Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Sai Miji Ya Faɗawa Matarsa Cewa Zai Ƙara Aure?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum. Malam, wai ko akwai wani dalili ne da ya nuna sai miji ya faɗa wa matarsa ko matansa na gida cewa zai ƙara wani auren?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

A gaskiya ban san wata doka daga cikin Al-Kitaab Was Sunnah da ta ɗora wa miji cewa sai ya sanar da matarsa ko matansa, ko kuma sai ya nemi yarda ko amincewarsu ba da farko kafin ya fara neman ƙarin auren wata matar.

Hasali a ƙaida fa ba sharaɗi ne ba sai kowa-da-kowa ya san cewa za ka yi aure, an dai so ne kawai jama’a da yawa su san hakan. Domin ga Abdurrahman Bn Auf (Radiyal Laahu Anhu) ɗaya daga cikin Al-Asharatul Mubassharuun Bil Jannah ya yi aure amma har Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) bai sani ba. (Sahih Al-Bukhaariy: 5153).

Sannan kuma a lokacin yaƙin Khaibar da Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya auri Safiyyah Bint Huyay (Radiyal Laahu Anhaa) yawancin musulmi ba su sani ba. Har ma cewa suke yi:

إِنْ حَجَبَهَا فَهْىَ مِنْ أُمَّهَاتِ الْمُؤْمِنِينَ ، وَإِنْ لَمْ يَحْجُبْهَا فَهْىَ مِمَّا مَلَكَتْ يَمِينُهُ

Idan ya yi mata hijabi, to ita ɗaya daga cikin Ummuhaatul Mu’mineen ce. Idan kuwa bai yi mata hijabi ba, to ita ɗaya daga cikin kuyanginsa ce. (Sahih Al-Bukhaariy: 5085).

Amma dai miji ya sanar da matar gida ko matan gidansa batun ƙarin aurensa domin su zama cikin shiri, musamman a wannan zamani da lokacin da muke ciki, abu ne mai kyau ƙwarai. Ko ba komai dai, duk abin da ake jin tsoron sa na ɓacin rai da tashin hankalinsu a farko, shi ɗin ne dai zai iya aukuwa a lokacin da suka samu labari daga baya.

Kuma tun farko shi miji dole ne ya zama namijin gaske a gidansa, ta hanyar ɗaukar nauye-nauyen iyalinsa da gwargwadon ƙarfi da ikonsa. Ya yi tsayin daka wurin tarbiyyar matansa da yayansa iyakar iyawansa. Kar ya zama mai kaushin hali ko mayaudari ko mahainci a gare su. Kuma kar ya zama shashasha santolaɓi mara iya jagorancin gidan. Watau dai ya zama mai ƙarfi ba da zalunci ba, kuma mai tausayi ba da shashanci ba.

Shari’a ta halatta ƙarin aure ga namijin da yake da iko kuma wanda zai iya yin adalci a tsakanin dukkan matansa na gida da mai shigowa a cikin abubuwan da suke a bayyane na haƙƙoƙinsu a kansa, kamar ta fuskar abinci da tufatarwa da rabon kwana da makamantansu. Kuma dole ne miji ya yi tsayin daka wurin kare mutunci da lafiya da matsayi da sauran haƙƙoƙin kowacce daga cikin matansa a cikin amana da adalci.

Idan miji ya tsare waɗannan abubuwa da gwargwadon hali da iko a cikin matsakaicin matsayi abin yabo - ba da ƙoro ko almubazzaranci ba - babu dalilin wani tsoro ko rashin natsuwa balle kuma tayar da hankali a wurin mace musulma, domin mijinta musulmi zai auro wata matar musulma, ko kuma domin za ta auri namiji musulmi mai aure da wata matar musulma.

Allaah ya ƙara mana fahimta da shiriya.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments