Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Yiwa Kafiri Sallama

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

shin ya halatta musulmi ya yiwa kafiri sallama, ya yi musafaha da shi. Kuma ya Hallata Amsawa kafiri Sallama idan ya yiwa Musulmi sallama?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

الحمد لله العلي الكبير.

Dalilai Ingantattu sun tabbatar da hani dangane da fara yiwa kafiri sallama, bayahudene ko kirista, Kamar yanda Muslim yaruwaito acikin Sahihin littafinsa (2167) Daka Abu huraira Allah yakara masa yarda Manzan Allah Sallallahu Alaihi wasallam ya ce: ( Kada kufara yiwa bayahude ko kirista sallama) .

Haka dalilai Ingantattu sun nuna za a Amsawa kafiri Sallama idan ya yiwa Musulmi sallama.

Bukhari yaruwaito hadisi (6257) da Muslim (2164) daka Abdullahi Bin Umar Allah yakara masa yarda Manzan Allah Sallallahu Alaihi waslam ya ce: ( Idan bayahude ya yi muku sallama, yana cewa( Assalamu Alaikum, ka ce dashi: wa'alaika).

Haka wajan yin musafaha kada kafara baiwa kafiri hannunka dan kuyi musafaha, Idan yamiko maka hannu dankuyi musafaha saika mika masa.

Ibnul Qayyeem ya ce: Idan wannan sababin yakau, kirista ya ce: Maka Assalamu Alaikum Adalci shi ne kamayar masa irin Abun da ya yi maka Sallama dashi.

" Ahkamu Ahlul Zimmah".

"Sama" Abun da take nufi shi ne mutuwa.

Da Sallama da Musafaha ba aso Musulmi yafara yiwa kafiri, Amma idan kafiri ya yima yanada cikin Kyautatawa kamiqa masa hannu kugaisa, kakuma Amsa Masa Sallama.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments