙare
da, Hutun Jaki da kaya a baya, shafi na 74-80. |
68 |
I |
Icce gidana inuwa gidan wani, sai aka ƙare da, Iya yi kai mayya ɗaki, shafi
na 80-97. |
417 |
J |
Jaɓa ba ta jin warin jikinta, sai aka kare da, Juma’ar da
ke da kyau tun Laraba a ke gane ta, shafi na 97-100. |
67 |
K/Ƙ |
Ka bari a yi da waɗanda suka iya Bamaguje ya shiga maganar addini, sai aka
ƙare da, Kyawon wuya a tambayi soja, shafi na 100-126. |
699 |
L |
Labari ba shi yin daɗi sai an haɗa da ƙarya,
aka ƙare da, Lomar dutse da ga ba hannu ba sai dai jifa, shafi
na 126-128. |
56 |
M |
Ma’abucin barka ko gidan mutuwa sai ya yi, aka ƙare da, Mutuwa ba ki ƙyamar raggo, shafi na 128-143. |
458 |
N |
Na ciki bai san asirin na waje ba, aka ƙare da, Nuna sani kasuwar jahilci wauta ne, shafi na
143-146. |
68 |
R |
Raba mugu da makami ibada, aka ƙare
da, Ruwan zuma mai haɗa al’umma, shafi na 146-151. |
153 |
S |
Sa’a ka sa makaho taka kuɗi ya ɗauka, aka ƙare
da, Suri dare ɗaya ka ka girma, shafi na 151-160. |
350 |
T |
‘Ta’Allah ba taku ba, in ji matsoraci, aka ƙare da, Tsutsar nama ita ma naman ce, shafi na 160-167.
|
177 |
U |
Uban kasada zalɓe mai tura ƙafa
rami, aka ƙare da, Uwar wani
matar wani, shafi na 167-168. |
16 |
W |
Wace ni da ɗaura zane uwar miji tsirara, aka ƙare da, Wuyar wuta sainƙarfe, shafi na 168-176. |
104 |
Y |
Ya amshi makulli ga zakara, aka ƙare
da, Yunwa mai kashe raggo, shafi na 176-183. |
175 |
Z |
Zaɓe mai fidda gwani, aka ƙare da, Zuwa da wuri ya fi zuwa da wuri, shafi na
183-186. |
72 |
A – Z
|
JIMLA
|
4722 |
A jimlace an sami magangunan hikima da azanci 4722, amma
a jadawalinsu cikin littafin an kawo 4724. A shafi na 150 ba a kawo ire-iren waɗannan magangunu ba
a lamba ta 3797 da kuma 3798.
A cikin littafin an ƙawata shi da hotunan da suka fito da wasu maganganun
hikima na Hausawa waɗanda za su ƙara wa mai karatu
nishaɗi da fahimtar saƙon da ake son
isarwa.
A gaban
bango na wannan littafi an ɗora hoton gidan Bahaushe wanda yake ƙunshe da ɗaki na gargajiya wanda aka zagaye wani ɓangare na gidan da
katangar bulo. Ɗaya ɓangaren kuma da
dangar kara. Sannan aka nuna hoton wani mutum a tsakiyar gidan, yana zaune a
gaban tukunyar dafa abinci yana riƙe da ludayin motsa
miya ko abinci. An kuma kawo hoton akuya tana kiwo da kaza ita ma tana kiwo. Wannan
zubi da aka yi yana bayyana dukkan abin da za a gani cikin littafin, zai yi
bayani ne kan Bahaushe da yadda yake tafiyar da rayuwarsa ta yau da kullum.
A
bangon baya kuma, aka kawo hoton mawallafin wannan littafi da taƙaitaccen tarihin rayuwarsa da kuma alama da sunan maɗaba’ar da ta buga
littafin.
