Matsayin Sana’o’in Gargajiya na Hausawa Jiya da Yau: Ƙalubale ga Matasan Wannan Zamani

    Published in Champion of Hausa Cikin Hausa, A Festschrift in Honour of Professor Ɗalhatu Muhammad, Published by the Department of African Languages and Cultures, Ahmadu Bello University, Zaria

    Matsayin Sana’o’in Gargajiya na Hausawa Jiya da Yau: Ƙalubale ga Matasan Wannan Zamani

    English Rendition as The Position of Hausa Traditional Occupations Yesterday and Today: A Challenge Facing Present day Youth 

    BASHIR ALIYU SALLAU, Ph. D.
    DEPARTMENT OF NIGERIAN LANGUAGES
    UMARU MUSA YAR’ADUA UNIVERSITY, KATSINA

     

    Tsakure

    Tun shekaru aru-aru da suka gabata kafin shigowar Turawa ƙasar Hausa mutanen wannan ƙasa suna da ingantattun hanyoyin da ke taimaka wa tattalin arzikinsu domin dogaro da kai, waɗanda suka haɗa da noma da kiwo da fatauci da sana’o’in gargajiya irin su ƙira da dukanci da rini da saƙa da sassaƙa da jima da wanzanci da fawa da ɗori da sauransu. Tarihi ya bayyana cewa, al’ummar Hausawa mutane ne masu ƙwazo da ƙoƙarin yin ayyukan da za su taimaka wa rayuwarsu yadda za su zama masu dogaro da kai. Wannan dalili ne ya sa a kowane gida da mutum ya ziyarta a ƙasar Hausa, zai tarar mutanen gidan na yin ɗaya daga cikin waɗannan sana’o’i da aka ambata a sama. A wancan zamani za a tarar matasa ne a gaba-gaba wajen tafiyar da waɗannan sana’o’i a inda za a tarar wasu sun mallaki masana’antu na gargajiya don sarrafa kayayyaki daban-daban waɗanda suke sayarwa a kasuwanni na cikin gida ga masu sayen ɗai-ɗaya da kuma masu yin sari don kaiwa kasuwannin da ke maƙwabtaka da ƙasar Hausa na kusa da na nesa. Haka kuma, za a tarar wasu daga cikin waɗannan matasa an ɗauke su domin yin ƙodago a ire-iren waɗannan masana’antu. Shigowar Turawa ƙasar Hausa a cikin ƙarni na 19 da kuma farkon ƙarni na 20 wanda ya haifar da samuwar ilimin zamani (boko) ya kawo babban sauyi wanda ya shafi yadda ake tafiyar da waɗannan sana’o’in gargajiya na Hausawa, don kuwa matasan ƙasar Hausa sun yi watsi da waɗannan sana’o’i suka mayar da hankali wajen samun aikin gwamnati ko na kamfanoni waɗanda Turawa suka kawo a ƙasar Hausa. Yau da kullum ana samun ƙaruwar matasa waɗanda suka kammala karatun sakandare da na gaba da sakandare da ma na Jami’a, sai yawansu ya riƙa ƙaruwa sosai wanda ya haifar da cikowar masu neman aiki a ma’aikatu da hukumomin gwamnati da ma kamfanoni. Wannan ya sa matasa masu yawan gaske duk da suna da ilimin zamani suka rasa wuraren da za su sami aikin da za su yi. Saboda haka ne, wannan takarda za ta yi tsokaci ne kan sana’o’in gargajiya na Hausawa dangane da yadda matasan ƙasar Hausa suka yi watsi da su suka taɓarɓare yadda a wannan zamani har wasu na neman mutuwa a manta da su.

     

    1.0     Gabatarwa

    Dukkan al’ummar da take son zama lafiya da ci gaba mai ɗorewa da bunƙasa dole ne ta yi riƙo da ingantattun hanyoyin zamantakewarta waɗanda suka danganci abubuwan da ta gada tun iyaye da kakanni musamman waɗanda suka shafi sana’o’in gargajiya da aka gada waɗanda su ne, a zamanin da ya gabata kafin shigowar wasu baƙi, suka taimaka wa tattalin arzikinta ya bunƙasa har ya dogara da kan shi. Tarihi ya bayyana cewa, ƙasashen da a yau ake kira waɗanda suka ci gaba ta fuskar kimiyya da fasaha da ƙere-ƙere, ba haka nan suka tsinci wannan ci gaba ba, sun same shi ne ta hanyar gudanar da binciken da ya taimaka musu bunƙasa abubuwan da suka gada iyaye da kakanni yadda ya tafi daidai da zamanin da muke ciki a yau. Dangane da haka, idan muka waiwaya muka dubi yadda sana’o’in gargajiya na Hausawa suke a jiya za mu amince da cewa, idan aka gudanar da ingantaccen bincike a kansu aka kuma ƙara bunƙasa su, za su taimaka wa tattalin arzikin ƙasar Hausa da ma na Tarayyar Nijeriya ya ƙara bunƙasa yadda za a ƙara samun kuɗin shiga ga wannan ƙasa. Wannan kuwa ya faru ne saboda tun kafin shigowar Turawa da wasu baƙi cikin ƙasar Hausa, Hausawa na yin fataucin kayayyakin da aka ƙera ko aka sarrafa a ƙasar Hausa zuwa wasu sassa da suke maƙwabtaka da wannan ƙasa ta kusa ko ta nesa. Irin wannan fatauci ya taimaka matuƙa gaya wajen bunƙasar tattalin arzikin ƙasar Hausa a wancan zamani. Shigowar Turawa ƙasar Hausa da kuma irin yadda suka kawo sauye-sauye, sun taimaka wajen sauya tunanin wasu Hausawa musamman matasa waɗanda suka yi watsi da yin ire-iren sana’o’in da suka gada, suka ɗauki tsarin ayyuka a ma’aikatun gwamnati da kamfanoni waɗanda Turawan suka kawo. Wannan al’amari ya taimaka matuƙa gaya wajen raunana ko ruguza wasu daga cikin sana’o’in gargajiya na Hausawa a wannan zamani. Hakika, wannan al’amari ne da yake bukatar a yi masa karatun ta natsu don warware matsalolin da matasanmu suke fuskanta na rashin ayyukan yi a wannan zamani.

     

    2. 0 Ƙasar Hausa da Mutanenta

    Yana da matuƙar muhimmanci kafin a tsunduma cikin wannan batu a bayyana inda ƙasar Hausa take da kuma mutanen da suke zaune a wannan wuri. Ƙasar Hausa ta asali tana a Afrika ta Yamma ne, a farfajiyar da ke tsakanin hamadar Sahara da dazuzzukan da suka doshi gaɓar tekun Atlantika daga kudu. Kuma ana kiran ƙasar da sunan Sudan ta Yamma, watau tsakanin Tafkin Cadi da gwiwar Kogin Kwara a can Yamma (Alhassan, 1981:1).

