𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu
alaikum warahmatullahi wa barakatuh, Allah ya karawa malam imani, tambaya zan
yi game da ma'aikata musamman na asibiti. Idan abokin aiki ya zo da Mara lafiya
sai ayi anfani da sanayya a sallame shi da wuri alhali akwai waɗanda suka Daɗe a layi, sannan kuma
suna cewa wai alfarma ce ta tsakanin abokan aiki, shin ya hukuncin yin hakan,
kuma an Shiga hakkin waɗanda
suke layi idan har ba a nemi izinin su ba? Allah ya bawa malam damar amsa mana.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa alaikum
assalam.
Mutukar
yanayin ciwonsu iri ɗaya
ne, babu bambancin tsanani ko hauhawar ciwon bai halatta a gabatar da wani Mara
lafiya akan wani, saboda kusancinsa da likita, ya wajaba a jera su gwargwadon
zuwansu.
Hukuma ta ɗauki ma'aikaci ne don ya
yiwa jama'a aiki, ba tare da nuna Bambanci ba a tsakaninsu.
Ana biyan
Likita ne da kuɗin
al'umar da yake yiwa aiki, don haka zalunci ne ya fifita wani sashe akan wani
sashen na jama'a, saboda dukkansu matsayinsu iri ɗaya
ne.
Rikon amana
yana jawo ci gaban rayuwa.
Allah ne mafi
sani
Dr. Jamilu
Yusuf Zarewa
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄��𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.