4. 0 Manufar Wannan Littafi
Kamar
yadda aka bayyana dangane da tarihin mawallafin wannan littafi, Ali Kano, yana
da matuƙar sha’awar bayar da gudummuwa a
fannin rubuce-rubucen tarbiyyantar da al’umma a cikin salo da nishaɗi. Babu shakka
wannan sha’awa tasa ta fito a cikin wannan littafi Magana Iyawa ce. Masana da manazarta da ɗaliban adabi da
fannin nazarin maganganun hikima na Hausa, irin su Abdulƙadir Ɗangambo da Sa’idu
Muhammad Gusau da Muhammad Balarabe, a rubuce-rubucen su sun bayyana cewa, hanyar
da al’umma za ta sami nishaɗi na cikin maganganun hikimar da magabata suka bari ta
hanyar karin magana da habaici da azancin magana da baƙar magana da sauransu. Dangane da haka, manufar wannan
littafi ita ce, a fito da ire-iren baiwar da Allah ya yi wa Hausawa ta iya
magana, waɗanda ake yi ta hanyar karin magana da haibaici da azancin
magana da baƙar magana da shaguɓe da gugar-zana da
hannun-ka-mai-sanda don koyar da tarbiya ga al’umma musamman yara ƙanana da matasa maza da mata, a kuma taskace su yadda
al’umma za ta amfana. Wannan marubuci ya yi ƙoƙari matuƙa wajen fito da ire-iren waɗannan maganganun
hikima na Hausawa a cikin wannan littafi, waɗanda za mu ɗan tsakuro wasu
daga cikinsu ta fuskar karin magana da baƙar magana da
azancin magana da habaici, kamar haka;
4. 1. 1 Karin Magana
Karin
magana wata hikimar magana ce da Hausawa suke yi a dunƙule a cikin zance da ‘yan kalmomi kaɗan. Ƙamusun Hausa na Jami’ar Bayero ya bayyana karin magana, a
matsayin,
“magana ta musamman wadda sai an yi
tsokaci ake ganewa” (2006:
235).
Mafi yawancin karin magana yana da ɓangare biyu, na
farko yana yin jimlataccen bayani ko furuci na wata manufa, ɓangare na biyu kuma
yana yin sharhi ko ƙarin bayani, kan abin da ɓangare na farko ya
faɗa (Ɗangambo, 2008:67). An
kawo karin magana masu ɗimbin yawa a wannan littafi. Ga misalin kaɗan daga cikinsu:
10. A bar yabon ɗan kuturu, sai ya tashi da yatsunsa.
26. Abin dariya, yaro ya
tsinci haƙori.
563. Ba a canza wa mage
gida, sai an sanya ta cikin buhu.
1199. Ɗan da uwa ta bari, shi
yake yin kuka.
2235. In ruga ba ta
zauna lafiya ba, rundawa ba su zama lafiya.
3000. Ƙulalliyar kyauta, ita ke
tada hankalin mai karɓa.
3678. Raba ni da koken
uwa kuturwa, kaka makauniya.
3721. Rana mudun aiki, ko ta gobe sai ta faɗi
3734. Rashin kira, ya sa Karen bebe ya ɓata.
3849. Sabon salo, kukan mutuwa da guɗa.
3869. Sai hali ya yi
daidai, ake abota.
4030. Sanin asali, ka sa kare ya ci alli.
4133. Shimfiɗar fuska, ta fi shimfiɗar tabarmi.
4182. Taɓa ka lashe ba shi maganin kwaɗai,
sai an ci.
4187. Tabarmar kunya, da hauka kan naɗe ta.
Idan
muka nazarci wasu daga cikin waɗannan karin maganganu da aka kawo a sami za mu fahimci
kowane daga gare su yana ɗauke da wani saƙo ga al’umma, Misali,
karin magana mai lamba 4030 “Sanin asali ya sa kare cin alli”, za a iya bayyana
shi da wani abu ko mutum ko dabba wanda aka san asalinsa, idan ya yi wani abu
wanda zai ƙara jaddadda sanin asalin abun ne ya
sa shi karɓarsa ko yin amfani da shi da sauransu.
Haka
kuma, karin magana mai lamba 4187 “Tabarmar kunya da hauka kan naɗe, yana bayyana
lokacin da mutum ya yi wani kuskure, misali, yi da wani mutum, a lokacin da ya
fahimci lokacin da yake yi da wannan mutum yana wurin ko wani ɗan’uwansa ko
abokinsa yana wurin kuma ya ji abubuwan da ake faɗa, shi wanda yake
yin magana a lokacin da ya gane kuskurensa sai ya hau borin ƙarya, yana sabbatu don kawar da hankalin wannan mutum ko
wanda zai iya gaya masa abubuwan da aka ce game da shi.
A
nazarce za a iya cewa waɗannan misalai na karin magana da ka ɗauko daga cikin
wannan littafi sun ɗauki dukkan halayen da masana suka ba karin maganar Hausa,
don kuwa dukkansu suna da ɓangarori biyu kuma sun isar da wani muhimmin saƙo ga al’umma.