    A wata faɗar kuma an bayyana cewa Ƙasar Hausa tana shimfiɗe ne a can Arewacin Nijeriya da kuma kudancin Jamhuriyar Nijar a cikin Afrika ta Yamma. Daga Gabas ta yi iyaka da ƙasashen Borno. Daga Yamma ta yi iyaka da ƙasashen Dahomey a gaɓar Kogin Kwara. Daga Arewa ta yi iyaka da ƙasar Adar a cikin Jamhuriyar Nijar. Daga wajen Kudu kuma ta yi iyaka da ƙabilun Gwari da kuma ƙabilun kudancin Zariya da na Kudancin Bauci  (Ibrahim, 1982:1).

    A wannan zamani a iya cewa Ƙasar Hausa yanki ne wanda ya mamaye dukkan Jihar Katsina da Jihar Kano da Arewacin Jihar Kaduna da wasu ɓangarori na Jihohin Bauci da Gwambe da Neja da kuma kudancin Jamhuriyar Nijar. Idan aka tayar da saiti daga Arewa zuwa Kudu ƙasar Hausa ta fara daga Azbin har ya zuwa kusurwar Arewa maso gabas da tsaunukan Jos. Daga nan sai ta shararo ta yi Yamma har zuwa wurin da Kogin Kaduna ya yi wani babban doro. Daga nan kuma sai ta malala ta yi arewa maso yamma ta yi mahaɗa da ƙaton rafi na kogin Kabi. Daga wannan wuri sai ta karkata ta nufi arewa maso gabas har Azbin (Birnin-Tudu, 2002:11-12).

    Ƙasar Hausa wadda tana shimfiɗe a shiyyar Sudan ta Tsakiya, a tsari na gargajiya a iya cewa ta haɗa da ƙasashen sarakunan Katsina da Kano da Daura da Zazzau (idan aka ɗebe kudancin Zazzau) da Kabin Argungu da Gwandu da Gumel da Haɗejiya da Ƙwanni da Maraɗi da Tassawa.

    Idan muka juya kan mazauna ƙasar Hausa, a iya cewa mafi yawancin mazauna ƙasar Hausa al’ummar Hausawa ne, amma akwai wasu ƙabilu waɗanda suka yi ƙaƙa-gida waɗanda a yau wasunsu sun koma Hausawa a harshe da al’adu da adabi waɗanda suka haɗa da Fulani da Buzaye da Barebare da Nufawa da Yarabawa da sauransu. Shin su wanene Hausawa? Dangane da amsar wannan tambaya, za a ga cewa masana da manazarta daban-daban sun kawo ra’ayoyinsu kan waɗanda suke ganin cewa su ne Hausawa. A ra’ayin wani masani ya bayyana cewa Hausawa su ne mutanen da ke zaune a ƙasar Hausa tun tuni, kuma suna magana da harshen Hausa a matsayin harshen uwa (Ibrahim, 1982:1)

    Wani masanin kuma na ganin cewa,  Hausawa sun haɗa da mutanen nan waɗanda saboda ƙaura da magabatansu suka yi daga ƙasar Hausa zuwa wasu sassa da ke maƙwabtaka ta kusa ko ta nesa da ƙasar Hausa, ko da kuwa ba sa magana da harshen Hausa ko yin al’adun Hausawa sun ɗauka su Hausawa ne. Misali, Abakwariga da ke zaune a Jihar Taraba ta Nijeriya da kuma wasu da ke ikirarin cewa su Hausawa ne waɗanda ke zaune a ƙasashen Cote de Ɓoire da Burkina Faso da Mali ( Adamu, 1983:3).

    Akwai kuma waɗanda saboda da ƙaura da magabatansu suka yi zuwa ƙasar Hausa sun manta da harshensu da adabinsu da al’adunsu na asali sun ɗauki na Hausawa. A taƙaice sun koma Hausawa a harshe da adabi da al’ada. Misalin ire-iren waɗannan mutane sun haɗa da Barebari da Kanbarin Barebari da Barebarin Katsina da Buzaye da wasu Fulani (Sallau, 2000:71).

    Wani masanin kuma ya bayyana cewa Hausawa dai su ne mutane waɗanda harshensu shi ne Hausa sannan dukkan al’adunsu da ta’addunsu na Hausa. Haka kuma addinin Musulunci ya yi cikakken tasiri a kansu ( Magaji, 1986:3).

     

    3. 0 Sana’o’in Gargajiya na Hausawa a Jiya

    Al’ummar Hausawa kamar kowace al’umma tana da manyan hanyoyi da dama waɗanda suke taimaka wa tattalin arzikinta bunƙasa wato sana’o’in gargajiya. Daga cikin waɗannan hanyoyi akwai waɗanda aka gada tun iyaye da kakanni, wato su ne na asali. Ire-iren su sun haɗa da noma da kiwo da fatauci da sana'o'in gargajiya. A jiya waɗannan sana’o’i sun taimaka wa al’ummar Hausawa samun zaman lafiya da kwanciyar hankali da ƙaruwar arziki don kuwa kowa ya ɗauki irin sana’ar da ya gada ko yake yi da matuƙar muhimmanci saboda tana biya masa bukatunsa na yau da kullum ba tare da ya dogara ko yin maula wurin wani mutum ba. Wannan dalili ne ya sa kowane gida yana gudanar da ɗaya ko wasu daga cikin waɗannan sana’o’i kuma da yaro ya fara girma za a fara koya masa wannan sana’a yadda idan ya girma zai dogara da kansa.

     

    3. 1 Noma

    Hausawa suna yi wa noma kirari da suke cewa, “noma na duƙe tsohon ciniki kowa ya zo duniya kai ya tarar”. Wannan kirari na bayyana sana’ar noma daɗaɗɗiya ce a wannan duniya ba wai ga Hausawa kaɗai ba. Wannan ne ya sa idan ana maganar tattalin arzikin ƙasar Hausa, noma ne za a fara kawowa don kuwa shi ne ƙashin bayan tattalin arzikin wannan ƙasa. Wannan kuwa ya faru ne saboda sana’a ce wadda kowa-da-kowa yake yi talaka da saraki, attajiri da matalauci, maza da mata, babba da yaro don a sami abincin da za a ci da kuma wanda za a sayar don yin hidimomin yau da kullum. A faɗar Dr. Barth cikin shekarar 1850 lokacin da ya kusa isowa Katsina daga Tassawa ta cikin Jamhuriyar Nijar a yau, ya bayyana cewa, da wuya ka ga saura domin kuwa dukkan filayen an shuka amfanin gona na ci ko na kaiwa kasuwa waɗanda suka haɗa da dawa da gero da taba da makani da dankali da wake da auduga da sauran abubuwa (Adamu, 1978:10).

