Ko Da So… (Kashi na 1)

    Bismillahir rahmanir raheem

    Idon ta cike da hawaye take kallon sa, fuskar ta ɗauke da mamaki gami da tsoron yadda lokaci guda ya birkice kamar ba masoyinta abin alfaharinta ba.

    Anya shi ɗin ne kuwa?

    Hannu tasa ta goge hawayen da ke famar zarya a kuncinta, don ta fi ganin SA da kyau, duk da tasan gogen su ba wai shi zai sa zafafan hawayen nata su tsaya ba.

    Warware manyan idanunwanta akan sa.

    Shi ɗin ne dai, Mukhtar. Mukhtar dinta. Mijinta, uban yayanta. Sanye yake da farar shadda kamar ko wacce ranar juma’a. Farin kaya ba karamin ƙara masa kwarjini da kyau da haiba yake ba.

    Ta sake goge wasu hawayen da ke zuba daga kwarmin idonta ta kalle shi.

    “Kar ka yi mana haka Abban Abdallah… dan Allah…” ta faɗa cikin karaya. ba ta san me za ta ce masa ba amma abun da yake bukata daga gareta ya fi girman tunaninta. Ba za ta iya ba. Shi ma ya fi kowa sani.

    Kamar ba zaice komai, kamar yanayin nata ya ba shi tausayi sai dai ɗan guntun tunanin da ya yi ya sa shi kau da kai daga kallon, saitin da ya juya ta matsa ta ko yi nasarar jefa kwayar idanun ta cikin nasa.

    Ta sa ni Muktar ɗin ta na son ta domin tana iya ganin zallar tausayin ta gami da madarar son ta a idanun sa, ta sani soyayyar Muktar gare ta ba ta gushewa a zuciyar sa. Takan gane haka ne a idaniyarsa da ba sa taɓa iya boye zallar ƙaunar ta, duk kuwa da tsananin bacin ran da yake ciki. Take ta ji hawayen idonta sun fara ƙafewa, saboda wani hope da ta ji ya ziyarci zuciyarta.

    Karkarwar da take yi tuni ta tsaya, hawayen ma kamar an ce su tsaya. Cike da kwarin gwiwa ta matsa kusa dashi, murmushin kwarin gwiwa tuni ya mamaye fuskar ta, kallon sa take tana neman irin nata murmushin a fuskarsa. A hankali ta kamo hannun sa tana tsara mai za ta ce a ranta da zai sa ya sauko daga fushin nan, sai dai yadda ya juyo a fusace ya sata sakin sa da sauri kamar wadda ta taɓa wuta.

    Cikin daƙiƙu idanunsa suka gauraye jajir kamar garwashi cikin kausasasshiyar murya mara amo yafara magana wadda inda a ce Hafsa tasan abin da zai furta ke nan da tuni ta toshe masa baki ta hau magiyar kar ya furta.

    “Na sake ki Hafsa. Na sake ki saki daya. Ki bar mun gida yanzun nan…”

     

    Kalmomin da ba ta taɓa koda da wasa tsanmanin jin su daga bakin Muktar ba, kallmomin da suka saka dukkan wata gaba jikinta ta sage. Kalaman da ta ji su tamkar saukar dalma a zuciyarta.

    “Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un… Muktar ka sake ni fa kace?” Sam sam idaniyar ta sun dena gane komai ya yin da ɗakin ya hau juyawa da ita tamkar fanka.

    Yaraf ta zube a gurin, a ruɗe ya yi kanta yana Faɗin, “Ummu Abdallah...”

    Yadda ya yi maganar ya sa yaran su da ba su san mai ke wakana ba suka yo falon da sauri, kamar wata ƙaramar ɗiyar sa haka ya ɗauke ta ya yi waje yaran suka bi shi yuuu...