4. 1. 2 Baƙar
Magana
Baƙar magana maganganu ne na hikima da ake yi wa wani mutum
don ɓata masa rai, kuma a wasu lokuta sukan fito a sigar karin
magana ko zance. Al’ummar Hausawa na
danganta masu yin sana’ar fawa da matsayin waɗanda suka fi kowa
iya baƙar magana (Ɗangambo, 2008:63). Baƙar magana tana da babban matsayi a maganganun hikima na
Hausawa, don kuwa tana ɓata ran wanda aka yi wa ita. A wasu lokuta, baƙar magana kan iya haifar da hayaniya ko rikici kai har ma
ta kai ga faɗa da ka iya kawo ji wa juna raunuka ko kisa. Hausawa sun ɗauka baƙar magana cin mutuncin ne mai danganta da zagi, amma Makaɗa Ibrahim Narambaɗa Tubali a cikin waƙarsa ya ce ba zagi ce ba, amma ta ɗari zagi zafi.
Gindin Waƙa: Gogarman
Tudu jikan Sanda,
Maza su ji tsoron ɗan Mai Hausa.
Jagora : Ɗan Sarki duka ab ba kowa,
Ɗan Sarki duka ab ba komi,
Sannan
yat tsira yawon ƙarya,
‘Y/Amshi : Ya san ba ya
sarauta,
Sai
fa ya kwan nan,
Gobe
ya kwan nan, jibi,
Dangi
na mashi Allah waddai,
Jagora : Baƙam magana ba ɓaci ta ba,
Y/Amshi : Amma ta ɗara ɓaci zafi (Gusau, 2003:72-73).
A wannan littafi an kawo nau’o’in baƙar magana da yawan gaske waɗanda suka ɗauki sigar karin
magana kamar haka;
413. An yi gadon ciwo
bare na dukiya?
445. Ana wata ga wata, an
yi wa shege ƙane.
507. A su wa kwabsar ƙwai a kicin.
508. A taka ruwa a ɗebo ruwa?
550. Ba a ɓarawo makaho.
555. Ba a ba turmi
labarin taɓarya.
590. Ba a haɗa ƙwai da dutse.
2241. In so cuta ne haƙuri ma magani ne.
2261. In za ka yi aski
ka lura da wanzamin, don kowane da halinsa.
2280. Ina marabarsa da
makaho? An watsa wa mai ido ɗaya tasshi.
Yana da matuƙar kyau a fihimci baƙaƙen maganganun da aka kawo cikin
wannan littafi su ne ƙunshe da darussa da nishaɗi ga dukkan wanda
ya karanta su. Misali, idan muka karanta karin magana mai lamba 508 Ba a taka
ruwa a ɗebo ruwa. Ana yin wannan baƙar magana ga wanda ya zo neman wani abu, sai ya tarar da
wani wanda yana da wannan abun, maimakon ya nema wajen sa sai ya tura ya nemo
masa wajen wani. A mafi yawanci an fi yin amfani da wannan baƙar magana a lokacin da saurayi ya zo
wajen wata budurwa. Kafin ya ganta sai ya ga wata budurwa ya bukaci ta kira
masa wadda ya zo wajen ta. Saboda rashin jin daɗi
wadda aka aika na iya yi wa wannan sarauyi irin wannan baƙar magana.
Bisa nazartar misalan baƙar magana da aka tsakuro a cikin wannan littafi, an
fahimci lallai ire-iren zantukan da aka yi amfani da su ka iya ɓata wa dukkan wanda
aka yi wa rai, ya ɗauka an ci mutuncinsa.
4. 1. 3
Azancin Magana
Azancin
magana kamar karin magana, wasu maganganun hikima ne da Hausawa suke cikin
guntayen zantuka. Azancin magana ya bambanta da karin magana ne, don shi ba ya
da ɓangarori biyu, wato ɓangare ɗaya ne kawai. Ba a
gajiya ba, don kuwa an kawo azancin magana masu yawa a cikin wannan littafi
kamar haka;
193. Ai gaba ta fi baya
yawa.
196. Aiki ba ya son wasa.
201. Aiki ya kwana.
324. Allah raba ɓarawo da yari.
344. Allah ya fidda A’i
ga rogo.
396. Angulu da kan zabo.
601. Ba a jarumi raggo.
606. Ba a ƙarya kusa da gida.
636. Ba a rasa nono ruga.
784. Baƙo bai wuce tsakiyar gida.
926. Biyu gafiyar Ɓaidu
1537. Fitila maganin
duhu.