    Saboda haka ne, manoma a dukkan faɗin ƙasar Hausa da kewayenta suke samun wurare masu nagarta waɗanda suka haɗa da fadama da jigawa don noma amfanin gona mai kyau. Al’ummar Hausawa na yin noma iri biyu, na ci da na sayarwa. Kayan noma na abinci sun haɗa da gero da dawa da masara da maiwa da dai sauransu, na sayarwa kuma sun haɗa da auduga da gyaɗa. Haka kuma, ƙasar Hausa tana da albarkar da ake noma wasu abubuwan kamar rogo da dankali da sauransu (Nadama, 1977:90 – 92).

     

       3. 2 Kiwo

    Kasancewar ƙasar Hausa shimfiɗaɗɗiya ce ga kuma sarari da ciyayi a ko’ina ya sa kusan a kowane gida ana kiwon dabbobi ko tsuntsaye. Hausawa na tsare dabbobi da tsuntsaye a gidajensu ta hanyar ba su abinci ko kuma a kora su zuwa daji don su nemi abinci a can. Ire-iren dabbobin da Hausawa suke kiwo sun haɗa da shanu da tumaki da awaki don cin namansu da kuma sayarwa. Haka kuma, ana sayar da fatunsu da ƙiragansu don yin amfani da su. Ana kuma ɗaukar kashin da suka yi don kaiwa gona a matsayin takin da zai ƙara wa gona albarkar ƙasa. Bayan waɗannan dabbobi, Hausawa na kiwon dawaki don hawa na ƙawa da jin daɗi. Haka kuma, suna kiwon jakuna da alfadarai don ɗaukar kaya da yin wasu ayyuka irin su fatauci. Ire-iren waɗannan dabbobi dukkansu ana kiran su da sunan dabbobin gida.

    Bayan dabbobi Hausawa suna kiwon tsuntsaye irin su kaji da agwagi da zabi don cin namansu da ƙwayayensu da kuma sayarwa. Haka kuma, saraki da attajirai suna kiwon tsuntsaye na alfarma irin su aku da ɗawisu da kanari don sha’awa da nishaɗi.

     

    3. 3 Fatauci 

     Tun kafin wannan zamani al’ummar Hausawa suna da irin nasu tsari wajen tafiyar da harkokin kasuwanci. Wannan tsari ana iya dubansa ta fuska biyu, kasuwancin cikin gida da kuma na waje. A cikin gida akwai kasuwanni na garuruwa waɗanda ake tafiyar da harkokin kasuwanci ta hanyar furfure. A irin wannan kasuwanci ana musayar abubuwan sayarwa ne, misali manomi ya ba masaƙi kayan gona don ya amshi kayan saƙa, ko ya ba makiyayi don ya amshi wata dabba da sauransu. An daɗe ana yin irin wannan tsari na cinikayya a ƙasar Hausa har zuwa cikin ƙarni na goma sha takwas da aka shigo da hanyar yin amfani da kuɗin wuri da biringizau don yin saye da sayarwa a duk faɗin Afrika ta Yamma (Nadama, 1977:137 – 138).

    Ta fuskar kasuwancin wajen ƙasar Hausa ‘yan kasuwa daga ƙasar Hausa na yin fataucin kayayyaki daga wannan ƙasa zuwa garuruwan Adar da Azben da Nufe da ƙasashen Yarabawa da Gwonja. Bayan sun sayar da kayayyakinsu a can, suna kuma sawo wasu kayayyakin daga waɗannan ƙasashe su kawo ƙasar Hausa don su sayar. Ire-iren kayayyakin fatauci da suka riƙa saye daga ƙasar Hausa suna kaiwa waɗannan ƙasashe, sun haɗa da daddawa da kayayyakin sutura irin waɗanda aka saƙa a ƙasar Hausa da kuma shunin gadi da baba da dabbobi da sauransu. Haka kuma, suna sawo kayayyaki irin su bindigogi da kayan albarushi da riguna girken Nufe da kayan ƙarau daga ƙasar Nufe. Suna kuma sawo balma da kanwa da dabino da dawakin Azbin da awaki da tumaki da raƙuma daga ƙasashen Adar da Azbin da kuma Borno. ’Yan kasuwar da suke zuwa fatauci kudu watau ƙasashen Yarabawa da Gwonja suna sawo goro don kawowa ƙasar Hausa da maƙwabtanta na arewa don sayarwa (Nadama, 1977:142 – 143).

     

    3. 4 Sana'o'in Gargajiya

    Kafuwar garuruwa a ko’ina cikin ƙasar Hausa da kuma bunƙasar da noma ya samu ya ƙara taimakawa wajen samuwar sana'o'in gargajiya inda ake ƙera da kuma sarrafa kayayyaki iri daban-daban domin amfanin mutanen ƙasar Hausa da maƙwabtansu na kusa da kuma na nesa. Ire-iren waɗannan sana'o'i sun haɗa da ƙira da saƙa da rini da jima da dukanci da sassaƙa da sauransu. Akwai kuma sana'o'in da ake yin ayyukan taimaka wa rayuwa kamar wanzanci da fawa da ɗori da sauransu. Bayan waɗannan akwai ƙananan sana'o'i waɗanda mata suke tafiyar da su kamar kaɗi da kitso da koda da dakau. Waɗannan sana'o'i na gargajiya sun taimaka matuƙa gaya wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasar Hausa. Yanzu za a ɗauke su ɗai-ɗai da ɗai-ɗai domin ganin yadda suka taimaka wa tattalin arzikin ƙasar Hausa.

     

    3. 4. 1 Ƙira

    Yana da matuƙar wuya a ce ga lokacin da Bahaushe ya fara narka tama ya mayar da ita ƙarfe don yin amfanin yau da kullum da shi, amma duk da haka nan, an ɗan sami haske wanda ya bayyana cewa, al’ummar Hausawa sun ƙware wajen narka tama a mayar da ita ƙarfe wanda ake sarrafawa zuwa abubuwan amfanin gida da makamai da kayayyakin aikin gona da na kwalliya. Misali, a cikin shekarar 1992 wasu manazarta tsofaffin kayayyakin da aka bizne daga ƙasar Jamus ƙarƙashin shugabansu Dr. G. Liesegang tare da haɗin gwiwar Hukumar Kula da Ɗakunan Adana Kayan Tarihi da Tsofaffin Wuraren Tarihi, da kuma Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al’adu ta Jihar Katsina sun gudanar da bincike a ƙaburburan da suke a Durɓi ta Kusheyi da ke Ƙaramar Hukumar Mani ta Jihar Katsina inda suka tono kayayyaki masu tarin yawa waɗanda maƙeran ƙasar Hausa suka ƙera shekaru ɗaruruwa da suka gabata waɗanda suka haɗa da mundaye da bokiti wanda ya yi kamanni da irin bokitin wannan zamani da sauran kayayyakin ado waɗanda aka samu a wurin ƙwarangwal ɗin mutumen da aka rufe a wannan ƙabari (Mahuta, 1992:2-5).