    A karo na farko ke nan a rayuwarsu. Tun tasowar su da suka taɓa ganin Mamin ta su a irin wannan yanayin. Tuni jikin su ya yi mugun sanyi. Mami mace ce mai kuzari gami da jarumtar ɓoye ciyo, duk runtsi tana daurewa ta farantawa yaranta sun shaƙu da ita ita ce koman su, kamar yadda suke koman ta. Ko kadan ba su san menene rashinta ba a rayuwar su. Ko wannen su yana samun lokaci daga gareta dai-dai gwargwado. Wasu lokutan in suna hira takan ce musu su zama masu dogaro da kansu domin wataran za su tashi babu ita a duniyar ma gaba daya.

    Sai gashi yau rashin lafiya ta kwantar da ita ji suke tamkar duniyar ta tsaya musu. Ko da yake a wajensu duniyar ce ta tsaya domin Mami ita ce rayuwar su.

    Tun jiya kawo ta ba wani bacci suka samu ba, Aiman ɗan ƙaramin cikin su ne ke ta faman zarya lokaci lokaci yana leƙa ƙofa da alamu mahaifin su yake tsanmanin gani wanda tun jiya da ya zo ya tabbatar an kwantar da ita bai dawo ba. Jiƙin yayan sa matsa, Yaya wai Yaushe Abie zai dawo.

     Abdullahi ɗan kimanin shekaru goma sha biyu da kana kallon sa kasan idanuwan sa ba su samu runtsawa ba, wanda har kuka sai da ya yi. Shine dan ta na biyu kuma ya fi kowa jinta a zuciyarsa kamar yadda uwar take dukkan kokarin ta ita ma ta boye yadda take jin sa daban a cikin yaranta. Ya dubi ƙanin nasa a hankali ya ce anjima kaɗan sam yaron bai cika som magana ba, bare yanzu ga tashin hankalin Umman su.

    Juyawa Aiman ya yi ya ci gaba da zaryar sa tamkar wani banban mutun, haka duk yaran Hafsa suke a nutse domin ita ɗim jajir tacciya ce wurin ganin yaran ta sun taso abin kwatance.

    Kallonta suke yi dukkan su, alokacin da numfashin ta ke sama da kasa. Bacci take yi amma a baccin ma mutum in ya nutsu zaiga yadda take fusga da firgita kadan kadan. Sosai suka kura mata ido dukkan su suna jira suga kawai ta tashi.

    Aiman ne ya matsa kusa da Babban wan su Faruk “Yaya wai Mami yau she za ta tashi ne? Ni yunwa nake ji.” Ya faɗa yana tura baki. Kursum da ke kusa dashi ta kwadeshi. Da gani itace a saman sa.

    “Kai dallah malam waye yake ta abinci? baka ga Mami a kwance ba, Silly boy kawai.” ta yi tsaki tana sake mayar da taguminta kamar dazu.

    Babban yana ta kallonsu bai ce komai ba kuma sai aka yi sa’a karamin baiyi kuka ba.

    Suna zaune sunyi jugum jugum baban nasu ya fado dakin da gudu Aiman ya faɗa jikin sa, yawwa Abie tun jiya nake jira ka zo ka tashi Mami. Kallo daya babban ya ma su yana shafa kan Aiman sannan ya dauke kan sa.

    Tsai Abdallah yake kallon mahaifin na su babu wanda ya faɗa masa kuma babu ma alama a tattare da mahaifin nasu amma yasan shine silar kwanciyar mami. An yi kwana biyu yana lura da irin yadda suke mu’amala kamar makiyan junan su.

    “Ya me jikin?” Abie ya sake tambaya bayan sun gaishe shi amma sai aka rasa wanda zai ba shi amsa kamar sun haɗa baki gaba ɗaya.

    “Mami will be fine. Kuzo in kai ku gida ku shirya ku ya fi islamiyya…” ya faɗi yana so su tafi don baya son ta farfaɗo akan idansu domin bai san yadda zai yi ba.

    Kamar wanda ya faɗi wani abun tashin hankali Abdallah ya zuba masa ido kafin ya maida kallonsa zuwa ga Mamin ya ce, “hutu mukeyi ai Abba ka manta kuma in mun tafi waye zai zauna gun…” bai ƙarasa ba yaga kamar hannunta yana motsi. Ba shiri ya bar maganar tasa ya miƙe ya yi kanta. Dukkan yaran suka mata rumfa suna kallon yadda take motsa yatsun ta a hankali gami da ƙoƙarin buɗe idanun ta.