1693. Gudu rawar kare.
Idan
muka nazarci wasu daga cikin waɗannan maganganu na azanci za a fahimci suna isar da irin
hikimar da take ƙunshe cikin harshen Hausa. Misali, azancin
magana na 344 “Allah Ya fidda A’i ga rago”, na nufin a cikin kasuwanci akwai faɗuwa da riba. Lokacin
da ɗan kasuwa ya sawo kayan sayarwa idan waɗanda suka ga abin
da ya sawo da kuma yawan kuɗin da ya sawo abin suka fahimci akwai matsala, suna
amfani da wannan azancin magana don bayyana wa wanda ya sawo kayan akwai
yiwuwar ya faɗi, sai idan Allah Ya taimake shi ne zai mayar da kuɗin da ya sawo kayan.
Kazalika,
wannan littafi yana ɗauke da maganganun azanci masu yawa kamar yadda aka kawo
misalansu a sama, don kuwa sun fito da wasu zantuka na hikima kuma a cikin
jimla ɗaya, waɗanda sai an natsu kafin a fahimci saƙon da suke ɗauke da shi.
4. 1. 4 Habaici
Habaici
wata magana ce mai ɓoyayyar manufa. Ana yin ta ne ga wani don mayar da martani
ga wanda ya yi wa wani mutum wani abu. Wanda aka yi wa zai jefo wata magana a
cikin mutane yadda wanda aka yi domin shi zai fahimce saƙon da aka isar. Dukkan wanda bai san abin da ya faru ba, da
yawa ya fahimci irin wannan magana (Ɗangambo, 2008:72). Wannan
dalili ne ya sa Hausawa suke yi wa habaici kirari da “mai kashe auren sakarai”.
A cikin wannan littafi an kawo zantukan habaici masu yawan gaske kamar haka;
147. A ci na ƙurya a ci na bakin gado.
1187. Ɗan Adam butulu
1195. Ɗan da ya hana uwar sa
barci shi ma ko na ya yi ba.
1445. Duk irin ikon
sarki bai shafi kadangare ba.
2132. Indararo ba ka ba
gida sai daji.
2991. Kunkuru bai yi wa
bushiya ba’ar ƙafa.
3454. Marar Gaskiya ko
cikin ruwa ya yi jiɓi.
4359. Ungulu ba ta ƙaunar batta.
4413. Wanda bai san yaro
ba shi yaro kan rena.
4713. Zubda yawu bai
hana tusa wari.
Misalan waɗannan
habaice-habaice da aka kawo suna ƙunshe
da saƙonnin ga al’ummar Hausawa. Idan muka
nazarci habaici mai lamba 147 “A ci na ƙurya
a ci na bakin gado”, na
bayyana wani hali ko yanayi tsakanin al’umma ‘yan uwa ko abokai ko waɗanda
suke wuri ɗaya. Idan daga cikinsu wani ya ware shi
kaɗai, shi
yake yin kome, shi kaɗai ake nema wajen yin wani
abu, kuma shi kaɗai ake ba wani abu duk da
kasancewar ba shi kaɗai ba ne. Don jin zafin abin
da ake masu, suna iya amfani da wannan habaici don bayyana masa abubuwan da
suke cikin zukatansu.
A
wannan littafi dai ba a gajiya ba, don kuwa tarin zantukan habaici da aka kawo
suna ɗauke da wasu saƙonni waɗanda duk wanda aka
yi wa su, ya san akwai wani abu ɓoye da ya yi ake son bayyana masa don nuna masa an san
abin da ya yi, ko ya ce.
5. 0 Ƙunshiyar Wannan Littafi
Marubucin
wannan littafi ya fito da maganganun hikima na Hausawa masu ɗimbin yawa waɗanda suka tabbatar
da littafin ya cancanci wannan suna da aka ba shi Magana Iyawa ce. Wannan kuwa ya samu ne sakamakon ire-iren
maganganun hikima na Hausa waɗanda suka haɗa da karin magana da habaici da baƙar magana da azancin magana da sauran dangoginsu sun fito
a cikin wannan littafi.
6. 0 Kammalawa
Idan aka bibiyi tarihin mawallafin wannan
littafi za a ga cewa, dukkan karatun da ya yi babu inda aka bayyana ya karanta
Hausa. Ta la’akari da ƙoƙarin da ya yi na fito da wani babban sashe na nazarin
Hausa, wato maganganun hikima na Hausa, za a iya cewa ya cancanci babban yabo, kuma
mai babbar daraja. Wannan littafi Magana
Iyawa ce, ya fito da maganganun hikima na Hausa masu yawan gaske waɗanda za su taimaka
wa al’ummar Hausawa taskace su don amfanin gobe ga su kansu Hausawa da ɗalibai da manazarta
da masana don samun abin nishaɗi da nazari.
Dole ne
a yi wa Ali Kano uzuri idan aka ga wasu kurakurai a wannan littafi, don kuwa
kamar yadda na bayyana a sama, kuma tarihin rayuwarsa ya nuna, Ali Kano bai
karanta Hausa a matsayin darasi a sakandare ko gaba da sakandare ba, amma duk
da haka, saboda sha’awa ya yi wannan gagarumin aiki. Hasali ma, shi malamin
kula da lafiya, ko a ce, malamin asibiti ne. Hakika! Ya cancanci yabo.
Dangane
da haka, ina ba da shawara idan za a sake buga wannan littafi, a sake tsara shi
zuwa babi-babi don fito da rukunonin maganganun hikimar da suke cikin littafin
waɗanda suka ƙunshi karin magana
da baƙar magana da azancin magana da habaici da
hannun-ka-mai-sanda da shaguɓe da gugar-zana da sauran makamantansu. Yana kuma da matuƙar muhimmanci a duba ƙa’idojin rubutu da dokokin nahawu da na adabi da shekarar
da aka wallafa littafin. Yin haka zai ƙara wa littafin
inganci da sauƙin nazari. Haka kuma, littafin zai ƙara samun karɓuwa ga ɗalibai da manazarta da masana da hukumomin shirya
jarrabawa irin su WAEC da NECO da makamantansu.
Ina
kuma amfani da wannan dama, don yin kira ga matasan marubutanmu waɗanda suke ƙoƙarin rubuce-rubuce da su ɗauki irin hikima da
fasahar shahararren marubucin ƙasar Hausa, Marigayi
Alhaji Abubakar Imam, OBE, CON, lokacin da ya rubuta Littattafan Magana Jari ce, ta ɗaya zuwa ta uku, inda
ya riƙa amfani da karin magana ko azancin magana ko habaici a
matsayin kan labari. A cikin labarin zai fayyace ma’anar wannan maganar hikima
da ya yi amfani da ita a matsayin kan labari. A rayuwar da muke ciki a yau, akwai
abubuwa na zahari da dama da suke faruwa ko suka faru, ko kuma a ƙirƙiri wani labari
wanda za a iya amfani da maganganun hikima na Hausawa ire-iren waɗanda Ali Kano ya
kawo a wannan littafi, a matsayin kan labari wajen isar da saƙon da al’umma za ta ilmanta ko ta nishaɗanta ko kuwa abin
ya zama darasi ga dukkan wanda ya yi shi yadda al’umma za ta amfana.
Daga ƙarshe, ina taya Mande Muhammad Kurfi, RN, CNO (Ali Kano)
murna bisa ga wani namijin ƙoƙari da ya yi na wallafa wannan littafi Magana Iyawa ce. Duk da kasancewar
wannan littafi ba shi ne littafinsa na farko ba, muna roƙon Allah Ya ƙara ba shi fasaha
da juriya da jajircewa wajen ƙara rubuta wasu
littattafai waɗanda suka shafi rayuwar Hausawa. Lallai! Hausawa sun faɗi gaskiya da suka
ce, “Himma ba ta ga raggo”. Allah Ya sa albarka.
Manazarta
Ɗangambo, A. (1990) “Gadon
Feɗe Adabin Hausa (Ba a Buga ba).
Ɗangambo, A. (2008) Rabe-Raben Adabin Hausa (Sabon Tsari) Amana
Publishers Limited. Zaria: New Kano Road, Kaduna State.
Ɗanhausa, A. M. (2012) Hausa Mai Dubun Hikima, Kano-Nigeria:
Century Research and Publishing Company.
Gusau, S. M. (2003) Jagoran Nazarin
Waƙar Baka, Kano. Benchmark Publishers Limited.
Junaidu, I. da Yar’aduwa, T. M. (2007) Harshe
da Adabin Hausa a Sauƙaƙe don Manyan Makarantun Sakandare, Ibadan: Spectrum Books Limited.
Kurfi, M. M. (Ba ranar Bugu) Magana
Iyawa ce, Katsina: Kanki Classical Media Ɓentures.
Madauci da Wasu (2009) Hausa Customs, (Zaman Hausawa da Tadodinsu) Zaria:
Northern Nigerian Publishing Company.
Skinner, N. (1980) An Anthology of
Hausa Literature in Translation. Zaria: NNPC.
Yahaya, I. Y. (1981) “Adabin Gargajiya a Makarantun Sakandare. Lacca da ya
gabatar a Makarantar ‘Yammata ta Dala.
Yahaya, I. Y. (2015) Labarun
Gargajiya 1, Ibadan: University Press.
Umar, M. B. (1984) Dangantakar Adabin Baka da Al’adun Gargajiya na Hausa. Kano: Triumph Publishing Company.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.