    A yanzu waɗannan kayayyaki an gudanar da bincike a kan su a ƙasar Jamus inda aka gano yawan shekarunsu a cikin waɗannan ƙaburbura, kuma an maido su Katsina an ajiye su a Hukumar Kula da Ɗakunan Adana Kayan Tarihi da Tsofaffin Wuraren Tarihi a Tsohuwar Kwalejin Katsina da ke Ƙofa – Uku, Katsina (Liesegang, 2012:83-97).

    Ƙira sana’a ce wadda aka fi yi a lokacin rani domin tanadar kayan aikin noma, amma duk da haka ana yin ta a kowane lokaci na shekara domin samar da kayan amfanin gida na yau da kullum. Maƙera sun kasu zuwa kashi biyu, akwai maƙeran baƙi da maƙeran fari. Maƙeran baƙi su ne suke tono tama su narka ta don ta zama ƙarfe wanda suke amfani da shi domin yin nau’o’in kayan ƙira. Ire-iren kayayyakin da maƙeran baƙi suke yi sun haɗa da fartanya da masassabi da gatari da lauje da sungumi da adda da dai sauransu domin yin ayyukan gona. Haka kuma maƙeran baƙi suna ƙera takubba da gariyo da tsitaka da masu da kibau da sauran kayayyakin da ake amfani da su wajen yin farauta da yaƙi. Bayan waɗannan suna yin kalaba da wuƙaƙe ƙanana da manya waɗanda ake amfani da su wajen yin ayyukan cikin gida na yau da kullum. Haka kuma su ne suke samar da kayan aikin wanzanci waɗanda suka haɗa da asake domin yin aski da kaciya da kuma kalaba wadda ake amfani da ita wajen cire belun-wuya. Suna kuma yin askar tsaga wadda ake amfani da ita wajen cire angurya a farjin mata da yin tsagar gado da ta magani da ta kwalliya da sauransu.

     

    3. 4. 2 Saƙa

    Saƙa sana’a ce wadda ake sassarƙa zare ko gashi ko ɓawo ko kaba don a mayar da su wani abu mai faɗi kamar tufafi ko shimfiɗa. Saboda haka a iya cewa, saƙa ta kasu zuwa iri biyu, ta tufafi da ta kayan shimfiɗa. Ana amfani da zaren auduga ne wanda mata suke kaɗawa domin saƙar tufafi. Masaƙa wato masana’antar da ake sarrafa zare domin yin sutura ita ma ta kasu zuwa iri biyu. Akwai masaƙar tsaye wadda mafi yawanci mata ne suke amfani da ita don yin saƙar gwado ko zanen kujera ko ɗan goyo wanda ake goya jarirai. Akwai kuma masaƙar zaune wadda maza ne suka fi yin amfani da ita wajen yin saƙar sauran abubuwa.

    Hakika wannan sana’a tana da matuƙar muhimmanci a ƙasar Hausa domin kuwa ba domin ita ba da an riƙa tafiya tsirara. Wannan a fili yake, sutura ita ce alamar da take bayyana bambanci a tsakanin mutum da dabba. A cikin mutane ma da sutura ake iya rarrabe bambancin al’adu. Da ita ake gane cikakken mutum da akasinsa. Haka kuma da ita ake sanin mawadaci da mabuƙaci. Masana’antar saƙa ta taimaka sosai wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasar Hausa. Wannan kuwa ya samu ne sakamakon kayayyakin da ta riƙa samarwa waɗanda ake sayarwa a kasuwannin cikin gida da na ƙasashe maƙwabta (Alhassan, 1982:52-54).

    3. 4. 3 Jima

    Jima sana’a ce wadda ake sulluɓe fata don a fitar da gashin da yake jikinta. A irin wannan masana’anta da ake kira majema ana sauya fata daga halinta na asali na gashi da kaushi a sarrafa ta, a gyara ta yadda za ta yi laushi kamar sutura wadda a wancan zamani ake kiran ta ‘yar Morocco (Rodney, 1972:50).

    Bayan an gyara fata ta yi kyau ana sayar da ita ga dukawa, kuma mafi yawancin fatar da aka gyara tana daga cikin manyan muhimman hajoji da ake safararsu daga ƙasar Hausa zuwa ƙasashe maƙawabta na kusa da na nesa. Ana yin wannan safara tun lokaci mai tsawo da ya gabata kafin shigowar Turawa wannan ƙasa. Irin wannan fata na daga cikin kayayyakin da aka riƙa fataucinsu daga Kano da Katsina da Zamfara da Sakkwato ana ƙetare hamadar Sahara da su ana kaiwa Morocco da sauran ƙasashen da suke arewacin Afrika ana sayarwa. Daga nan ne kuma Turawa suke sayen ta su kai ƙasashensu inda suke sarrafa ta domin yin jikunkuna da takalma da riguna maganin sanyi da sauran abubuwa waɗanda kuma suke kawo wasu daga cikinsu zuwa ƙasashen Afrika da sauran ƙasashen duniya don sayarwa (Nadama, 1977: 109-110).

     

    3. 4. 4 Dukanci

    Dukanci sana’a ce wadda ake sarrafa fata don mayar da ita wani abu na amfanin yau da kullum. Ire-iren abubuwan da dukawa suke yi sun haɗa da jikunkuna da takalman fata da igiyar linzamin doki da burgami da zabira wadda ake zuba kayan wanzanci da jakar zuba ma dawaki dawa ko dusa. Haka nan kuma suna yin warki da gafaka da tandun kwalli da kuben wuƙa da na takobi da sauran abubuwa.

    Bayan dukawa sun yi waɗannan abubuwa suna sayar da su ne ga waɗanda suke buƙata da kuma masu yin sari waɗanda suke kaiwa kasuwanni na cikin gida da na waje. Haka kuma ‘yan kasuwa na waje na shigowa cikin ƙasar Hausa don sayen ire-iren waɗannan kayayyaki da dukawa suka sarrafa. Wannan masana’anta ta dukanci ta bayar da gagarumar gudummuwa wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasar Hausa.