    A nata bangaren kuwa ji take kamar an ɗora mata dutsen Dala a kanta. Wani irin nauyi da ciwo ya mamaye gaba daya jikinta. A sannu a hankali take binsu da idanuwa.

    Kamar a tare suka fara jero mata sannu sai dai babu wanda ta tanka.

    “Alhamdulillah.” Mukhtar ɗin ya furta ganin ta farka, da dan damuwa a muryarsa sannan ya matsa kusa da ita. Daidai sanda idonta ya kama nasa, sannan ta fara zubar kwalla. Kamar wasa sai hawayen ɓakin ciki ya fara zirya akan kumatun ta.

    “Mami, jikin ki ciwo?” Dan Aiman ya tambaya, su kuwa manyan sun ma rasa me zasuyi. Ba ma za su iya tambayar ta mene matsalar ba musamman yadda suka ga ta kafe mahaifin su da ido.

    “Mami please ki mana magana…”

    “Mami sannu kinji, a kira miki doctor?”

    “Mami sannu, dan Allah ki daina hawaye, yana min ciwo…”

    Haka muryoyin yaran nata suke tashi a cikin ɗakin amma kamar ba da ita suke ba. Shi take so ya yi magana. Har yanzu tana da kwarin gwiwa akan makomar su. Har yanzu tana son shi. Har yanzu shi din, shine farin cikinta. Kalamai uku kawai take so ta ji daga gare shi.

    “Na maida ki.” Shi ya sa ta zuba masa idanuwanta ba tare da kula da cewa yaran suna sane da su ba.

    Sai dai Mukhtar ma ba tare da la’akari da yaran ba kawai ya juya ya fice daga dakin sam ci gaba da kallon masoyiyar tasa a haka zai iya sawa ya canja hukuncin da ya yanke, hukuncin da sam baya fatan janyewa.

    Ko sannu bai ce mun ba.

    Ko murmushin nan nasa kai sani farin ciki bai min ba, anya ba mafarki nake ba?

    Hawayen da suka fi na ɗazu zafi suka ziraro zuwa kuncin ta lokacin da ta ɗora idanun ta bisa kofar da ya ja ya rufe.

    A hankali ta rufe idanuwanta. Daga nesa nesa take jin yaran suna rokarta ta tashi sai dai ta yi nisa daga duniyar da take yanzu. So take ta koma duniyar soyyayar su da Mukhtar don taga a ina ne ta kuskure. Ta san ko wanne labari yana da tushe, ko wanne labari yana da asali. Yana da mafari…

    Nasu Mafarin ya fara ne a birnin Kano da ke Najeriya.

    **

    Dala, Kano.

    Sauri yake ya kammala cin tuwon da ke gaban sa duk da ya ji daɗin dumamen sosai zai so a ce a hankali zai cinye shi sai dai baya so ya makara.

    Daga gefe kuwa Inna ce ta ke ta faman jan ruwa daga rijiyar da ke tsakar gidan tana cika bokitan da ke gefenta. Mace ce ba za ta haura shekara hamsin da biyar ba. Yar karamar mace ba tsawo babu kiba a tattare da ita. Fuskarta doguwa ce, hancinta madaidaici ne, leben ta ma mai tudu ne ba ka ce wuluk sai dai kaf yaranta babu wanda ya yi bakinta. Gaba ɗaya su hasken mai gidanta suka ɗauko, farin bafulatani, Malam Adamu Mujeili. Duk da a Kano ya tashi amma yan asalin Yola ne. A nan Kanon suka hadu sukayi aure har suka haifi yara shida kafin Allah ya yi masa rasuwa.

    Malam Adamu mutum ne me zuciyar nema duk da ba shi da wadata amma ba a taba kwana da yunwa a gidansa. Yaran sa kuma suna zuwa makaranta har zuwa lokacin da Allah Ya dauke shi. Mukhtar shine dan shi na fari sai mata hudu reras a kasan sa. Mai bin Mukhtar tun ba ta shekara ba ta rasu sakamakon cutar kyanda da ta yi.

    Tun bayan rasuwar malam Adamu a lokacin Mukhtar yana gab da kammala sakandire, sauran yaran ba su ci gaba da karatu ba. Mukhtar haka zai fita ya yi buge bugensa a kasuwa ya samo musu na abinci.

     

    Ganin wahalar ta yi wa Mukhtar yawa ya sa mahaifiyar tasa ta fara sana’ar saida abinci wadda dama shi ta tashi taga mahaifiyarta tana yi sai dai bayan ta auri malam Adamu sai ya nuna sam baya so ta yi sana’a. A yanzu kuwa dole ta kama sai ta yi.

    Haka dai sukayi ta faman ciyar da gidan har suka aurar da Rashida inda sauran yaran kuma suka koma makarantar gomnati. Zuwa yanzu kuma Mukhtar ya kammala jami’a inda ya karanci civil engineering don ya kasance yana da fasaha da kokari. Yanayin rayuwa da halin da kasarmu ke ciki ya sa yanzu shekarar su hudu da gamawa amma bai samu aiki ba.

    Satin da ya gabata ne Inna Kulu ta ji wata sanarwa a rediyo na wata makaranta da take neman malamai. Sai da ta tabbatar ta haddace bayanan da aka yi. Bayan Mukhtar ya dawo daga kasuwa ne take sanar dashi abun da ta ji ta kuma karfafa masa gwiwa ya gwada ko za a dace. Duk da ya na ganin kamar ba ta lokaci ne zai yi, haka yaje ya gabatar da takardunsa a makarantar. Jiya kuma aka kira shi ya zo yau a musu gwaji.

    “Ashe Muntari ba zaka yi sauri ka tafi ba?” Ta fada tana juyowa taga me yake yi.

    Murmushi ya yi. “Tuwon ya yi dadi inna. Yanzu zan tashi.”

    Ba tare da tace komai ba, ta dauki murfin rijiyar ta rufe sannan ta samu gefe taja kwanon nata tuwon.

    “Allah dai ya sa a dace.” Ta faɗa cike da damuwa tana kai loma bakinta.

    “Amin Inna.” Ya amsa mata a gajarce yana mikewa. Bakin inda take wanke wanke ya nufa ya tarar duk ta dauraye komai saboda haka shi ma a take ya wanke kwanon nasa.

    A hankali ya dubi tsakar gidan da shi kadai ne abun da mahaifinsu ya bari. Idonsa ya fara kan katangar dakinsa da ta fara zubowa daminar da ta wuce. Sannan ya kalli gefen dakin inna wanda babu ko fitila balle fanka cikinsa. Kafin wannan ma yana bukatar gyara. In sha Allahu da alba shinsa na farko zai gyarawa Inna dakinta da yake yoyo.

    Yana yarfe hannunsa ya nufa inda ya ajiye jakar sa a kofar dakin su Hajara yana tabe baki.

    “Sai yaushe zaki tashi wadancan magunan Inna? Wallabi ki dena shagwaba su.” Ya fada yana shan kunu alamun abun yana ba ta masa rai.

    Dan murmushi Innar ta yi sannan tace, “maza maza Allah ya kiyaye ya bada nasara.” Ya san ba za ta tanka shi ba shi ya sa kawai shi ma ya yi mata murmushin yana mata sallama.

    **

    Harabar makarantar cike yake da jama’a kamar haɗin baki yau iyaye masu biyan kuɗi sun cika makil ga kuma mutanen da aka gayyata suzo gwaji. Dukkan su a tsaye suke masu hira nayi masu korafi nayi. Wasu daga iyayen kuma suna ofishin admin suna abun da ya kawo su.