     

    3. 4. 5 Rini

    Rini na nufin sauya launin tufa ko zare don ya zama wani iri. Ana kiran masana’antar da ake yin rini marina. Abubuwan da ake amfani da su wajen yin rini sun haɗa da muciya da kwatarniya da guga da itace da ƙaiƙayi da ɗan kutuɓu da baba da katsi da shuni da zarta da marina da ruwa. Wannan masana’anta ta taimaka sosai wajen bunƙasa tattalin arzikin ƙasar Hausa. An fahimci haka ne kuwa ta la’akari da kayan rini irin na ƙasar Hausa na daga cikin muhimman abubuwan da fatake suke yin safararsu daga ƙasar Hausa zuwa ƙasashen maƙwabta don sayarwa.

     

    3. 4. 6 Sassaƙa

    Sassaƙa sana’a ce wadda ake gyara icce don a mayar da shi wani abu na amfani. Masassaƙan ƙasar Hausa na sassaƙa turmi da taɓarya da kujerar zama ta mata da kujerar gwado ta maza da ƙotar fartanya da ta masassabi da ta gatari da ta garma. Haka kuma masassaƙa suna sassaƙa akushi da ƙoshiyar dama fura da ludayin itace da allunan karatun Alƙur’ani mai girma da dai sauran abubuwa masu yawan gaske.

    Wannan sana’a ta sassaƙa tana taimaka wa tattalin arzikin ƙasar Hausa matuƙar gaske. A iya ganin haka ta yadda take samar da wasu kayan aiki ga sauran masana’antun gargajiya. Misali, manoma na amfani da ƙotoci, wanzamai na amfani da ƙoshiya don cire belun-wuya, makaɗa na amfani itacen da ake yin kayan kiɗa, masaƙa na amfani da gwafa wadda ake kafa masaƙa ta zaune da ta tsaye da sauran abubuwa.

     

    3. 4. 7 Wanzanci

    A Hausance, sana’ar “wanzanci” tana nufin amfani da askar aski domin yin aski da gyaran fuska da yin kaciya da kuma amfani da kalaba da ƙoshiya don cire belun-wuya. Sana’ar wanzanci ba ta tsaya a nan ba don kuwa ana amfani da ‘yar tsaga don yin ƙaho da cire angurya a farjin mata da yin tsagar gado da ta kwalliya da ta magani. A sana’ar wanzanci dai ana yin hujen kunne da yanke yatsan cindo (shiddaniya) da yanke linzami a cikin bakin jarirai da wasu ayyuka da dama. Haka kuma masu yin sana’ar wanzanci na bayar da magungunan gargajiya ga waɗanda suke buƙata.

    A taƙaice a iya cewa sana’ar wanzanci ta taɓo aikin likita a ƙasar Hausa kafin zuwan asibitin zamani. Dalili kuwa shi ne wani daga cikin ayyukan wanzanci shi ne kula da lafiya musamman ta jarirai da ƙananan yara, ta wani fannin ma har da lafiyar manya. Masu yin ire-iren waɗannan ayyuka ana kiran su wanzamai waɗanda dole su kasance masu cikakkiyar lafiya, masu hankali da natsuwa.

    A mafi yawanci maza ne suke yin sana’ar wanzanci, amma ana samun wasu mata waɗanda saboda rashin wani namiji a gida, ko kuma don wani dalili sukan koyi wannan sana’a daga mahaifansu. Ana gadon wannan sana’a a wajen iyaye ko kakanni na wajen uba. A gargajiyance yana da matuƙar wuya a sami wani mutum wanda bai gaji wannan sana’a ba yana yin dukkan ayyukan wanzanci. A wannan zamani ana samun waɗanda kan koyi yin askin zamani na saisaye wanda suke yi da kayan askin zamani, amma iyakarsu askin don kuwa ba sa iya yin sauran ayyukan wanzanci. Haka kuma wajen yin ayyukan wannan sana’a gado na taka muhimmiyar rawa, don kuwa kowane wanzami yana da gidajen da yake zuwa don gudanar da ayyukansa. Wani wanzami daban ba ya zuwa gidan da wani wanzami ɗan'uwansa yake yin aiki ya yi. Kowane gida ko zuri’a suna da wanzamin da suka gada wanda yake yi masu aiki, daga shi sai ‘ya’yansa ko wani da ya wakilta ne kaɗai suke iya zuwa waɗannan gidaje nasa don yin waɗannan ayyuka. Haka su ma masu gidajen ba sa kiran wani wanzami daban don yin ayyukan wanzanci a gidajensu dole sai wanda suka gada tun asali daga iyayensu.

     

    3. 4. 8 Fawa

    Fawa sana’a ce wadda ake sayen dabbobi a yanka don samar da nama ga al’umma. Mafauta suna sarrafa nama ta hanyoyi daban-daban waɗanda suka haɗa da balangu da tsire da kilishi da ragadada da sauransu. Masu yin wannan sana’a suna taimaka wa al’umma ta hanyoyi dadama waɗanda suka haɗa da sayen dabbobi daga wurin waɗanda suke yin kiwo da kuma sarrafa naman dabbobin ɗanye ko gasasshe don sayarwa ga masu bukata. Wannan dalili ne ya sa wannan sana’a take cikin manyan sana’oin gargajiya na Hausawa masu yin ta suka shahara, kuma ana yin fataucin naman da aka sarrafa musamman kilishi zuwa sassan da ke maƙwabta da ƙasar Hausa ta kusa ko ta nesa.

     

    3. 4. 9 Ɗori

    Sana’ar ɗori na daga cikin sana’o’in gargajiya na Hausa da suka shahara a jiya wajen kula da lafiyar al’ummar ƙasar Hausa da ma maƙwabta, don kuwa a wancan zamani idan ƙashin mutum ya kare ko ya goce ko kuwa ya sami targaɗe a wata mahaɗar ƙashinsa idan aka kira masu yin ɗori za su ɗora shi ko su gyara wurin da raunin yake ya kuma warke cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ba tare da fuskantar wata matsala ba. Wannan kuwa ya faru ne saboda waɗanda suka gaji yin wannan sana’a sun tsaya sun koya wurin mahaifansu kamar yadda su ma mahaifan nasu suka koya daga wurin nasu mahaifan.

     

    3. 4. 10 Sana’o’in Mata

    Bayan waɗannan sana’o’i waɗanda mafi yawancinsu maza ne suke aiwatar da su, akwai waɗanda mata ne kawai suke yin su kamar kaɗi, wanda ake yi don samar da zare da abawa ga masu yin sana’ar saƙa. Haka kuma, mata ne suke yin sana’ar kitso ga ‘yan’uwansu mata. Suna yin salon kitso iri-iri don yin kwalliya ga kan mata wanda yake ƙara masu kyau da jawo hankalin maza. Akwai kuma sana’ar dakau wadda mata suke amso hatsi don yin dakau na fura ko garin da za a yi amfani da shi don yin abinci. Haka kuma, mata na yin sana’ar koda wato sussuka hatsi, gero ko dawa ko masara ko shinkafa don fitar da tsaba daga ƙaiƙai. Waɗannan sana’o’i na mata suna taimaka masu yin hidimominsu na yau da kullum da kuma yin bikin dangi ba tare da sun dogara kan wani ba.

     

    4. 0 Matsayin Sana’o’in Gargajiya na Hausawa a Yau

    Matsayin sana’o’in gargajiya na Hausawa a yau na cikin wani hali na ƙaƙa-ni-ka-yi don kuwa ba kamar a jiya ba da kowa da kowa ya dogara a kansu, a yanzu ire-iren waɗannan sana’o’i sun zama abin ƙyama ga matasan wannan zamani. Wannan kuwa ya faru ne saboda matasa sun fi son yin ayyuka a ma’aikatu da hukumomi da kamfanonin da Turawa suka kawo ƙasar Hausa waɗanda za a iya samun kuɗi cikin ɗan ƙanƙanin lokaci ba kamar a ire-iren sana’o’in gargajiya na Hausawa waɗanda abin da ake samu bai taka kara ya karye ba, sai dai yana biyan bukatun yau da kullum na masu yin waɗannan sana’o’i.

    Idan muka ɗauki sana’o’in gargajiya na Hausawa a yau za a fahimci cewa sun shiga wani hali na taɓarɓarewa wanda ya faru saboda matasan wannan zamani ba su koyi yin su ba. Misali, sana’ar noma wadda kowane mutum a ƙasar Hausa a jiya ya dagara a kanta domin samun abin da za a ci da kuma sayarwa, a yau matasanmu na ƙyamar yin wannan sana’a wanda wannan dalili ne ya haifar da ƙarancin abinci a wannan zamani. Wannan kuwa ya faru ne saboda yawan masu cin abinci ya nunka yawan masu yin sana’ar noma a yau. Wannan ba ƙaramar matsala ce ga Hausawa ba don kuwa har yanzu ci gaban ƙasar Hausa bai kai matakin yin noman zamani ba, an dogara ne da abincin da aka noma ta hanyar noma irin na gargajiya.

    A ƙasar Hausa a jiya ta fuskar kiwon lafiya masu gudanar da sana’o’in gargajiya sun taka muhimmiyar rawa wajen bayar da magungunan cututtuka iri daban-daban, don kuwa wanzamai da maɗora da maƙera da mahauta da sauransu sun taimaka matuƙa gaya wajen bayar da magungunan cututtuka iri daban-daban. A yau saboda matasan wannan zamani ba su mayar da hankali wajen yin waɗannan sana’o’i ba mahaifansu waɗanda suka naƙalci waɗannan magunguna ba su sanar da su ba. Wannan dalili ne ya sa a yau ire-iren waɗannan magunguna sun ɓata saboda waɗanda suka san su sun mutu ba tare da sanar da wani ba. A yau idan wata cuta ta kama mutum wadda a da can masu sana’o’in gargajiya na iya warkar da ita, sai a ce a tafi Amurka ko Turai ko Misra domin neman magani. Misali, a da can duk irin yadda ƙashin mutum ya kare maɗoran ƙasar Hausa na iya ɗora shi, amma a yau saboda matasanmu ba su mayar da hankali suka koyi yadda ake yin wannan sana’a ba, idan an yi kariya kome ƙanƙantarta, sai a ce a tafi asibitin ƙashi ko kuma a kai wannan mutum ƙasar Misra. Wannan hali na ko in kula da matasan ƙasar Hausa suka ɗauka ba ƙaramin koma baya ya kawo wa ƙasar Hausa ba a wannan zamani.

     

    4. 1 Ƙalubalen da ke Gaban Matasan Hausawa a Wannan Zamani

    A wannan takarda idan an ce matasa ana nufin samari ko ‘yanmata majiya ƙarfi waɗanda shekarunsu na haihuwa suka fara daga goma sha shida zuwa talatin da biyar. A kowace al’umma wannan rukuni na taka muhimmiyar rawa wajen kawo ci gaba da bunƙasar wannan al’umma ta fannoni daban-daban, don kuwa su ne suke amfani da ƙarfinsu da hikimominsu da dabarunsu su kare al’ummarsu daga kowane irin hari daga abokan gaba ko hamayya, kuma su ne manyan gobe wato waɗanda za su jagoranci wannan al’umma shekaru masu zuwa. Haka kuma, su ne suke gaba-gaba wajen tafiyar da harkokin tattalin arzikin al’ummomin da suka fito.

    Kamar yadda aka bayyana a bayanin da ya gabata, kowane gida a ƙasar Hausa yana gudanar da wata daga cikin sana’o’in gargajiya na Hausawa kuma suna koya wa ‘ya’yansu don su sami abin dogaro da kai, a wannan zamani al’amarin ya sauya. Dalili kuwa shi ne, shigowar Turawa da kawo ilimin zamani da suka yi wanda ya haifar da samuwar ayyuka a ma’aikatun gwamnati da kamfanoni ya sa matasan ƙasar Hausa yin watsi da sana’o’in gargajiya da suka gada suka fifita ire-iren waɗannan ayyuka kan waɗannan sana’o’i. Da tafiya ta tafi, sai aka sami ƙaruwar ‘yan makaranta waɗanda suka kammala karatun sakandare da na gaba da sakandare da Jami’o’i. Dalilin haka an sami ƙaruwar matasa masu neman ayyuka a waɗannan ma’aikatu wanda ya haifar da raguwar guraben ayyuka a waɗannan ma’aikatu. Haka kuma, saboda wasu dalilai waɗannan ma’aikatu kan rage ma’aikata ko ma su kore su daga aiki, wannan ne ya sa a wannan zamani aka sami cunkoson matasa masu neman aiki, kuma ba guraben da za a ɗauke su, sai wasu daga cikinsu suka kama sana’ar da tafi noma wuya watau maula, wasu kuma suka zama ‘yan bangar siyasa, ‘yan mata kuma suka shiga sana’ar karuwanci, kai wasu ma sai suka kama sace-sace da fashi da makami da ta’addanci. Abin kunya za ka iske daga cikin ire-iren waɗannan matasa akwai waɗanda suka fito daga gidaje waɗanda suka ƙware a ɗaya daga cikin waɗannan sana’o’i, amma saboda ba su tsaya suka koya ba, idan za ka zaunar da ɗaya daga cikinsu, ka ce masa ya bayyana maka ire-iren kayayyakin da ake amfani da su wajen yin wannan sana’a, ba ma yadda ake yin wannan sana’a ba, ba zai iya ba, sai dai ya yi ta ‘yan kame-kame. Wannan ba ƙaramin ƙalubale ba ne ga matasan Hausawa a wannan zamani.