    Dai-dai lokacin da Mukhtar ya shiga harabar makarantar ya ji zuciyarsa ta harba. Bai san dalili ba, kafin ya ankara kuma sai ya ji nutsuwa ta saukar masa. Nan ya sami inuwa ya rakube kusa da wata matashiya ita ma rungume da jakar takardunta ta sha gilas amma fuskarta babu kwalliya. Sallama ya yi mata ta amsa da fara’arta sannan suka yi shiru.

    Suna wannan jiran ne motar me makarantar ta faka a kofar makarantar. Alhaji Muhammad mutum ne mai karamci da sanin ya kamata. Mutum ne da ya buɗe makaranta don amfanin jama’a sama da neman kuɗi domin dan kasuwa ne da yake da rufin asirin sa ba laifi kuma ya kasance likitan ilimi ne.

    Kamar ko yaushe sanye yake cikin babbar riga. A hankali ya futo daga motarsa, mai gadi ya taho da sauri duk da ko yaushe sai Alhajin ya dakatar dashi.

    “Abba ka jira ni mana…” wata murya ta faɗa a shagwabe.

    “Hafsah ke nan, kin makarar dani ina sake gaya miki.” Ba shiri ta fisgo jakarta tare haƙura da shan shayin da taso ta shanye kafin ta fito.

    Kyakkyawa ce. Duk wanda ya kalle ta haka zai fara cewa game da ita. Ba doguwa ba ce can can amma ba gajera ba ce. Sanye take a abaya kalar ruwan goro wadda ta yi bala’in yi mata kyau.

    Da sauri take tafiya ta kamo Baban nata da har ya shige ciki. Ba tada kiba shi ya sa ma saurin nata ya yi kamar gudu take. Kallon lokaci ta yi taga takwas dinma ba ta cika ba Baba yake ta wannan saurin.

    Sanda ta kamo shi har ya fara gaisawa da mutanen wajen ya kuma tsawarar akan barin su da aka yi ba a buɗe musu aji sun zauna ba. Nan take aka buɗe ajin da za a musu interview din.

    Alhaji Muhammad office dinsa ya nufa tana binshi a baya.

    “Ni fa ba zama nazo yi ba Abba. Nima so nake naga yadda kake yin komai.”

    “Hafsah ke nan.” Abun da ya ce kawai sannan ya yi magana da principal da wasu malamai da suka shigo suka nufi ajin da za a yi gwajin.

    Lokaci na tafiya, Hafsah tana hammar gajiya don ba ita kadai ba har su Baban sun gaji saboda yadda mutanen suke ta wahalar dasu ba su san komai ba balle su cancanta. Ko ita da yanzu ta fara jami’a tafi wasun su.

    Ganin saura mutum biyu ya sa ta yi hakuri ta zauna. Ita ma biron ta a hannu ba ta yadda ba sai grading take.

    Wata macece me gilas ta fara magana. Kaf cikin jama’ar babu me kwazon ta. Anan take Hafsah ta sa a ranta an samu malamar wannan subject din. Ganin ita kamar ta gama nata aikin ya sa ta jawo wayarta ta fara dannawa tana dora selfie din da ta yi a snapchat.

    Tun da ya fara magana abu ɗaya Hafsah ta ji duniyar ta dakata.

    “Sunana Mukhtar Adam.” Duk wani abu da ya ce bayan nan ba ta ji shi domin ta faɗa wata duniyar daban, ta shagala da kallonsa tana yabonsa a ranta. Ta nutse a duniyar da ya kaga ba tare da ya sani ba, da muryarsa.

    Wannan shine mafarin labarin su. Kafin ta fahimci hazakarsa, haibarsa ta fahimta. Kafin ta gane me kokari ne, sai da ta gane me kyau ne. Kafin ta gane ya hadu, sai da ta rasa hankalinta, sainda zuciyarta ta fara kitsa mata wani abu a kansa. Wani abu da a lokacin ba ta san menene shi ba.

    Ta so a ce, zamanta ta yi a gida a wannan ranar!

    Rubutawa

    AeshaKabir
    Fadimafayau

    Soyayya
    Credit: LuckyTD

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.