    Dangane da wannan al’amari matuƙar muna son mutuncinmu da arzikinmu da ɗaukakar da Allah Ya yi wa al’ummar Hausawa ta dawo yadda za mu sami ci gaba mai ɗorewa, dole ne mu koma wa sana’o’inmu na gargajiya, mu yi amfani da ilimin zamani da muka koya, mu haɓaka su yadda za su tafi daidai da zamani. Haka kuma, ina kira ga matasanmu da su yi koyi da ni, don kuwa ni na fito daga gidan da suka gaji yin sana’ar wanzanci, mahaifina ya koya min har sai da ya tabbatar da na fahimci yadda ake yin wannan sana’a, ya kuma sanya ni makarantar zamani har sai da na kammala karatun digiri na uku (Ph. D. ), a yanzu kuma na kai muƙamin Ɗangaladiman Farfesan Al’adun Hausawa a Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya a Jami’ar Umaru Musa Yar’adua da ke Katsina, amma duk da haka ban ƙyamaci yin wannan sana’a ba. Wannan dalili ne ya sa mahaifina ya yi murabus daga sarautar Sarkin Askar Yariman Katsina Hakimin Safana, ya amince Maigirma Yariman Katsina ya naɗa ni wannan sarauta, na gaje shi a ranar 14 ga watan Disamba, 1996. Haka kuma, Maigirma Gwamnan Jihar Katsina, Rt. Hon. Aminu Bello Masari, ya ba ni shugabancin Hukumar Binciken Tarihi da Kyautata Al’adu ta Jihar Katsina a ranar 19 ga Watan Agusta, 2015.

    Saboda riƙo da wannan sana’a ta wanzanci na cim ma nasarori da ɗaukaka a wannan zamani don kuwa na shiga cikin wasu matsaloli waɗanda Allah cikin ikonsa ya sa na warware su ta hanyar yin sana’ar wanzanci.

    Da farko a shekara ta 1984 lokacin ina ɗalibi a Kwalejin Ilimi ta Kafanchan, mun fuskanci matsalar rashin kuɗi saboda Hukumar da ke tallafa wa ɗalibi ba su ba mu tallafin wannan shekara da wuri ba. Wannan dalili ya sa ɗalibai shiga cikin mummunan hali na rashin abin da za a ci, a wannan lokaci sai na tuna na zo da zabira ta. Daga nan duk lokacin da muka gama darasi sai in ɗauki zabira ta in shiga gari. Cikin ɗan ƙanƙanen lokaci sai in samo kuɗin da zan sayi abinci har in taimaka wa abokai na waɗanda muke zaune tare. Babbar sa’ar da na ƙara samu ita ce, a garin Manchok inda makarantarmu take babu wanzami, idan aka yi masu haihuwa ko za a yi wa yara kaciya sai an je Zangon-Kataf a kira wanzami, amma tun da na fito da kaina da yin wannan sana’a, idan an haihu ko za a yi wa yara kaciya sai su kira ni in yi masu. Wannan ya sa na zauna lafiya ba tare da fargabar abincina zai ƙare ko in rasa kuɗin yin bukatuna a zama na wannan makaranta.

    Al’amari na biyu ya faru ne a shekara ta 1993 lokacin da Allah Ya ba ni ikon zuwa aikin Hajji, a rana ta goma ga watan Zul-Hajji ranar da ake yi wa Alhazai aski, a nan ma na fitar da maita ta fili, don kuwa na fito da kayan askina don yi wa Alhazai aski. Da mutane suka fahimci na iya aski, kuma nan da nan sai in gama ma mutum ba tare da na yanke shi, sai Alhazai suka taru wurina inda na yi aski har na gaji. A wannan rana da na tashi na ƙirga kuɗin da na samu na kuma juya su zuwa kuɗin Nijeriya, sai na ga na kusa mayar da kuɗin da na biya domin zuwa aikin Hajji. Washegari da na ci gaba, lokacin da na tashi na haɗa abin da na samu a wannan ranar da waɗanda na fara samu, sai na ga na mayar da dukkan kuɗin da na biya don zuwa aikin Hajji har ma na ci riba. A lokacin da nake aski ne sai na ji wasu Alhazai na magana ƙasa-ƙasa suna cewa, wancan wanzamin da kuke gani fa digiri gare shi, amma duk da haka bai jin kunyar yin aski. Da suka fahimci na ji abin da suke faɗa, sai ɗaya daga cikinsu a kunyace ya tambaye ni “Wai Alhaji gaskiya ne kana da digiri amma kuma kake aski? Sai na amsa masa da cewa, “Ƙwarai kuwa!”. Daga nan ne zumunci ya ƙullu tsakanina da su. Daga cikinsu akwai wani ma’aikacin gidan talabijin na jihar Katsina mai suna Alhaji Kabir Yusuf ‘Yar’aduwa, da aka dawo gida Nijeriya ya sa aka kira ni inda aka yi hira da ni a wannan gidan talabijin dangane da yadda ake yin aikin wanzanci.

      Al’amari na uku wanda ya faru da ni na kuma sami cin nasara ya faru ne a shekara ta 2006 lokacin da Allah Ya ƙara ba ni ikon komawa Makka don yin aikin Hajji. A wannan shekara Alhazai sun daɗe Makka ba a maido su gida ba, wannan ne ya sa guzurin mafi yawancin Alhazai ya ƙare wanda ya kai ga matakin wasu suna fito da kayan tsaraba suna sayarwa. A nan na sayar da halin nawa inda a kullum sai in fito da kayan askina don yi wa masu son aski da gyaran fuska. A kullum ina samun kuɗin da zan sayi abinci har in taimaka wa waɗanda muke tare.

    Wani al’amarin da ya faru da ni wanda Allah Ya taimake ni zauna lafiya saboda riƙo da sana’ar wanzanci shi ne, a shekara ta 2009 na rasa aikina a Jami’ar Umaru Musa Yar’adua, Katsina. Sai da na yi shekara biyu da wata uku ba ni aikin gwamnati ko na kamfani, amma ina yin sana’ar wanzanci, wadda ta wannan hanya ce na riƙe matana huɗu da ‘ya’ya ashirin da bakwai da tsoffina da wasu dangina da ‘yan cin arziki.

     

    4. 2 Shawarwari

    Hausawa na cewa, kayan aro ba su rufe katare, haka kuma, ranar a tafi tare mai rigar aro gida ake barinsa. Dangane da wannan babbar matsala da al’ummar Hausawa suke fuskanta a wannan zamani, matuƙar ana son warware ta, dole ne a waiwayi sana’o’inmu na gargajiya a kakkaɓe dukkan wuraren da gara ta kama su, a yi masu kwaskwarima yadda za su tafi daidai da zamani, a kuma ba su irin muhimmanci da suke da shi kafin zuwan wannan zamani. Domin cimma nasara bisa ga wannan gagarumin aiki, ya dace a yi amfani da waɗannan shawarwari:

    1.      Ya dace gwamnati ta sa a binciko gidajen da suka shahara wajen gudanar da waɗannan sana’o’i ta taimaka musu farfaɗo da waɗannan sana’o’i.

    2.      A sanya koyar da sana’o’in gargajiya na Hausawa cikin Manhajar karatun jihohin Arewacin Nijeriya tun daga Firamare zuwa Jami’a.

    3.      Ƙirƙiro gasa nuna ƙwarewa a sana’o’in Gargajiya don zaɓar waɗanda suka ƙware don ba su wata kyauta wadda za ta ƙara jawo hankalin al’ummar Hausawa rungumar sana’o’insu na Gargajiya.

    4.      Kafa wata hukuma wadda za ta riƙa kula da harkoki da gudanar da sana’o’in gargajiya na Hausawa yadda za su tafi daidai da zamani.

    5.      Ko kuma, a ƙara wa Hukumomin Binciken Tarihi da Kyauta Al’adu na jihohi ƙarfi yadda za su riƙa kula da yadda ake gudanar da sana’o’in gargajiya na Hausawa a wannan zamani.

     

    Kammalawa

    Hakika gaskiya ɗaya ce, idan aka bi ta a zauna lafiya, idan kuwa aka kauce mata sai a ɓace. Za a iya ganin gaskiyar wannan magana idan aka alaƙanta ta da matsayin sana’o’in gargajiya na Hausawa a wannan zamani dangane da yadda wasu suka taɓarɓare wasu suka durƙushe yadda ba a ma ko jin ɗuriyarsu. Wannan kuwa ya faru ne saboda halin-ko-in-kula da matasan ƙasar Hausa suke nunawa na ƙyama da ƙin yin waɗannan sana’o’i. Yana da matuƙar muhimmanci a sani ƙasashen da yau ake cewa sun ci gaba ta fuskokin rayuwar wannan zamani, ba haka nan ci gaba ya zo masu ba, sun same shi ne ta hanyar bunƙasa abubuwan da suka gada, suka bunƙasa su yadda za su tafi daidai da zamani da suke ciki. Saboda haka, yana da kyau a sani cewa, matuƙar muna son irin wannan ci gaba, dole ne mu koma wa abubuwan da muka gada mu bunƙasa su yadda za su tafi daidai da zamani.

    Manazarta

    Adamu, M. (1974) “The Hausa Factor in West African History”, Unpublished Ph. D. Thesis. Birmingham: University, UK.

    Adamu, M. (1978) The Hausa Factor in West African History, Zaria/Ibadan: Ahmadu Bello University Press/Oɗford University Press of Nigeria.

    Alhassan, H. da wasu, (1982) Zaman Hausawa. Zaria: Institute of Education Press, ABU.

    Bargery, G. P. (1993) A Hausa – English Dictionary and English – Hausa Vocabulary, Zaria, ABU Press.

    Bunza, A. M. (1990) “Hayaƙi Fid da na Kogo (Nazarin Siddabaru da Sihirin Hausawa”, Kundin Digiri na Biyu. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

    Bunza, A. M. (2003) “In ba ka san Gari ba Saurari Daka: (Tarihin Adabin Magani da Bunƙasarsa)”, Jawabin Bukin Shimfiɗa Buzun Karatu. Sakkwato: Babban Kwamitin Kula da Bukukuwa da Tarukan Ƙara wa Juna Sani, Jami’ar Usmanu Ɗanfidiyo.

    Ibrahim, M. S. (1987) “Gudummuwar Sana’o’in Gargajiya na Hausa Wajen Farfaɗo da Tattalin Arzikin Nijeriya”, Maƙala: Kano. International Conference on Language, Literature and Culture, Organised by the Centre for the Study of Nigerian Languages, Bayero University.

    Ikime, O. (1977) The fall of Nigeria, the British Conƙuest, London: Heinemann.

    Liesegang, G. (2012) “The Eɗcaɓation at Takusheyi in 1992”, in Gold, Slaɓes and Iɓory, Medieɓal Empires in Northern Nigeria. Germany: RGZM.  

    Mahuta, I. A. (1992) “Eɗcaɓations at Durɓi-ta-Kusheyi – Its Significance to Katsina History, Internal Seminar Series, Katsina State History and Culture Bureau.

    Mani, A. (1966). Zuwan Turawa Nijeriya ta Arewa. Zaria: NNPC.

    Musa, R. (1983) “Wanzanci a Ƙasar Hausa: Asalinsa da Yanayinsa da Matsayinsa Jiya da yau”, Kundin Digiri na Ɗaya. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

    Nababa, I. D. (1997) Katsina State Historical Guide II: Crafts Deɓelopment, Produced by the Katsina State History and Culture Bureau: Katsina. Government Printer.

    Nadama, G. (1977) ” The Rise and Collapse of a Hausa State: A Social and Economic History of Zamfara”, Kundin Digiri na Uku. Zariya: Sashen Koyar da Tarihi, Jami’ar Ahmadu Bello.

    Rodney, W (1972) How Europe Underdeɓeloped Africa, London. Bogle- L ‘Ouɓerture.

    Sallau, B. A. S. (2000)”Wanzanci: Matsayinsa na Al’ada da Sana’a a Ƙasar Hausa”, Kundin Digiri na Biyu. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

    Sallau, B. A. S (2008) “Negligence of Traditional Occupations as a Contributing Factor in the Youth Unemployment in Northern Nigeria”, Being a Paper Presented at a 2 Day International Conference on Nigerian Youth, Political Participation and National Deɓelopment, on August 5 – 6, 2008: Kano. Organised by The Centre for Democratic Research and Training, Mambayya House, Bayero University.

    Sallau, B. A. S. (2009) “Sana’ar Wanzanci da Sauye – Sauyen Zamani Jiya da Yau”, Kundin Digiri na Uku. Kano: Sashen Koyar da Harsunan Nijeriya, Jami’ar Bayero.

    Sallau, B. A. S (2010) Wanzanci da Muhimmancinsa ga Rayuwar Hausawa. Kaduna: M. A. Najiu Professional Printers, No. 3 Kenya Road.

    Sallau, B. A. S (2010) Magani a Sha a yi Wanka a Buwaya. Kaduna: M. A. Najiu Professional Printers, No. 3 Kenya Road.

    Sheriff, B, (2000) “The Kanuri Barber and His Art”, in Borno Museum Society Newsletter, Number 42 and 43. Maiduguri: The Ƙuarterly Journal of Borno Museum Society.

    Yahaya, I. Y. (1988), Hausa a Rubuce: Tarihin Rubuce-Rubuce Cikin Hausa. Zaria: NNPC.

     

    www.amsoshi.com

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.